Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 35 of 46

Ruwan wanka aka hada mata, bayan Falmat da kan ta ta gyara mata daki. Sai ta ke ganin komai daban musammam da ta shiga bandaki, wai itace cikin tangaran maimakon zagayen kara da Usman ya sa aka mata, cikin kokarin tsayar da hawayen ta yi wanka ta fito. Cikin kayan ta da ta bari a gida ta sami wata doguwar riga mara hannu ta sanya. Gaba daya jin ta ke tamakar bakuwa, komai na gida ya zame mata tamkar sabon abu, gadon katako maimaikon gadon karar da ta saba, carpet maimakon tabarma ko ledar da ta saba, tiles maimakon kasa da tsakuwar da ta saba takawa.

Ta idar da sallah kenan sai ga Halitta dauke da farantin abinci, ta aje gaban ta tare da fadin

"Yakura ki daure ki ci abinci"

Zainab ta yi mata shiru kawai ta na duban ta. Ganin ba ta da niyar bude kolar ne Halitta ta bude ta fara zuba mata, shinkafa ce jellof ya sha bushesshen kifi, yanayin turirin da ke fitar da kamshin kifin ne ya daki hancin yakura, tun ta na iya jurewa har ta kai ga toshe hanci da hannu, cikin ta ne ki hautsinawa sanadiyar rashin abincin da ba ta ci ba tun safe, ba ta ankara ba sai ji ta yi amai ya taso mata, ta tashi a guje ta shiga bandaki. Nan ta yi ta amai kamar wacce za ta amayar da hanjin cikin ta. Hankali tashe Halitta ta kira Ammy.

Cike da tsoran abin da zuciyar ta ke ayya na mata Ammy ta furta

"Yakura ayya kuwa? Tun da na gan ki na san ba ki da cikakkiyar lafiya, tin kafin dare yayi mu tafi asibi..."

"Ammy gajiya ce kawai da yunwa, tun safe ban ci abinci ba hanji na ya kulle, da na sha ruwan zafi I will be fine"

"Duk da haka gobe sai mun je asibiti Yakura....."

"Allah ya kai mu"

Cewar Zainab cikin kaguwar su tafi ko ta samu ta huta. Ammy ba ta barta ba sai da ta tabbatar ta sha ruwan bakin shayi kamar yanda ta bukata, bayan shi ba ta iya cin komai ba, dole haka su ka bar ta ta kwanta.

Tun da su ka fita take juyi kan gado, Baccin gaji ya ke diban ta amma hakan be sa ta dena ganin Usman da ke mata gizo cikin idanun ta ba. Filo ta ja ta rungume tamkar shi ne Usman cikin magagin bacci ta furta
"Ina san ka Usman, ba zan iya rayuwa da wanin ka ba, dan Allah ka rufa min asiri ka dauke ni daga nan......."

Inda Zainab ke cikin radadin san Usman, shi ma a nashi bangaran gaba daya ya rikicewa su Iyalle tun bayan da ya dawo ya tadda Bello ya cika umarnin shi ya tafi da Zainab.

Ko zaman cikin Rugar baya iya yi bare ya yarda ya shiga bukkar sa ko wanda Zainab ta koma bayan ya farfado da ga ciwo. Kamar yanda ya ke mata gizo shi ma din gizo ta ke masa. Fatan shi Allah ya sa ta isa gida lafiya gashi be da hanyar da zai gane hakan.

***

Anty Sauda tare da Ammy da Halitta ne su kai Zainab asibitin premier washagari da azahar bayan isowar ta, tare ta ke da sojoji wanda a fadar ta su ne za su rubuta statement din da Zainab za ta ba su bayan sun dawo daga asibiti, ta sha alwashin kama Usman da duk wani da ya ke da sa hannun dauke Zainab. Babu gwajin da ba a yiwa Zainab ba, ciki har da na HIV, hepatitis da na juna biyu.
Bayan an gama gwaje gwajen suna zaune jiran fitowar sakamako Zainab ta yi zaman ta can gefe a reception, ba ta iya zama cikin su Halitta bare ta saki jiki da su.

Anty Sauda wacce ke zaune tare da Halitta da Ammy, ta girgiza kai bayan ta karewa Zainab kallo ta ce

"Wallahi wannan tsinannan almajirin ya cuce mu! Dan Allah ki ga yanda yayi breaking Zainab completely? Ji yanda Zainab ta koma, ji irin shigar da Zainab ta ke yi ta fita?"

Duka ukun kallan ta su ke yi, ita kuwa sam hankalin ta ba ya wajan su, tunanin sakamon gwajin da aka mata ta ke na game da juna biyu, duk da dai ita kan ta ba ta san wani irin sakamako ta ke fata ba, burin ta dai Allah ya tabbatar mata da abin da ya fi alkhairi.

Sanye ta ke cikin hijabi ruwan toka wanda ya sauka har kasa, sam babu wani alamar rawan kai da jin kai da aka san Zainab da shi. Hannu ta sa ta goge hawayen da ke gangarowa daga idanun ta, hakan ya sa Ammy dauke kai cike da jin zafin halin da diyar ta take ciki, ta na mai zargin kan ta da Malam da laifin sanya ta cikin duk wata masifa da ya afka mata.

Halitta da Anty Sauda ne su ka koma wajan ta, inda Halitta ta rungume ta cikin rarrashi, Anty Sauda kuwa fadi ta ke

"Ki dena kuka Yakura, wallahi sai an kwatar mi ki hakkin ki, na mi ki alkawarin kamo duk wanda ke da sa hunnu cikin wannan lamarin ko da kuwa wannan tsinannen almajirin ne! Ai ga irin ta nan! Na dage sai ya sake ki uwar ku ta ki goya mana baya, yanzu wa gari ya waya?"

Likita ce ta fito ta bukaci ganin Zainab ita kadai domin bata sakamakon gwaje gwajen da aka mata, Anty Sauda ta ki yarda lelle sai dai a fadi sakamakon a gaban su, ai su ne su ka kawo ta, da abin na sirrin Zainab ne da ba za su kawo ta ba sai su ce ta yi tafiyar ta ita kadai.

Sai da Zainab ta ba da izini sannan likitar ta yarda su ma din su ka bi Zainab zuwa ofishin likitan, Halitta ce kadai ta zauna waje.
Zainab da Anty Sauda zaune kujerar da ke fuskantar teburin likita, in da Ammy ta sami kujera can gefe ta zauna. Da Ammy har Anty Sauda likita su zubawa ido cikin jaran tsammani. Cike da nutsuwa likita ta musu bayanin cewa duka kwaje kwajen Zainab negative results aka samu ma'ana ba ta dauke da wani cuta da ake tsoro, likita ta kare jawabin ta ta hanyar fadin

" Sai dai kuma sakamakon gwajin juna biyun da aka mata ne mabambamci, dan kuwa ya nuna ta na dauke da juna biyu...."

Wani irin shauki ne ya ziyarci zuciyar Zainab ta tsinci kan ta tana mai runtse idanu, yayinda ta ke jiyo maganganun Anty Sauda tamkar ruwan zafi, fadi ta ke

"Ko juna dari ne zubar da shi za a yi wallahi! A yi polishing tsinannen......"

Ammy kuwa kuka ta saka ta salati, cewa ta ke

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Anty Sauda ta kara da

"Sai yanzu ki ke da bakin salati? Ai dama aka ce wanda be ji bari ba ya ji hoho, mu ka yi mu ka yi ki dakile auren nan ki ka min kunne uwar shegu! Ai ga irin ta nan! Kai idan har ba a kama min yaran nan ba ban isa Sauda ba! Likita mu na so a cire cikin nan da gaggawa....!"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.