Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 39 of 46

Usman na mai gyada kai ya furta
"Allahu akbar"
Umar ya kara da

"Wannan rudun da ka ke gani na duniya, ba wayewa ba ne, wannan ba komai ba ne illa zamananci, ka ga wannan shiga tawa da ka ke gani ya ke burge ka, nan da shekaru masu zuwa sai ka ga ana kiran sa da old fashion, ma'ana an bar yayin sa, zamanin sa ya wuce, Allah shi ne zamani Usmanu! Haka kuma mutane nawa ne ga su yan birnin kuma yan boko amma hakan be sa sun kasa shirme ko rashin azanci a rayuwar su ba? Soboda sun yiwa wayewa fahimta daban har ya kai su ga halaka. Haka kuma ita jami'a da ka ke gani, waje ne koyan rayuwa, waje ne in da mutane iri iri daga sassa daban daban ke taruwa domin koyan ilimin boko, toh amma daga karshe ba ilimin kadai ake koya ba, har da dabi'u na dan Adam, mai kyau da mara kyau sai dai wanda yayi dace, da kuwa ilimin addini shi ma ya na da gurbi irin yanda boko ya samu a zukatar bil adama da kuwa boko ya zama ba koman komai ba"

Umar ya fadi ya na mai kallan Usman. Ya kara da

"Ai kai ma wayayye na Usmanu, in kuma ka na so ne ka zama dan zamani zan maisheka dan zamani na koya maka shigar yar birni, Amma fa idan matan birni su ka sako ka gaba ba ruwa na"

Ya karasa maganar ya na dariya. Shi ma Usman din dariyar ya ke, nan kuwa be san Umar har zuciyar sa ya ke magana ba, dan kuwa daga lokacin ya sha alwashin wanke Usman tas ya mayar da shi dan zamani kuma dan birni.

*****
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, in da Zainab ke renon cikin Usman, tare da fama da son shi da tsananin kewar sa, har ta kai in ta yi sujjada ta kan roki Allah ya cire mata soyayyar Usman daga zuciyar ta, amma sai ya zama tamakar abin ma dada karuwa ya ke, dan haka sai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Halitta ce ta dage sai da Zainab ta sami waya, amma iyakar ta WhatsApp, bayan shi ba ta wani social network. Zainab the slay Mama ta zama salihar Dady a zahiri da badini, haka kuma ta na kokarin yiwa Malam addua sosai,

Bangaran Usman kuwa yanda Umar ya dage akan mayar da shi dan zamani ya sanya shi mika wuya wajan daukan darasi, ta suturun Usman ya fara, sai da ya tabbatar Usman ya ba da dukkanin kayan sa na ruga sannan tasa shi gaba ya masa ordering shaddu getzner na gani na fada daga SAFFAD Fabrics and more na Hajiya Safiyyah Ummu abdoul, . Rabin shaddu farare ne guda ishirin, sai kuma shudi, ruwan kwai, da kalar toka guda goma. Haka kuma ga material na maza da su boyel. Kanana kaya da takalma ne ya sa ka abokin sa mai shigo da kaya da Uk ya kawo masa. Tun Usman na kokawa akan kudin da Umar ya ke sa shi kashewa, sai gashi shi ma ya zo ya na alfahari da su bayan isowar kayan ya ga kyan su.

Dinki irin na zamani wanda yawanci irin na Umar din ne ya sa aka yiwa Usman, kai hatta roll on sai da Umar ya koyawa Usman yanda ake amfani da shi. A hankali ya ke kokarin fito da Usman gari duk da ba karamin fama ya ke sha da shi ba wajan saka kananan kaya, sai Usman ya ce masa shi wallahi ya na jin kan sa tamkar tsirara musammam idan rigar mai karamin hannu ce. Ran da kayan sa na Uk su ka iso ranar Umar ya zo har gidan gona ta tasa Usman a gaba lalle ya saka daya daga cikin su ya fito ya same shi ya na jiran sa cikin mota.

Umar na zaune cikin mota har ya fara tunanin sake komawa ciki ya taso kyeyar abokin na sa, sai gashi ya fito cikin kananan kaya, shudin riga mai haske, da shudin wando mai duhu, shi kan sa Umar be san sanda ya saka ihu ba ganin yanda kayan ya karbi Usman kwarai, fadi ya ke

"Yo mutumina! Lalle yau za mu dau magana!"

Cike da kunya Usman ya karasa gaban sa, sai a sannan Umar ya lura da silifas ruwan dorawa da ke kafar Usman. Ya na dariya har da kwarewa ya furta

"Toh Malam Shehu! Wannan silifas da ka sha haka ina zuwa?"

Usman na mai kallan kafar sa, da iya gaskiyar sa ya furta

"Yo menene toh? Silifa din ma ba ni sawa?"

"Ka ga wannan magana ta ka sai ka canza Alhaji, kar a ga gaye iya gaye amma in ya bude baki sai aji maganar yar Rugar Shehu"
Usman ya kai masa duka, Umar ya kauce ya na dariya, ya kara da

"Haka kuma tsakanin ka da silifas dan Usumanu sai dai a bandaki, wallahi babu in da zan kara zuwa da kai da silafas kafar ka!"

"Sai na yi zamana! Kai ni fa da na san haka za ka uzzara min da ban ce ina san wayewar nan ba!"

Umar na dariya ya wuce ciki ya na mai furta

"Zamananci dai ko, na fada ma ilimin addanin musulunci shi ne wayewa, wannan da ka ke koya zamananci ne, gishirin zaman duniya"

Usman na duban shi har ya shige ciki, cikin ran sa ya na mamakin yanda ya saba da Umar sosai, dan tun da ya ke be taba yin aminci da abota da kowa ba kamar Umar, cikin kankanin lokaci su ka saba da juna sosai kullum su na tare, haka kuma Alhamdulillah harkar gidan gona ta karbe shi, haka kuma shawarar Umar da ya bi shi ma da alama za ta bulle masa. Ya siyar da shanu fiye da dari biyu da hamsin daga cikin shanun sa, da kudin su ka yi cinikin wani katan fili duk da dai yayi wajan gari kadan amma babu laifi wajan da kwanciyar hakanli da kuma tsaro kasancewar yayi kusa da daya daga cikin check point na sojoji, in da dama nan su ka yada zango kusan na dundundin.

Umar ya fito dauke da daya daga cikin sau cikin da aka turowa Usman. Da kyar Usman ya yarda ya saka. Haka su ka fita ya na masa mitar ya takura masa, shi fa takalmin nan ya matsa masa. Asibitin hakurin da ya ke zuwa ya kai Usman, ga mamakin sa sai gashi dentist din da su ka gani ta ce Usman ba ya bukatar wanke hakori, hakoran sa are so perfect, sai dai Umar ne ke bukata. Ko da Umar ya koka sai Usman ya murmusa kana ya ce

"Kai ne fa Umar ka fadakar da ni cewa addinin mu shi ne wayewa, Manzo (SAW) ya ce ba dan kar ya takurawa al'umar sa ba da ya ce su dinga asuwaki kafin kowacce alwala. Ka ga ban san brush da wannan abun da ku ke shafawa kai ba, Amma na san aswaki da Manzo ya koyarda da mu, shi ya sa baki na ke da tsafta da haske"

Umar na gyada kai ya furta

"Hakkun ka yi gaskiya, Amma kuma wannan karan za ka kara da zamani, idan mu ka gama da asibitin nan za mu biya shopping mall mu siyo su brush da abin goge bakin ka ga sai ka kara wasai ko?"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.