Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 46
Ko da su ka tsaya sallar la'asar nan Zainab ta kakare, tsabagen tafiya kafarta har ta fara kumburi. Amma Usman be tausaya mata ba bare ya ce su yada dogon zango, sai dai ta sami saukin daukar akwaiti, dan da tafiyar ta yi tafiya shi ya dauki akwatin.
Yana yin duhu da gari ya fara be sa Usman ya fasa tafiya ba, da taimakon tocila su ka cigaba da kutsawa cikin daji, Allah kadai ya san adadin macijai da Usman ya kashe, tun Zainab na saka masa ihu tare da dane jikin sa, har gajiya ya sa tsoran ta ya gushe, tafiya ta ke tamkar za ta fadi, ganin haka Usman ya É—auke ta cak ya saba a kafada, ba ta jima ba baccin wahala ya dauke ta, a haka har su ka isa Rugar Shehu wajan karfe shabiyu na dare.
Rugar duhu dulum yawanci jama'ar rugar sun kashe fitilar su ta aci balbal sun kwanta. Sai matasa yan kalilan ciki har da Muhammadu Bello ne zaune suna hira, ganin mutum dauke da wani abu bisa kafada ga kaya nan hannun sa ya ruko ya na tafiya niki niki ya tasarwa Rugar Shehu ya sa su Muhamadu Bello zabura, su na mai daukar gororun su suka nufo Usman, cikin harshen fulatanci su ke fadin
"Kai hattara Nan! Waye Nan!"
"Usman! Shehun ku Usman!"
Usman ya ba su amsa ya na mai tadda su. Ganin da gaske Usman ne, dauke da mace su ka sauke gogorun su cike da mamaki, Amma aka rasa wanda zai iya budar baki ya tambayi baasi. Bello ya karbi akwatin hannun Usman har rumfar Shehu su ka raka shi, sannan su ka juya da tambaya fal bakin su.
Bello ne kadai ya tsaya taimakawa Usman ta hanyar bude ma sa kofar kara, ya daga assabari yanda Usman zai iya wucewa ba tare da ya buge Zainab ba. Bello na biye da shi su ka shiga dakin yayinda ya aje akwatin Zainab gefe. Bisa gadon kara Usman ya kwantar da Zainab tare da gyara mata kwanciya.
"Shehu ka dawo mana da sabon abu a wannan ranar"
Cewar Bello ya na duban Zainab da har lokacin bacci ta ke. Shiru ne ya biyo baya yayinda Usman ya zauna gefan gado yana duba kafar Zainab da ta kumbura. Ganin Usman be da niyar tanka masa ya saka Bello sake fadin
"Wacece wannan matar? Daga ina ka dauko ta? Shin ba ka gudun ace Shehu ya zama dan garkuwa da mutane kamar Tanko dan Baffa....."
"Bello!"
Usman ya dakatar da shi cikin tsawa hakan ya sa shi kame bakin sa. Ya juya zai fita ya ji Usman ya ce
"Ina so ka duba cikin garke, ka tatsar min nonan saniya mai dauke da juna biyu ka kawo min yanzun nan!"
Kallan sa Bello ya tsaya yi cikin faduwar gaba, kenan da abin da Shehu yayi ya dauko baiwar Allah nan ba wai cikin hankalin ta ta biyo shi ba.....
"Ka na nan tsaye ne?"
Cewar Usman wanda ya lura da halin rudanin da Bello ya shiga. Cikin azama Bello ya fice, Jim kadan Bello ya dawo dauke da kwaryar nonon da ya tatso, ya tadda Usman na shirin kunnan wani ice da su ke amfani da shi wajan koran soro.
Ya mikawa Usman kwaryar, bayan Usman ya karba yayi Bisimillah sannan ya fara karanto wasu adduo'i a zuci bakin sa na motsi, ya na gamawa ya tofa cikin kwaryar nonon yayinda ya fara kokarin tada Zainab. Cikin magagin bacci ta ke jin maganar Usman ya na fadin
"Tashi ki Sha Abu"
Hakan cikin mamagi Zainab ta kurbi nonon, ba ta jima da sha ba bacci mai nauyi ya sake dauke ta. Usman na duban Bello da ya tsura masa idanu cike da al'ajabi ya ce
"Ka jira ni daga waje"
Bello ya sa kai ya fice. Bayan fitar shi Usman ya cire hijabin da ke jikin Zainab saboda zufa da ke tsattsafowa daga jikin ta sanadiyar nonan da ta sha, ya rage daga ita sai doguwar riga ruwan hoda mara hannu, kan ta rufe da dankwali. Sai da ya karanta ayatul qursiya da falaqi da nasi ya tofe ta tsaf ya fito ya tadda Bello tsaye ya na ciran sa.
"Mata ta ce Muhamadu Bello"
Cewar Usman ya na mai kokarin cire rawanin sa. Mamaki ne ya bayyana fuskar Bello, kana ya ce
"Dama da gaske ka na da aure? Kar dai ita ce matar da ake neman sakin ta daga waje na?"
"Ita ce sanadin kashin da aka baka sanda Iya ta aiko ka kira na, haka kuma sanadiyar ta Iya ta kwanta dama ba tare da mun gana ba"
Usman ya bashi Amsa. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani Bello ya furta
"Ya aka yi ta zama matar ka? Dama ka yi aure ban sani ba?"
"Zan maka bayani daga baya, yanzu na gaji matuka"
"Shin ya aka yi ta yarda ta biyo ka? Nonon da ka bata yanzu kar dai......?
Bello ya kasa karasa maganar cikin shakkar tambayar da zai yi. Usman na mai girgiza kai ya ce
"Kiranye?"
Bello ya girgiza kai. Usman na mai murmushin mugunta ya cigaba da fadin
"Tabbas shi na mata, shi ne hanya mafi sauki da zan iya taho da ita, ka ga wannan yarinyar da ke kwance bisa gado na? Hatsabibiya ce, fitinanniya ce dan haka kada ka taba tausaya mata! Idan har ka ga na mata wani abu na alkhairi toh ka tabbata darajar mahaifin ta za ta ci, na kuma ba ta makarin kiranyen da na mata ba don komai ba da dai ina bukatar ta cikin hayyacin ta, ina so na gan ta cikin kunci kamar yanda zuciya ta take cikin kunci!"
Jikin Bello ne yayi sanyi kwarai, tun da ya zo duniya be taba ganin Usman cikin halin bacin rai da neman daukar fansa kamar yanda ya ke a yau ba, shi da ya sha duka ma be kullece ta kamar yanda Usman ya kulla ce ta ba, lalle Zainab abar a tausaya mata ce tunda ta iya tado fushin mai hakuri, tabbas ta kai bango.
"Ka na nufin babu soyayyar ta cikin ran ka?"
Cewar Bello cikin adduar Allah ya saukaka. Usman na mai girgiza kai ya furta
"Daukar fansa shi ya kawo Abu Rugar Shehu, Abu ce mace ta karshe da zan iya so a duniya!"
Ya na gama fadin haka ya wuce ya bar Bello cikin tunani da sakar zuci.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
3
Allah yayi dare gari ya waye, carar zakara tare da kukan shanu, gami da guje guje da ihu da yara ke yi ne ya sanya Zainab sanya hannayen ta bisa kunnuwan ta, tare da runtse idanu, ga wani zugin azama da take ji a kafafun ta, haka kuma kan ta ya mata nauyi. Tun tana jin komai tamkar cikin mafarki, har ya fi karfin kunnuwan ta ya kai ga sanya ta bude idanu a hankali. Maimakon ta ga silin da fanka sai ganin karare ta yi jere reras, idanun ta ta rufe a karo na biyu ta na mai fatan farkawa daga mafarkin da ta ke. Ko da ta sake budewa ta ga dai har lokacin rufin kara idanun ta ke gane mata ta shi zaune a firgice ta na mai bin bukkar da idanu, bukka ce maidaidaciya wacce aka gina da jar kasa mai dauke da yayin ciyawa da rufin kara. A kideme ta kai kallan ta ga in da ta ke kwance, sai a sannan ta lura da gadon kara mai dauke da matacciyar katifar da ta ke zaune kai. A hankali ta ke karewa bukkar kallo tundaga ledar da ke shimfide kasan bukkar, har zuwa koren akwaitin karfe da ke aje gefe kusa da katan kwaryar da aka rufe da wani fefe, sai butoci guda biyu, na roba da na karfe.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.