Best / Popular Hausa Novels

an Daba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 23

Page 25-26

Ta na kawowa bakin get ta ci sa'a babu kowa a gun tayi saurin buɗe ƙofar ta fice a guje,ba ta san inda ta ke saka ƙafarta ba kawai dai gudu ta ke ko takalmi babu.
Ta na tsaka da gudun ne taji an yi sama da ita ta faÉ—i can gefe,mai motar ko tsayawa bai yi ba sai mutanen kan titi ne suka taimaka suka sa ta a taxi ya kai ta asibiti.
Siya na farfaɗowa ta gan ta da ƙarin ruwa ga bandeji a ɗayan hannun saboda raunin da ta samu,wata datijuwa ce ta shigo ta dubata tare da tambayar ta jikinta.
Da maganar kurame Siya ta mayar mata duk da dai ba jin English ta ke ba sosai ta fahimta,ashe datijiyuwa ta iya maganar kurame da ta tambayi Siya ina ne gidan su sai ta fashe da kuka tace ba ta sani ba.
Sérum ɗin ta cire mata tare da taimaka mata ta sauka daga gadon,ta na jaye da hannun Siya har ta tsayar da mai taxi ta gaya mashi unguwar da za su.Siya ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta bi bayanta kuma sosai zuciyarta ta kwanta da matar shiyasa ba taji wani ɗarrr ba, lokacin da aka kawo su da murmushi ta shigar su cikin gidan wanda ya ke tsit ba kowa sai kukan tsuntsaye da ƙwari.
Tsabar ni'imar gun sai da Siya ta lumshe ido,gidan duk shibke-shibke ne a ciki ga ruwan piscine inda mutum zai yi wanka.Wani tsoho ne ya fito daga ɗakin ya na wangale bakin shi maras haƙora ya na magana da granny ya na kallon Siya,nan ta gaya mashi yadda aka yi ta same ta.
"Papi wacece ni ke gani nan kamar baƙuwa?"muryar wata ƴar budurwa ta faɗa wacce ke can saman bene ta na kallon su,da hannu yayi mata alama ta zo.
Wani irin kallo ta ke bin Siya da shi wanda har sai da tsargu,granny tace "ki tafi da ita É—akin ki"a nan take tace Siya ba za ta shigar mata É—aki ba tana gama faÉ—a ta wuce É—akinta.
Ƙarƙashin gado ta duƙa ta jawo kwanonta na maita,sosai yawunta suka biya da kurwa Siya tunanin yadda za ta tsotse mata jini ta ke amman ta rasa daga ina za ta fara.
Granny ta koma gun aikinta Papi ya ja hannun Siya zuwa wani ɗaki da ya ke share tsaf sai dai babu komi ciki sai ƙaton akwati irin wanda ake sa kaya,tabarma da matala une place ya shimfiɗa mata.
Cike murna da yaba karamci irin na Æ´an gidan Siya ta kwanta ta na jin wani barci na É—ibarta,Papi tsohon maye kuma É—an iska baki ya ke lasa ya na shafar al'aurar shi ya rasa daga ciki wane zai yi Zina koko canye Kurwa?a haka dai ya fita dan bai son saurin nuna halin shi.

Wani irin tururi ne da masifar zafi ke tsatsafowa ya na fasar simintin É—akin wanda hakan ya haifar mata da yin zufa sharka duk da AC a É—akin amman gumin da ke ketowa ya mamaye sanyin.
A wahalce Siya ta farka saboda azabar zafi ji ta ke tamkar an saka ta cikin magasar burodi,gumin goshinta ta goge ta na sauke numfashi kamar wacce tayi tsere.Yadda ya simintin ɗakin ya ke yi mata gizo ya sa ta jin tsoro,tamkar toka haka ta ke ganin shi ga wani hayaƙi da ya ke fitowa,ta na ƙoƙarin tashi sai taji kamar ana magana ta cikin ƙarƙashin ƙasa.
Kunnenta ta kara ai kuwa magana ake sai dai muryoyin ba su fita sosai,cike da mamaki "to ko dai akwai wasu mutanen a cikin gidan bayan uwanda na gani?ƙila akwai wasu tunda ga hirar su nan ina ji"ta faɗa a zuci ta na mai fita waje haka kawai taji ta na son sanin iya adadin mutanen gidan,da ta fito waje ba ta ga wata ƙofa ba da zai nuna akwai wani ɗaki bayan wanda su ke ciki da tunanin abun ta nufi ƙaton piscine ɗin da ta gani tun farkon shigowa.

Tsaye tayi bakin ruwan ta na ganin hoton ta a ciki,hannu ta saka da niyyar ɗebowa sai ji tayi an ruƙo hannunta,ta saki ƴar ƙara tare da saurin ciro shi da ƙarfi fatar hannun har tayi kwalkwali cike da tsoro ta miƙe ta na jin zuciyar ta na bugawa.
Wata bishiya ta tsinkaya ta mangwaro sai dai abinda ya bata mamaki sunayen mutane da ta gani a ko wane mangwaro,ta na nan tsaye Papi ya fito ya tsaya daga baya ya na ƙare mata kallo yawun shi na tsinkewa.
Baby ma fitowa tayi cikin wani yare tace "Papi ka taimaka ka bar min ko da ɗan da ke cikin cikinta ne in ya so kai ka ɗauki uwar"Papi ya kalli Baby yace "Ɗan cikin da ko wata ɗaya bai yi ba shine za ki ce na baki dan dai kin cika mayya"ta ɓata fuska tace "haba Papi kai fah ka ce na haƙura na bar ma da yanzu tun tuni har na gama da ita,am yanzu abinda za'a yi bari za mu yi har ta haifo ɗan sai na ɗauka kaji Papi?"kai kawai ya jinjina mata ya fara takawa zuwa gun Siya wacce ke tsaye ta na ta aikin karatu,sunan mutum guda ne ya banbanta da na sauran ta na cikin tunani taji muryar Papi na cewa "mi kike yi yarinya?"juyowa tayi da fara'a ta nuna mashi Mango ɗin alamun ta na so sai dai ƙayar da aka zuzuba gun ya hanata ƙarasawa.

"Wannan ba na sha ba ne tawo ciki sai baby ta kawo maki nunanu masu daÉ—i da sanyi"ya faÉ—a ya na mai jawota suka nufi ciki,a falo suka zauna Baby ta kawo mata kayan marmari dayawa cike da murna Siya ke cin kayan ta yayinda Papi da baby suka sakata a gaba suna kallo.

William ne zaune abun duniya sun sha mashi kai , system ɗin shi ya ɗauko tare da buɗe saƙon da Khan ya turo mashi ta email.

```Prety ita ce budurwar Danee ya sun yi soyayya shan minti lokacin suna karatu inda ta samu ciki ta haifi Abbas wanda ya kasance rayuwar Oga Danee duk duniya babu abinda Danee ya fi so kamar Abbas na biyun shi kuma Prety ce wacce tuni tayi aure ya fi goma duk mijin da ta aura Danee sai ya kashe shi inda a ƙarshe ta haƙura ta dawo suna zaman dadiro ita da Danee.Abbas na da mashayar giya tafi goma inda a ko wane gida ya zuba ƴan matan da ya ke hutawa da su,sai dai gidan shi guda ne tal ya na can a unguwar bowa duk jerin gidajen na shi ya fi kowane kyawu da tsaruwa``` wane shine cikakken bayanin da abokin William ya turo mashi tare da hoton shi Abbas ɗin,rufe system ɗin yayi ya shiga toilet ya yo wanka ya shirya ya shirya cikin wata fuskar shi ta sirri.
Mota ya É—auka bai zarce ko ina ba sai unguwar bowa,da kallo ya ke bin gidajen da kallo har ya samu nasarar ganin wanda zuciyar shi ke raya mashi na Abbas ne.
Horne yayi mai gadi ya buɗe mashi get tare da ƙarewa William kallo ta jikin madubin,ba sai ya tsaya tambayar shi wanene ba shigar shi kawai ta tabbatar da *ƊAN DABA* ne irin yadda ya zuba zabba ga uwar sarƙar wuyan shi kuma rigar jikin shi mai ƙananun hannu ce.

Ƙawayen yaran Abbas suka yiwa motar William ganin baƙuwar fuska,cike da gadara ya fito daga mota ya cire baƙin gilashin fuskar shi ya ɗaga gira yace "ya ko za ku dake ni ne?"yadda yayi maganar cikin murya basawa yasa su ja da baya ɗaya daga cikin su yace "Barka da zuwa Oga sai dai kayi haƙuri Boss na cikin fushi wata yarinya ya ƙwamuso bai kai ga shan romo ba ta gudu yanzu haka Boss ya bar gidan ya tafi mashaya bayan yayi mana sanbaɗebaɗ..."bai ida rufe baki ba William yayi mashi wata kumbutsar tsiya a baki a take haƙoran shi rabi suka zube.
Jinin sauran ne ya koma ga akaifa suka bashi haƙuri, "a wace mashayar ya tafi?"wani daga cikin su ya matso yace "Oga mu tafi na kai ka"mota suka shiga ya kai William mashayar da Abbas ya fi so ai kuwa tun daga nesa suka tsinkayo shi zaune a kujera ƴan mata sun zagaye shi ga kwalaban giya a gaban shi.
William na zuwa bai yi wata-wata ba ya kashe Abbas da mari tare da naushi duk wanda ya zo tare mashi haka William ke mazgar shi a ƙarshe ya cakumo wuyan Abbas ya tura shi mota tare da yi mata key......

Comment and share Please🙏🏻

Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story

``` _MRS SADAUKI_ 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM

*QUEEN OF THE MONTH*👸🏻🥳

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.