Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 30 of 46

Cewar Tanko, be gushe ba ya mayar da kallan sa ga Zainab ya na mata irin kallan nan na kurulli ya furta

"Ke kuma zan mayar da ke gida amma sai na karfi kudi makudai daga wajen iyayen ki sannan na more jikin ki san rai na....."

Be san sanda Usman ya matsa gaban sa ba sai saukar mari ya ji kawai, ya ja da baya ya na mai dura zagi. In da yaran sa su ka yo kan Usman a fusace su na Shirin bugun sa, Tanko na mai huci ya furta

"Ah ah kada ma ku soma, Ni nan ni zan jibgi dan bantan uba! Ku daure min shi!"

Nan su ka fara yunkurin daure Usman in da shi kuma ya ke kokarin bubbuge su musammam da ya ga Tanko ya kai hannun sa jikin Zainab wacce ke kuka da ihu ya ja ta gefe, fadi ta ke

"Dan Allah ku rabu da shi, duk abin da ku ke so za a baku, kada ku kashe shi"

Sai da su ka sa igiya suka daure Usman tun daga kafadar sa har zuwa kafafun sa, sai gashi kwance tamkar gawa. Tanko na mai duban Zainab ya furta

"Abu uku na ke so, kuma duka sai na dauka, sarautar Rugar Shehu! Jikin ki! Sai kuma raba mijin ki da ran san sa!"

Ba Zainab ba, ita kan ta Rahila sai da gaban ta ya fadi jin har da jikin Zainab cikin lissafi. Zainab kuwa yawu da kaki ta tofa fuskar Tanko, tare da fadin
"Sai dai gawa ta kaskantacce mara mutunci! Za ka sake shi ko sai na bata ma ka rai!"

Tanko ya tunzura saboda sam ba ya iya jure tsiwa, bare kuma ga yawu Zainab ta tofa masa. A fusace ya dauke ta da marin da sai da Usman ya motsa ya na kokarin kuncewa, Zainab kuwa sai ta ga wuta a idanun ta ba, ba ta gama warewa daga zafin marin ba Tanko ya soma jibgar Usman da bakin bindigar sa har ya kai ga fasa ma sa kai. Kuka sosai Zainab ta ke yayinda ta ke kokarin shigar masa, Tanko ya hankada ta gefe, ya durkusa gaban shi ya furta

"Ka san dalilin da ya sa na ce a daure min kai haka dan uwa na? Saboda ba zan kashe ka da bindiga ba gudun kar yan sharo su ji karar ta, haka kuma ba zan kashe ka da wuka ba, mutuwar za ta ma ka sauki da yawa, yanda ka ke haka haka zan jefa ka cikin kogi, ka sha ruwa ka koshi har ka sheka barzawu, ni kuwa ina can ina morewa da matar ka, sai na tabbatar dukkanin tudun jikin ta ya saki sannan na mayar da ita ga iyayan ta, Rugar Shehu kuwa ka tabbatar ta zama tawa yanda na yi ma ka, haka zan wa Bello! Bissalam"

Ya tashi tsaye yayinda ya bawa yaran sa Umarnin su dau Usman su jefa shi ruwa. Akan idan ta su ka dau Usman gadan gadan, idanun sa wanda su ke rabi a rufe a kan ta, ta fara ihu kamar wacce ke shirin zarewa fadi ta ke

"Dan Allah ku yi hakuri kar ku kashe shi! Dan Allah Rahila ki sa baki kar su saka Usman cikin ruwan nan!"

Karar saukar Usman cikin ruwa da yanda ruwan ya tashi daboda yanda su ka jefa shi da karfi ne ya sanya Zainab saka ihu mai tsananin kara kafin ta zube kasa sumammiya.
Auren shehu 2.

Tanko na dariyar mugunta ya dauki Zainab ya É—aura a kafada, ko kallon in da Rahila ta ke be yi ba bare ya lura da yanayin da ta shiga na sanadiyar zantukan da ya ke fada game da Zainab. Da sauri ta sha gaban sa, cikin bambami ta furta

"Me ka ke nufi Tanko? Ina fatan kalaman da ka ke akan tarewa da wannan kaÉ—on ba gaskiya ba ne, In kuwa da gaske ka ke wallahi ba ka isa ba! Ba ka isa ka tara da wata mace wacce ta ke ba halas din ka ba gaban idona na"

"In kuma na yi fa? Me za ka yi? Ku ji mu da shashasha! Jiki duk ya bushe ya jeme ki na tunanin zan ga jiki kamar na kado na bari? Sakarya kawai!"

Cike da bacin rai Tanko ya maida mata da martani yana mai cigaba da tafiya, ganin da gaske tafiya yayi da Zainab nan take wani turirin kishi ya yi gaba da ita, gaba É—aya ta daina ganin gabanta, juyawa ta yi a guje, tana tafe kamar kububuwa, daga Tanko har yaran sa ba su lura da juyawar Rahila ba, halin su ya raja'a kan nasaban da su ka ci kan Shehu, ga kuma Kado an samu, idan Tanko be yi san zuciya ba kila su ma su sami raban su daga jikin ta.

Inda ake sharo Rahila ta koma a guje, ihu take ba ta ko iya tantance mai take fadi. Ganin yanda ta iso filin da ake sharo É—in ne ya dawo da hankalin mutane gareta

"Me ya faru? Me aka yi?"

Æ´an matasan da ke wajen su fadi a tare suna masu É—aga sanduna da addunansu. Haka Kuma Muhammad Bello ya shiga raba idanu, nan ya ankare da rashin Usman da Zainab a filin.

"Tannn... ko! KaaaaÉ—o!! Sheehu ruwa!!!"

Rahila ta ce muryarta na haɗewa. Nan wajen ta faɗi tana mai kuka cike da ƙunan zuciya, tana jin labarin kishi amma Sam ba ta san haka ya ke da raɗaɗi ba, ta san ko kusa ba za ta haɗa kanta da abu ba, ta san matukar Tanko ya lashi zumar kaɗo tabbas ba za ta sake ji ta kansa ba. Kuka ta ke yi mata na rarrashinta duk a tunaninsu su zainab ta ke tausayi.

Su Bello kuwa tare da sauran ƴan matasa har ma da wasu daga cikin manyan da su ke da saurin ƙarfin su, Rarraba kansu su ka yi cikin daji Allah suna neman zainab, wainda su ka iya ruwa a cikin su kuwa su ka far ma ruwan da Rahila ta ce an jefa shehu.

Wajen zaman Tanko aka fara zuwa nan su ka iske babu kowa a wajen, har tawagar su Bello za su juya su ka hangi wata sabuwar bukka can nesa ta gabas daga inda su ke, ba su yi ƙasa a guiwa ba su ka isa, mazan da su ka gani a tsaitsaiye riƙe da bindigogi ya sanya su yin turus, sai da su ka ƙaraso ne su ka ga ashe ba ma bukka ɗaya bane sun kai biyar.

ÆŠaga bindigogin su ka yi suna mai sai ta su, dakatawa su ka yi da fari, amma tunawa da su ka yi Shehu ya sa an haÉ—a maganin bindiga sun sha kwanaki ya sanya su dosar bukkar ba tare da ko wace shakka ba.

Karar fitar harshashi ne ya sanya Zainab farfadowa daga suman da ta yi. Ta mai raba idanu cikin kokarin gano in da ta ke, idanun ta ya sauka kan Tanko, wanda ke tsaye kan ta ya na shirin afka mata kenan ya ji alamun isowar su Bello.

Cike da bakin cikin an katse masa abin da ya ci buri ya ja tsaki, ya dau bindigar sa a fusace ya na duban Zainab ya ce

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.