Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 46
Auren Shehu 2
Afuwan akan rashin cika alkwari, aiki ya min yawa, a yi min hakuri.
Nan Kawu Iliya ya bar Usman da Bello ba tare da yayi kokarin rarrashin su ba, yana cike da tsabagen takaicin dauke kafa da Usman yayi daga Rugar Shehu. Sun kai kusan minti talatin gaban kabarin Mahaifiyar su, Usman gani yake tamkar ita din ce zaune kusa da shi. Sai da sauran matasan Ruga su ka zo su ka ja shi suna mai bashi baki sannan ya hakura ya ta so su ka nufi cikin Rugar Shehu.
Tuni labarin dawowar Usman ya zaga lungu da sako na Rugar Shehu, har ya ga kai kunnan Baffa Mudi, hankalin sa tashe ya zo ganin shin da gaske Usman din ne dan kuwa bai taba tsammanin zai sake taka kafar sa a Rugar Shehu ba bayan kurciyar da ya masa, babban tashin hankalin sa be wuce kar Usman ya ce zai kwaci sarautar Rugar Shehu ba dan shi kan sa ya san jama'ar Rugar sun gaji da mulki irin na sa.
A dandalin shadi ya tarar da jama'a sun taru makil maza da mata, Yara da manya, mata da maza, masu kida na yi, haka masu tafi, tsuffin cikin su kuwa kuka biyu su ke, kukan dawowar Usman da kuma kukan rashin Iyar sa. Cike da tsana da faduwar gaba Baffa ya tsaya gefe ya na duban duk abubuwan da ke wakana, ganin yanda Usman ya ƙara girma ya zama cikakken matashi ma'abocin karfi da kwarjini, ga matasa zagaye da shi, sai koda shi su ke, su na masa kirari da fulatanci, fadi su ke
"Dan Shehu jikan Shehu, karen bana mai maganin zoman ba na, Shehu ya tafi, Shehu ya dawo!"
Ya sanya Baffa Mudi barin wajen a fusace, cikin ran sa ya na saka yanda zai dauki mataki akan dawowar Usman. Shi kuwa Usman gangan jikin sa ne kawai a wajan, zuciyar wacce ke cike da bakin cikin rashin Iyarsa tuni ta yi nisa wajan saka yanda za ta hukunta wacce ta ke da alhakin rashin ganawar sa da iyar sa na har abada, Amma ya kudiri niyar fara raba Rugar Shehu da ummul abasin dalilin da Iyar sa ta tilas ta masa barin Rugar a karan farko, wato Baffa Mudi.
Duk yanda ya so ya kadaice shi kadai yayi makokin Iyar sa abin gagarar, mutane ke ta kai kawo cikin sashen su domin masa maraba da kuma ta'aziya. Haka kuma kishiyoyin Iyasar sa Yagwalgwal da Duduwa su ka sako shi gaba da mitar barin Rugar Shehu da ya yi. Ba shi ya sami kan shi ba sai bayan ishi'i, ya na shirin shiga bukkan sa sai ga yan uwar Mahaifiyar sa sun zo. Yayar ta wacce ake kira da Huwaila, sai kuma kanwar ta mai suna Iyalle, da kuma matar shi Kawu Iliya Hansai.
Sune su ka sa Usman gaba da fadan barin gida da yayi shekara da shekaru babu ko waige, har Iyar sa ta fadi ta mutu. Usman ya kasa musu bayanin umarnin Iyar ta sa ne ya sanya shi barin Rugar dan kuwa har lokacin be yi niyar tonawa Baffa Mudi asiri ba. Jin su na rokan sa da ya kaunaci Allah ya karbi mulkin Rugar Shehu, a cewar Huwaila wasiyar da Iyar sa ta bar ma sa kenan, ya sa shi tambayar ko da wani abun da be sani ba ne?
Nan su ka bude ciki su ka bayyana masa mulkin zalinci da Baffa Mudi ya ke aikata mu su, tare da sana'ar da babban dan sa Tanko ya shiga na garkuwa da mutanen birni ana biyan shi kudi kafin ya sake su, Kuma duka ya na yi ne da sanin Baffa Mudi. Matukar ba so ya ke a maishe da duk matasan garin yan garkuwa da mutane ba, har gwamnati ta gane ta turo a ayi kan mai uwa da wabi toh lalle yayi wani abu.
Cikin bakin ciki da jimami su ka tafi su ka bar Usman, ba su dade da fita ba sai ga dattawan Rugar Sheshu su ma sun iso gare shi da irin bukatar da dangin Mahaifiyar shi su ka zo da shi, cewar su dan babu yanda za su yi ne da tuni sun bawa Muhammadu Bello sarautar Rugar Shehu, ya duba girman Allah ya fanshe su daga wannan ukuba da su ke ciki, Allah ne ya dube su ya dawo da shi.
Cike da girmamawa Usman ya sallame su tare da mu su alkawarin zai kwana da maganar cikin ran sa, in Sha Allah zai samar mu su mafita.
Sai da kafa ta dauke sannan Usman ya sami damar shiga dakin Mahaifiyar sa cikin faduwar gaba, gani ya ke kamar zai gan ta kwance bisa gadon karar ta. Har lokacin dakin cike ya ke da kayan ta kamar ta na raye. Duk yanda ya so daurewa kasawa yayi, Yana mai rungumar zanin Iyar ta sa hawaye ke fita daga idanun sa, haka ya zauna bakin gadon ta ya ci kukan sa ya koshi, be fita ba sai da ya daukarwa kan sa alkwari biyu, na farko shi ne tabbatar da cigaba da yancin Rugar Shehu ta hanyar karbar ta daga hannun Baffa Mudi kamar yanda Mahaifiyar sa ta bar masa wasiyya, na biyu kuma shi ne Zainab, ya yi alkawarin sai ta yi da na sanin zama silar rashin sake ganawa da mahaifiyar sa har abada, zai iya yafe komai amma ban da wannan.
Washegari tun kafin Usman ya je in da Baffa Mudi ya kafa fadansa dattawan Ruga su ka tada bukatar Baffa Mudi ya bawa mai mulki mulkin sa, dama ya kan yi ikirarin rashin Magajin Shehu ya sanya shi zama kan mulkin, toh Allah ya dawo da magajin Shehu.
Nan fa Baffa Mudi yayi kyememe ya ce be san zance ba, mulki ya rigada ya koma gidan sa, saboda haka be da wani magaji da ya wuce Tanko, in Sha Allah kuwa ko bayan ya mutu Tanko ne mai gadon Rugar Shehu. Nan fa aka hau kace na ce, masu goyan bayan Baffa Mudi na yi, haka kuma masu rantsewa sai ya sauka ba su fasa ba, ana cikin wannan yanayi ne Usman ya karaso.
Ganin sa gaban Baffa Mudi yayi mummunar faduwar, ga shi dai Usman din da ya sani ne, haka kuma tufar jikin sa ba ta sauya ba, rigar saki nan dai da kowa ke sakawa ne jikin sa, Amma wani irin cika ido da kwarjinin da Allah ya wa Usman sai ya zamewa Baffa Mudi tamkar Dodo, dan kuwa yanda ya ke shakkar Usman be ji shakkar Maihaifin Usman marigayiya Shehu ba. Usman be fasa gaishe shi cike da ladabi ba a matsayin sa na kanin mahaifin sa ba. Ba komai ne ya dagawa Baffa Mudi hankali ba sai jin furucin Usman na
"Baffa abubuwa da dama sun faru, wanda mun sani, ka sani, ka kuma san mun sani, wanda tonasu na nufin zubewar darajar ka a Rugar Shehu na har abada, haka ba ya cikin abin da na tanadar ma ka....."
"Zancen banza zancen hofi!"
Baffa Mudi ya katse Usman cike da burin kunya, be gushe ba ya cigaba da fadin
" Kai Usman ni za ka zo ka nunawa bude idanu? Wai kai na birni idon ka ya bude ko? Nan ba kafa ka sa ka tsallake Rugar Shehun ba? Sai da ka ji labarin mun fara samin cigaba, shugaban kasa ya ce zai tallafawa fulani ta hanyar gina mana Ruga mai inganci, da asibitoci, da makarantu da kayan more rayuwa shi ne za ka wanko kafa ka dawo ko? Toh ko uban ka Tanko be isa ba....."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.