an Daba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 14 of 23
Page 29-30
Shiga motar tayi wacce ita kanta ba ta san inda za'a kaita ba,mota na cika suka ɓaga zuwa Dakoro ana kawowa kowa ya fita banda Laila wacce ke rabar ido.
Muntari na dawowa daga sayen abinci ya yiwa motar shi key ya nufi gida ba tare da yayi la'akari da Laila da ke can ƙarshen mota,"tsaya min"ya ji muryarta lokacin da ya ya kashe mota ya na ƙoƙarin sauka.Ya waro ido cike da mamaki sai da ta fita sannan yace "wacece ke?miyasa ba ki sauka tun atasha ba?"hawaye sharrr suka zubowa Laila tace "ni marainiya ce ban san kowa ba gidan da ni ke aiki kuma suka koro ni dan Allah ka taimaka na zauna gidan ka"tunda ta fara magana Muntari ya ke kallonta har ta kai Aya,ajiyar zuciya ya sauke ya na mai nunata mata cikin gidan shi wanda ya ke na laka an yi mashi yaɓe.Ta shiga sallama ɗauke da bakinta Inna kawai ta amsa yayinda Asabe ke binta da wani kallo,gaishe su tayi Inna ta amsa cikin fara'ar ta wa ta ke nema?bayanta ta waiga sai ga Muntari ya shigo yace "Inna tare mu ke da ita ai"cikin sakin fuska Inna ta nuna mata gefen tabarma tace "zauna yarinya ya gajiya?"Laila ta zauna tace "alhamdullah Inna"ta na mai aje ƴar ƙaramar trollynta.
Aje wankin da ta ke tayi ta bi bayan Muntari da ya shiga É—aki "ban gane tare kuke ba?wacece ita?"Asabe ke faÉ—a cikin É—aga murya har su Laila da ke waje suna ji,cikin tausasa murya yace "haba Asabe yanzu ko sannu da zuwa ba ki yi min sai masifa?to ban sani ba ki zura ido ki kalle ta tunda ba bisa kan ki ta ke ba"ya ida maganar a hasale saboda sam a rayuwa Asabe ba ta da wani uzuri ga É—an karan nace ga shi ba ta ganin girman shi.
Fita yayi waje sai ya tarar tuni Inna ta zuba mashi ruwan waka ta kai mashi bakin banÉ—aki,ya shiga ya yo wanka sannan ya samu kujera ya zauna.
Ludayi Inna ta miƙa mashi sai ya saka shi cikin furar da Laila ke sha,duk da kasancewar ta ƴar birni sai da taji kunya saboda duk talaucin Muntari bai ɓoye ƙwar jinin shi duk da dai bai da wasu shekaru dayawa dan ba zai wuce 43years ba.Haka suka dinga shan furar har Laila ta aje ludayin ta ya kalleta yace "har ta ishe ki haka?"ta ɗaga kai tace "ai na sha sosai"Inna tayi murmushi tace "to tashi ki ɗauko alala cikin ɗaki sai ku ci duk da ba wani yawa gare ta ba yau kam na samu ciniki"babu muso taje ta ɗauko ta wanke hannunta suka faraci daman ta na son alala,suna ci hannun su na haɗu ita Laila sam ba ta damu da hakan ba Muntari dai ne ya ke jin wani iri ganin ta na son alala ne ya fidda nashi ba dan ta ishe shi ba.
Alwala yayi domin tafiya sallah asar haka ma Inna da Laila suka yi, Asabe kuwa ta na can ɗaki baƙin halinta ya hanata fitowa.
Ƙarfe biyar nayi Inna ta ɗora tukunyar tuwo Laila na daga gefenta ta na ɓanɓarar tafarnuwa dan kuwa tace ita za ta yi miya,tamkar sun saba haka su ke ta firar su ita da Inna wacce ke tankaɗe gari.
Wani murhun Laila ta sawa itace ta É—ora miya,a haka har suka gama komi kafin magrib nan Laila ta shiga wanka ta canza kaya.
Har É—aki Inna ta kaiwa Asabe tuwonta sannan ta zuba miya ita da Laila suka ci suka yi nar, Muntari da ya shigo É—akin matar shi ya wuce ya ci nashi.
"Sake ni Muntari,ka sake ni kar na tara maka mutane"Asabe ta faɗa ta na fizge zanen ta da ke hannun shi,cikin rarrashi yace "ki yi haƙuri ki bar ni in yi dan Allah,Asabe haƙina ne fah kar Mala'ikun Allah su la'ance ki"ya na maganar ne ya na ƙoƙarin jan ɗan tohinta (sket ɗin nan wanda ake sakawa daga ciki) "su yi ta tsine min ɗin amman wlh yau ba za ka ko gan shi balle ka..."saurin janyota yayi zuwa jikin shi ai ko ta fasa ƙara da sauri ya saketa tare da sauka kan gadon ƙarfen ya na jin wata masifafar sha'awa na taso mashi amman babu halin kawar da ita,zagayen ɗakin ya fara kamar mai zikiri ya rasa ya zai yi da ran shi bai san miyasa a ko da yaushe in sun samu matsala da Asabe ta ke mashi hukuncin hana mashi kanta.Duk abinda ya ke ta na kallon shi ƙasan ranta kuwa fal farin ciki ko ba komi ta gulala mashi sannan za ta huta tayi kwana ba tare da ciwon jiki ba.
Washegari Muntari ya tashi da wani ciwon mara idon shi sun jawur kamar wanda aka sawa barkono,a haka ya daure ya zo ya gaishe da Inna wacce ta ke yi mashi kallon tsaf dan jiya ƙarar da Asabe tayi sun ji ita da Laila dan dare suka raba suna hira.
Cike da tausayawa ta kalli Murtala tace "ba tun yau na ce ka sake yin aure ba amman ka ƙi,saboda Allah rayuwa tayi haka?yanzu shekara ku biyar da aure amman har yanzu babu canji dangane da lafiyar ka tsabar baƙin ciki kuma ta sha maganin hana haihuwa dan kar ta haihu da kai amman kai uban naci ka liƙe mata"sunne kai Murtala yayi cike da kunya,dan shi har ga Allah kunya ya ke ji tun ranar da aka gano ƙarfin sha'awar shi ne ya ke yawan sa shi ciwon mara dan har sai da aka yi mashi opération to nan ne fah aka haɗa su auren gida da Asabe dama shi tun farko ya na sonta ita ce dai ba ta son shi dan ita burinta auren mai kuɗi ne gaban ta.
"Inna ba auren ba ina zan saka matar ?sannan kuma ni banda budurwa"Inna ta gyara zama ta na murmurshi jin ya dai yarda zai ƙara auren tace "ba ga Laila nan ba"yace "wace kuma haka?"Inna tace "wacce ka zo da ita jiya"Muntari yace "haba Inna ni da ban santa ba kawai daga ganin ta jiya sai aure?".
"To minene?jiya sai da ta bani labarin ta kaf babu wanda ta rage min a ƙarshe tace in dai kuma mu ka ce sai mun maidata kashe kanta za tayi dan haka kawai ka aureta"nan Inna ta bashi labarin Laila a taƙaice kamar yadda ta gaya mata.
Murtala yace "to ki na ganin za ta iya aure na?"Inna tace "mi zai hana kuwa tunda ita dai mijin aure ta ke nema ta samarwa rayuwarta inganci"Murtala na shirin magana Laila ta shigo da sallama "ina kwana Yaya?"sai da ya ɗan ƙare mata kallo ya amsa,a shagwaɓe ta zauna kusa da Inna tace "layi na iske sosai kingin kaɗan nayi zuciya na dawo"dariya duk suka yi mata ta juye wainar cikin kwano.
***
Dariya yayi yace "wai wannan zumɓurar bakin duk na miye?"ta sake turo baki tace "ya lalace ne shiyasa nike yi mashi haka ko ya sha iska ya dawo daidai"ya harareta yace "kuma shine kike magana raɗau haka?"ta miƙe tace "tunda kuwa Allah ya tsaga shi"ƙafa ya sa ya taɗeta ta faɗi ƙasa, dariya ƙeta ya shiga yi har da riƙe ciki ya na nunata ita kuwa shagala tayi da kallon shi a zuci ta ke tambaya "dama ya na dariya har haka?"ya ɗaga gira yace "mi kike kallo?"ba ta bashi amsar shi ba sai miƙewa tayi ta zauna kusa da shi tace "yi dariya in gani " "ga taɓaɓe ko?ni mahaukaci sai yin ta dariya ki na kallo"ta marairaice fuska tace "please Dawooddd kawai dimple ɗin ka ni ke son gani"yanayin yadda ta kira sunan sai da ya tsaki zuciyar shi ya riƙo hannun ta yace "wa ya gaya maki sunana?"ƙyafƙyaf da ido ta yi tare da girgiza kai tace "kai ne ko?"yace "a'a ba ni ne ba""to Maye ne ken..."buge mata baki yayi yace "ba na hanaki faɗin sunan shi ba?kin raina ni ko?"yayi maganar ya na tanke fuska ya dawo ainahin *ƊAN DABA* tsoro ne ya kama Leemat jin hatta sautin bugun zuciyar shi ya sauya tsabar ɓacin rai.
Hannunta da ya riƙe ya na wani murzar shi tayi ƙoƙarin janyewa amman ya riƙe shi sosai ya na gana mashi azaba,hawaye na yi mata zuba tace "kayi haƙuri ka sake min hannu zan koma part ɗin mata"saketa yayi ta miƙe tare da ɗaukar hijab ta fita.....
Comment and share Please
Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story
``` _MRS SADAUKI_ 💫
*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰
â˜€ï¸ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀ï¸
____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
*QUEEN OF THE MONTH*👸ðŸ»ðŸ¥³
*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇ðŸ½
*500MB* 200
*1GB* 300
*2GB* 600
*3GB* 900
*6GB* 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.