Complete Hausa Novels

Auren Shehu Part 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Shehu_Part_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 28 of 46

Ko da ya ga fitilar bukkar a kashe be damu da ya kunna ta ba, kai tsaye ya nufi gadon su ya na mai lalube har hannun sa ya sauka jikin Zainab wacce ta dan firgita ta na kokarin tashi yayi saurin janyo ta jikin sa tare da fadin

"Shhhh Abu....Ni ne"

Ya kara rungume ta sosai kamar mai kokarin mayar da ita cikin jikin sa, hakan ya sanya Zainab narkewa ba ta san sanda hawaye ya fara fita daga idanun ta ba, sai saukar su da Usman ya ji a kirjin sa, ya furta

"Subhabanallahi me ya faru? Ba ki da lafiya ne? Bari na dauko haske Abu"

Ya yi yunkurin tashi, amma Zainab ta kamkame shi ta hana shi tashi

"Menene Abu?"

"Babu komai"

Ta bashi amsa cikin rawar murya. Shiru ne ya biyu baya, inda Usman ya ke tuntuni, ya san ko Zainab ba ta fada ma sa ba tunanin gida da su Ammy ne ya sanya ta kuka, dan haka ya furta

"Kin ga Abu, na san dalilin kukan ki, kada ki damu dama akwai maganar da na ke so mu yi......"

"Ba yanzu ba dan Allah, please..."

Zainab ta katse shi, babu abin da ta ke so a lokacin fyace tarayyar ta da Usman, dan kowa komai da ta ke masa na bankwana ne. Yanda ta ke dada kamkame shi ne ya sanya Usman ya fahimci abin da ta ke bukata, tuni ya aje maganar da ya ke so su yi, shi ma ya bi yarema a sha kida. Yanda Zainab ta saki jiki ta nuna masa salo iri iri ne ya kara jaddawa Usman irin san da ta ke masa, nan kuwa be san duka na bankwana ba ne.

Sanda su ka sami nutsuwa Usman ya kara kokarin zayyanawa Zainab abin da ke ran sa, Amma be an kara ba sai ji yayi ta kara nauyi a jikin sa, Ashe bacci yayi awan gaba da ita. Dan haka a dole ya hakura, ya na mai sumbatar da a goshi ya furta

"Ina kaunar ki Abu, so na tsakani da Allah, da fatan za ki yafe min ki karbi soyayya ta"

******

Washagari sassafe aka tashi da girkin bikin sharo, masu daka fura na yi, masu tuka tuwo ma haka, haka ma masu tatsa da dafa nono ba a bar su baya ba. Zainab kuwa tun da garin Allah ya waye ba ta saka Usman a idon ta ba, haka shi ma Usman wanda tun fitar shi sallar asuba be sami damar dawowa ba bare ya samu yayi magana da Zainab. Cikin dabara ta ja Rahila gefe, ta fada mata cewa da zarar an fara sharo ta saci jiki ta dawo gida ta tafi mata da dan akwatin ta can inda su ka yi za su hadu da Tanko, ta duba girman Allah kada ta bari a ganna ta, Rahila ta amsa da an gama.

Sai wajan sha biyu sai gashi ya shigo gidan, ya tadda Zainab sai kai kawo ta ke cikin bukka domin kuwa lokacin da su ka yi da Tanko sai gabatowa ya ke, dan kuwa ana idar da sallar azahar za a fara bikin.

Jawo ta yayi bangaran jikin sa na dama, tare da sumbatar ta a goshi, sam be lura da yanda Zainab ta kasa daga ido ta kalle shi ba, ya na mai damka mata ledar da ya ke dauke da shi ya ce

"Ga kayan fitar Sharon ki, na so ace kin taba gani da ba zan yarda ki je wajan ba dan kar a kalle min ke, toh amma dan Allah idan kin je kada ki jima...."

Jin haka Zainab ta yi saurin fadin

"Toh idan na bar wajan ina zani? Sai na dawo gida na zauna ni kadai kamar mayya bayan an ce kowa can zai tafi..."

Usman na dariyar tsiwa irin na Zainab ya furta

"Ba fa kowa ba, ko kowa zai tafi ai ban da Iyalle.."

Zainab na mai buga kafa cikin shagwaba ta furta

"Ni dai ban yarda ba, Ni dai sai dai za ka biyo ni mu je yawo, dama ka ce akwai maganar da za mu yi, ka ga sai mu cikin annushuwa daga ni sai kai"

Kalmar daga " ni sai kai ne" ya sa Usman cin dadi har cikin ran sa, Wai yau shi ne Zainab ke san kebewa da shi, da ga ita sai shi yanda babu wanda zai dame su.

"Kamar dai yanda ya kasance a gidan gona?"

Ya tambaya ya na mai kokarin kallan idanun Zainab. Yanda kwayar idanun sa ke rawa ya sanya tsigad jikin Zainab tashi, ta yi saurin kawar da kai gefe, ta furta

"Ko ma ka kai ni wajan ruwan nan, ban taba ganin shi ba sai dai na ji labari"

"An gama gimbiya Abu, in Sha Allah za mu je, sai kuma tafiyar ta mu za mu yi ta da dabara, idan an fara da minti talatin haka sai na miki alama ni zan fara yin gaba, sai ki bi sahu na, ai dai za ki gane hanya ko? Ba nisa zan mi ki sosai ba"

Zainab ta gyada masa kai alamar "eh". Sallamar da aka yi ana neman Usman ne ya sa ta sake ta ya fita. Nan ya barta jiki na rawa, in da ta sami gefan gado ta zauna. Sai da ta yi kusan minti goma zaune sannan ta iya bude ledar da ya ba ta. Atamfa ce koriya da ja, dinkin riga da zani, rigar an dinka ta doguwa sosai dan za ta kaiwa Zainab har gwiwa, ga fadi ko ado babu jiki, sai kuma mayafi shi kuma shudi da ruwan dorawa. da ka gani ka ga kalar fulanin kauye, sai kuma sifas shi ma din ruwan dorawa ne. Ko da ta gama dagawa sai ta ja tsaki, a zahiri ta ce

"Yau dai Allah zai raba ni da wannan gidadanci! Dan ji wani jahilin kaya da ya kawo min! Macuci azzalumi!"

Da kamar ba za ta saka kayan ba, Amma da ta tuna da hudubar Rahila haka ta rufe idanu ta sanya kaya, tun da ta zo duniya ba ta taba muni irin na ranar ba, ita kan ta sai da ta tsargu da kan ta.

Amma ko da lokacin tafiya yayi ta fito waje, hankalin kowa kan ta ya koma, in da ake ta yaba kyan ta da koma kyan kayan jikin ta. Ita kan ta Rahila kasa shiru ta yi ta furta

"Kai wannan ko ke ce amaryar sai haka! Gaskiya kin fito ziza da ke, ko da shi ke ai matar Shehu guda!"

Wani malulun bakin ciki ne ya tsaya makoshin Zainab, Amma daga baya da ta lura da irin shigar da sauran jama'ar su ka yi, daga matan har mazan wani irin farin takalmin roba su ka sanya sau ciki, inda yawanci matan atamfa ne jikin su irin wannan ma su kalar rambatsau din nan, yan matan cikin su sun ci gilashin roba kala kala, haka ma samarin wajan wanda ba za su ba da gudunmawa wajan Shadin ba dauke da rediyo a kafada, sai bada iska su ke a dole gayu su ka sha.

Tun Zainab na daurewa har ta fara dariya musammam da su ka isa filin Sharon, ta ga shigar da Bello yayi, kan sa har da gashi da wata irin hula na angwanci. Amarya Raqeeba kuwa can ta hango cikin kawayen ta, tabbas babu wani bambamcin shigar ta da na Zainab idan aka dauke gilashin robar da ta sanya da kuma farin takalmin robar da ke kafar ta. Kallo daya Zainab ta mata ta dauke kai dan kuwa ji ta ke ta yi mugun tsanar Raqeeba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.