Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 23

*PAGE 31-32*

Leemat na shiga part ɗin duk kallo ya dawo kanta sai ƙus-ƙus mutane ke yi,gun Ladidi ta nufa wacce ta miƙe ƙafafu saboda yadda cikinta ya tsufa.Gaishe ta tayi tace "wai miye na gani ana ta kallona kamar wacce tayi sata ko mayyta?"cewar Leemat ta na yamutsa fuska,Ladidi tace "Nana ta basu labari wai budurwar Maye ce ke duk yadda Boss ya riƙe ki sai da kika ci amanar shi kika kwanta da abokin shi"ido Leemat ta zaro tare da dafe ƙirji sai kuma tayi gun Nana gadan-gadan ba ta wani ɓata lokaci ba ta rufeta da duka nan kuwa faɗa ya kancame.
Ƴan ɗakin sai ihu suke wanda hakan ya jawo hankalin mazan da ke waje suka shigo raba su,amman abu ya cuttura hakan ya sa ɗaya daga cikin su ya kirawo Arne amman da ya ke Maye ya ji an ce da Nana ne sai ya biyo bayan shi.
Yadda Leemat ta riƙe ta gam ta na bugu kai kace uwarta ce,ganin shilar Boss ce ya sa Arne ja baya ya tsaya tare da daka masu tsawa wai su bari 🙄 Leemat tamkar zugata ne yayi haka ta cigaba da nausar Nana waya Arne ya yiwa Dawood,Maye ganin ana shawowa da Nana ya sa hannu ya fizgo Leemat tare da ɗauke ta da wani mari wanda ya ɗauke jin ta da gani.Ihu tayi tare da yin wani tsalle za ta faɗi Dawood ya tareta ta faɗa jikin shi,ta na shaƙar ƙamshin bodyn shi ta ƙara ƙanƙame shi ta na mai tusa kanta a ƙirjin shi tana jujuya shi tare da cigaba da kuka sai faɗi ta ke "ban gani na makance"ƙara matseta yayi a ƙirjin shi ya na mai ƙanƙance idon shi da suka yi ja lokaci ɗaya.
Sunne kai Maye yayi zuciyar na dukan tamanin tsabar fargaba,duk jama'ar gun watsewa suka yi ya rage su biyar amman sai leƙen su suke dan ganin mi zai faru.
Ɗago kanta tayi tana ƙoƙarin buɗe ido,tsura mata na shi idon yayi tare da ɗan hura mata iska kafin ya kai bakin shi ya na lasar ta saman idonta.Ajiyar zuciya ta sauke ta buɗe idanu idonta ɗaya har yayi ja,saurin mayar da kanta yayi a ƙirjin shi sannan yace "akan wannan abar ce ka daki flower mai tsada?mi tayi maka?minene dalilin marin?ban taɓa kisan kai ba amman yau zan ɗaura ɗamarar fara shi sannan ka sani za ka fuskanci hukunci mai tsanani a guna,Arne samo min reza da bandeji".
Da sauri Maye ya duƙa ya fara bada haƙuri har da kukan shi,dan ya gane kalar muguntar da za'a aiwatar kan shi Dawood zai yanke fatar jikin shi ne kamar yadda ake kalsar rake sannan a naɗe gun da bandeji.
Can ƙasan maƙoshi Leemat ke magana ta yadda Dawood kawai ya ji,wani kallo ya yiwa Nana a nan take ɗan ƙaramin cikinta ya fara zuba.Dawood na shirin magana kiran Oga Darma ya shigo "ka shirya za ka tafi Moumbay gobe saboda an sace ɗan Oga Danee,kai kaɗai ne za ka iya ceto shi a duk yaran mu dan haka sai ka kimtsa"cike da rashin jin daɗin haka Dawood yace "Ok"kafin ya ja hannun Leemat suka nufi part ɗin shi.

Kaya ya fara zubawa cikin trolly ta kalle shi tace "ina za ka ?"yace "wai Moumbay kuma ni sam na tsani garin zuciyata ma bugawa ta ke kamar za ta faÉ—o".
"Ina bin bayan ka"ta faɗa a shagwaɓe yace "no wannan tafiyar fah sai an shiga jirgi ke kuma ba wani paspo gare ki ba kuma ba ma wannan ba aiki ne mai hatsari zan yi sosai"gabanta ne ya faɗi tuna Dawood fah *ƊAN DABA* ne sharrr hawaye suka zubo mata ya rufe trollyn ya zauna tare da ɗaukar ta ya aza a cinyarsa yace "gayamin minene?ki na son zuwa ko?to fine zan sa yadda zan yi amman da haɗari kar a tai siddabarun nawa ya ƙi aiki"ta ɗora hannunta a bayan shi tace "ni ina tsoron kar su kashe ka"yace "su wa fah?"tace "ai na san opération ne aka tura ka,ni dai ban so kar ka tafi"tsura mata ido yayi "ba ki so na mutu ne wly? Miyasa kika damu da ni"gemun shi ta ja tare da yin murmushi tace "kawai dai am babu komi fah"Dawood ya sauke ajiyar zuciya yace "m'aimes tu?"ta tsaya da wasa da gemun shi da ta ke,ya ƙara tambayata"ki na sona?"kokowa ta fara da numfashinta tare da ƙoƙarin tashi ya riƙe ta ya na mai jawo fuskarta ya haɗe da tashi tsinin hacin su waje guda yayinda idon su suka sarƙe cikin na juna,wani shock da wani abu mai kama da zare haka dukkansu suke ji.
Lumshe ido tayi ganin ya fara É—an karkata kan shi,abinda tayi zaton ne kuwa kissing É—in ta ya fara na tsawon minti uku sannan ya zare bakin shi.
Lips ɗin ta ya shafa wanda ya jiƙe da yawun shi,ta turo baki shi kuma ya harareta yace "yaushe rabon da ki yi brush ma wai?"wani ƙululun baƙin ciki ne ya kama Leemat wani iskanci bayan ya tsotseta ya ke tambayarta in tayi brush,"tun shekaru biyu da suka wuce"ta faɗa ta na mai tashi ta nufi toilet shi ma tashi yayi ya na dariyarta tace "kar ka biyo ni bar ni nayi wankana cikin nutsuwa"ta faɗi haka ta mai rugawa da sauri ya bi bayan ta.

****Moumbay

Sai dare granny ta dawo,a falo suka zauna suna ta hira ita dai Siya na kallon télé ta na jin lokacin da granny ke faɗa miyasa ya kai Siya ɗakin sirri shi dai bai ce da ita komi ba sai haƙuri da ya bata kafin ya tashi ya faki idon su ya ɗauki kular abinci ya shige ɗakin da aka sauke Siya.
Akwatin ya janye nan wata ƴar ƙofa wacce ta kasance ta raga kamar grillage ta bayyana,wasu ɗalasiman tsafi ya karanta ta buɗe step ɗin da za ta sada ka da ɗakin ya taka ko minti biyu bai yi ba ya fito.

Dare nayi Siya ta shige É—aki ta kwanta,can tsakar dare taji kamar ana magana da sauri ta tashi zaune.
"Ruwa!ruwa..a bani ruwa"haka ta ke jin muryar na fitowa daga cikin ƙasa,akwatin nan ta janye saboda haƙin da ta gani ta wajen.
Wani tsoho ne ta gani zaune a kan kujera fuskar shi duk ta cika da gashi,ya ɗago kan shi sama ya na ta kiran a bashi ruwa toilet ta shiga ta ciko moɗa ta shiga tsiyaya mashi da sauri ya tara hannu ya na shan ruwan har da suɗe shi tamkar wani abinci.Ganin ruwan kamar ba su ishe shi ba ta ƙara komawa ta ciko ta bashi tayi mayi ya fi sau biyar amman tsohon nan na shanye ruwan kafin daga ƙarshe ta ga ya je ya kwanta.
Mayar da akwatin tayi yadda ya ke sannan ta dawo ta kwanta tunani fal zuciyarta.

A ɓangaren William kuwa tun da ya ɗauko Abbas ya ke gana mashi azaba amman amsa guda ce ya ke bashi shi ma bai san inda Siya ta ke ba,daga ƙarshe William ya fara bugun cikin shi ko ya samu wani sirri dangane da Danee sai dai abinda ya fahimta Abbas bai da labarin miyagun ayyukan da Danee ke yi bayan dabanci.

Dawood na dira garin Moumbay ya mayar da Leemat mutum ba kamar yadda ya shiga da ita a jirgi a matsayin jakar hannu😱,hotel ya kama masu Leemat sai shagwaɓe mashi ta ke.
Suna kwance suna hutawa bayan sun ci abinci wayar Oga Darma ta shigo bayan daga bisani ya bashi wani détail Na gidan da zai fara zuwa.
Washegari gari haka Dawood ya shirya shi da Leemat suka nufi gidan da zai fara yin wani aiki,mai taxi na aje su Dawood ya danna ƙarar rawa Papi ne ya buɗe ya na mai sakar masu murmurshi dan dama ya san da zuwan Dawood ɗin.
Wajen piscine Papi ya fara nufa da su ya na mai cewa "wannan ruwa sun yi shekara da shekaru suna jiran zuwan sai yau Allah yayi nufi"murmushi Dawood yayi yace "haka ne,yanzu ya ne zan yi"Papi yace "shiga kawai za ka yi ka fito kuma ba sai ka cire kaya ba"kai Dawood ya jinjina tare da yin Bismillah ya faɗa kwacal,da sauri Siya wacce ke bayan wasu flower ta leƙo jin ƙarar shigar mutum cikin ruwan da kusan kullum sai Papi yayi mata hani da zuwa kusan su.
Leemat ta ƙurawa ido na wani ɗan lokaci kafin ta maida idonta ta na jiran ganin wanda zai fito,wani abu taji kusan ƙafarta da sauri ta duba sai ta ga wani zare ne duƙawa tayi ta na warware shi ko da ta ida tuni Dawood wanda ya fito daga cikin piscine sun bar gun.....

Comment and share Please

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇🏽

*500MB* 200

*1GB* 300

*2GB* 600

*3GB* 900

*6GB* 1800

(CHECKING BALANCE * 461*4# )

VALIDITY : 1 MONTH

For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.