Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 23

*PAGE 45-46*

Tamkar ta zuba mashi ruwan zafi haka yaji zafin maganar ta amman cike da mamakin kan shi maimakon ya rufeta da masifa sai samun kan shi yayi da cewa "please baby ki yarda da ni wlh ke ce my first love tunda ni ke ban taɓa son wata ƴa mace ba"ya faɗa ya na mai juyota suna facing juna "ta yaya zan so ɗan shaye-shaye *ƊAN DABA* wanda bai ɗauki mace a bakin komi ba sai abar kawar da sha'awa,ta yaya ne ma wai mutum wanda ke rayuwa kamar irin ta dabbobi zai ce ya na Sona alhalin ni na kasance mai ƙaurace duk wani saɓon Allah?"Deeya ke faɗa a zuci yayinda idonta ke cikin na Abbas wanda ko ƙyaftawa bai yi.
Ganin ta kasa cewa komi yace "stp bb.."sunne kai tayi zuciyarta na dokawa tace "to ka mayar da ni da school ka na ga dare na yi"ta ida maganai ta na mai É—agowa kallon da yayi mata na ba kida hankali ne yasa ta ce "eh gobe ba sai ka zo mu tattauna ba"huci ya sauke mai zafi kafin yace "naji"ya na mai kai bakin shi bisa lips É—in ta ya sumbaceta.
Mota ya buɗe mata ta shiga sannan yayi mata key,a hanya ya tsaya ya saya mata gasasun kaji masu zafi tare da exotic.Shigowar motar shi a harabar school ɗin yasa ƴan ganin ƙwam leƙowa,zagayawa yayi ya buɗe mata ta fito hannun shi riƙe da leda sai da ya raka ta har room ɗin su sannan ya dawo.
Nadiya tayi saurin nufota da gudu ta na tambayarta "bai mi ki komi ba?"murmurshi ta sakar mata tace "ke ki nutsu babu abinda ya yi min É—auko mana plate mu ci"Nadiya ta É—auko plat ta dubi Deeya da luhuluhun idanun ta da ta sha kuka tace "amman wannan ya cika *ÆŠAN DABA* na gaske kin kuwa yadda duk ya firgita mutanen school?yanzu haka fa wasu su na can ana basu magani saboda tasowar cutar huka humm nima ba laifi an firgita ni"Deeya tayi É—an murmushi ta shaidawa Nadiya yadda suka yi da shi.
"Kin ga fah kamar ya san mu na jin yunwa ya sayo mana kaza yanzu sai mu ci mu kwanta"cewar Deeya,Nadiya ta sheƙe da dariya tace "Ni fah tunda Faruq ya shaida mana halin shi na manta da wani abu wai shi abinci,tom bari mu ci kayan masoyi"Deeya ta kai mata duka tace "daga wace ya zama masoyina?ɗan ta'addar?"Nadiya ta cizgi kaza tace "amman fah Guy ɗin ya haɗu ga shi da kyau kamar shi ya halicci kan shi,abun burgewa kuma sajen fuskar shi"Deeya ta taɓe baki tace "duk da haka dai bai kai ga Boss ɗina ba wanda tsabar kyawu shi dabancin ma kyau yayi mashi"Nadiya dai tayi shiru ta na kallon Deeya tare da cigaba da cin kazar ta.

Cike da jarumta Daddy ya nufi kogon hatsabibai domin ɗauko kambun sarauta,duk inda ya ratsa gawarwaki ne birjit na bil Adama wanda ko tantama babu sun yi yunƙurin zuwa gun ne ba tare da sun shirya da kyau ba.Tafiyar shekaru da dama sai ga Daddy yayi a kwana biyu ita ma ɗin ƙarfin tsafin jikin shi ne ya sa haka,motsi yaji bayan shi da sauri ya waiga sai ya ashe William ne ke biye da shi duk da ya hana shi murmushi ya sakarwa Daddy nan ya fara wani siddabaru sai gasu gaban wata ƙofa mai haske wacce tsabar haskenta sai da su Daddy suka rufe ido da tafin hannu.Tsawon ƴan daƙiƙu hasken ya ɗauke nan ƙofar ta buɗe da kanta,shiga suka yi da ƙafar hagun ko tako uku ba su yi ba wani narkeken aljani ya bayyana gare su hannun shi riƙe da wannan kambun sarautar da suka zo nema.
Fuskar nan a murtuƙe ya ke kallon su kafin ya kai ga tambayar su William ya buɗe baki da niyyar magana kawa sai hasken hauren da Oga Danee ya sa aka saka mashi ya mamaye ɗakin ta yadda idon aljanin suka rufe har Daddy ya samu nasarar ƙwace wannan kambu daga hannun shi,a guje suka fito suna tsaka da gudu suka ji ihun wannan aljanin wanda ya baiwa manyan-manyan burwai🐒damar fitowa nan suka yo kan su.
William na cikin karanta formules ɗin da za su ɓace wani biri ya halbo mashi wata wuƙa ta caki ƙirjin shi nan ya faɗi ƙasa jini na zuba,cikin fitar hayyaci yace "Daddy ka gudu kawai kar ka tsay..."cike da azama Daddy ya duƙa ya cire huƙar burwan ne suka yi cikin su tare da zagaye su,babu zato ba tsammani wani doki mai fukafuki ya bayyana🐴sauran ƙarfin da ya rage mashi ya miƙe ya hau dokin haka ma Daddy nan ya tashi sama da su suka.
Dawood da Oga Darma da ke kallon su ta allon sihiri suka sauke ajiyar zuciya,nan oga Darma ya cigaba da yin karatun da zai taimakawa dokin wajen kawo su lafiya dan dama shi ya aika shi.

Ko da suka ƙaraso gida William tuni ya fita hayyacin shi,magani aka shiga yi mashi amman shiru ya kasa farfaɗowa.
Cike da tashin hankali duk suka gewaye shi,Siya sai kuka ta ke ta na kallon mijinta wanda ya ke a sheme.
Oga Darma ya kara wani cokali daidai ciwon nan ƙwayoyin cutar da suka hana shi farfaɗowa suka shiga yin sama suna shiga cokalin,ba'a ɗau lokaci ba ya fara tari mai ƙarfi haɗe da amayar da jini mai cike da guba.
Ruwan sanyi aka bashi ya sha, Dawood ya naÉ—e mashi ciwon da bandeji.
Murmushi ya saki ganin Siya tayi tsit ta na ƙyaf-ƙyaf da ido,sai ta baiwa kowa dariya babu kunya ta rungume William "auushhhh!"ya fidda ɗan sauti saboda ciwon da ta ɗan buge.
Hancin shi ta laƙace ta na dariya,Momy da ke gefe ta harareta ai kam Siya ta noƙe kai tayi kamar ba ta gani ba.
Da taimakon Dawood ya isa part É—in shi, Siya ta haÉ—a mashi ruwan wanka masu É—an É—umi sannan ta nemo mashi tea da maganin da zai sha.

Dawood kuwa falo ya zauna ya tisa Leemat gaba ya na kallo cike da mamaki dan yi ta ke tamkar ba ta san shi ba,wani zubin ma sai in shi yayi mata magana.
Ganin irin kallon ƙurilla da ya ke bin ta da shi yasa ta miƙe tsaye ta turo baki ta na gunguni,ta tai wucewa yasa ƙafa ya taɗeta ta faɗi ƙasa kanta ya bugu da salon dan ƙeta kuma ya shiga yi mata dariya.Daddy da ke can gefe ya na kallon su ya taso ya fara yiwa Dawood faɗa ya tada Leemat ya na tambayarta in ba taji ciwo ba.Gwalo ta yiwa Dawood😝 sannan ta murguɗa mashi baki😏 ta tsere part ɗin Momy,wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare Dawood ya bita da ido sai yaji ina ma babu kowa gidan kamar can yadda suke a Niger da ya koya mata hankali.
Murmushi Daddy yayi dan kuwa ya gano yaron nashi ba ƙaramin so ya ke yiwa Leemat ba amman a ganin shi ai tayi mashi ƙaramta ina za ta kai gwabran shi balle tazuranci?.Kamar wani ƙaramin yaro ya shagwaɓe fuska yace "Daddy ka na fah ganin abinda ƙaramar yarinya ta yi min"Daddy ya zauna kusa da shi yace "ai kai ka fara,yauwa ya kamata ka yanke lokacin da za ka tafi samo jinin Danee dan maido bawan Allahn mutum kamar kowa ka ga daga nan sai ayi maganar auren ku in komi ya lafa"cike da kunya Dawood ya sunne kai yace "to Daddy"a ƙasan zuciyar shi kuwa godiya ya ke yiwa Allah da yasa Daddy ya gano da kan shi ya na son Leemat dan dai shi girman kan shi ba zai bari ya faɗa ba dan kar yarinya ta raina shi😎

***

Cikin ƙarfin hali ta daure ta ɗora masu girkin rana shinkafa fara da miyar albasa,sai da miyar ta dafu sannan ta jaye itace ta bar garwashi ta cika boki ta tsalo wanka tare da gasa jikinta sosai ta kama ruwa da bagaruwar da Inna ta aiko mata da safe.Cikin riga doguwa ta atamfa ta shirya bayan ta shafe duk jikinta ambre da humura mai ƙamshi,ba tayi ƙwalliya ba kawai ta shafa man leɓe ne.
Abincin ta juye cikin sabbin kwanoni ta jera bisa ɗan madaidaicin table ɗin ta na roba,ba'a jima ba kuwa Muntari ya shi cike da kunya ta tarbe shi tace "sannu da zuwa"ta ɗan duƙa ta karɓi ledar hannun shi amsawa yayi ya na bin ta da wani mayatacen kallo.
Lemun kwalba ne sai ƙanƙara,tarmus ta ɗauko ta nasa ƙanƙarai lemun kuwa ta aje shi a table,ruwa masu sanyi ta zuba mashi a kofi yanzu ma sai da ta ɗan rusuna sannan ta bashi ya karɓa ya na murmushi.Ruwan wanka ta zuba mashi a bokiti tare da kwandon sabulu ta kai banɗaki sannan ta dawo ɗakin ta shaida mashi,farar jallabiya ya ɗauko sannan ya wuce ya yo wanka.Ko kafin ya fito ta gama zuba abinci a plate,a gaban shi ta ajiye tare da cewa "Bismillah"gefen shi ya nuna mata ta zauna ya fara ciyar da su da cokali ɗaya duk da nanoƙewar da Laila ke yi,lemun ta tsiyaya masu kafin su miƙe su ɗauro alwala shi ya wuce masjid ita kuma a ɗaki.

Ta na shafa addu'a ya shigo,jallabiyar shi ya cire ya zamana daga shi sai culotte.Gaban Laila ne ya bada das ganin Muntari ya zauna bakin bed ya na kallonta da alamu ita ya ke jira,sanin haka ne ya sa ta miƙe ta ƙara ƙabarta wata sallah😂 murmurshi Muntari yayi a zuci yace " wayo.com kiyi dai ki gama sai na fidda wannan dattin Allah ma ya so ni da sallata ba ta lalace ba adadafe nayi ta"ya na nan zaune sai da Laila tayi raka'a huɗu ta sallamce ta na shirin tashi dan kawo wata yayi wuf ya ɗauki ke ta ya dire kan bed,sharrr hawaye suka zubo mata ya kai bakin shi ya na lashe su amman sun ƙi su tsaya ganin za ta fara kuka mai sauti yayi saurin kai bakin shi cikin nata ya fara bata hot kiss wanda ya sa Laila jin wani iri kamar za ta shiɗewa.
Ɗan dakatawa yayi ya na kallonta da idanun shi da suka canza kala,baki ta taɓe za tayi kuka ya girgiza mata kai da dubara ya kai hannun shi ya cire zip ɗin rigarta tare da yin sama da ita.
Saurin rumtse ido tayi saboda zugin da breast ɗin ta ke yi dama ba wani wucewa suka yi da azabar jiya ba yau kuma ga wata sun fara gani, lokacin da ya fara having sex da ita kuwa wani uban ihu ta ƙurma dan ji tayi kamar an yankata da wuƙa.
Cikin fitar hayyaci ba tare da yayi duba ita ɗin yarinya ce ba ya cigaba da bidirin shi,sai da komi ya lafa ya shiga rarrashi tare da gaya mata da sannu za ta saba dama kusan duk ko wace amarya sai tayi haƙurin haka musamman in angon shi ma sabon shiga ne babu safe babu rana sai haƙuri😹 shi nan maneji ne ya ke har ta saba tukun cikin yayi kaɗan 5roun par jours.
Ita dai Laila sauraren shi kawai ta ke wani irin tsoron shi ya samu waje a zuciyarta ya zauna.

Cikin sati guda Laila duk ta rame saboda hankalinta da ya ƙi kwantawa game da lamarin Muntari,kullum abu ɗaya ko gajiya ba yayi balle ya tausayawa yarintar ta.Ganin kamar abun zai fi ƙarfin ta ne ta shige ɗaki ta fasa kuka tare da tattara kaya wai za ta koma gun Inna da zama😂 juyin duniya da magiya Muntari yayi amman inaaa tuni Laila ta zuba kayanta a leda ta matse a kafaɗa ta na sharar ƙwalla tare da turo baki gaba saboda tare hanya da Muntari yayi.
"Please babyta kiyi haƙuri ba zan sake ba kin ji?"cikin kuka tace "ai jiya ma haka kace "ya dafe kai yace "to yau dai nayi maki alƙawari ba zan maki komi"ya faɗa ya na mai game hannuwa alamar roƙo,ta ɗago ta kalle shi sai kuma ya bata tausayi hakan ya sa ta aje ledar kayan.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fita ya na maganar zuci "ai ya zame mani doli na je bikon Asabe tunda wannan da alamu kwabsa min ta ke son yi in taje gun Inna ai shikenan ƙila ma ta riƙe ta".
Wajen Inna ya tafi cike da kunya yace "Inna ya kamata fah kije ki tawo da Asabe "sai da Inna ta dube shi da kyau tace "na ƙi ɗin ai ba ni na aiketa ba, lokacin da tayi yajinta wa ya kaita?yadda ta tafi da kanta haka za ta dawo da ƙafarta dan haka ka sake zance ko ka fita ka ban wuri"Muntari ya sunne ya na jin haushi sam ba haka ya so ba.

Da dare kuwa cikin tsoro Laila ta kwanta can ƙarshen gado ta na jin zuciyar ta na bugawa kamar ko wane dare,ƙuri Muntari yayi mata ya na ankare da ita "tabbas tsorona ta ke shiyasa ma ta kasa barci"ya faɗa a zuci kafin ya fita ya ɗauro alwala.Tafi ya shimfida ya shiga jero nafiloli tare da roƙon Allah ya rage mashi wannan cuta ta sha'awa dan yanzu kuwa ya yarda cewa ta wuce yadda ake so ta zama cuta,bayanta ya kwanta ya na haɗiyar yawu.....

Comment and share Please

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.