Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 38 of 46

In da Allah ya kawo abin da sauki, sai ya hada jinin Umar da Usman, yanda ado da wayewar Umar ke burge Usman, shi kuma Usman kamala da ilimin addinin Usman ke burge shi, musamman da ya ji ya na larabcewa da wasu daga cikin abokan sana'ar su da su ke Larabawa, sannan duk wani muhadara da majalisin malamai Usman na kokarin zuwa wani lokaci har gayyatan Umar din ya ke. Kullu yaumin Umar na kokarin jan Usman jiki kamar yanda mahaifin sa ya ba shi umarnin, duk dai Usman na dan janye jikin sa ba dan komai ba sai gudun kar ya kwafsawa Umar, duk wata harka da ya shafi shiga cikin mutane sai Usman ya nemi ya janye jiki, har sai Umar yayi da gaske kafin ya yarda ya bishi. Duk wanda kuwa ya kuskure ko kallan banza ne ya yiwa Usman lalle kuwa a ga fushin Umar.

***

Hutun Halitta wacce ita ce mai debewa Zainab kewa ya kare, Sudais ya ce lalle ta hado nata ya nata ta koma Saudi ba zai iya zuwa Nigeria ba kamar yanda ya mata alkawari ba saboda yanayin aiki da ya yi yawa.

Da yamma likis Halitta shirye tsaf, sanye cikin bakar doguwar riga, suna tafe suna hira Zainab ta raka ta har mota in da Ammy da Falmat ke zaune suna jiran ta su kai ta Airport. Har ta zauna ta dubi Zainab wacce ke tsaye ta na duban ta. Sanye da hijab ruwan dorawa da ya kai mata har kasa, gaba daya ta sauya ba walwala ba farin ciki, kullum cikin damuwa ta ke har ta kai ya fara nunawa a jikin ta.

"Dan Allah Yakura ki rage damuwa ko dan cikin da ki ke dauke da shi"

Cewar Halitta cike da damuwa. Ta kara da.

"Zan mi ki addua in Sha Allah......"

"Idan har irin adduar da kuka min ne har Allah ya sa na dawo gidan ba na so, da ba ku min ba da yanzu ina tare da miji na..."

Jin haka Ammy ta kauda kai gefe. Falmat cikin ran ta cewa ta yi 'aha dama zancen kenan Yakura ta zama sai ka ce mayya!"

"In Sha Allah zan mi ki adduar mafi alkhairi a rayuwar ki"

Cewar Halitta. Zainab ta kada baki ta ce

"Usman ne mafi alkhairi Halitta"

Halitta na mai murmushin yake ta furta

"In dai shi ne toh Allah zai warware komai Yakura, bi'izinllah"

"Allahumma amen, Allah ya tsare ya sauke ku lafiya"

"Ameen ameen, ma yi chatting, ko da yake ke fa ko wayar ma ba ki da shi bare na chat, ki taimake ni Yakura, kira daga Saudi tsadi, ki samu yar waya sai mu ke gaisuwa ta social network, ki taimaka"

Zainab na murmushi ta bata amsa da

"Yar ana ce zai yi tunani akai"

Da haka su ka yi sallama jikin kowa a sanyaye.

***

Watannin Usman uku suna kasuwanci tare da Umar Balla. Hidimar da ke gaban sa be sa ya manta Zainab daidai da sakan daya ba, da ita ya ke tashi da ita ya ke kwanciya cikin ran sa. Wani sa'in sai yayi da gaske ya ke iya jure rashin ta. Har Umar ya kai ga ganewa akwai damuwar da ke tattare da shi, amma ko da ya tambaye shi dalili ce masa yayi babu komai kawai yakan dan yi tuntuntuni ne akan Rugar Shehu da kuma yanda zai bunkasa Rugar a sami cigaba.
Tafe su ke cikin motar Umar, kan hanyar dawowar su daga Mambila in da su ka je su ka yi cinikin shanu. Umar wanda ya ke baki, be da tsayi sosai amma kuma ba a kira shi gajere ba, haka kuma kyawun sa na ba yabo ba fallasa, sanye ya ke da kanana kaya, bakin wando da jar riga mai gajeran hannu. Usman da ke gefan sa sanye da wannan shigar ta sa da ya saba, riga yar shara, da rawanin sa da ya koma yi tun bayan tafiyar Zainab. Hankalin Umar kan kwalta ya furta

"Ni kuwa da za ka bi shawara ta Usman da fili za ka siya babba ko da kuwa a wajan, ka gina gidaje ciki in ya so ka kwaso duka jama'ar Rugar ta ka, ku yi zaman ku ciki "

Cikin kaguwa Usman ya furta

"Shin ka na ganin haka me yiwuwa ne? Kai mutane na fa ba kamar na ku ba ne, zaman bukka ya fiye mu su zaman binni da wahalar ta, Ni dai da ka ganni nan ni ke da kwadayin birni..."

Dariya Umar yayi jin furucin Usman, dan kuwa ya san har ga Allah ya sosa masa in da ya ke masa kyakayi. Kana ya ce

"Ina ce so kake ka bunkasa Rugar ta ku? Ka na tunanin wannan tsarin da Shugaban kasa ya ke so ya aiwatar mai yiyuwa ne? Ko ba ga yanda kudanci da wasu bangare na arewacin kasar nan ke sukar tsarin ba? Ka ga wannan Ruga settlement din ba abu ne mai faruwa nan kusa ba, Amma kai a karan kanka za ka iya kwatantawa ta ka Rugar, tun da babu laifi Allah ya ba ku arziki na dabbobi kwarai da gaske, da kuma taimakon yan kasuwa na nan Nigeria da kuma na kasashen waje wanda za su sa hannun jari a tada hanyar arziki mai girma, ina mai tabbatar maka za ka shahara kwarai"

"Kai wannan maganar ta ka ya sa ni tunani Umari, wa ya ga jama'ar Rugar Shehu kusa da birne!"

Umar na dariya ya furta

"Kai ba ma kusa da birni ba, idan ma cikin birni ka ke so ka kawo su ai ba abu ba ne mai wuya, dama naira ce wuyar, kuma Allah ya hore, ana nan ana nan sai ka aure matar birni, dama ana ta min maganar ka, ana ta kawo sakon gaisuwa fa"

Gaban Usman ne ya fadi, yayinda da Zainab ta fado zuciyar sa. Cikin kokarin waskewa da maganar aure ya furta

"Wace matar birni ce za ta so bagidaje dan kauye Irina? Ai mata sun fi son wayayyan mutum"

Umar na duban sa ta wutsiyar ido ya ce

"Wai kullum aka yi magana sai ka ke kawo wayewa wayewa wayewa! Wai kai wata irin wayewa ka ke magana?"
Zuciyar Usman daya ya furta

"Wayewa ai shi ne boko, ka ga kai da ka ke dan boko Umari hatta shigar ka daban ta ke, yanayin ka daban kai komai na ka ya fita daban ba kamar ni dan daji dan Ruga ba, wanda ko aji ban taba shiga ba bare a kai ga jami'a, ko zo a kashe ka da turanci ba ban sani ba...."

"Da larabci fa?"
Umar ya katse shi ya na mai take mota ganin ya sami sararin hanya.

"Ah wannan Alhamdulillah ai har labari sai na baka da shi"

Kai Umari ya gyada, be gushe ba ya kara da

"Wannan larabcin da ka iya ya fi turancin da ka ke ihun ba ka iya ba, ilimin da ke da shi na addini ya fi wannan bokon da ka ke tunanin shi ne wayewa, da ilimin boko shi ne wayewa da tun lokacin manzo (SAW) za a fara boko, addinin islama shi ne wayewa, ba ka taba yin bokon ba ne, da ka yi da za ka gane cewa komai da ake koyarwa a bokon musammam na bangaran kimiyya akwai su cikin alqur'ani da hadisin Manzo (SAW)"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.