Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 46

"Kai zo ka zuba min ruwa...."

Yaro ya tsaya ya na kallan ta ba tare da ya motsa ba, Zainab ta ja tsaki yayinda ta aje bokitin, hannun ta na dama ta sa ta bude randar, da modar da ta gani bisa randar ta debo ruwa ta na mai murzar sabulu ta wanke hannun ta, sannan ta goga sabulun cikin bokitin ta na cudawa da hannun ta. Kan ka ce me tuni yara sun matso suna mamakin kumfar da sabalun Zainab ke bayarwa, dan kuwa ba kowa ba ne ke samun damar wanka da omo bare kuma uwa uba sabulu.

Sai da ta wanke bokitin tas, ta dauraye da ruwan randar nan da dama rabi ne ciki, har ta karar da ruwan, sannan kuma ta bude randar da ke cike da ruwa, Amma babu damar dauka, hannun ta ruke da sabulun ta, ta jefa modar cikin bokiti ta fara ja, ta yi ta na hutawa haka kuma ruwa be fasa zubewa ba, haka ta shige bukka ta na jiyo maganganun mata gidan da ta tabbatar da ita su ke akan ruwan da ta kwasa.

Cikin bukka ta aje bokitin gefe guda, tana mai tura kwararen abincin da aka aje mata karkashin gadon kara, ta sa hannu ta tattare yar ledar da ke shimfide, da ke dama ba wata ledar arziki ba ce, bukkar ya zama sai kasa ne kamar yanda tsakar gida da bandaki. Assabarin daki ta saka ta na fadin

"Duk wanda ya shigo kan sa yayiwa in ba dai wannan tsinannan ba ne"
Ta na mai juyawa kofa baya ta cire kayan ta, ya rage daga ita sai dan fantari. Nan tsakar bukkar ta dau moda ta shiga kwararawa jikin ta ruwa, duk sanda ruwan ya sauka jikin ta sai ta kusan shidewa tsabagen sanyi, Amma haka ta zake dantse ta cigaba watsa ruwa ta na kwashewa Usman albarka.

Can tsakar gida kuwa kanwar mahaifyar Usman wato Iyalle ce ta shiga bandaki, Nan ta tarar da kashin Zainab malale bisa dankwali. Ta juyo ta na salati da sallallami ta ke shedawa jama'ar gidan ta'asar da Kado ta mu su na bahaya a bandaki. Hansai matar Kawu Iliya wacce dama ta fi kowa zafi cikin gidan ce ta fusata cikin harshen fulatanci ta ce

"Kan uban can! Kashi ta mana a bayi? Ita sarauniya ba za ta iya yankar daji ba? Nan fa kuna kallo ta kwashe ruwan shan gidan nan kaf ta shige daka da shi! Zan yi magana aka hana ni! Wallahi ba za sabu ba!"

Fuuuu ta wuce bukkar Usman, su Iyalle na tsayar da ita amma ta mu su banza, ta na isa bakin bukkar ta sa hannu ta daga assabari ta cusa kai, Nan ta yi arba da Zainab daga ita sai fantari ta juya baya ta na saba jikin ta sabulu. Hansai ta saki assabari ta na salati har da kuka fadi ta ke

"Innalillahi ni Hansai an cuce ni! Wayyo na shiga uku na lalace wannan Kadon be da mutunci! Wayyo na yi gamo Allah ya isa ban yafe ba! Wayyoo...."

Da gudun ta ta bar bakin kofar bukkar in da ta tsugunna musu a tsakar gida ta na rafka ihu kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa, jama'a na tambayar ta lafiya amma ta kasa magana sai nuni ta ke ga bukkar Shehu, Iyalle ta yi kokarin zuwa ta duba abin da ya birkita Hansai haka amma Hansai ta ruke kafar ta, fadi ta ke

"kada wanda ya je kusa da bukkan can! Ku kira Shehu! Fitina ta sauka Rugar Shehu! Masifa ta saukar mana!"

Zainab kuwa tun da ta ji alamar an daga assabari gaban ta ya fadi, jin salatin mace ya tabbatar mata ba Usman ba ne ya leko, cikin azama ta dauraye jikin ta tas ruwa na malalewa tsakar dakin. Bisa gadon kara ta haye, tana daga durkushe ta fitar da dan towel din ta ta tsane jikin ta sannan ta daura, ko da ta duba ta ga tana da fantari har hudu cikin akwatin ta, wulgi ta yi da wanda ta cire. Kaya set biyar ne kacal cikin jakar, atamfa dinkin doguwar riga guda uku, duk da akan kallabin daya daga ciki ta yi kashi, sai kuma dogwayen ruguna, wanda ta bar makaranta sanye jikin ta da shi, da kuma wata koriya mara hannu, sai panties guda hudu, da bra guda hudu, sai kuma bumshort din ta guda biyu da yan rugunan su suma guda biyu. Koriyar doguwar rigar ta fitar, cikin azama ta ke shiryawa saboda hayaniyar da take jiyowa daga waje duk da dai ba ta san takamammen abun da ake cewa ba.

*****
Usman na zaune fadar Shehu, tattaunawa su ke akan maganar cigaba da Shehu ya kawo mu su, wato na azancin Shugaban kasa Muhammdu Buhari akan 'Ruga settlement policy'. Cewar shi zai so ace Rugar Shehu na daya daga cikin Rugar da za ta amfana da wannan tsari da shugaban kasa ke kokarin kafawa cikin kasar Nigeria. Kawu Iliya ne ya nisa, kana ya ce

"Allah ya gafarta Shehu, ban tari numfashin ka ba, na san ka yi zaman birne, Kuma ka san halayyar Kado, Kado ba mutunci sai shegen san zuciya! shin ka na tunanin wannan ba wani salo na zalunta da toye hakkin mu fillo na ne? Ace za a killace bafulatani da shanun sa waje guda? Ba kiwo ba yawo? Ni fa na fi zatan hadi ne! Hadin baki ne da manoma domin a tauye hakkin mu!"

"Fakat! Fakat!"

Cewar sauran jama'a cikin nuna amincewa da da maganar Kawu Iliya. Wani ya kada baki ya ce

"Wai tunda mu ke kun tabajin wani shugaba a kasa nan ya taba waiwayar mu? In ba da tsiya ba ko laifi, sai dai fa ace mun haura gonaki a taro mu! Ko kuwa a kira mu yan ta'adda ma su kidinafan"

Shehu na mai jinjina kai ya ke jin jawabin su. Wani matashi ne ya ce

"Ni kuwa sai na ga kamar cigaban ne da gaske, matukar za a kawo mana asibiti, da makaranta da wutan lantarki...."

"Asibiti? Makaranta?wutan lantarki?"

Wani Dattijo ya katse shi a fusace, kana ya kara da

"Su kawo mana makaranta irin ta su ta boko su lalata tarbiyar 'ya'yan mu musammam mata ko? Ko kuwa asibiti za su kawo mana daga nan su cusa mana hana haihuwa? Su hana matan mu haihuwa dama sun ce mun fiya haihuwa, to dan Allah idan ka dauke saduwa da matan mu wani abu ne ke kawo mana jin dadi ko nishadi duk duniya? Ina su ke so mu sa kan mu ne saboda Allah? Matan mu idan sun kai ma su tallan nono su hure mu su kunne wasu har cikin shege su ke kawo mana, yawanci 'ya'yan shegun su ne ke girma su ke koma mu su kidinafas!"

"Gaske Malam Madu, maganar ka gaskiya ta ke!"

Shehu na duban su ya furta

"Na ji koken ku duka, na kuma fahimta, Amma zan so mu dubi wannan lamarin ta bangaran amfani da masalaha......"

Tahowar yaro da gudun famfalaki ne ya katse Usman, yaro na haki yayinda ya karasa gaban Usman ya zube har kasa tare da fadin

"Allah shi taimaki Shehu, gida dai kam babu lafiya, Hansai ta na can Kado ta sa ta kuka har da firgici, Allah kadai ya san abin da ta mata...."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.