Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 23

*PAGE 43-44*

Furgici,bugun zuciya,tashin hankali ƙarara suka bayya a fuskar Oga Danee wanda ya kunna hasken ɗakin idon shi ya sauka kan Jasmine wacce tuni jinin jikinta ya ƙare ƙwaf har wani yalow ta ke fuskar nan tayi fari ƙal.
"Jasmine mi ni ke shirin ganin , Jasmine mi ya kawo ki nan na shiga uku na lalace kar ku shanye min jinin Ƴa ba ita ba ce na bayar a matsayin sacrifice"Oga Danee ke wannan furci cike da tashin hankali kafin yayi dialing number Oga Darma "hahhh to ya ka ga kafcen? wannan salona kenan kai tantiri ka iya zamba balle ni ɗan siyasa?ka cutar da ni ka bayar da ƙwan halitta ta gun matsafa nima yau na bayar da ta ka ƴar mafi soyuwa gare ka.Ko ka zata ban san kafi son Jasmine ba kawai ɓoyewa ne kake dan kar a cutar da ita kai mai wayo hhhh.To tsaya ba ma wannan akwai abinda ya fi wannan kafcen furgici shine Ahmad na nan da ran shi ko akaifar shi ba ta bar jikin shi ba saboda David da ka tura in sheƙe rainon shi nayi ya koma Dawood shi kuma ɗayan William da ka ɗauka na hannun damar ka to ba kowa ba ne face jinin Ahmad hhhh"Oga Darma ke faɗar haka ya na sheƙewa da dariya kafin oga Danee ya kai ga yin maganar wasu halittu maras kyawun gani sun sauka cikin ɗakin suna mai kama-kamar zanen gadon da Jasmine ke kwance suka ɗaga shi sama suka tafi da ita da zanen.
Zaman ƴan bori Oga Danee yayi ya fashe da kuka kafin ya miƙe tsaye ya suturta jikin shi ya nufi waje a mugun sauri,tsabar yadda ya ke cikin tashin hankali ya sa bai tsaya jiran drever ba yayi tuƙi da kan shi bai zarce ko ina ba sai gidan Papi a hasale ya shiga gidan ya na huci.

Kwalbar giya Papi ya bashi ya tultula sosai kafin ya bashi wani abu cikin marfi mai masƙi ya shanye wanda a ciki ne Papi ya nasawa Oga Danee ƙwayar maita😱ba a ɗau lokaci ba kuwa Danee ya fara tanɗar baki ya na kallon Papi wanda har ƴan cikin shi ya na gani.

Papi ya juya baya yace "kar kace komi duk na san abinda ke faruwa shiyasa na shirya maka yadda za ka ɗauki fansa a sauƙaƙe ba komi ba ne sai ta hanyar lashe kurwar su saboda mayyta tafi tsafi girma"tamkar wani mayunwacin zaki haka Oga Danee ya miƙe yace "Papi ina son ka tattara min duk wani maye da mayya na duniya da wanda ke yi a ɓoye da wanda ke a sarari ka shaida masu yanzu sun samu ƴanci zan gina babbar MASARAUTAR MAYU (Oum Hairan)yaro da babba mace ko namiji duk za'a tare a can zan ɗora sarauta wacce ba'a taɓa gani ba zan fito cikakken *ƊAN DABA* kuma babban maye zan adabi garin Moumbay da duk wasu magoyan hana tsafi a duniya hhhhh"cike da jin daɗi Papi yace "an gama".

Abun haushi abun takaici Oga Danee na komawa gida ya sa aka dafa wake da shinkafa da mai,nan ya jefa ƙanƙarar maita duk yaran shi suka ci suma suka zama Mayu😰,cikin ƙananan lokaci garin Moumbay ya fara hargitsewa da yawan rashin lafiya gefe ɗaya kuma wani ƙaton gini ne aka ɗora wanda ya kusa canye rabin garin.

Miƙa Siya tayi ta buɗe idonta uwanda ta ke jin sun yi mata nauyi,shafa kanta William yayi ya na kallonta yace "kin tashi?"da mamakin shi raɗau ta amsa mashi da bakinta.
Oga Darma wanda ke gefe yace "ayi haƙuri na shaƙa maki maganin barci ba da son raina ba yanayin aikin ne ya zo da haka,am Nas amshi kuɗi ka hau taxi ka koma hotel zan neme ka"Nas da ke gefe yayi wani sukuku da shi dan sam bai ji daɗin mutuwar Jasmine ba,karɓar kuɗin yayi ya fita.

Daddy wanda tuni yayi aski yayi wanka ya fito fes da shi gwanin kyau ya gyara zama ya dubi duk mutanen ɗakin"am to yanzu dai babu abinda za mu ce sai godiya da Allah,abu guda ya rage mana shine dawowar Michel izuwa yadda ya ke tun farko"Oga Darma ya karɓe zance "eh kam haka ne ya kamata mata su tashi su bamu waje mu san dan tsara yadda abun zai kasance"Mama ta ja hannun Siya ita da momy suka bar gun.

Wata takarda Darma ya fito da ita yace "wannan shine kogon da kambun sarautar ya ke ya zama doli mu nemo shi kafin Danee ya kawo mana hari dan na san doli ya farauce mu,sannan abu na gaba shine jinin Danee mu ke da buƙata ko yaya ne dan dawo da Michel mutum wannan ne makarin "shiru dukan su suka yi suna nazari Dawood ya gyara zama yace "Ni zan nemo shi nayi alƙawari,dan ƙaramin aiki ne gare ni"cike da gamsu Darma ya tare Daddy da hankalin shi ya tashi yace "kar ka damu na san ko wanene Dawood dan tuni ya tashi daga David ɗin da kai ka sani ni na hora kuma ƙarfin ikon jikin shi ma ba zai bari a cutar da shi ba"cikin nutsuwa Daddy yace "shi kambun ni zan ɗauko shi Siya ta bani duk pouvoir ɗin da ke jikinta yanzu babu tsafi ko ɗaya a jikinta".
William yace "zan rakaka wajen ɗauko shi Daddy dan kai ma ka na buƙatar garkuwa"cike da jin daɗi Oga Darma yace "to hakan yayi kyau ni kuma zan ji da duk wani motsi naku ta allon sihiri na duk wanda ya tai shiga matsala zan zama garkuwar shi"haka dai suka cigaba da tattaunawa har lokacin cin abincin rana yayi.

Tamkar kar ta fito saboda gamo da tayi da ƴar uwar ta kuma abun farin ciki ta warke daga makantar ta,tun da ta fito Dawood ya kafeta da ido ko ƙyaftawa bai yi.Ba ta ko kalli inda ya ke ba amman taji idanun shi kanta,turo baki tayi ta wuce Kitchen a zuci yace "eh lalle waccan yarinya ta raina ni ma yanzu ko gaishe ni ba za ta yi ba?"kasancewar shi ɗaya ne falon William na part ɗin shi wajen yin wanka,Daddy da Darma kuwa a can masjid ya baro su hakan ya sa ya tashi ya nufi kitchen ɗin.

Shi ɗin mai rauni ne idan ya na tare da ita hakan yasa shi kasa yin komi kawai sai ya tsaya ya na ƙare mata kallo,yadda ta ke motsa miyar da ta ke réchauffer matsowa yayi ya tara mata alamun ta bashi shi ma ya ɗanɗana.
Rufe tukunyar tayi ta juya mashi baya wai ita fushi ta ke da shi,juyo da ita yayi tare da laƙace mata hanci ta buge hannun shi tayi "Ni ka ƙyale ni shine ko nema na ba kayi ba alhalin tunda da safe kake nan"ta faɗa a shagwaɓe dariya ta bashi ita ala doli wai nan fushi ne ta ke kuma in yace ta na son shi tace a'a."Ka koma falo please kar wani ya gan mu"cewar Leemat ta na ɗan leƙa falo da taji kamar motsin mutum "to mu ma ba sai mu gan shi ba🤷🏻‍♀️"dukan shi ta shiga yi a ƙirji ta na ɗan kukan Shagwaɓa ya riƙe duka hannuwanta tare da ware su zuwa can ya sake su ya na mai ɗora ɗaya a ƙugunta ya matsota zuwa jikin shi saurin rumtse ido tayi jin ya na hura mata iska a fuska.
"Leemat tun ɗazu ke ni ke jira ki ida bani labarin nash..."sauran maganar ta maƙale Siya ta waro ido tare da saurin yin baya ta na dariya ƙasa-ƙasa William da ya ke saukowa daga step yace "hy"ta ɗaga ta kalle shi murmushi ya sakar mata tare da yi mata alama ta zo.
Ba tare da ta kawo komi ba ta tafi gun shi,hannunta ya ja suka koma part ɗin shi kan gado ya tureta ta faɗa ta na dariya rigarta ya ɗaga ya na shafa cikin ta ya ɗan ɗaga gira yace "kamar fah nayi ajiya fah a nan na ga kin ƙara kyawu"kafin tace wani abu ya kusanta fuskar shi ga ta ta, lumshe ido tayi ta na jin yadda ya ke kissing nata cikin ƙwarewa.

Daidai bakin wasu fararen ruwa Abbas yayi parking mota,zagayowa yayi ya buÉ—e mata ta fito hannunta cikin nashi.
Ta lumshe ido ta na shaƙar dadaɗar iskar da ke kaɗawa,ba ka jin komi sai kukan tsuntsaye da sauran ƙwari.
Baya ta juya mashi ta na kallon ruwan da hasken wata ya haske su fyau ka na ga iya ganin yadda suke gudana,ba ta san da zuwan shi sai ji tayi yayi hugingta ta baya ya na mai ɗora haɓar shi bisa kafaɗarta ya na mai lumshe ido.
Cikin cool voice yace "Ma raison de vivre ina son ki ke ma ki soni "cikin tattaro jarumta tace "akwai wanda zuciyata ta ke so tun tuni"......

Comment and share Please🥺

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

*ƊAN DABA FANS* ```BABU ABINDA ZAN CE SAI ALLAH BAR ƘAUNA INA GANIN RUWAN COMMENTS WASU MA BAN REPLY, ALHERIN ALLAH YA KAI MA DUK MABIYAN WANNAN BOOK```🥰

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.