Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 32 of 46

"Toh Shehu"

Amma ya kasa cewa Zainab ta fita, dan haka sai yayi saurin juyawa ya fita. Usman ya koma yana kokarin zama, ganin yanda ya ke cikin ciwo sai da ta yi da gaske wajan dauke kan ta gudun kar ya kyamace ta kamar yanda yayi mintinan baya.

"Wacece za a kai Mambila?"

Maimakon ya bata amsa, sai yayi kwanciyar sa kamar be ma san ta na dakin ba. Ran ta yayi rauni, ta kara furta

"Kai waye! How dare you! Wa ya ba ka damar ka dauko ni ka mayar da ni sanda ka ga dama! Zaman Rugar nan yanzu na fara kai ka yi ka kadan! Ka ci moriyar gangan ko? Toh zama daram!"
Usman ya mata banza, ya na mai juya mata baya. Ganin haka ta yi saurin fita daga dakin. Su Iyalle na mata barka Shehu ya fara warwarewa ko tan ka su ba ta yi ba ta tsallake su da saurin ta ta shige dakin Iyalle. Nan ta fashe da kuka mai karfin gaske har da shesaheka, su Iyalle da su ka biyo bayan ta ne ma su rarrashi, fadi su ke

"Yo toh yar nan ai murna za ki yi ba kuka ba, tunda Allah ya sa an tsira da rai ga shi har ya farfado...."

Hansai kuwa fadi ta ke

"Ina ga kuka ai na murnar ne, ai mun tarba arziki kwarai kuwa"

Zainab kuwa ita kadai ta san radadin da ran ta ya ke yi, yau an wayi gari Usman da kan shi ya ce zai mayar da ita gida, maimakon ta yi farin ciki, kishiyar haka ta yi, dan Allah ya dasa mata son Usman, sai da Allah ya jarabce ta da kaunar sa shi ne ya ke ikirarin zai mayar da ita gida, kamar yanda ta ce babu in da za ta je, babu in da za ta je.

Su Iyalle ba su kara karaya ba sai da su ka dare yayi, Bello ya fito da akwaitin Zainab ya mayar da shi wata bukka daban wacce babu wanda ke kwana ciki, da kan shi ya gyara yayiwa Zainab shimfida. Ko da Iyalle ta tambaye shi dalili, ya ce umarnin Shehu ya ke bi. Jin haka su ma su ka fara shan jinin jikin su, lalle wannan lamari mai wuyar ganewa ne.

Sai da Zainab ta yi da gaske sannan ta iya runtsawa. Har cikin ran ta so ta ke ta sami Usman ta bashi hakuri, ta fada masa ta yi kuskure ta kuma bayyana masa sirrin ran ta, dan kuwa ba ta iya ji za ta iya rayuwa babu Usman ba, bayan ganin yanda ya kusa rasa ran sa a sanadiyar ta, lalle za ta iya rasa ran ta idan ya rabu da ita. Amma wani bangare na zuciyar ta ne ya hana ta tashi ta same shi. Haka tai ta juyi dab da asuba bacci ya sace ta. Sai tashi ta yi ta ga an tafi da su Tanko, haka kuma Usman ya ba da umarnin kada wanda ya shigo masa daki idan ba Iyalle ba, idan kuwa aike za a masa, za a iya aiko matar da Bello zai aura, wato Raaqeeba.

Ganin yanda Raqeeba ke kai kawo cikin dakin Usman fashewa ne kadai zuciyar Zainab be yi ba tsabagen kishi. Sai a sannan ta gane tsabagen kishi ya rufe mata idanu ne ta aikata abin da ta aikata. Tun tana iya jurewa har ta kasa ta je ta sami Iyalle ta ce da ita

"Iyalle ina ga zai fi in ki na da sako gun Shehu ki ba ni, ki dena aika Raqeeba ai tunda ni ce matar shi ko?"

Daga jin maganar Iyalle ta gane kishi ne na mata karara, dan haka sai ta murmusa cike da siyasa ta ce

"Wai da nauyin aiken na ki na ji, Amma ai an gama kai komai, zuwa gaba idan da aike na ba kira ki"

"Toh Iyalle, na gode"

Cewar Zainab amma har ga Allah ba haka ran ta ya so ba. Haka ta wuni ta ja jiran tsammanin kiran Iyalle, ba ta san an yiwa Iyalle gargadin kada ta sake ta bari Zainab ta kusance shi ba, dan haka ne ma Iyalle ta gwammace da ta aiki Zainab din ko kuma Raqeeba da Zainab ta nuna kishi akai, gwara ita din ta yi kai kawo zai fi mata sauki.

Balain so ta ke ta gan sa, ta ji ya jikin sa amma jin kai ya sa ta kasa shiga hakan nan, ta gwammaci ta jira a sami dalilin shigar na ta, Amma abin ya gagara har ta na shirin fita daga hayyacin ta. Haka ta hakura ta na mai neman sauki daga Allah dan kuwa shi ya jarabce ta, jarabawar ma kuwa babba.

Sai washagari su Bello su ka dawo. Ranar har tsakar gida Usman ya fito amma ko inda Zainab ta ke be tambaya ba, bare ya yi yunkurin shiga wajan ta. Ta na daga cikin daki ta ke jiyo hirar shi da mutan gidan da harshen fulatanci, wanda har ta fara tsintsinta kadan kadan. Jin har ya karaci hirar shi ya koma be neme ta ba, ita ma ta sha alwashin ko da kuwa zuciyar ta za ta fashe ba za ta neme shi ba. Cikin kankanin lokaci sai ta kara zama bare a Rugar Shehu, kullum ta na cikin bukka idan ba dai uzuri ne ya fito da ita ba, haka kuma ta lura ko giftawa ta yi gaban Usman matukar ya na fara'a sai fuskar sa ya hade ya murtuke tamkar hadari, ya guje ta ya juya mata baya farat daya, yayinda ta ke bukatar shi, ta ke kaunar sa tamkar ran ta. Idan akwai ranar da ta ke tsoro ya bi bayan juma'ar da Usman ya ce za a tafi da ita, duk ran da rana ya fadi garin Allah ya waye sai ta yi kuka, ranar alhamis kuwa ko kafa ba ta iya sakawa tsakar gidan ba, bukkar ta ta wuni cikin bakin ciki da adduar Allah ya sa Usman ya canza ra'ayi.

Ranar Juma'a da asubar fari sai ga Iyalle dauke da irin kayan da Usman ya bata ranar shadi. Ta tarar Zainab zaune kan tabarma in da ta idar da sallah ta na jan jarbi, Iyalle ta zauna kusa da ita tare da fadin

"Ayya Abu, ashe hukuncin da Shehu ya yanke kenan? Mun yi bakin ciki kwarai ke abin alfahari ce a Rugar nan, ba mu ji dadin sakin ki da yayi ba....."

A kidime cike mummunar faduwar gaba Zainab ta yi saurin fadin

"Saki! Cewa yayi ya sake ni? Wa ya ce ma ki ya sake ni?"

Ganin yanda ta kidime Iyalle wacce dama da biyu ta yi maganar ta maganar ta furta

"Ashha babu wanda ya fada min, ganin ya bani kaya ya ce na kawo mi ki, tare da sheda min Bello zai mayar da ke birni ki koma can uwa uba Kano na yi zaton ko hakan aka yi, dan kuwa aure ke kina can shi ya na nan kusan sai a ce ya mutu, ki yi hakuri da azanci na"

Ta karasa maganar ta mai fatan Zainab za ta bijire ta ki yarda da maganar Usman. Aikuwa nan Zainab ta ce sam ba ta san zancen ba ta juya ta mayar masa da kayan sa, babu in da za ta je.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.