Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 41 of 46
"Allah sarki, Allah ya ji kan sa ya kuma raya dan sa"
Zainab ta amsa da "amen"
Babu wanda be yi murna da haihuwar Zainab ba, hatta Anty Sauda sai da ta aje fushin ta gefe da ta ga dan da Zainab ta haifa. yaro sak uban sa, kai ka ce balarabiya ta haifo sa. Jin Zainab ta saka sunan Usman ba Malam da kowa yayi zato ba sai da aka yi dan kananan maganganu. Zainab kuwa ta ce da dai ita ta haifo kayan ta, kuma Usman ta ga daman saka masa, za kuma ta kira shi Shehu, ta ga wanda ya ke da ikon canzawa dan ta suna.
Ranar suna aka sha shagali, Hajja Kilishi da na ta ayarin sun yiwa Ammy kara kwarai dan kuwa sai bayan suna da kwana biyu su ka tafi.
****
Bangaran Usman kuwa ya na can ya na hidamar kafa Rugar Shehu cikin saban gidan gonar da ya ke ginawa sam be san an masa takwara ba. Umar ya mayar da shi dan zamani, dake dama mutum ne mai ilimin addini gashi ya hada da zamananci nan da nan ya zama goge. Kullum cikin masa tayin aure ake, abokan sana'ar su ne, mata masu kawo kan su kai har ma daga bangaran Alhaji Ibrahim Balla, Amma kullum Usman cikin zillewa ya ke. Har Umar ya gaji ya fito ya tambayi Usman shin lafiyar sa kalau kuwa? Usman ya bashi amsa da kada ya damu, dake su na shirin zuwa Rugar Shehu domin taho da wasu daga cikin shanun Usman, ya ce ya bari idan su ka dawo zai masa bayanin komai. Da haka su ka dauki hanyar su na Rugar Shehu.
Amma ko da su ka isa Mambila, aka yiwa Umar bayanin tafiyar kasa da za su yi kafin su karasa Rugar Shehu nan yayi kememe ya ce ba shi iyawa. Usman dai ya je ya dawo shi zai yi tsimayin shi nan Mambila. Hakan ko aka yi, Usman shi kadai ya niki hanya har Rugar Shehu.
Ganin yanda Usman ya canza kasa gasgata zatan su na Shehun na su ne da gaske. Nan fa Usman ya zama abin kallo kamar yanda Zainab ta zama farkon zuwan ta Rugar Shehu, bambamcin dai shi wannan mamakin yanda Usman ya canza gaba daya ne ya rufe su. Kowa burin sa ya taba Usman. Shaddar da ke sanye jikin sa, hular kan sa kai hatta takalmin kafarsa abin kallo ne gare su. Cikin su har da masu fadin babu shakka cikin wannan injin kyera mutane da aka ce akwai a birni aka sanya Usman, ya zama dan birni tamkar kado.
Bayan komai ya lafa ya mu su bayanin abin da ya ke tafe da shi. Wato na mayar da Rugar Shehu cikin birni. Kamar yanda yayi hashashe, dayawa daga cikin su sun yiwa maganar mummunar fahimta, ciki har da Kawu Iliya. Amma ko da Usman ya tsaya ya mu su bayani mai gamsarwa sai su ka dan sauko, Amma duk da haka su ka ce bazai yiyu kowa yaye a bar daji ba. Duk sanda Usman ya gama shirin sa ya zo wasu daga cikin jama'ar Rugar su bishi, a fara ganin yanayin zaman da yanda zai kasance, idan har abu yayi kyau saura jama'a su bi bayan su, idan aka sami kishiyar haka kuma toh lalle wanda su ka bishi sai su dawo gida. Haka kuma shanu mallakan sa ne, ko da kuwa dubu zai kore zuwa birni ba zai talauta Rugar Shehu ba, dan haka babu mai tsayar da shi, adduar su dai kawai Allah ya idda nufi, ya kawo mu su alkhairi.
Kwanan Usman biyu kacal a Rugar Shehu, ana gobe zai koma Bello ya zo masa da sakon Raqeeba na ta na so ta gan shi. Usman ya ce toh bisimillah mana. Nan cikin bukkar shi ta zauna tare da mijin ta Bello. Usman na daga zaune can gefe yayinda zuciyar sa ta masa nauyi jin maganganun da ke fita daga bakin Raqeeba. Ta kwashe abin da ya faru tsakanin ta da Zainab, da kuma yanda ta tunzura ta har ta yarda ta hada baki da su Rahila ta fada mu su. Cike da nadama ta kare da
"Abu mai kaunar ka ce kwarai, sharrin shedan ya sa na aikata abin da na aikata amma sam babu laifin ta, laifin ta daya shi ne zafin kishi, dan sai a sannan ni kai na na gane Abu mai kaunar ka ce....."
Ganin Usman ya runtse idanu ya sanya Raqeeba kasa magana, cikin neman agaji ta ke kallan Bello wanda tun da ta gano ta kamu da san shi ta fada masa abin da ta aikata. Bello ya gyara muryar sannan ya furta
"Ta yi kuskure, tun da ta fada min na nuna mata bacin rai na....."
"Tun da ta fada ma ka? Ka na nufin ta ma fada ma ka amma ka kasa sheda min Muhamadu?"
Ya na kokarin kare kan sa ya furta
"Ah ah watan jiya ta sanar da ni, dama jira na ke...."
"Ya salam matar ka ta cutar da ni, ni Kuma na cutar da Abu! Har ka san wannan maganar amma ka kasa fada min? Watan jiya? Kasan kwana nawa na yi kullum da kewan Abu? Ka san dare nawa ya shude kullum da ita na ke mafarki? Kasan kwanaki nawa na yi kullum zuciya ta na kukan rashin ta? Haba Muhamadu Bello! Haba dan Allah!"
Cewar Usman yayinda ya tashi a firgice ya shiga hada kayan sa. Alama Bello ya yiwa Raqeeba da ta tashi ta tafi. Tsoran fushin Usman ya sanya ta kiran su Kawu Iliya. Su ka tadda Usman ya dau jaka har ya fito. Sun yi sunyi su bashi hakuri ya bari gari ya waye sai su tafi amma Usman yaki. Gani ya ke kowani sakan idan ya wuce ba tare da ya na hanyar Kano ba asara ne a gare shi. Dole suna ji suna gani su ka bar shi ya dau hanyar Mambila cikin daren.
Sai da gari ya waye tangararan rana ta hudo kai sannan ya isa Mambila. Nan ma abinci kawai ya ci sannan ya tasa Umar a gaba lalle su dau hanya Kano. Yanda dawo masa afujajan ya sanya Umar shiryawa su ka dau hanya ba tare da ya masa mu su ba. Tun da su ka dau hanya Usman ya je rama baccin da be yi daren jiya ba. Umar ya daga masa kasa har sai da su ka isa Jalingo, bayan sun yada zango hotel din da su ka saba sauka ya je har daki ya same shi.
Babban daki ne wanda ya kai matakin dakunan da alhazawa su ke kamawa. Bayan ya buga masa kofa ya bude masa, ya sake komawa ya yi zaman sa bakin gado, sanye da farar singileti da gajeran wando. Umar ya dube shi ya ce
"Na lura tun da ka dawo ba ka cikin hayyacin ka, me ke faruwa? Me za su yi Kano?"
"Abu zan dauko"
"Wacece Abu Kuma?"
Umar ya tambaya cikin nuna rashin fahimta. Nan Usman ya bashi wani bangare daga cikin rayuwar shi da Zainab ba tare da ya tona sirrin da ya shafi dakin auren sa ba. Kafadar shi Umar ya dafa sannan ya ce
"Sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ka ki kula kowa. Lalle ni zan raka ka har Kano, Amma fa gaskiya ba za mu je haka yanda ka ke a burkice ba Malam! Sai ka nutsu ka kuma kwantar da hankalin ka!"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.