Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 23

Page 13-14

Ɗaki Mami ta koma bayan ta cilla Leemat waje,tana wani murmurshi irin na cin nasara ɗin nan,kafin ta ja dogon tsuki ta kalli kanta a madubi tace "wato ni za ka rainawa hankali ka bar min yarinya ina rainon ta ina kulawa da ita kawai dan ka aureta? to na yadda ƙwllon mangoro na futa da ƙuda can kaje ka nemo *ƊAN DABAN* da ya ɗauke ta ɗin"ta ƙare maganar ta na mai saɓule kayan jikinta ta na ƙarewa surarar jikinta kallo.
Mami mace ce wace ba za ta haura shekaru arba'in da biyar ba,in ka gan ta ka zata Æ´ar 35years ce nan kuma uwa ce ga zaratan Æ´an mata biyu masu ji da kan su.Murmushin nan ta saki wanda a duk lokacin da ta kalli kanta a madubi ya ke gaya mata ba daidai ba,jin kanta ta ke kamar Æ´ar 20years saboda irin budurwar zuciyar da ta ke da.
Turaren wuta ta turara nan ɗakin ya ɗau haramar ƙamshi,ta na shirin shiga toilet taji muryar Jasmine na cewa "Mami za mu tafi sai mun dawo"ba tare wani tambayar inda za su je ba tace "ku dawo lafiya sannan ku kula da kan ku,samarin yanzu babu tabbas"da "toh"kawai ta amsa ta nufi inda Laila ke tsaye ta sha ado cikin riga da wando suka taɓa kafin su fita waje inda su Leel-H ke jiran su a mota.
Suna shiga Big boy ya yiwa motar key ba su zarce ko ina ba sai club,duk uban ruwan da ake sheƙawa bai hana club ɗin cika ba.Ƴan mata ne da samari kowanensu yayi mugunyar shiga a doli sai an zama turawa,kiɗa ke tashi tamkar wajen zai tsage.
Masu raye-raye nayi masu shan sigari da giya ma haka,wasun su kuma su na can keɓaɓen wuri suna aikata masha'ar su.
Leel-H ya kama hannun Laila suka shige cercle ɗin da ake rawa yayinda Jasmine da Big boy suka fara kurɓewa suna shan whisky,a ƙarshe ya ja ta zuwa gefe suna abinda suka saba romance wanda ko a cikin aji suna fakar idon jama'a su yi shi balle yanzu da suke gidan da aka tanada domin masha'a kawai.
Duk yadda Big boy ya ƙware da tantiranci Jasmine kar ta ke kallon shi ba ta yarda ya kai ga yin oga kwata-kwata,ya na ƙoƙarin kwaɓe kayanta ta buge mashi hannu tace "no sex Big boy kai ma ka san tsarina juste romance"cikin magiya yace "baby sau ɗaya tak,kuma da na tsoma zan fidda"ture shi tayi tace "ni kam rawa zan tafi nayi jikina ya fara min ciwo"babu yadda Big boy ya iya doli ya biyo bayanta suka fito daga ɗakin.Laila wacce a gaban idon ta suka fito ta saki hannun Leel-H ta ƙarasa gun Jasmine tace "mi kuka yi a can ɗin?"fuzge hannunta tayi tace "ke banza minti kawai mu ka sha ke a tunanin ki mi mu ka yi?"Laila tace "ni dai ban son keɓewar ku gudun kar a samu matsala"Jasmine ta taɓe baki ta barta nan tsaye, Allah na gani ita dai Laila ba ta son zuwan nan da suke Mami ce ta matsa mata har ta fara zuwa kuma ko ta zo rawa kawai ta ke,ba ta shan ko da sigari balle giya.

Sai wuraren ƙarfe ukun dare suka dawo, lokacin wasu masallatai har an fara kiran sallah.
Jasmine wacce ta ke a buge ta zube a kan salon tana sharɓar barci,Laila na shirin wuce part ɗin su ta fara jiyo sautin muryar Mami da ta wani namiji ko ba'a faɗa mata ba yanayin kalmomin ya tabbatar mata miye su ke.
Wani irin kyarma jikin Laila ya fara yayinda zuciyarta ke bugawa kamar za ta faɗo ƙasa,har ta aza hannunta bisa handle ɗin ƙofar sai kuma tayi sauri ta janye shi ta koma ta kwanta bisa salon da ƙudirin sai ta ga ko wanene.
Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba wani ɗan yaro matashi ya fito daga ɗakin Mami yayinda ita kuma ta ke biye da shi a baya daga ita sai ɗaurin ƙirji.
Yadda ta ga Nas ya ƙurawa Ƴaƴanta ido ya sa ta zungure mashi ƙeya tayi mashi nuni da ƙofa alamun yayi sauri ya fita,ba dan ya so ya bar gidan a lokacin ƙarfe huɗu ta gabato goshin asubah.
Bedroom Mami ta wuce ta faɗa toilet,Laila na kwance ta ji ƙaran saukar ruwa tayi sauri ta rumtse idonta a zuci ta furta ZINA ?(Zulfa'u Sa'eed Ibrahim) Innalillahi wa'inna iley raji'un da auren ki?kuma ki rasa da wanda za ki yi Mami sai da ɗan yaro sa'ar ɗan cikin ki?"wasu hawaye suka shiga zubo mata na takaici da baƙin ci.
Sai da Mami tayi sallah asubah sannan ta fito tana jan tazbaha tace "ƴan mata na ku tashi ku je ku yi sallah yau kun gaji sosai a falo ma kuka kwanta?"tayi maganar tana zuba masu tazbaha Laila wacce zullimi ya aureta dama ba kwana take ba ta tashi tana miƙa Jasmine kuwa sai da Mami tayi dagaske sannan ta tashi ta wuce part ɗin su tare da zubewa kan bed ta cigaba da barcinta.
Laila kuwa wanka tayi tare da yin Sallah nan ta zauna tana ta roƙon Allah yafiya tare da yin alƙawarin ba za ta sake zuwa gidan rawa ba.

Washegari bayan sun gama breakfast Laila ta dubi Mami tace "har yanzu babu wani labari akan ɓatan Siya kuma ita ma Leemat ɗin taje tayi zamanninta"Jasmine ta taɓe baki tace "halan ke a tunanin ki ɓata ne su kayi?to ki ma fitar da su daga cikin tunanin ki dan kuwa Siya ita da dawo sai lahira ban ƙi ba dai ko Leemat ita kam banda masaniya akan ɓatan ta"ta ida magana tana ƙas-ƙas da cingam,ba Laila ba hatta Mami sai da tayi mamakin jin furucinta tace "Jasmine kenan kin san inda Siya ɗin ta ke ?"tace "ƙwarai kuwa Mami,ina bawan Allah nan wanda ya ke zowa ya na min wankin kaya?"da sauri Laila tace "ɗan kurman almajiri?"Jasmine tace "shi fah,nuna min yayi ya na sonta ni kuma na haɗa plan ta yadda zai sace ta shine na baiwa Leemat kuɗi nace suje foire su yi sayayya to suna fita na kira na shaida mashi"cikin ɓacin rai Laila tace "Jasmine kin yi hauka ne?almajirin za ki baiwa ƴar uwar mu ya tafi da ita?"wata uwar harara ta watsa mata tace "ja can banza wannan makauniyar da kike gani bala'i ne zamanta a nan dan kuwa ya tabbatar min muddin ta na nan gidan mu da samu samari sai lahira ina ce ke shaida ce duk wanda yace ya na son mu da aure fasawa ya ke da zarar ya gan ta ko?kuma ma ba wannan ba na gaji da cin kashin da Abba ke yi mana saboda ita"murmurshin jin daɗi Mami tayi ta na godewa Allah da ya bata Ƴa sak mai irin halinta.

Laila ta miƙe tsaye tace "ai kuwa sai na gayawa Abba"da sauri Mami tace "kul!kar naji kar na gani in kuma kika kuskura kika faɗa mashi ban yafe maki nonona da kika sha ba, shashasha da ba ki kishin uwar ki to in baki sani ba Abban ku so ya ke auri Siya"Jasmine ta waro ido tace "aure ?"Mami tace "eh kin san bai san ciwon kan shi ba balle yaji kunyar haka" "ai duk wani maras kunya bayan ki ya ke dan kuwa ba ƙaramar tantiriya ba ce ke ni dai nan ban yi sa'ar uwa ba"Laila ta faɗa a zuci tana kuka.

Leemat na tafe tana waiwayen Dawood wanda ke tsaye ya harɗe hannuwa ya na kallon yadda Arne da Maye suka tisa ƙeyarta zuwa ɓangaren mata,suna shiga Maye yace "kin ga ɗakin ku nan sai jawo tabarma ɗaya wacce za ki rinƙa kwana,in kin ga dama ki zauna lafiya da mutanen ciki in kuma kin ƙi ki sha duka"yayi maganar ya na hararenta.Kuka Leemat ta fashe da shi da ta ƙarewa tangamemen ɗakin kallo wanda aka tsila tabarmi tuli guda yayinda kuma gefe guda kayan mutane ne zube a ƙasa.
"Haƙuri za ki yi ƴan mata da fatan Allah fidda ki lafiya daga wannan mugun waje,kin gan ni nan tun cikina na wata uku suka kamo ni har yanzu ba'a samu wanda ya biya kuɗin da za'a fanshe ni ba daga cikin dangina"Ladidi ta faɗa cike da tausyi,tsayar da kukan Leemat tayi tace "to ina shi mijin ki?"Ladidi ta samu waje ta zauna tace "ai shi aka kira aka shaidawa sai cewa yayi in dai sai ya biya kuɗi su kashe ni in su na so,tun daga rannan in an kira wayar shi a kashe hakan yasa na cigaba da zama a nan"Leemat tace "to miyasa ba ki bada lambar wani ba?"Ladidi ta girgiza kai tace "banda lambar kowa kuma ina tunanin ƙin biya ne suka yi tunda ai bai rasa gaya masu halin da ni ke ciki"Leemat na shirin magana wata jiniya ta shiga ruri a zabure Ladidi ta miƙe tace "mu tafi lokacin gyaran kayan miya na rana yayi "ta na gaba Leemat na bin ta abaya har suka je ɓangaren da ake girki.
Nan fah kowa ya shiga yi wasu na wankin kwanonin da aka ɓata wasu na ɓere kabewa da tafarnuwa.
Leemat aka baiwa atarugu da poivron sai tafarnuwa domin ta jajagawa,tana jajagen tana maganar zuci tare da tunanin Siya ba ta ankare ba ya waltsar mata a ido.Taɓaryai ta saki tare da ƙwala uban ihu da ya game duk illahirin gidan.
Ruwa Ladidi ta miƙa mata ta wanke fuska amman sam ta kasa buɗe idon sai kuka ta ke.
Dawood har cikin ran shi ya ji kukanta ya soke shi amman ya danne,ya na zaune ƙarƙashin bishiyar mangwaro Ladidi ta jawo hannun ta zuwa ɗaki kamar wata Makauniya.

Tashi Dawood yayi ya koma ɗaki zuciyar shi na suwa,a fili ya furta "wai miye ruwana ma da ni ke damuwa da ita?sai kace dai ita ce macce ta farko da aka taɓa kawowa nan mtws"wata zuciya ta bashi amsa da "kawai tausayinta ne kake"ya zauna kan salon ya kunna Nolywood inda suke wani série na Ibo.
Sam hankalin shi bai ga tv ya tafi can duniyar tunani na rayuwar shi ta baya amman ya kasa tuna komi,hankalin shi ne ya dawo inda King ɗin ke embrassé baiwar shi tsuki yayi sai ya ga tamkar exemple ɗin su ne shi da Leemat.
Wanka yayi tare da haye bed ya kashe hasken É—aki a doli ya sa kan shi barci ba tare da ya shirya ba.

Har aka gama hidimar cin abinci Leemat ba ta farka ba sai yamma lis sannan ta tashi da wata irin yunwa sai dai mi?ba'a aje mata abinci ba haka ta zauna da jiran abinci dare sai kash abinda ba ta sani ba babu tsarin yin girkin dare a wannan gidan.
Tsakar dare yunwa ta hana Leemat barci sai juyi ta ke haka ta ke wajen Dawood shi ma kasa rumtsawa yayi, tunanin Leemat ne shimfiɗe a ran shi.Da sassarfa ya fito waje ya nufi ɓangaren mata wanda hakan shine karon farko a rayuwar shi shiga sashen uwanda suka kamo,har ya kusa kaiwa sai ya ga ana murɗa handle alamun za'a fito da sauri ya laɓe bayan bishiya.
Ya na kallon Leemat lokacin da ta fito har ta nufi ɓangaren da suke aiki domin shan ruwa,Maye da ke murƙusar wata cikin kitchen ya hangi Leemat da sauri ya tada Nana ya nufi Leemat wacce ta duƙa ta tara hannunta tana shan ruwa ga pampo,ba zato ba tsammani taji mutum bayan ta ya na zungurar ta wani uban ihu ta ƙwala tana kiran sunan Allah......

Comment and share 🙏🏻

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.