Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 12 of 46
Usman yayi zumbur ya tashi rai bace cikin ran sa ya na ayyana hukuncin da zai aikata matukar Zainab ta cutar da al'umar Rugar sa, Musammam ma ahalin gidan Shehu.
"Ka ga sharrin Kado ai, ga shegentakar nan ai, ita dai tilo tun da ta wayi gari cikin Rugar nan ba ta bari an huta ba! Kado ba mutunci! "
Cewar Kawu Iliya. Bello ne ya tashi tare da fadin
"Bari na je gidan na ga abin da ke faruwa"
"Ni zan je da kai na, ku yi hakuri yanzu za a kare zaman yau, sai kuma Allah ya kai mu gobe, bissalam"
Ya na fadin haka ya zura takalmin sa, yanda ya ke tafe cikin sauri kadai ya isa ya nuna yanayin bacin ran da ya ke ciki.
Auren Sheshu 2
4
Tafiya ta ke ta na dingisawa, tsoron duhun daji be hana ta kutsawa cikin dajin ba dan kuwa a zaton ta za ta iske titi nan kusa. Yanayin duhun bishiyoyi da kuma kukan tsuntsaye da birrai ne ya hana ta zama duk yanda ta so ta zauna ko tafin kafar ta zai sarara daga zugin da su ke mata. Ta na tafe tana kwashewa Usman da jama'ar Rugar Shehu albarka, hannu daya na jan akwatin ta da ke makalewa cikin itace lokaci lokaci, dayan kuma ruke da wayar ta, har lokacin ba ta fasa neman sabis ba ta na ta gwada numbobin waya ko zai shiga. Ganin hasken rana kusa ya sanya ta kara himma a zaton ta titi za ta bullu, ko da ta karasa sai ganin ta ta yi cikin wani fili mai bishiyu yan tsirara wanda hakan ne ya bawa rana damar haskaka filin. Wayar ta ta yi kukan karshe sai dib ta dauke gaba daya chaji ya kare.
Cike da taikaici Zainab ta karasa inuwar wata yar bishiya yayinda ta yi cilli da akwatin na ta gefe guda ta zube a kasa ta na kuka mai fitar da sauti, ji ta ke ina ma bacci ta ke Allah ya taimake ta wani ya tashe ta da kuwa duk abin da wanan nan zai ce ya na so daga gare ta sai ta masa. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru sai ajiyar zuciya cikin ranta ta na mai tunanin mafita
Sam ba ta lura da lallausan abin da ta kafar ta ke take kai ba, bare ta ankare da katoton koran macijiya wanda ake kira kasa da ke kwance karkashin in da ta aje kafar ta ta ba ta na bacci. Sai da kasar ta dan motsa kadan sannan ta ankare, tsabagen firgice kasa ihu ta yi, haka kuma ta kasa tashi ta ruga dan karshen tsami kafar ta tayi dan zaman nan da ta yi bayan ta gama fama kafar. Dan rarrafawa ta yi ta na mai cije lebe yayinda duwatsu da itacen wajen ke sukar gwiwowin ta ta cikin duguwar riga, sai da ta tabbatar ta yi nesa da macijiyar sannan ta yi zaman ta dirshen a kasa tamkar zararriya. Hanyen ta biyu ta saka ta rufe fuskar ta tana fadin
"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Allah ka fitar da ni daga wannan kangin rayuwa, Allah ka kawo mafita, Allah ka kawo min doki....."
Kamar daga sama ta ji muryar shi ya ce
"Bar kuka Abu, Allah ya amsa gani ya kawo ni!"
A firgice ta dago kan ta, ganin wanda ke tsugunne gaban ta, idanun sa har sheki suke, duk da rabin fuskarsa rufe ya ke be sa ta kasa ganin murmushin mugun ta da fuskar sa ke dauke da shi. Wani irin tsanar sa ce ta mamaye zuciyar sa, kai tsaye ta furta
"Na tsane ka!"
"Alhamdulillah! Dama na fi so ki tsaneni, me zan mi ki ki kara tsana ta? Dan Allah ki ta tsana ta har illa mashaAllah! Ni Usman na mi ki alkawari zan mi ki rainon wannan tsana da ki ka mi ni!"
Cikin rashin fahimtar in da ya dosa ta ce
" Me ya sa? Me ya sa ka biyo ni? Kudi ka ke so? Idan shi ka ke so wallahi Ammy za ta ba ka ko nawa ne......"
Ya na mai dariyar mugunta ya sami waje ya zauna hakan ya sa Zainab kara jan na ta jiki domin yin nesa da shi. Sai da yayi dariya mai isar sa ya ce
"Kudi? Da shi ki ke takama ko? Shi ya sa ki ke tunanin kowa shi ne burin sa? Ki na tunanin dukiya ya sa na dauko ki? Wallahil azim in da za a hade dukiyar ku kaf ba zai yi kwatar dukiya ta ba, Ni bakauye ne amma ba matsiyaci ba, Dan haka dukiya ba ta daga cikin dalilin zuwan ki Rugar Shehu....!!!"
Baki bude Zainab ta ke kallan sa, ta na mai hadiyan yawun azaba domin kuwa makogaron ta ya bushe, ta kada baki ta ce
"Menene dalilin ka? Ya aka yi na zo nan? Ka mayar da ni makaranta yanzun nan!"
"Shhhhh!"
Usman ya katse ta ya na mai dora yatsa bisa labban sa ya ce
"Kul kar da ki tada macijiya, a matsayi na na Shehun rugar ga ba zan iya hana ko wani halitta abincin sa ba, ko da kuwa abincin halittar nan mata ta ce!"
Wani irin zufa ne ya ketowa Zainab yayinda da ta kai kallan ta ga inda kasar ke kwance ta na bacci, sannan ta mayar da kallan ta ga Usman ta sake furta
"Na tsane ka wallahi! Ka mayar da ni gida na ce! Damn you!"
Yana murmushin mugunta ya ce
"Umarni ki ke ba ni halan? Har yanzu ba ki gane cewa a dajin da Rugar Shehu take ki ke ba, Ni Usman ni ne Shehu, ba bil'adama kadai ba, hatta dabbobin dajin nan ni an Shehun su, Ni an shugaban su! Ina mi ki bayanin nan ba dan komai ba sai dan kar ki halaka....."
"Mtswww!"
Zainab ta ja masa dogon tsaki wanda ya tunzura Usman, ya tashi tsaye cike da motsawar zuciya ya ce
"Idan har ban cire mi ki wannan rashin kunya ta ki ba Abu cikin kwanaki kalilan wallahi ban isa Usman ba! Sai kin roki sassauci Abu, da bakin ki za ki roke ni sassauci...."
"Tir! Allah ya sauwake! Ba zan taba rokan ka ba ko da kuwa zan rasa rai na!
"Idan kin shirya rasa ran na ki ki zauna anan duk sanda maciyar can ta tashi ta yi kalaci da ke, idan kuwa kina son ran ki tashi ki bi mijin ki dakin auren ki"
Banza ta yi masa, ta na gani ya juya ya tafi zuciyar ta na dukan uku uku tsabagen tsoro, Amma kafiya ya sa ta dauke kai. Usman kuwa be yi zaton zai yi takun da yayi ba tare da ta biyo shi ba. Jin ba ta biyo shi ba har ya fara nisa ya sa ya juyo, ya gan ta zaune in da ya bar ta ko motsawa ba ta yi ba. Ya na mai girgiza kai ya dawo gare ta. Dan akwaitin ta ya fara dauka, ganin ya nufo ta ta kafe shi da manyan idanun ta da ta san ya na firgita duk wanda ta yiwa irin kallan, ba ta ankara ba sai ji ta yi ya furta
"Idanun ki ba za su taba firgita ni ba, idan kuma mutuwar ki ke son yi ba zan bari ki yi ba tare da na cimma buri na kan ki ba, ba ki isa ba"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.