Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 23

Page 11-12

Su na shiga falon ya cillata saman gujera cike da masifa yace "uwar miye za ki yi da tsintsiya na ga kin nufi toilet?aikin mata ne balle kiyi kawai neman magana koko mi?"cewar Dawood ya na mai hararta cikin shagwaɓar da ita kanta ba ta san yaushe ta koyeta ba tace "ba wannan ba ne yace na wanke toilet bayan ya sa na wanke kayan maza masu warin giya"waro ido yayi yace "warin giya?ke a ina kika taɓa jin warinta har kika gane ta?am ba ma wannan ba miyasa da yace kiyi wankin kika yi"ta bashi amsa "ni tsoron shi ni ke"ya tako inda ta ke tare da zama gefenta yace "au kenan ni ne kika raina"ya faɗa ya na mai jan hannuwanta baya ya banƙare su ƙara ta saki ta shiga bashi haƙuri "Allah kai ma ina tsoron ka please ka sake min hannu kar ya cire daga yau ban sakewa" saketa yayi ya na mai dangwale mata goshi da yatsa yace "in ki na so ma ki sake ki ga yadda zan hukunta ki da wasu ido nata kamar ƙyaya"ta turo baki ta na gunguni ya cabke duka laɓan nata biyu ya shiga basu hot sumba mai game da ƙeta dan har ciciza su ya ke.
Gemun shi ta ja da ɗan ƙarfi ta yadda zai ji zafi da sauri ya saketa,ta miƙe za ta gudu ya taɗeta da ƙafa ta yo baya za ta faɗi ya caɓeta tare da yi mata masauki tsakiyar ƙafafun shi.Kan shi ya ɗora kan wuyanta yayinda ya manna ƙirjin shi ga bayanta ya sa baki ya ɗan ciji kunnenta ta saman hijab ya na mai yi mata ƙawanya da hannuwan shi yace "daga ina kike jiya cikin wannan tsohon daren ki na mace?"kamar ba za ta tanka ba tace "neman Siya na fito""wacece Siya?"yadda abun ya kasance ta bashi labari tun ɗauketa har izuwa Korar ta da Mami tayi.Dawood yace "amman wannan akwai rashin imani yanzu mi Makauniyar Allah ta yi ma shi ya ɗauke ta?"cike da mamaki Leemat ta ɗan juyo ta kalle shi sai ya ɗaga mata gira yace "ba ɗaya ba ne ai ke kina gani ita kuma fah?am ba ma wannan ba ita Mami miyasa ta ce doli sai kin je neman Siya alhalin ta ga ana ruwa?"Leemat tace "saboda ba ita ta haife mu ba ne,ni dama na gane ba ƙaunar mu ta ke ba kawai ta na zaune da mu ne ba dan ta na so ba sai dan tsoron Abba"ya jinjina kai yace "to shi Abban ya na ina har ya bari ta fitar da ke daga cikin gida?"Leemat tace "ya na Moumbay can ya ke da kasuwanci ya na ɗaukar shekaru kafin ya zo Niger".
"Moumbay...Moumbay"Dawood ya shiga juya sunan sai yaji kamar ya taɓa jin shi amman ya kasa tunawa,sai yace "to wacece mahaifiyar ku?"shiru tayi kafin tace "nima ban sani ba abinda na sani kawai Mami ba ita ta haife mu saboda yadda ta ke nuna mana tsangwama dama-dama ma Siya ita ta na rangwanta mata saboda ita ce farin cikin Abban mu yace duk ranar da ta cutar da Siya akan aurenta"Dawood ya jinjina kai yace "a haka ne kuma jiya kike min kuka na mayar da ke gida dan ki na sakara tashi ki ban guri"ya faɗa ya na ɗan tureta.
Leemat tace "Ni dai dan Allah ka kai ni wajen Siya ka ga ba gani ta ke ba kar wannan azzalumin *ƊAN DABA* ya cutar min da ita"kallon shashasha yayi mata yace "toh je ki nemo su ni ai ba aljani ne ba balle na san inda suke"yayi maganar ya na miƙewa tsaye,tace "to ai ka iya tsafi sai ka tambayi aljannun ka"waro ido yayi yace"ni ne matsafin?"ta ɗan ja da baya tace "a'a ni ban ce ba"ya matso kusanta yace "kin ce mana"a zuci tace "masifafe"yace "ni ne masifafen ko?to yayi kyau yarinya za ki wuni ba ki ci komi ba kuwa"narai-narai tayi da ido tace "ayya Yayana kar ka min horon yunwa ban iya jurewa ka taimaka ma ƴar ƙanwar ka"girgiza kai kawai yayi ya fita zuwa can ya dawo shi da Arne wanda ya ɗauko tray abinci.
Bisa table ya aje ya na gaishe da Leemat ta amsa tana mai sakar mashi murmurshi ashe wannan abu ya yiwa Dawood ciwo😂wanda hakan yasa ya yiwa Arne waya wakitar tsiya wacce yasa shi fita daga ɗakin bai shirya ba.
Hararta yayi yace "miye ruwan ki da shi ne?"tace "shi fah ya gaida ni"cikin masifa yace "sai kuma aka ce kiyi mashi murmurshi?"ta girgiza kai yace "stupide girl!É—auki abinci ga shi nan ki ci in kin gama ki zo kiyi min tausa"da "toh"ta amsa ta na mai É—aukar jalof É—in macaroni ta fara ci shi kuma ya na kwance daga bisa salon ya na kallonta.
Ya girgiza kai yace "acici in kin gama fah kar ki manta da abinda na ce maki zan É—an rumtsa"ta ture plate É—in tace "ni dai ba acici ba wannan girkin duk wacce tayi shi ba ta iya sai shegen yaji da wani mai latsatsa kai kace wani abun kirki sai kaci kaji salaf"tayi maganai ta na mai É—aukar gorar ruwa ta sha.
Sai da ta ƙare mashi kallo tsaf ta turo baki tace "to wai ni ta ina ma zan fara ga ka da tsayi ga kuma girma"murmurshin ƙeta yayi yace "nan za ki tausa min"ya nuna mata ƙirjin shi tare da fidda riga.
Ta waro ido tace "yanzu in ba neman magana ba ina ka taɓa ganin a matsa ƙirji aikin mi kayi da har zai yi ciwo"ta faɗa tana kallon ƙirjin nashi da ya ke suluf babu gashi.Ya ɗan ware idon shi da suke lumshewa yace "kin manta jiya dakon ki nayi?kika wani ɗale min ƙirji kamar katifa to yanzu sai a ramawa kura aniyyarta,matso mana"ya ida maganar cikin ɗaga murya.Ƙarasowa tayi gaban shi ta na ɗan turo baki kafin ta danna cikin shi ya saki ƴar ƙara tayi saurin jayewa zuwa awazun shi har ta zo daidai saitin zuciyar shi da ta ke bugawa da ƙarfi,ganin idon shi na lumshe yasa ta duƙa tare da ɗora kunnenta daidai saitin zuciyar shi.
Sautin bugu ne wanda ke nuni ko mutum ya na cikin wani hali na tashin hankali ko kuma wani abu mai motsa zuciya ba tare da ka shirya zuwan shi ko tsammani ba to wajen Dawood ma haka take a duk lokacin da suka samu kusanci da Leemat ya kan ji bugun zuciyar na ƙaruwa.Ahankali ya fara ɗaga gashin idon shi har ya buɗe su bisa kyakkyawar fuskar ta mai kama da ta Fulanin asali,hura mata iska yayi hakan yasa ta buɗe ido caraf suka yi ido huɗu da shi ɗaga mata gira yayi sai ta janye kanta ta na mai cewa "dan Allah wanene kai sannan wannan abun minene aka yi ma?"ta faɗa tana mai taɓa wani zane da ke tsakiyar ƙirjin shi.
Shafar zanen yayi yace "tambarin India ne an fiya yi ma uwanda suka yi karatun siddabaru shi" "kenan kai ma kayi karatun ?"ya gyaɗa mata kai tace "to mi ya kai ka Indiya na ga kuma kai baƙar fata ne?"shiru yayi ya na tunani can yace "eh a can nayi makarantar siddabaru,ina ɗan 20years malamin mu ya turo mu ƙasar Nigeria dan koyon karatun tsibo sai kuma aka samu akasi ƴan fashi suka tare mu".
Leemat tace "shine sai suka riƙe ka wajen su suka koya maka dabanci har ka zama ɗan ta'adda?"kallonta ya yi cike da mamakin yadda ta samu izzar da har ta ke gaya mashi duk abinda ya fito bakinta ba tare da tauna kalaman ta ba,ganin alamun ɓacin rai a fuskar shi yasa tayi saurin cewa " kayi haƙuri ina son sani ne ko da taimakon da zan iya baka"ta faɗa ta na mai jimƙe hannun shi.
Murmurshin gefen baki yayi yace "ƙaramin alhaki ke har akwai abinda za ki iya?hum ai ni duk duniya abu guda kawai ne zan iya nema gun ki"Leemat tace "miye fah?"ya girgiza kai yace "ba yanzu ba,dan ban buƙatar ki ban shi yanzu sai ya zama mallakina"kallon shi ta tsaya yi ta na auna maganar ta shi har ta gane miye nufin shi.A zuci tace "Allah raba ni da auren *ƊAN DABA* wai shi a haka har ya na tunanin akwai macen da za ta so shi?"Leemat ta manta shaf da cewa Dawood na karantar abinda ke ran mutum har tayi kuskuren kallon shi ta na maganar zuci."Ashhh!"ta furta da ɗan ƙarfi sakamakon haɓarta da ya matse a hasale yace "ni kike cewa *ƊAN DABA*?raini ko samun wurin zama?"ya faɗa ya na mangare ta kafin ya ɗauke ta da wani gigitacen mari wanda ya ɗauke jinta da ganinta na ɗan lokaci.
Bugunta ya shiga yi da hannu ta na tarewa tare da yin kuka ta na bashi haƙuri, Dawood irin mutanen nan masu zuciya kusa ya na saurin fushi abu ƙanƙane ke fusata shi shiyasa kaf yaran shi ke tsoron shi.Kiiii ya ja Leemat ya cillata waje nan kallo ya dawo kanta kama da ga mutanen da aka yi kidnapping har zuwa su Arne da ke zaune suna shan shayi.Da sauri suka ƙarasa kafin su kai ga tambayar lafiya Dawood yace "ku ɗauke ta ku kaita ɓangaren mata sannan ku gaya mata tsarin gidan nan"cike da jin daɗi Maye ya je kama hannunta Dawood ya kai mashi naushi tare da harar shi yace "kar ka saki ko akaifarta ka taɓa juste kayi abinda nace"......
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.