an Daba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: an_Daba_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 23
*PAGE 37-38*
Cike da mamaki Dawood yace "Oga dama yau ne za ka zo?na zata sai nan gaba dan naji kace kamar ka na wani abu mai muhimmanci ne"murmurshi Oga Darma yayi wanda Dawood zai iya cewa "yau ne karon farko da ya gan a kan fuskar uban gidan nashi,bai bashi amsar tambayar tashi ba sai cewa "ina ita Leemat ɗin?"ya na maganar tare da shiga gidan yayinda William ya zauna seat ɗin draber, Dawood shanye da mamaki ya shiga baya ya na mai tambayar shi ko dai kunnuwan shi ba su jiyo mashi daidai ba?amman kuma kamar ya ji ya ambaci sunan Leemat?to ta yaya ya san a tare suka zo yaushe ma ya santa? Dawood bai yanke da lamarin ba sai da ya ga sun nufi hotel suna tsayawa Oga Darma yace "yi sauri kaje ku tawo tare sauri mu ke"babu muso Dawood ya fita,zuciyar shi na das..das.das haka ya nufi ɗakin.A kwance ya tarar da ita tsakiyar gado daga ita sai towel da alamun wani wankan ta sake bayan fitar shi,surar jikinta ya fara ƙarewa kallo Leemat kuwa jin ƙara buɗe ɗaki da shigowa kuma taji shiru shiyasa tayi shiru hakan ya sa ta juyo,ɗan turo baki ta na mai tashi ya taɓe baki ya nufi wadrob ya ɗauko mata wata rigar shi ya saka mata da kan shi sannan ya shafa mata mai da turare.
Mayafi ɗan ƙarami na riga ya yana mata a kai ai kuwa Leemat tace ba ta san wannan ba ita ba za ta fita a haka ba,gira ƙasa da ta sama ya game ya na shirin yi mata magana ya ƙara jin wani kiran ya shigo da sauri ya ja hannunta dan kar ta ɓata mashi lokaci.
Oga Darma da Dawood tuni sun fito daga motar suna shirin shiga ciki dan kuwa Oga Darma ya fi kowa sanin wanene Dawood ya ga damar yayi siddabarun da za su ɓace,cak Leemat ta tsaya ta na kallonsu su ɗin ma ita su ke kallo da sauri ta koma bayan Dawood ta laɓe jiki na karkarwa hannunta ɗaya kan kafaɗar shi ɗaya kuma ga ciki.
Cikin murya mai cike da furgici tace "Alhajin Abba ?wlh *ÆŠAN DABA* ne kar ka matsa kusa da shi shan jini ya ke kum kuma munafuki ne"Leemat ke faÉ—a ta na kuka, murmurshi Oga Darma yayi dan dama ya san za'a rina.
Cikin mota ya koma ya na kallon yadda Dawood ke tambayarta tare rarrashinta dakyal ta bi bayan shi suka shiga mota William yayi mata key ba su zarce ko ina ba sai gidan su.
Ta ƙanƙame Dawood ta na mai fashewa da kuka,"yi shiru mana kin san dai in ina nan ga guri ba zan bari ya cutar da ke ba ko?"kai ta gyaɗa tare da tashi daga kan ƙirjin shi suka fito inda su William ke tsaye suna jiran su suka taka.
A falo suka tarar da Maman gefenta Momy ce ta na shayar da bbynta,duk waje suka samu suka zauna bayan sun gaisa ne Oga Darma ya gyara zama.
```Shekarun baya da suka wuce mu uku mun kasance manya abokaina,tun a makaranta Danee ya kasance mai son fifiko da nuna mana izza ba mu ɗauki komi ba mu ka rinƙa bin shi sau da ƙafa.Mu ukun nan mun kasance kowanenmu na da buri,Ni siyasa ni ke so na zama shugaba,Danee kuma mai son faɗa a aji a rinƙa tsoron shi duk duniya ta san shi yayinda Daddyn ku (cewa da su William)ke son zama shugaban ƴan dramer da siddabaru.Da mu ka zauna mu ka yi lissafi kuwa sai mu ka gane doli ko wane buri sai da kuɗi zai cika duk da dai mu na da kuɗi bakin gwagwardo,ba'a wani ɗau lokaci ba Danee ya kawo mana wata proposition mu shiga wata ƙungiya ba tare da binciken mi ƙungiyar ta ƙumsa ba mu ka amince nan ya kai mu gun Ogan su.Abu kamar wasa haka kowanenmu cikar burin shi ta fara tafiya kamar yadda ya kamata muna ta jin daɗi ba tare da mun san akwai tashin hankali gaba ba,abinda ƙungiya tace kowa ya bada jinin mutum ɗaya daga cikin ahalin shi to a nan ne fah Daddyn ku ya farga da ƙungiyar asiri ce kasancewar shi musulmi yace Indai sai ya bada jinin wani to daga yau ya fita,hankalin Oga ya tashi saboda ya na matuƙar ji da Ahmad saboda ko wata opération za'a je da salon siddabarun shi ya ke ɓatar da idon jama'a akan mutanen mu wannan ne ya sa ƙungiya tace banda shi tunda dama dai ba kuɗi ake bashi ba kawai ƙarfin iko ne.Ni kuwa Kakata wacce ta riƙe ni na bada, ɓangaren Danee kuwa Ɗa ɗaya tal gare shi sannan Abbas kuma bai ji zai iya bada ɗan uwan shi Auwal ba shine ya bayar da ƴar sa,maƙasudin mayar da ita makauniya daga zuwa Vacance ya sa Auwal bin didigi a ƙarshe ya tonowa kan shi abinda ya fi ƙarfin shi to nan ne fah Danee yayi mashi barazanar mutuwa shi da duk ahalin shi in yace zai tona asiri,bayan wasu ƴan watanni ne ƙungiya ta gano tabbas Auwal in ya na raye komi zai iya faruwa Danee yayi tsalle bisa yace ba za'a kashe mashi ɗan uwa ba nan ne kuwa aka bada shawar mayar da ƙwaƙwalwar shi irin ta kare da farko ɗabi'un shine suka fara sauyawa daga na mutane zuwa dabbobi a ƙarshe kuma Danee ya je har gida ya baɗe shi da wani magani har ya zama kare.Danee na shaida min abinda ya faru naje na ɗauke Michel da Miki na aje su guna ba tare da ya sani ba,matsayin Oga Danee ya ƙaru haka ma ƙarfin tsafin shi to a nan fah alƙalamin tsafin shi ya gano yaron Ahmad ne zai zama sanadin rushewar duk wani mulki na shi,kasancewata na hannun damar shi ya aike ni dan kashe shi a lokacin ya na makarantar India ta koyon tsafi,ban wani sha wuya ba wajen tawo da David saboda malamin ya san ni abokin Ahmad ne tun daga wannan lokacin kuma nayi amfani da tsafina na mantar da Dawood duk wani abu da ya shafi rayuwar shi sannan na sanya mashi a kai ƴan fashi sun tare su kuma ni na cece shi daga nan kuma na cigaba da rainon shi sannan na saka shi makaranta addini gefe guda kuma ana bashi training.Saboda gudun matsala mu ka gama ƙarfi da Danee wajen ɗauke Ahmad mu ka ɓoye shi dan kar ya san an kashe Dawood, dukkanin mu ba mu san ya na da wani ɗa ba sai daga baya ne gane na nemo William inda mu ka fara shirin yaƙar Danee sai na kai mashi William a matsayin ƙwararen *ƊAN DABA* duk da lokacin nan bai daɗe da zama soja ba amman sai yaje da wata fuskar wacce ba tashi ba,cikin ikon Allah Danee ya aminta da shi har ya ke gaya mashi wasu sirrika to a nan ne William ya fara samun labarin Siya ni kuma na bashi labarin komi to fah tun daga nan ne ya kamu da tausayin iyayenta soyayyar ta kuma ta shiga zuciyar shi ba tare da ya sani ba.Michel da Miki suka dawo hannun shi ya cigaba da kula su,a waje guda nayi wasa da hankali William shine aje wani book a matsayin na Daddyn su ne ya aje mashi shi.Ni na tura William gidan Danee na Niger a matsayin almajiri a lokacin kuma tuni an ɗaura igiyar auren su, yayi aikin shi ya samu nasara,daga nan kuma sai na kira Dawood a kan lalle sai sun fita opération duk da ruwan da ake sanin Baratu ba za ta barin Leemat ta zauna gidan ba sai ta nemo Siya to a nan Dawood ya gamu da ita dama tuni na tsara komi Dawood na ganinta ya faɗa soyayyarta.Tun daga zuwan Leemat har abinda ke wakana duk na sani a ranar da mu ka je ma lokacin da ka ɗaga gado na hangeta har sautin ɗan kukan da take duk naji,nayi hakan ne kuma dan gwada jarumtar kariyar ta na ga in za ka iya.``` Oga Darma na kawowa nan ya tsaya ganin kallon da Dawood ke yi mashi ya sa shi yin murmushi,cikin ƴar hassala Dawood yace "to yanzu fah inda ka sa na keta haddin ƴar mutane sai yaya kenan?"Oga Darma yace "sanin halin ka ya sa na aikata hakan kuma ko da kayi yunƙurin ketawar ba za ka iya ba saboda ita kanta Leemat ɗin ba banza na barta ba,ƙaryar mazinaci ya kusanceta sai dai mijinta"numfashi ta sauke wanda har sai da Dawood ya banka mata harara ta turo baki ya buge shi da hannu.
"William ga Gift É—in da nace nan zan kawo maka Dawood shekaru da dama kayi kukan rashin É—an uwanka yau ga shi na maido ma, Dawood wannan É—an uwanka ne uwa É—aya uba É—aya"kuka Maman ta fashe da shi wacce tun É—azu ta ke kallon Dawood É—in saboda kama da mijinta da ya ke, William ya taso ya rungume Dawood ya na hawaye bubuga bayan shi yayi kafin ya je ya rungume Maman ya na sauke wata ajiyar zuciya.
Cikin kuka Leemat tace "ina Siya toh?"Oga Darma ya kalli William nan ya shaida masu komi,ganin Leemat za ta É—aga hankalin ta yasa William gabatar da ita ga Momynta amman bai gaya mata Michel ne Abbanta ba,waro ido tayi ta na kallon Momy wacce ke hawaye game da murmurshi.Gun ta taje ta rungumeta tare da É—aukar bbyn hannunta ta na kallo,su Oga Darma tashi suka yi suka wuce room É—in William dan tsara yadda komi zai kasance cikin tsari kafin kowa ya kama gaban shi inda Leemat migididi tace gun Momynta za ta zauna.
Dawood hôtel ya koma,da dare yayi sai juyi ya ke kan bed ya kasa rumtsawa a doli Leemat ya ke son kasancewa da itaðŸ˜saboda sabo ya kasa rumtsawa sai tsuki ya ke ja wadda ita ma gefenta haka abun ya ke wata sha'awar shi ma ta ke ji dan tuni jikinta ya saba da wasannin da suke duk dare kafin su kwanta kuma ba ta iya barci sai akan Æ™irjin shi,pilow ta aza daga gaba ta kwanta wai Dawood ne amman duk da haka ba ta ji wani daÉ—i ba sai sake salo ta ke har Momy ta lura da ita,Æ™asan zuciyarta taji babu daÉ—i zaman É—iyarta da Æ™asurgumin Æ™ato sauÆ™in ta ma babu abinda ya shiga tsakani.
Comment and share Please
Jikar Rabo ce😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story
``` _MRS SADAUKI_ 💫
*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰
â˜€ï¸ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀ï¸
____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇ðŸ½
*500MB* 200
*1GB* 300
*2GB* 600
*3GB* 900
*6GB* 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*
```JOYEUX ANNIVERSAIRE MA PRINCESSE INDO JE TE SOUHAITE TOUT LE BONHEUR DU MONDE,QUE CETTE ANNÉE TE SOIT UNE ANNÉE DE RÉUSSIR, SUCCÈS,PAIX ET SURTOUT LE MARIAGE```🎂
*PAGE 39-40*
Zaune ta ke tsakiyar gado ta rafka uban tagumi hawaye na tsiyaya a kan kyakkyawar fuskar ta,ba ka jin komi ɗakin sai sautin ƙira'a Abdullahi Matrood.
"Badiya yanzu ke sabida Allah tabi'ar da kika ɗaukarwa kan ki kenan?kullum kuka sai kace wacce ta rasa uwa da uba?amman kin san wannan ba hanyar ɓullewa ba ce kullum tunani in kuma an tambaye ki kice babu komi"cewar Moma da shigowarta kenan.Badiya ta ɗaga kai ta kalli mahaifiyarta cike da tausayin halin da Moma kan shiga in ta ganta cikin damuwa, murmushi ta ƙirƙiro tace "laaa Moma babu fah komi ni ban ma san lokacin da hawayen suka zubo ba"tayi maganar ta na mai tashi ta shige toilet tari tayi nan take jini ya fito daga bakinta ta kurkure baki ta wanke fuskarta sannan ta fito.
Mai ta murza a fuska sannan ta fito,duk familyn sun hallara kan dining suna breakfast kujera ta ja ta zauna ta gaishe da Dad sannan yayunta uwanda suka kasance duk maza.
Dad ya tsaya da cin abincin da ya ke yace "Diya na kula tunda wannan abun ya faru ba ki sake yin walwala ba,na tambaye ki kin ce bai yi maki komi ba to damuwar ta mice ce? amman babu komi gama cin abinci zan kira docter Maryam ta duba min ke"tari Diya ta shiga yi jin wai a dubata,ɗan tea ɗin da ta sha ta maido sai kuwa gudaje-gudajen jini cike da tashin hankali duk suka yo gun ta tarin kuma ya ƙi tsayawa.
Babu ɓata lokaci Dr Maryam ta amsa kiran Dad,teste ɗin ciki tayi mata duk da ta duba she is Virgin sannan ta ɗibi jininta ta tafi da shi asibiti dan yin exam.
Kanta Moma ke shafawa cike da tausayi Ibrahim, Mustapha da Omar kuwa tuni sun wuce gun aikin su yayinda Dad ke saffah da marwah hankali duk a tashe dan kaf ɗiyan shi ya fi son Diya ƙila kuma hakan bai rasa nasaba da ita kaɗai ce mace.
Babu jimawa Dr Maryam ta dawo riƙe da farar takarda bayani ta fara yiwa Dad da tsureta da ido ko ƙyaftawa bai yi "a gaskiya nayi mamakin yadda aka yi ƴar ƙanƙanuwar yarinya da ba ta fi 17years ba ace ta kamu da hawan jini ba,amman da sauƙi kar ku tada hankalin ku zan ɗorata kan magani in shaa Allah za'a dace"karɓar ledar maganin tayi ta aje kusan Diya wacce ke barci saboda ƙarin ruwan da aka yi mata.
Dad kuwa zaman ƴan bori yayi sai kace wata mace ya fara share ƙwalla "son zuciya ya kai ni ya baro yanzu ga ɗiyata a haɗari ƙila sai da suka firgitata abun ya zame mata psychique"Dad ke maganar zuci.
Haka suka cigaba da gadin ta har ta farka daga barci, Dad ya zauna gefenta ya kamo hannunta "Diya na faɗa min mi ke maki ciwo yanzu? "Kai ta girgiza alamun babu sai ya cigaba da cewa "to faɗa min minene ya saka ki damuwa har kika shiga wannan hali?Dr tace za ki iya samun sauƙin ciwon"da mamakin Dad sai ya ga Diya ta lumshe ido ta na murmurshi sototo yayi ya na kallon Moma wacce ta ke shaye da mamaki.
"Tsarin zubin shi,yanayin tafiyar shi,salon maganar shi,tausayin shi,tsoron Allah shi duk sun yi min ina son shi Dad ka nemo min shi" "wa kenan?"Dad da Moma suka faɗa a tare saurin buɗe ido tayi ta na kallon su sai ta farga ashe a fili ne tayi maganai ba a zuci ba.Miƙewa zaune tayi tace "zan sha jus"Moma ta tai ta ɗauko mata,ta na sha ta na tunanin abinda za ta ce dan kuwa ba za ta iya faɗawa iyayenta *ƊAN DABA* ta ke so.
Cikin son kawar da zancen tace "Dad ya kamata fah a gyara min takarduna ina son yin karatun likitanci,déjà Nadiya har ta gama shirinta"ta na yin maganar ne cikin Shagwaɓa da son nuna ita yanzu babu abinda ke damunta.Ajiyar zuciya Dad ya sauke yace "to babu matsala zan duba lamarin"ihu tayi ta rungume Dad ta na godiya kafin ta fara taka rawar murna dan tun can farko ta yiwa Dad magana amman ya ƙi amincewa.
Wayarta ta É—auko ta kira Nadiya wacce ta kasance Æ´a ga ciyaman na Maradi kuma abokin Dad ne,da murnarta ta shaidawa Nadiya kafin tace "zan zo zuwa marice ki yi min frite irin suyar ki ni ke so tom kar ki ba Æ´an aiki"yadda ta ke nishaÉ—i ya sa Dad da Moma sakin jikin su.
Wuraren ƙarfe biyar na marice Diya ta shirya draber ya kaita gidan su Nadiya wanda ya ke ADS,ta na cin frite suna hira tare da tsara yadda komi zai kasance."to wai yanzu da kayan mu na atamfa za mu je ne?"Nadiya ke magana,Diya ta tuntsire da dariya tace "kin ji banza a India za ki saka kayan atamfa hum lalle shopping za mu je mu yi na riga da wando,abaya da sahari"suka taɓa suna murna Nadiya tace "haka za ayi".
Cikin kwanaki ƙalilan aka shirya masu tafiya zuwa India wajen karatu,magunuka tamkar Diya za ta buɗe wata pharmacie haka Dad ya saya mata su.
"Diya ki kula da kan ki da lafiyar ki kar ki gani dan ban kusa da ke ki zama shashasha,banda kula samari ki yi abinda ya kai ki"cewar Moma ta na mai riƙe da hannun Diya wacce ke ɗokin tafiyar,kiss ta yiwa Moma a kumatu tace "in shaa Allah Momana sai na dawo"nan dai mutane suka fara shiga jirgin.
***
Ya kurɓi cofee ɗin ya dubeta tare da ɗaga mata gira ɗaya yace "ya ki sha mana"tayi murmurshi tace "zafi shiyasa,am kace mu haɗu a nan Plaza"Jasmine ta faɗa ta na mai bashi dukan hankalinta Nas ya ɗan murmusa ya na juya cokali cikin cofee ɗin yace "Yes ina son mu magana ne sérieusement shiyasa na ga da buƙatar keɓewa ta yadda za mu fahimci juna sosai"Jasmine ta gyara zama tace "to ina jin ka "Nas yace "am maganar gaskiya tun ranar da na ɗora idona kan ki naji kin yi min ina son ki da aure ban so kuma ya ɗauki lokaci Daddyna ya kusa dawowa na san kuma doli ya ƙara min maganar aure yaya kin shirya zaki aure ni ?"wani irin gudu zuciyar Jasmine ta fara ta ma rasa mi za tace ita tayi tunanin yadda za ku rinƙa haɗuwa suna cashe ayar su zai yi mata sai gashi ya zo da maganar aure,cikin daburcewa tace "aure?am ka na fah tarayya da Mamina ta yaya kuma za mu yi aure?"ya ɗage kafaɗu yace "so what dan ina tarayya da Mami?zina daban aure daban dan haka kar ki ma damu kan ki in dai dan wannan ne"Jasmine tace "to amman ka na ganin Mami za ta yarda da auren?"murmushi yayi yace "no kar ki damu ai duk na shirya komi iyayen bogi zan samo a matsayin iyayen ki kin ga ana ɗaura mana aure za mu bar ƙasar kwata-kwata mu je can mu sha amarcin mu"saurin rufe ido Jasmine tayi wai kunya🙄Nas kuwa ji ya ke kamar ya haɗe ta dan so tun ranar da ya tarar da su a falo suna barci ita da Laila lokacin da suka je club ya ji Jasmine ta kwanta mashi a rai.
Cofee É—in suka sha kafi su fara cin chawarma suna yin komi ne tamkar masoyan da suka daÉ—e cikin soyayyar juna,haka kawai Jasmine taji mutu karaba ita Nas tare da yi mashi babban gurbi cikin zuciyarta ko dan shine saurayi na farko da yayi mata maganar aure?oho.
Jasmine tayi mamakin ganin dalleliyar motar da Nas ke hawa dan a yadda ya ke zuwa gidan ba za kace ya na da kuɗi ba,shi yayi draving nata har gida a mota sai da Nas ya ɗan rage zafi ita ma ba ta wani hana shi ba.Kasancewar motar irin mai baƙin glash ce babu wanda ya san wainar da su ke toyawa,cire bakin shi yayi daga nata ya na sauke numfashi yace "baby est ce que tu es vierge?"Kai ta ɗaga mashi tace "eh Virgin ce ni miyasa kayi min wannan tambayar?"ya shafi kumatun ta yace "kawai na tambaya ne yadda kika iya kissing haka in sex ma haka ne ai babu kanta na san kingi ne za'a ban"ya ida maganar ya na ɗaga gira Jasmine kuwa har ƙasan ranta taji babu daɗi.Ganin haka ya sa Nas cewa "ke babu fah komi wasa ni ke,ai ni ke ni ke so"murmushin yaƙe tayi kafin ta kimtsa tayi mashi sallama.Ya na kallonta har ta shige gida ya tuntsire da dariya yace "hegiya ni zan auren ƴar duniya duk an ƙwaƙule ki a club ai ni sabuwa dal a leda zan aura ƴar shila wacce komi ni zan koya mata".
Jasmine na shiga gida ta tarar da Mami a falo ta na shan tsamiya gefenta kuma ƙaton tray ne cike da rake sai kwalshi,kai kawai ta jinjina ta shige ɗaki toilet ta shige tayi wanka tare da gasa jikinta sosai ta yadda wai Nas ba zai gane ita ba Virgin ba cece.
Bayan kwana biyu da yin magana Nas ya kirata ya shaida mata gobe za'a kai lefe tuni kuma ya samu iyaye bogi,cike da murna Jasmine ta ce "yauwa my Nas yanzu yaushe zan je na gaishe da iyayen ka" yace "ai gobe ana kai kayan takeyanke za'a É—aura auren dan Daddy yace zai koma India kuma babban albishir a tare za mu je tunda Momyna ma ta na can"dan murna Jasmine har da yin É—an tsalle.
Washegari kuwa Nas ya zo ya É—auke ta zuwa gidan iyayen bogi,akwatinan lefen suka nuna mata cikin jin daÉ—i ta rungume Nas daga nan ya É—auke ta suka wuce hotel Horizon.
A tare suka yi wanka suka fito suka shafa mai,kazar amarci ya buɗe suka ci suka ƙoshi suka hauda madara tare da jus sannan suka yi brush.
Jasmine tsakiyar gado ta zauna zuciyata na das.das.das tunani ta ke ko ya za taji a karo na biyu da ciwo ko babu,ta na wannan tunanin Nas ya hauro gadon ya na mai kashe masu hasken ɗakin.Ba'a fi minti goma ba Jasmine ta fara kuka na fita hankali ashe gaba ma da gabanta yadda Nas ke yi mata tamkar ya samu maƙiyar shi duk ihunta bai dame shi ba.
Sauka yayi a kanta ya ɗauko wata roba da ƴar ƙarama da ya aje tun lokacin da zai hawa gadon,wani abu ne shi ba mai ba shi ba ruwa ba ya zubawa Jasmine a gabanta sai da tayi wata irin kururuwar azaba ta na ji a sannu ƙasanta ya fara matsewa kamar ana mata ɗinki.
Washegari tun da safe ya tara ruwa masu É—umi yayi mata wanka shi ma yayi suka shirya zuwa filin jirgi ba'a daÉ—e ba jirgin su ya É—aga zuwa India.
Comment and share Please
Jikar Rabo ce 😎
*ÆŠAN DABA*
```love
and
romantic story
``` _MRS SADAUKI_ 💫
*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰
â˜€ï¸ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀ï¸
____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
*BUY MTN DATA AT AFFORDABLE PRICES*👇ðŸ½
*500MB* 200
*1GB* 300
*2GB* 600
*3GB* 900
*6GB* 1800
(CHECKING BALANCE * 461*4# )
VALIDITY : 1 MONTH
For more enquiry Call or Whatsapp this number: *08066268951*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.