Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 23

Page 9-10

A hankali ta ke buɗe idonta da ta ke jin sun yi mata wani sanyi kamar an watsa mata ƙanƙara,tas ta buɗe su suka sauka kan kyakkyawar fuskar Weeliam wanda sam bai cikin nutsuwar shi ƙoƙarin gamsuwa kawai ya ke ya na shiga da fita cikin jikinta.Azabar da ta ke ji tamkar ya na yi mata jajagen atarugu ne a ƙasanta amman babu bakin yin ihun,ƙuri tayi mashi tana kallo har lokacin da ya zare jikin shi.Ruwan da su ke ciki duk sun ɓace da jini,buton ya danna ruwan suka tsiyaye ya tara wasu kuma masu ɗan ɗumi ya na mai jawota jikin shi.Ƙuri suka yi ma juna can ƙasan maƙoshi yace "yanzu ki na gani na?"kai ta jinjina mashi kawai sai ya haɗe bakin su waje ɗaya,ture shi tayi ta mashi alama da hunnu"wanene kai?"da sauri Weeliam ya tashi daga kishingiɗen da ya ke "wata sabuwa in ji ƴan caca,miye kike maganar kurame ba ki iya magana ne ?"kai ta ɗaga mashi alamar eh.
Fita yayi daga ruwan ya ɗaura towel ya fice daga toilet ɗin,wani book ya fiddo daga ƙasan drawer ya buɗe shafi na uku ya fara karantawa ```Ranar da idonta ya buɗe to a ranar bakinta zai rufe saboda ƙarfin sihirin da ke cikin jikinta ba zai bari tayi magana in kuwa tayi magana tamkar mahauciya za'a ɗauke ta dan kuwa abinda za ta faɗa hankali ba zai ɗaukar shi.Weeliam kar ka yi ƙasa da gwiwa kayi ƙoƙarin hana faruwar kafuwar wannan ƙungiya ta tantirai,sannan ka sani kai ne garkuwa Shamsiya duk ranar da ta bar hannun su za su nemeta ne ruwa a jallo kar ka buɗe masu wata ƙofar```har buɗe page ta gaba ya ga can ƙasa an rubuta NB: *Sai wata buƙatar ta taso sannan ka tafi a page ta gaba*
Ajiyar zuciya William ya sauke ya na mai jinjina wannan cakwakiya,Siya ta fito ɗaure da towel ta na gwale ƙafa harara ta banka mashi kafin ta wuce ta zauna bakin bed.
Tausayi ta bashi ga shi dai idonta sun buɗe ta na gani kamar kowa sai dai kuma wata masifar ta sake samunta ta liƙewar baki,ƙarasawa yayi kusa da ita yace "ya jikin ki?"ta ɗago ta dube shi ta mayar da kai ƙasa ta na mai cigaba da tunanin cakwakiyar da ta ke fuskanta.Ta yaya hakan ta faru?miyasa idonta ya buɗe alhalin ita Makauniya ce?wanene William?mi ya sani game da ni da har ya san idona sun buɗe alhalin ban faɗa mashi ba?"wannan sune tambayoyin da Siya ke yiwa kanta.
Kaya ya ɗauko tare da miƙa mata ya fice daga ɗakin,ba ta da wani zaɓi doli ta shirya ta shafa mai tare da kwantawa saboda tsabar gajiyar da ke tattare da ita.
William ko da ya dawo ya tarar tayi barci shi kaɗai ya ci abinci kafin ya shirya cikin wasu riga da wando baƙaƙe sannan ya ɗauko wata fuska ya shiga sawa kan tashi ɗaram ta zauna ya dawo wani kumurcin namiji in ka gan shi ka zata dama tun farko haka fuskar ta shi ta ke.
Bindiga da alburushi ya ɗauka ya na mai lanƙama wani abu a kunne sannan ya fice,Mishel na ganin fitowar shi ya rugo ya na habshi tare da zagayen shi.Shafar shi yayi yace "t'inquiète ba jimawa zan yi ba"sai da Mishel ya lashi hannun shi sannan ya wuce,mota ya shiga ya fara gudu ya na nufar hanyar fita gari sai da yayi nisa sosai sannan ya rutsi daji.
Wani tangamemen gate na ƙarfe mai gadi ya buɗe mashi ya shiga,ya na gama parking ya wuce ciki inda tuni aka fara gudanar da taron.
Ƙarasawa yayi ya zauna ya na kallon farin allon da Oga Danee ke expliquer yadda attaque ɗin zai kasance,shiru William ya yi ya na kallon komi can ya miƙe ya nufi gun Oga Danee yace "bai kamata mutanen mu su tsaya a nan ba dan akwai tsaro sosai da zarar an yi digil za'a iya kama su, rond-point na biyu ya kamata su tsaya dan bai fiya mutane sosai ba,sannan za mu rufe hanyar global ta yadda motar kuɗin za ta sake hanya suna zowa daidai rond-point sai a halbi tayar motar amman a sa bindigar silence ta yadda ƙararta ba zai fito ba,ka ga doli drever ya tsaya duba ko lafiya daga nan sai Rohan ya kashe shi tun da ya fi kowa iya saiti."ganin Oga Danee na kallon shi yace "No Oga shawara ce in hakan bai yi ba ana iya canzawa tsari"ya faɗa ya na mai komawa mazaunin shi.
Oga Danee ya ɓata rai yace "yadda na faɗa maku haka za ku yi kun ji ko?"mutanen gun suka amsa a tare "Yes Oga"su na masu sanya masque baƙa wacce daga baki,ido da hanci kawai ke waje.Bindigogin su suka yi chargé tare da ficewa har William zai bi bayan su Oga Danee ya tsayar da shi,"yau ba da kai za'a fita ba"da sauri Weeliam ya waigo yace "saboda mi Oga ?"ƙara tamke fuska Danee yayi yace "ina ka tafi tsawon sati guda ba tare da neman izini ba?" amsa ya bashi "ban jin daɗin jikina ne kuma ai na gaya maka duk bayan wata uku ina zuwa ganin likita"Danee yace "amman ai ba kai wata uku kayi waccan tafiyar ba" "eh ai nace ma jikin ne naji ya na son motsa min shiyasa nayi riga kafi"kallon cikin ido Oga Danee ke yiwa William amman sam ya kasa ganin abinda ke cikin zuciyar shi saɓanin sauran mutane.
"Ina so ka rakani"Oga Danee ya faÉ—a ya na mai juya baya, William yace "ba damuwa ina za mu je?yaushe ne kuma tafiyar?"murmurshin gefen baki Danee yayi yace "yanzu za mu tafi mana sanin kuma ina za mu in ka shirya kawai ka matso"ba tare da tsoro ko fargaba ba William ya matsa.
Hannun shi Oga Danee ya matse tare da karanto wasu ɗalasimai na tsafi,kamar walƙiya haka suka ɓace suka aniya gudu cikin iska tamkar guguwa sai da aka ɗauki tsawon sakonni sannan suka bayyana gaban wani gabjejejen Kogi.
Waro William yayi kamar mai jin tsoro da fargaba yace "ina ne nan?ya aka yi na gan mu ba..ban gane ba"shiru Oga Danee yayi bai tanka shi ba sai ma wasu suratai da ya fara karantowa ido rufe ya miƙe dukan hannuwan shi ya na mai fuskantar kogin da ya fara rikiɗewa ya koma wuta🔥har wani ɓulɓulowa ta ke.
"Hahhh,uwayyyyy uwayyy"haka wani sauti marar daɗin ji ya fara fitowa daga kogin yayinda wani haƙi dogo ke ta wuwulniya ya na ƙara tsayi da kauri har sai da ya kai iyakar da ido bai iya gani sannan kogin yayi girgiza sai ga wani tsoho ya bayyana jikin shi fari fuskar shi baƙa yayinda gashin kan shi ya ke a murɗe ya zubo har ga kafaɗa.
Buɗe ido Oga Danee yayi lokacin da ya ji aljani Gamsak na magana cikin murya shi mai kama da ɓarɓarkiya "wannan zinaren da ni ke faɗa ma tun tuni shine cikar burin ka hhh ya daɗe tare da kai amman sai yau kawai ka gano shi dama na faɗa maka in ka aje hankalin ka za gane shi,yanzu abinda za'a yi ka riƙe shi matsayin makamin ka domin wannan ya na wata baiwa wacce shi kan shi bai san da ita ba"murmurshi ɗauke a kan fuskar Danee ya ke kallon aljani Gamsak cikin jin daɗi yace "ina maka fatan nasara kai ma na zama shugaban aljannu na duniya"aljanin Gamsak bai ce komi ba sai wani abu fari ƙal da miƙawa Danee a hannu ya ce ya sawa William shi a haure,bai wani ɓata lokaci ya buɗe bakin William ya laƙa mai shi daram ya zauna tamkar hauran Makka.
Wani irin haske jikin William ya ɗauka tamkar an saka shi cikin ƙwan fitila,hannun shi Danee ya kama ɓat suka koma ɓacewa.

Oga Danee ya gyara zama ya na kallon William da ke yi mashi kallon tuhuma,"William na zaɓe ka ne ka zamo makamina saboda cikar wani ɓoyayyen burina da na daɗe ina son gani, tabbas ba'a ɓoyewa abokin cin mushe wuƙa dan haka zan gaya maka kaɗan daga cikin labarin da fatan za ka riƙe min sirrina?"yayi maganar ya na mai zaunawa a kujerar da ke facing da wadda William ke zaune,"ina sauraren ka Oga Danee kar ka damu ni ɗin mai bin umarnin ka a ko da yaushe"cikin jin daɗin amsar shi Danee yace "wannan mutumen da ka gani ba ɗan Adam ba ne aljani ne"waro ido William yayi da sauri yace "aljani?ta yaya ka san haka?to ina ma ka ga mu da shi"yayi maganar a ruɗe.
Oga Danee yace "calm down kar ka wani ji tsoro ba zai cutar da kai ba,shi ɗin ya kasance aljanin da ni ke bautama ya na taimako na a duk lamurrana ya bani abubuwa masu tasirin gaske wanda kallo idon mutum kawai zan yi na gane abinda ke ran shi,to aljanin Gamsak ya faɗan burina ba zai taɓa cika ba sai na samu wanda ya fi ni ƙarfin iko wanda sam ba zan iya ganin abinda ke zuciyar shi.Na daɗe ina nema har ƙasashe da dama na tafi ban samu ba sai yanzu kwatsam na gano ashe kai ne shiyasa ban yi ƙasa da gwiwa ba mu ka tafi"William yace "ni kuma?to ni mi zan iya yi?"Oga Danee ya miƙe tsaye ya na gyara maɓallan rigar shi yace "in lokaci yayi za ka sani,am abinda da dai ni ke so da kai ka riƙe sirri"William na shirin magana sai ga abokan aikin su sun dawo jiki jina-jina.A firgice Oga Danee ke kallon su kafin yace "ya haka?ina kuɗin su ke da sauran mutanen?" "An kama su har sai da mu ka ɗauko kuɗin ashe an yi masu mugun tsaro ta yadda mu na taɓawa jiniya za tayi ƙara"a hasale William yace "aikin banza tirrr duk yawan ku aka rasa wanda zai iya ƙwace kuɗin?Oga Danee shiyasa na so in tafi mtws"ya ida maganar ya na jan tsuki tare da ɗauko gorar ruwa ya sha.
Oga Danee ya nufe shi ya na lalaɓa shi dan kaf cikin yaran shi ya fi son William saboda ƙwazon shi da iya aiki,hannu William ya ɗaga tare da ficewa ya bar gidan gaba ɗaya.Oga Danee ya rufe su da masifa "da kuka ga an kama ƴan uwan ku miyasa ba ku ceto su ba yanzu ga shi za ku ɓallo min ruwa,babban baƙin ciki kuma William ya tafi cikin fushi bari na aika mashi text".

Tsakar gado ya hangota ta game kai da gwiwa ta na kuka,ta na jin motsin buɗe ƙofa ta taso a guje ta na shirin faɗawa jikin shi ta tsaya cak sakamakon sabuwar fuskar da ta gani.Ja da baya ta fara yi har tayi nasarar shigewa toilet cike da mamaki ya fara kiran sunanta amman ta ƙi buɗewa,ya gota ya hango abinda ta ke ma gudu a zuci yace "wato fuskata ta biyu ta ke yiwa gudu"ya faɗa ya na mai kwale fatar a sannu har ya cire ya fito William ɗin shi sak.Wayar shi ya duba ya ga saƙon Oga Danee akan ya je ya sheƙe mutanen su da aka kama kafin a kaisu kotu,lekowa Siya tayi sai ta ga William zaune bakin bed.Fitowa tayi kamar mai koyon tafiya a shagwaɓe ta faɗa jikin shi "minene baby?"da hannu tayi mashi tambaya "who are you ?"tashi yayi ya ɗauko wani albums wanda ake da hotuna.
Ya buɗe hoton wani African man ya bayyana gefen shi kuma wata baturiya ce, William yace "wannan shine babana sunan shi Ahmad wannan kuma Maman ce , Baba ya kasance asalin ɗan Mali ne yayinda Maman kuma ƴar France ce.Sun yi auren soyayya inda suke a France zaune tunda na mahaifina ya ke aiki, kasancewar Maman a gidan marayu ta taso shiyasa ba'a wani samu matsala wajen auren su ba"hoton Siya ta shafa ta na murmurshi ta na son tambayar ta shi ina Baba ya ke amman ta kasa.Wani hoton ya sake buɗowa inda shi kuma ɗan matashin saurayina da ba zai wuce 20years mai kama sak da Baba sai dai shi baƙin shi mai sarkaye da fari hakan ya sa fatar shi bada wani kala na musamman,ganin William ya kasa cewa komi sai ma hoton da ya ke shafa ya sa ta ɗan zungure shi.Ya sakar mata murmurshi yace "wannan kuma Dawood kenan,Yayana ne ya na can India wajen karatun SIDDABARU (Muntasir Shehu)tun ina ɗan shekara shidda ya tafi bai sake dawowa ba wannan hoton ma malamin su ya bani shi lokacin da na tafi kai mashi ziyara"ya ida maganar hawaye na zubo mashi a ido.......
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.