Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 46
Duk yanda ta so musgunawa Usman ko ya ji haushi ya mayar da ita abu ya ci tira, haka kuma ba ta fasa yi masu kashi ko wanka in da ta so ba, Usman na dauke kai ya sa yara su gyara. A haka har Zainab ta yi kwana uku Rugar Shehu, gaba daya ta fita hayyacin ta, kafa kam Alhamdulillah ta warke sosai ta bar zuciyar Zainab da jinya, tun tana kuka har hawayen ya sauke sai dai na zuci.
Da Safe bayan ya tashi daga zaman fada, ya zauna wajan bitar karatu da ya saba yi tare da yara maza. Zaune su ke tsakar gida, sun saka Usman tsakiya kowannan su dauke da alqur'ani ko kuma allo sanadiyar rashin wadatuwar alqur'ani cikin Rugar. Kai kawo da Zainab ke yi a tsakar gidan na ba gyara ba dalili ya sa Usman kasa nutsuwa. Sanye ta ke cikin daya daga cikin doguwar rigunan da ta zo da shi, ramar da ta yi be saka kirji ko hips din ta raguwa ba, illa dai kashin wuya da tsayin wuya da ta kara, ba sururu Zainab kadai ba hatta tafiyar ta ma abin sha'awa ne ga duk mai kallo, duk sanda ta gifta sai ya bita da idanu hatta daliban na sa sai da suka fahimci hankalin Shehu yau dai ba ya gare su.
Sallamar Bello da kuma ganin wanda su ke biye da shi ne ya sanya Usman hade rai kamar hadari yaAuren Shehu 2
6
Haɗe ran da yayi bai sa sun fasa ƙarasawa har in da su ke ba, su uku ne namiji ɗaya da mata biyu da za a iya cewa miji, mata da ƴarsu ne don ƴar ba za ta wuce shekaru goma ba.
"Me ya kawo ku nan Tanko"
usman ya faÉ—i cikin tsawa, ya kara da
"Bello me kake nufi kenan? So kake ka nuna ka isa a Rugar nan ko me ye dalilin ka na shigowa da wainnan iblisan?"
Ya cigaba da faÉ—i yana mai kallon Bello wanda ya sha jinin jikin sa jin lafazan Usman. Gyara tsayawa zainab ta yi cikin nishadi wanda ya kira jinin sa ya mata aikin da ta dade tana yi baya kama shi, amma kuma kallo É—aya ta yi ma wanda ya kira da Tanko ta hango kamanni na jini tsakanin su sai dai shi din baki ne, sabanin Usman da ya ke farar fata. Duk da ba jin yaren ta ke yi ba za ta tsaya ta kalli dramar da za a yi.
Haka ma sauran jama'ar gidan su ka fito suna mai kallan Tanko cike da mamaki da al'ajabi, dan kuwa babu wanda be san mugun halin Tanko ba. Daliban Shehu kuwa musammam kanana cikin su har rawar jiki su ke ganin yanda Usman ke bambami.
"ka dubi girman Allah Shehu, ka dubi nasaba da martaban ka, ka dubi darajan yarinyar nan Cangwai da ta fito daga tsatsonka ka yafe mana"
Macen ta faÉ—i tana mai share hawaye.
"Baffa Allah ya masa cikawa bayan kun baro sa, ba mu da kowa shi ya sanya muka ce mu zo cikin Æ´an uwa mu zauna, wallahi duk wani mugun abu na bar shi a dajin falgore, Tanko mai kyawun hali ne nan, ka yafe mana"
Tanko ya caɓe cikin fullanci yana mai rusunawa kamar zai yi sujada. Cikin lafiya da nuna rashin tausayi Usman ya furta
"Rugar nan tsarkakakke ne babu É—igon mugun aiki a cikinta, saboda haka baku da matsuguni ku fice kafin na saukar da fushi na akanku"
yayi maganar ya na mai nuna masu hanyar ficewa daga ɓangaren nasu. Daga Tanko har matar shi zubewa su ka yi gwiwowi biyu, hawaye na zuba daga idanun sa ya ce
"Ka taimaka Shehu, ba mu da matsuguni Shehu, duniya ta juya mana baya, idan ma ba za ka karbe ni ba ka duba Rahila da Cangwai, Raliya diya mace ce, ko ba komai Cangwai diyar ka ce...."
"Cangwai ba diya ta bace!"
Usman ya katse shi cikin tsawa yayinda ya kai kallan sa ga yarinyar da Tanko ya kira Cangwai, be gushe ba ya kara da
"Na sani! Ka sani! Na san ka sani! ku kama hanyar ku tunkafin rai na ya fi haka baci"
Maimakon su juya Tanko ya shiga waige waige yana mai rokon mutanen da ke wajen da su sanya baki Shehu ya yafe musu a nan ne ya hango zainab da ke tsaye. Ba shigar da tayi na doguwar riga kaɗai ya ɗauke hankalinsa ba har da bambamta da tayi da sauran matan rugar, in bai yi ƙarya ba irin matan birni da su kan sace don neman kudin fansa ne.
'toh me ta ke yi a rugar shehu' ya tambayi kansa. Gaba É—aya ta manta abin da ya ke yi ya saki baki yana kallon zainab tare da zantawa da zuciyar sa. Yanda ya saki baki ya na kallan ta ne ya sa Usman ya kai kallo gare ta, ganin Tanko ya sa shaf ya manta da ita. Wani irin bakin kishi da tun da ya zo duniya be taba jin irin shi ba ya taso masa har kahon zuciyar ta, musammam da ya lura Zainab din ma Tankon ta ke kallo
"Me kike yi a wajen nan? maza shige ciki!"
Shehu ya daka mata tsawa da firgici ya hana mata musawa cikin sauri ta shige bukkan, sai da ta shige sannan ta ji haushin kanta na yin biyayya da ya daka mata tsawar. Daga bakin assabari ta laɓe tana kallon yanda mutane ke roƙon usman yana botsarewa.
"Kai an yi azzalumi! komai aka yi wani zalincin ya ke aikatawa! Wannan masifa har ina! Ina ma ina jin abin da su ke fada! Ya Allah idan har wannan bawa zai iya aikata sharri da zalinci ga jinin sa, Allah kai kadai ka san irin zalincin da zai iya aikatawa kai na, ya ke kuma kan aikatawa, ya Allah ka mana maganin shi.
"Zan iya karbar Rahila da kuma diyar tsohuwar mata Cangwai saboda raunin su na 'ya'ya mata! Wajan ka dai babu shi Rugar Shehu, idan har hakan ya maka toh, idan be ma ka ba su ma din kana iya tafiya da su!"
Cewar Usman wanda kallan da ya ga Tanko ya na yiwa Zainab ne dalilin shi na biyu na rashin yarda ya zauna a Rugar Shehu. Rahila matar Tanko ta na ji tana gani Tanko ya mata sallama tare da mata alkawarin zai dawowa da ya sami matsugunni. Kukan Rahila da Cangwai be sa Usman ya tausaya ma su ba, sai ma sallamar yara da yayi daga karatu, shi da Bello su ka tasa Tanko gaba, sai da su ka tabbatar yayi nisa da Rugar Shehu, sannan Usman ya ce da shi be hana shi zaman dajin ba matukar ya kiyaye kusantar Rugar Shehu.
Tuni labarin zuwan Tanko ya kadaye Rugar, ranar da jimamin abin da ya faru aka wuni, ita kan ta Zainab sai da zuciyar ta ta dan yi rawa sanadiyar ganin rikidewar Usman cikin kankanin lokaci duk da sam ba ta fahimci ainihin abin da ya gudana a tsakar gidan ba.
Usman kuwa tun bayan da ya tasa kyeyar Tanko, haka kuma ya tabbatar ya ja kunnan Bello be iya komawa sashan shi ba gudun kar ya kara saka Zainab a idanun sa, wani irin bacin rai ke addabar zuciyar duk sanda ya tuna yanda Tanko ya shagala ya na kalle Zainab, wacce ta tsaya kerere da ita ko mayafi babu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.