an Daba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 23
*PAGE 33-34*
Sai da ya maida Leemat hotel suka ci abinci sannan ya wuce gun Oga Danee wanda ya aiko mota har hôtel aka zo aka ɗauke shi.
Da isar su suka tarar da Oga Danee a farfajiyar gidan zaune kan kujera ta alfarma Æ´an mata duk sun zagaye shi,kallo guda za ka yi mashi ka gane uban daba ne.
Murmurshi kan fuskar shi ya ke kallon Dawood ya na mai son karantar zuciyar shi sai ruf ta ke a liƙe bai ganin komi tamkar dai ta William.
Gun zama aka bashi tare da tura mashi hotunan Abbas "aiki biyu za ka yi nemo min Ɗana sai kuma kashe wani gwaggon biri mai taurin kai sai dai kafin nan ina son yayi maka cikaken bayani na inda ya aje *littafin sihirin* da ya wallafa"amsar hoton Abbas ɗin yayi ya duba sai kuma ya saka shi cikin rigar aljihu yace "yaushe aka ɗauke shi ?su waye aboka nan shi?wane wurare ya fiya zuwa?"Oga Danee ya miƙe tsaye yace " aikin banza duk ƙarfin sihirin da ke jikin ka ba zai yi maka aiki ba ne ?ko ba ka yi wanka da ruwan ba ne?"Oga Danee na gama faɗar haka jikin Dawood ya shiga karkarwa jijiyoyin kan shi duk suka fito raɗo-raɗo yayinda idon shi suka fara sauyawa zuwa wasu kala tamkar na zaki.
Cikin muryar basawa Dawood yace "an gama ƴallaɓai am ina son rakiyar wani"murmushi Oga Danee yayi ya ɗaga waya ya kira William cikin ƙanƙanan lokaci ya zo.
Gun da Dawood ke zaune ya sunne kai Oga Danee ya nuna yace "wannan za ka yiwa rakiya daga yau ka zamo abokin shi na aiki na san ba ƙaramin citta abun zai bada ba domin kuwa zuciyoyin ku duk a rufe su ke na san kau wannan karon zan yi nasara hhh".
Tun daga ƙafafun shi wanda suke cikin takalmi har izuwa kan shi da ke sunne William ya ke bin shi da kallo bai san ko miyasa ba ya ke jin faɗuwar gaba.
A ɓangaren Dawood ma haka ta ke,bugun zuciyar shi ne ke ƙaruwa yayinda kwanyar shi ke tariyo mashi wasu abubuwa tun na ƙurciyar shi.
"Dawood ga William babban yarona ne zai yi maka duk abinda kake buƙata,am William wannan shine babban yaron Oga Darma "murmurshin yaƙe William yayi ya na jin zuciyar na ƙara wuntsilawa saboda ambatar sunan Dawood da aka yi,daidaita nutsuwar shi yayi yace "Barka da zuwa garin Moumbay Boss da fatan za ka ji daɗin kasancewa a nan har ka gama aikin da ya kawo ka?"ɗagowa Dawood yayi ya zubawa William ido bai ce komi ba sai tashi da yayi ya mashi nuni da ya biyo bayan shi.
"Bi bayan shi ka gwada mashi gari sannan ka danne zuciyar ka dama Oga Darma yace haka ya ke da shegen jiji da kai da izza sai kace shine *ÆŠAN DABA* na farko"Oga Danee ya faÉ—a ya na kallon William da ya bi Dawood da ido,jinjina kai William yayi ya bi bayan shi.
Babur É—in da William ya zo bisan shi Dawood ya ja ya tsaya ya na mai jin haushin katse mashi tunani da William yayi.
A gaba William ya hau ya na mai tada babur É—in, Dawood ya hau ya na mai cewa "ina son ka kai ni gidan babban malamin Æ´an siddabaru na nan garin"dafa.
Madubin babur É—in William ya gyara ta yadda zai ganin Dawood da kyau saboda yadda zuciyar shi ke raya mashi wani abu na daban,suna tsaka da tafiya William ya É—an tsaya yace "gidan malamin siddabaru na nan Moumbay koko na India?"cike da jin haushi Dawood yace "ita Moumbay É—in cikin wane gari ta ke in ba India ba?kaji wani shashanci"William ya É—an murmusa yace "ai duk da haka yankin Kulkata shi mutane suka fi kira da India kasancewar nan É—in Capital ne"banza Dawood yayi da shi tamkar bai ji shi ba.
Ta miror ya ke ƙare mashi kallo kamannin Daddy ne sak suka bayyana a fuskar sabon *ƊAN DABAR* da ya kasance baƙo a gare su,amman inda Dawood ɗin mu ne ta yaya aka yi bai gane ni ba?kuma fah ba lalle ya gane ni ba tunda tun ina ɗan yaro marabin shi da ni,to amman miyasa bai nemi iyayen mu ba?tabbas akwai lauje cikin naɗi doli akwai wani abun na daban ga shi rufafiyar zuciya gare shi balle na gano wani abu"William ke maganar zuci ya na kallon Dawood ta miror wanda shi ma shi ɗin ya ke kallo.
"In ka gama tunanin mu je ka sauke ni hotel tunda na ga alama ba ka san aikin ka ba"cewar Dawood ya na duba agogon hannun shi,cigaba da tuƙin William ya yi ya kai shi gidan mai siddabaru sai dai cikin rashin Sa'a nan aka shaida masu rasuwar shi.
A bisa hanya Dawood ya tambayi William"a ina ne hanyar madafur?"wani uban burki William yayi babu shiri yace "mi za ka yi a can?"Dawood ya tanke fuska yace "a can Abbas ya ke cikin wani gidan gona dan haka kai ni za ka yi ka tawo min da shi"wani irin ƙwarewa William yayi yace "ya aka yi ka sani?"amsa ya bashi da "ƙarfin iko ne da sihiri"ba dan William ya so ba haka ya kai Dawood unguwar ba tare da ya yarda ya kai shi har ƙofar gidan ba.
Makulin gidan ya taɓe tare da shiga cikin gidan ba'a jima ba ya fito da Abbas wanda duk ya galabaita,a tsakiya suka sa shi suka wuce gidan Oga Danee.
Kawo Abbas ba ƙaramin ƙarawa Dawood matsayi ya yi ba a zuciyar Danee,cike da murna ya kira Oga Darma ya shaida mashi aiki yayi kyau da alamu kuma lokacin cin nasara ne yayi, Oga Darma yace "Ni na gaya maka yarona babban *ƊAN DABA* ne kuma mai sa'a yanzu abinda za'a yi nima zan zo Moumbay ɗin ina jiran wani abu ne da ya kammala za ka gan ni "
"To Allah kawo ka lafiya sai dai kar ka manta da ajiyata ya kamata ka ɗaukota saboda bai fi kwana goma ba shekarun BIRTHDAY ɗin za su cika"cewar Oga Danee,cike da dariyar mugunta Oga Darma yace "kar ka damu ka ƙaddara ma yanzu haka ta na garin Moumbay har an kawar da budurci buri ya kusa cika hhh" kasancewar Danee wawa ne sam bai gane komi ba sai sallama da yayi mashi.
Ya aje waya yace "William kai Boss masaukin shi sannan ka dawo akwai plan É—in da za mu shirya kafin zuwan Darma am Dawood ka tabbatar da ka bincike shi da kyau"kai Dawood ya jinjina.
Har cikin farfajiyar hotel ɗin William ya shiga da shi,haka kawai Dawood ya ji ya na son ƙulla alaƙa da William har ya juya babur yace "am ka shigo daga ciki ka ga inda na sauka"cike da murna ya bi bayan shi knowking yayi Leemat ta buɗe ɗakin ta waro ido ganin baƙuwar fuska,gaban William ya bada dam a zuci yace "mi ya kawo leemat nan kuma?miye alaƙarta da shi?".
"Ka ga inda na sauka nan al gobe ka zo tun da wuri sai mu wuce tare"kai kawai William ya jinjina yayi saurin fitowa.
Ko da ya shigo gida bai tsaya komi ba ya wuce cikin ɗakin shi,book ɗin sirrin shi ya ɗauko ya shiga bincike har ya kawo wata page inda aka rubuta *ƘADDARA ZUKATA BIYU* (My next book in shaa Allah).
```Yadda ƙaddarar ka da Siya ke manne da juna haka ma ta ɗan uwanka Dawood za ta kasance da ta ƴar uwar Siya, wannan ƙaddarorin sune nasarar mu da farko haɗuwar kowanen ku da ɗan uwan shi,na biyu ku ɗin garkuwar juna ne,na uku ta hanyar Dawood farin cikin ka zai dawo``` tsayawa yayi ya shiga nanata "farin cikina zai dawo,farin cikina zai dawo to kamar yaya fah ban gane ba?"da yaji kan shi ya ɗau zafi kawai ya shige toilet ya sakarwa kan shi shower.
Da ya fito daga wanka falo ya wuce inda Maman ke zaune ta na cin abinci, kissing yayi mata a goshi ya saka hannun shi suna ci tare.
Kallon Miki yayi wacce ta kasa zaune sai zirganiya ta ke,tashi yayi yace "Maman ina gani fah kamar naƙuda ta ke"Maman ma ta fidda hannunta ta ƙarasa gun Miki wacce ta fara kuka zuwa wannan lokacin kuma alamun haihuwa sun bayyana,ba tare da sun kimtsa ba kan baby ya fara fitowa Maman da yau ne karonta na farko ta fara karɓar haihuwa kusan rikicewa tayi.
Kafin wani lokaci yaro ya faÉ—o tare da cibiya,komi na shi sak irin na mutane suna tsaka da gyara shi Miki ta fara wata birgima a sannu surarta ta fara sauyawa zuwa ta mutum har ta dawo farar mace bafultana, atishawa ta shiga yi ta na mai duban su Maman da su ma ita su ke kallo .
"sannu Madam"cewar William ya na mai sakar mata murmurshi,sharrr hawaye ke zuba kan fuskarta ta na mai kallon Michel da ke habshi.
Gefen da ta ke kallo William ya duba ya na mai cewa "Michel !"matsowa yayi ya na mai zagayen William,murya na É—an rawa tace "shi É—in mijina,a da mun kasance cikin farin ciki da rayuwa mai daÉ—i sai dai shigowar Dauda(Danee)ya rusa shi"zama William ya gyara yace "ta yaya kenan?ko zan iya sanin dangantakar ku da Danee?"
```Dauda da Auwal ƙane da magaji ne sun taso cikin maraici sai dai dukiyar da iyayensu suka bar masu ya sa ba su wani sha wahala ba, dukkanin su sun kasance masu son kuɗin tsiya babu ma kamar Dauda domin shi ya na karatu ne ya na gamawa da kasuwanci.Ban san abinda ya gama su da Auwal ba kawai dai na ga ya na fushi da yayan nashi kasancewar lokacin da ya koma India da zama ya kan zo mana musamman lokacin da na haifi Siya wacce ya ke so sosai dan har India ya taɓa zuwa da ita tayi wasu shekaru a can,da farko nayi tunanin larurar da ta samu Siya ce ta makanta a dalilin Dauda yasa suka samun saɓanin sai daga baya ne na gane akwai wani ɓoyayyen sirri da bai son in sani.
Sosai na sa mashi ido a nan na gano wani abu ta hanyar fifita Siya da ya ke a kan ƴar uwarta Leemat,ya kan yi abubuwa dan ganin farin cikin Siya inda kusan kullum ya kan ce "gwara kiji daɗin ki tun yanzu kafin lokaci yayi"a ƙarshe kuma ya zubar da hawaye.Ranar wata Laraba da ba zan taɓa mantawa ba Dauda ya ziyarce mu a ɗakin baƙi suka keɓe ni ban san abinda suka tattauna ba kawai dai na ga ya fito ya na murmurshi sai kuma ya ɗauki su Leemat wai za su je shopping,fitar su ke da wuya na ji ihun Auwal da gudu na nufi ciki sai dai mi?birkiɗa na tarar ya na yi yayinda bidin kare ya bayyana ta bayan shi.Cikin soyayya irin ta mata da miji na nufe shi na rungume duk da tsayar da ni da ya ke kar in ƙaraso amman ina tuni na jawo mijina wanda taɓa shi ke da wuya naji wani ƙaiƙayi duk jikina,gefe na koma ina susar jiki a gaban idona Auwal ya rikiɗe ya koma kare kafin nima na halittata ta fara sauyawa zuwa wannan lokacin Dauda ya dawo gefe ya koma ya na ƙyarƙyatar dariya ya na cewa "da kyau!da kyau ke uwar karanbani kika taɓa shi ke mai miji"daga nan na ida zama karya``` ta na kawowa daidai nan ta fashe da kuka.
William ya fassarawa Maman duk abinda ta ce tunda ita ba Hausa ta ke ji ba,ita ma kuka tayi tare da duban William tace "ya kamata kai ka ƙarasa ba mu labarin"William ya girgiza kai yace "Oga Darma ne zai ƙarasa domin shi ya san komi tun daga A har Z gobe ya ke shigowa yace min akwai wani Gift da zai bamu ni da ke sai tun kafin ya bani tuni na gano miye"ya ida maganar ya na murmushi.
Kamar kullum yau ma Siya sai da ta baiwa wannan tsohon ruwa ya sha,sai dai abun mamaki sunanta da taji ya ambata daga can ƙasan maƙoshi.Baki na rawa tace "na'am"sai kuma tayi mamakin buɗewar bakinta hakan yasa tace "tsoho ka na ji na?"kai ya ɗaga mata yace "ina jin ki Siya,gaya min ina ne aka aje kambun sarautar matsafan👑 duniya?"da sauri Siya ta rufe idonta tare da dafe kanta da ya fara sara mata.
```wata yarinya ce ƴar ƙarama wacce ba za ta wuce shekara biyar ba,zaune ta ke cikin wata roba wacce ta ke maƙil da jini wanda ya rufe dukan jikinta kanta kawai ake gani.Wani baƙin aljani ne mai dogon gashi ya ke zagayarta ɗan ƙaramin kaskon huta na hannun shi ya na zuba wani garin magani,yayi hakan kusan minti talatin sannan ya tsamota daga cikin jinin ya zuba wani gari cikin huta ya tsugunar da ita hayaƙin na shigarta.Ya na nasata cikin wasu ruwa farare ƙal duk ta kakafe waje guda,cirota yayi ya kaita gaban wani madubi wani haske ne ke fitowa ya na shiga idonta kusan awa guda kenan sannan ya janye ta daga nan kuma ganinta ya ɗauke ba ta ƙara sanin komi ba sai jin murya kawunta ya na cewa "Siya ki na gani na?" "A'a kawu ina dai jin muryar ka"kanta ya shafa yace "isa ok bari yanzu za mu koma gida kin ji ko?"kai ta gyaɗa cikin bagwariyar Hausarta tace "ina Leemat?"yace "ta na gun Mami ɗin ku yanzu za mu wuce jirgi za mu shiga na mayar da ke cin iyayen ki"Siya ba ce komi har suka shiga jirgin ya sauke su a Niger.``` ta na kawowa nan ta buɗe ido cike da furgici ta na kallon tsohon da yasa ta tuna wani ɓangare na labarnta na yarinta, murmushi tsoho yayi yace "ina kambun sarautar ya ke kin tuna?"girgiza kai tayi ta dafe can bayan ƙeya nan ta shiga wani babin tunani.
```Danee bai zarce da su Siya ko ina ba sai gidan da ya saye na Niger ,cikin ƙanƙanin lokaci ya kira yaron shi Darma akan ya na son ya samo mashi matar da za ta aure shi gobe-goben nan ba'a ɗau lokaci ba Darma ya gama shi da Baratu wacce iyayenta suka ce je ki ƙya gani,tamkar wasa yara aka ɗaura auren su da sharaɗin za ta riƙe mashi Yaren shi ta kuwa amince ta riƙe su Siya.Shekarar farko da auren su ta haifi Jasmine,a shekara ta biyu ta haifi Laila nan kuwa ta fara nuna banbanci,inda tun suna yara Leemat ke kula da Siya tun daga wanka wankin kayanta da sauran su.Lokacin da suka fara girma ne Leemat ta ankare da wani abu,shine duk lokacin da Danee ya zo Niger ya na baiwa Siya wani abu ta ci ita kaɗai shiyasa ta fara ƙoƙarin bugun cikin Siya amman ko tayi niyya faɗa mata sai ta kasa.Jasmine da Laila sun kasance ƴan gaban goshin Mami yayinda Leemat da Siya kullum su na ɗaki duk da dai suna nuna soyayyar ƙarya ga Siya kasancewarta makauniya.``` wani liquide ne ya shiga zubowa daga idon Siya ya na ɗiga cikin ragar da tsoho ya ke ciki,da sauri ya tara hannun shi liquide ɗin na zuba a tafin hannun shi sai da hannun ya cika ya shanye daga ƙarshe ya tsaya ruwan na ɗiga a jikin shi,tamkar wanda aka saka cikin injin haka jikin shi ya shiga wawalniya ya na haske yayinda Siya ta koma gefe ta na fidda numfashi,wani irin ƙishi ta ke ji da sauri ta mayar da akwatin ta shiga toilet ta buɗe pampon ta shiga shan ruwa kamar ba gobe.
***
Gonar shi ta gado ya sayar ya haɗawa Laila kayan lefe wanda aka yanke ɗaura masu aure ranar juma'a inda Liman ɗin garin su zai zama waliyinta,Asabe ba ta san wainar da ake toyawa ba ta na gudanar da mulki da isa akan abinda ya ke haƙin shi.Duk in zai kusance ta sai ya bata kuɗi ko ya sawo mata balangu wanda za ta ci ta ƙoshi a hakan kuma wani sa'in ture shi ta ke tun kafin ya gamsu,Muntari bawan Allah haka ya ke bin ta sau da ƙafa dan dai kawai a zauna lafiya.
Laila ce zaune ita ɗaya tayi zugum tana tunanin gida wanda shine karon farko da ta tuna su,ko dan gobe ne za'a ɗaura mata aure?oho kawai dai taji babu daɗi ta so ayi bikinta irin na ƴan ganta sai ya ta iya da ƙaddarar ta?Doli tayi haƙuri.
Wani tsoro ne ya kamata irin wanda kusan duk amarya tayi shi,tunanin yadda first night ɗin su zai kasance kai ta girgiza a zuci tace "kaiii ina ba ma zai kusance ni ba a yadda ni ke ƴar ƙarama ya na babba tausayina zai ji sai na ƙara girma"da wannan tunanin ta yakice fargabai.......
Comment and share Please
Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story
``` _MRS SADAUKI_ 💫
*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰
â˜€ï¸ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀ï¸
____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇ðŸ½
*500MB* 200
*1GB* 300
*2GB* 600
*3GB* 900
*6GB* 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.