Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 46
Kamar yanda ta saba masa gardama, yau din ma da kyar ya samu ta ci abincin da aka aiko musu, shinkafa ne da mai da yaji. Sai da ya ga ta danci sannan ya fara kokarin bata magani, nan ma sai yayi da gaske ta sha, aje kwaryar maganin yayi yayinda da ya jawo ta kirjin sa ya rungume. Yanda ya ji ta yi lamo ba tare da ta yi yunkurin kwatar kan ta ba Usman ya tabbatar Zainab na jin jiki. Cikin rada ya furta
"Ya zan yi da ke Abu? Duk yanda ki ka bata min! Duk yanda na so na gana mi ki azaba Abu na kasa, Abu kin cutar da ni amma gashi kin shiga rai na, ya zan yi da ke Abu?"
"Ka rabu da ni na mutu ko kuwa ka mayar da ni in da ka dauko ni"
Cewar Zainab daga can kasan makogaro. Usman ya dada rungume ta kamar wanda zai mayar da ita jikin sa ya furta
"Ba zan iya ko wani daya daga cikin su ba Abu, ba zan iya rabuwa da ke ba..."
Jin haka Zainab ta fara kokarin cire jikin ta daga na shi, hakan ya sa shi kara ruko ta sosai. Ya na shafa bayan ta ya ce
"Shhhhh! Ni da ke ba mu taba samun kusanci mai cike da nutsuwa irin na wannan yanayin ba, ki kwanta kawai Abu, ki yi shiru abin ki idan kin sami sauki za mu tattauna, Allah ya baki lafiya"
Karo na farko da Zainab ta bi umarnin sa cikin kwanciyar hankali, ta na mai runtse idanu ta yi kwanciyar ta jikin sa har bacci ya sace ta.
*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2
10
A hankali ya kwantar da ita tare da mata matashi da daya daga cikin kullin rawanin sa, ya mata addua ya tofe ta. Cikin sanda kar ya tashe ta ya wuce fada da niyar sauraran korafe korafen jama'ar Rugan Shehu kafin Zainab ta tashi.
Be yi cikakken minti ishirin da tafiya ba kukun daya daga cikin shanun gonar ya dami Zainab har ta kai ga farkawa. Duk wanda ya saurari yanda saniyar ke kuka dole ya gane ta na cikin azaba. Tun Zainab na iya jurewa a tunanin ta Usman na tare da shanu, har ta kasa ta fito, Nan ta ci karo da abin da ba ta taba gani ba tun da ta zo duniya, ba ga bil adama ba bare dabba. Saniya ce ke kai kawo, ta baro cikin yan uwan ta shanu zuwa farfajiyar bukka, duk sanda ta taka daya biyu sai ta tsaya ta na mai fitar da sauti yayinda wani farin abu ke kokarin fita daga jikin ta.
Ganin haka Zainab ta ja da baya a tsorace har ta na shirin rugawa duk da dai sam ba ta jin dadin jikin ta, kiran sunan Usman ta ke bilhakki yayinda ta duba lungu da sako na gidan gonar babu Usman babu alamar sa.
Jiki na rawa ta kara dawowa ga saniyar, sai sannan ta gane wannan farin abun mai yauki yauki ba komai ba ne fyace dan saniya ne ke kokarin fiitowa, Saniyar nan dai nakuda ta ke. Hankali Zainab ba karamin tashi yayi ba musammam yanda ta ga wajan na kara budawa duk sanda Saniyar ta dan tsaya tare da durkusar da kafafun ta na baya, haka kuma ta dan tasa sai ta cigaba da takawa, da ke dabba dabba ce ciwan da take be hana ta cin ciyawa ba duk sanda ta gifta ta gaban sa.
Kamar yanda Saniyar ke kuka haka Zainab ke taya ta, haka kuma ita ma ba ta fasa safa da marwa ba ta na mai bin sahun Saniyar. Usman tafe tun kafin ya iso gidan gonar ya ke jiyo kukan Saniyar, tsoran kar ta cutar da Zainab ya sa shi karasawa da gudu.
Sa kafar sa gidan yayi daidai da lokacin da saniyar ta durkusar da kafafun ta na baya, kamar mai Shirin zama kasa ta sullubo yar saniyar ta akan idanun Zainab. Idanun Usman kan Zainab, tashin hankalin da ta ke ciki be boye kyawun halittar ta ba, dan kuwa Usamn zai iya rantsewa tun da ya zo duniya be taba ganin bafulanar da kayan saki ya mata kyau ba kamar yanda yayiwa Zainab, rigar ya saukar mata har ciki, abun ku da mai hips sai zanin ya zauna mata a kugu ya mata cif cif.
"Abu..."
Usman ya kira sunan ta cikin wani irin yanayi, hakan ya sa Zainab juyowa da sauri dan sam ba ta lura da shigowar sa ba saboda idanun ta na kan saniyar nan da ke kokarin lashe abin da ta haifa. Ganin sa da gudu ta nufe shi, cikin kuka ta shige jikin sa hakan ya sanya Usman runtse idanun sa, kan ta bisa kirjin sa yayinda ta ruke sa gam ta ke fadin
"Haihuwa ta yi, a gaba na ta haihu! Wallahi ta haihu!"
Usman na mai shafa bayan ta cikin rarrashi yayi karfin halin furta
"Yi shiru bar kuka Abu, kin ga baki da lafiya, ai ta riga ta haihu ni ma kin ga wata rana haka za ki haifo min diya mai kama da ke....."
Cikin sauri ta zare jikin ta daga nashi, cike da tsiwa ta furta
"Allah ya sauwake na haihu da kai gwara...."
Cike da danasanin furucin sa da ya ja masa rage jin dadi ya furta
"Don Allah kar ki karasa! Kin ga dai muna da mai jego be kamata mu na hayaniya gaban yar jinjira ba! Bari na taimaka mu su"
"Mtswww"
Amsar da Zainab ta bashi kenan yayinda ya wuce ta ya na mata dariyar kyeta. Sai da ya cire rigar sakin sa da rawani ya rage daga shi sai dogon wando sannan ya shiga taimakawa saniya. Bini bini sai ya kama Zainab wacce ke zaune bisa kujerar tsakar gida daga gefe ta na satar kallan sa, daga sun hada ido ta yi saurin kau da kai gefe.
Cikin ranta mamakin kyau da kyan sura irin na Usman ta ke, lalle Usman ya isa wannan kalmar ta "Man" dan kuwa da a ce wayayye ne da Zainab ta yi alfahari da shi, duk abin da ta ke mafarki na kyawun da namiji Usman na da shi, gaba daya sai ya dishashe mata duk wani kyan Sudais da ta ke gani, sai dai Usman kauyenci ya masa kan ta.
"Ina ma a dauki wayewar Sudais a bawa Usman"
Cewar Zainab cikin ran ta, gaba daya ta shagala cikin tunani sai tsuntar idanun ta tayi cikin na Usman, hakan ya sa ta kawar da kai cike da jin kunya. Usman na murmushin jin dadin yanda matar ta sa ke satar kallan sa ya ce
"Babu komai Abu ki kalle ni da kyau, ai ni mijin ki ne lillahi warasulihi! Jira na ke ki shirya na fara biyan bashin sadakin da na mora!"
Cike da jin kunyar ya kamata a karo na farko Zainab ta nemi amsar da za ta bashi ta rasa, ta tsinci kan ta tana mai tambayar
"Mace ce ko namji?"
Cikin rashin fahimtar abin da ta ke tambaya ya ce
"Me fa?"
"Abin da ta haifa, mace ce ko namji"
"Oh mace ce"
Ya bata amsa a taikaice yayinda ya ke duban yar jinjirar saniyar, har lokacin saniyar na lasar abar ta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.