Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 34 of 46

Abincin na su babu laifi, Amma kasancewar ta na cikin bakin ciki da kewar Usman da kyar ta dan caccaka sannan ta yi sallah ta na mai rokan Allah mafita. Kasancewar Zainab ta kwana biyu ba ta kwana kan katifa ba, sai ta ji gadon ya mata wani irin, ta gwammaci ta yi kwanciyar ta bisa dadduma duk da ta san baccin ba zuwa zai yi ba.
Da sassafe wajan karfe Shida ya sanya ta motar Kano, Zainab na masa magiyar kar ya barta shi kuma Bello ya na bata hakuri, har ta kusa tara masa jama'a ciki har da masu cewa

"Toh ana tafiya dole ne? Tun da ta ce ba ta yi a rabu da ita mana"

Wani kuma fadi ya ke

"Kai kuwa ka juya da ita mana"

Cike da rarrashi Bello ya furta

"Ki yi hakuri uwar gida, ban san takamamman dalilin da ya sa Shehu hakuri da ke ba, bayan jaddada soyayyar ki da yayi a gare ni, Shehu na kaunar ki matuka kusan sai na ce ke ce diya mace dal tilo da zan iya bugar kirji na ce Shehu ya so, so daya tal! Shehu ya zabi barin mu, barin Rugar Shehu da komai na shi domin ya dawo birni ya rayu da ke. Dan haka ni sai dai na ce ki yi hakuri, wannan al'amari na ku da daure kai ya ke, Allah ya saka hakan ya fi zama alkhairi, Allah ya sada mu da alkhairin sa, bissalam"

Ya juya ya na mai matse kwalla, in da ya bar Zainab cike da da na sani iri iri, musammam na kasa rokan Usman da ta yi, da ta sani da ta nemi yafiyar shi, da ta san zai ce su dawo birni da ba ta ji zugar Rahila ba, da kuma ba ta bari zugar Raqeeba ya rude ta ba, duk da a lokacin neman hanyar tafiya ta ke Ido rufe, yanzu gashi Allah ya yassare mata lokacin da sam ba ta bukatar komawar ta gidan. Gaba daya rayuwar ta ta sauya cikin watanni kalilan, shin ina ta dosa? Daga ina za ta fara? Tunanin da ta yi ta yi kenan a hanya.

Ba kamar da ba duk check point in aka tsaya sojoji sai sun tanka ta, wannan karan babu wanda ya lura da ita saboda shigar fulanin da Usman ya sanya ta tayi, da kuma wannan shekin da fatar ta take gaba daya ya tafi. Sanda su ka isa Kano Magarib ta yi, dan sahu ta tara ya kai ta gida. Amma ko da ta doshi kofar gate din gidan Malam, gaban ta na faduwa ta shiga bugawa, wani saban maigadi ne ya bude. Ganin mace tsaye bakin kofa ta yi dagaje dagaje da ita cikin kayan fulani ya dube ta ya ce

"Lafiya? Ku barar ku ba dare ba rana?"

Cike da bacin rai Zainab ta furta

"Na ma ka kama da yar bara? Kai wanene ma?"

"Kut! Kanin uban ki ne ni! Ja'ira! Sai ki ta zama a nan tunda ke abin na ki ma har da rashin kunya!"

Baki Zainab ta bude, duk tsiwar ta yau sai gashi ta rasa ta cewa, wai ita ake kira almajira a gidan uban ta. Katan dutse ta dauka ta shiga buga kofar da iya karfin ta. Isowar mota tare da fitowar Jauro da saban maigadi wanda bugun da Zainab ta ke yiwa gate din ya sanya su fitowa a fusace lokaci guda ne. Motar ce ta dalle Zainab wacce Jauro ya hau da fada da shi kan shi be gane ta ba, fadi ya ke

"Wallahi sai mu yi kasa kasa da ke a wajen nan! Kofar gidan uban ki ne za ki kama da bugu ko akwai wanda ki ke bi bashi? Kai muntari ko wani ya siyi nono gun ta ne be biya ta ba?"

Cike da takaici Zainab ta furta
"Kai din gidan uban ka ne ai! Ba nono ba Shanu ya sa siya! Wallahi duka sai kun ci uban ka ni Zainab sai na yi maganin ku!"

Jin Murya irin ta Zainab Jaura ya bude idanu ya na duban ta, gaba daya ya ma manta da motar da ta tsaya ta na shirin a bude kofa su shiga. Muntari da har lokacin be gano komai ba cewa yayi

"Wallahi ban taba siyan nono gun ta ba, kai ni yau ma na fara ganin ta...."

"Hayaniyar me ku ke mana ne da ba za ku zo ku bude mana kofa ba?"

Cewar Falmat wacce ta gaji da sakarcin su Jauro, ta sauke gilashi cikin neman ba'asi. Gefan ta Halitta ce zaune, da ke sa'ad da su ka je umara ta makale lalle sai da Sudais ya bari ta biyo su Nigeria, za ta yi wata guda ya zo ya dauke ta.

Tsayawa Zainab ta yi ta na duban motar cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, dukan su biyun ba su lura da ita ba, musammam Falmat wacce ta ke bambamin sun ki su bude mu su gate su shigar da mota.

Cikin inina ya na mai nuna Zainab da yatsa Jauro ya furta

"Ran-ran-ki ya da-de ina ga fa kamar dai Hajiya Yakura ce......"

Sai a sannan su ka lura da Zainab, Halitta ce ta fara fitowa da sauri inda Falmat ma ta bi bayan ta, gaban ta su ka karasa idanun su kan Zainab yayinda ita ma din su ta ke kallo, shigar su, yanayin su da kamai na su yayi daban, musammam Halitta wacce ta yi jajur kamar balarabiya cikin bakar abaya. Sai Zainab ta ke jin kan na ta tamkar almajira kamar yanda saban mai gadi ya yi zato, hawayen da su ka dade ba su zuba daga idanun ta ne su ka fara shirin zubowa, ta yi saurin kawar da kai gefe.

"Yakura.........."

Cewar Halitta yayinda ta rungumo ta da sauri, kamshin turaren ta ya maye warin ranar da Zainab ta kwaso, ta ma rasa yanda za ta yi, murnar ganin Yakura ko kuwa kuka za ta yi, Falmat kuwa rugawa ta yi ciki ta ihu fadi ta ke
"Yakura! Yakura ce! Wallahi Yakura ce! Ammy Allah ya karbi adduar mu!

Halitta ta janye Zainab ciki dan kuwa yan unguwa har sun fara tsayawa ganin ba'asi. Ammy ba ta gasgata maganar Falmat ba sai da ta ga Halitta ta shigo hannun ta rike da na Zainab, nan ta zube ta yi sujjada na godiya ga Allah sannan ta tashi ta rugume Zainab, dukan su hudu kuka su ke, aka rasa wanda zai rarrashi wani, musammam Zainab wacce ita na ta kukan biyu ne, har da na rashin Usman.

Sai da su ka dan nusta ne Falmat ta fita shigo da mota, Halitta zaune kusa da Zainab har lokacin ta kasa sakin ta, Ammy ce ki ta kiran yan uwa da abokan arziki ta na sheda mu su Allah ya dawo da Zainab, Yakura ta dawo. Anty Sauda kuwa cewa ta yi da Yakura ta huta Ammy ta fara tambayar ta in da za a samo tsinannen almajirin nan da kuma in da ya kai ta, idan Allah ya wayi gari ita za ta zo.

Duk yanda su ka so Zainab ta fada mu su daga in da ta ke, ko kuma yanda aka yi aka tafi da ita, da kuma wanda ya tafi da ita sai Zainab ta sa mu su kuka. Hakan ba karamin dada tayarwa Ammy da hankali yayi ba, dan haka ta ce kada wanda ya kara tambayar ta komai, a bari ta huta tukunna ko zuwa gobe ne.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.