Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 50

*TYPING* 📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*👇

GARKUWA BIYU

*BABI NA D'AYA DA NA BIYU*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI,SARKI MABUWAYI GAGARA MISALI,MAI SHEKARANJIYA DA JIYA DA YAU DA GOBE DA JIBI,WANDA YAYI MINI BAIWA YA BANI BASIRA DA HAZAK'AR RUBUTU DOMIN FAD'AKARWA DA WA'AZANTARWA DA NISHAD'ANTARWA DA ILIMANTARWA.

KAMAR YARDA AKA SABA MASOYANA YAU MA GANI NA DAWO A SHIRYE TSAF DOMIN KU,DOMIN DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA,SOYAYYA DA ADDU'AR DA KUKE MIN TA FATAN ALKAIRI KAD'AI TA ISHENI TINK'AHO DA JIN DAD'I,INA FATAN ZAKU CIGABA,KUMA ZAKU BINI A CIKIN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA *GARKUWA BIYU* DOMIN KUJI WANE SALO YAKE D'AUKE DASHI,KUN SAN A KO DA YAUSHE SALON LITATTAFAINA SUNA SAUYAWA,TO WANNAN MA NASA SALON NA DABAN NE,ALLAH YA BANI IKON FARAWA LAFIYA KUMA NA GAMA LAFIYA.🥰🥰🥰👏👏👏🌹🌹🌹

A hankali ya shigo da motarsa cikin harabar Gidan,bayan mai gadi ya wangale masa k'aton get d'in,ya nufi parking space ,wucewar mintina biyu ya bud'e murfin motar ya zuro k'ayatattun k'afafuwansa ya sakko,hannunsa rik'e da briefcase, kyakkyawar fuskar sa sanye da glass, ya kulle motar ya tako a hankali cikin tafiyar nutsuwa da d'aukar hankali,da sauri mai gadin ya nufo shi ya zube a gabansa cikin girmama wa.

"Yallab'ai barka da dawowa"

Yayi murmushi yana gyad'a kai.
"Barka kadai Umar,ya Gidan ya wuni?dafatan komai lafiya?

Umar ya sake russunawa.

" Alhamdulillahi mun wuni lafiya,sai dai d'azu naga GARKUWA ya fito daga ciki yana kuka,amma da na tambaye shi yak'i yin magana,gashi can ma zaune a k'ofar shiga parlour "

Fuskarsa ta nuna rashin jin dad'i,ya D'an waiwaya yana hango yaron zaune ya zabga tagumi, da alamun damuwa a fuskarsa,ya dawo da kallonsa kan Umar ya D'an murmusa.

"Shikenan no problem Umar,koma wajen aikin ka zan ji damuwar da kaina".

Umar ya mik'e yana godiya,shi kuma ya fara takawa a hankali har ya isa gaban yaron D'an shekara shida,Wanda yake zaune a kan step's d'in shiga cikin parlour d'in Gidan

Ya D'an d'auki lokaci a gaban yaron yana ta kallon sa cikin damuwa da bugawar zuciya,kafin a hankali ya zame ya tsuguna gabansa,ya d'aga tattausan hannunsa ya d'ora akan hannun yaron yana zame tagumin da yayi,firgigit yaron ya d'ago kansa,yana ganin Wanda yake gaban sa da hanzari ya silalo ya fad'a k'irjinsa yana rik'e wuyansa,hawayen sa ya tsinke ya sauka kan kafad'ar mahaifinsa.

Tsawon minti biyu ya bar yaron yana kuka da shesshek'a,har sai da yaji ya lafa tukunna yasa Hannu ya d'ago shi yana kallon fuskarsa ,yasa Hannu ya share masa hawayen sa,yaron ya bishi da kallo yana k'ara kwab'e fuska zai kuma wani kukan,da sauri ya girgiza masa kai yayi magana a hankali.

"Bana son sake ganin hawaye a idanuwan HAMZA GARKUWA,kai fa jarumi ne Hamza,shi Jarumi baya kuka kullum zuciyarsa a dake take,abin da yasa ma yanzu na k'yale ka kayi domin kaji dad'i ne,ka san wani lokaci idan yaro yana kuka a kan so a barshi yayi domin wata damuwa ta yaye daga k'irjinsa,daga yanayin da naji hawayen ka sun zubo da d'umi na tabbatar na damuwa ne,shiyasa na barsu suka zuba domin kaji sauk'in damuwar,amma menene damuwarka da har ka kasa zama a cikin gida ka fito kana kuka"?

Ya sunkuyar da kai yana wasa da yatsun mahaifin nasa,yayi magana cikin muryar rauni da yarinta.

" Bana son ganin hawayen Ammina ne Abba,shine na fito nan"

"Yau ma tayi kukan ne"?

Ya tambayeshi da Hanzari.

Ya gyad'a kai yayi rau rau da idanu.

" Eh tayi sosai Abba,har idanuwanta sun yi ja"

Ya lumshe idanu ,a hankali ya ambaci.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
Da hanzari kuma ya mik'e yaja hannun yaron yace .
"Tashi mu shiga ciki"

Yaron Ya mik'e,sannan ya mik'a Hannu yace.
"Abbana kawo jakar na rik'e maka"
Ya mik'a masa,sannan ya rungumeshi a gefensa suka shige parlourn.

Ta na zaune a d'aya daga cikin kujerun parlourn,kanta kwance akan cinyoyin ta,sallamar su bai sa ta d'ago kanta ba,suka tsaya suna dubanta suna sauke numfashi,a hankali ya juya ya kalli yaron Yayi magana a hankali.

"Tafi ka kai min jakar bedroom, daga nan kayi zamanka kayi karatu".

Ya amsa ya wuce ya na waiwayen su,har ya shige bedroom d'in,shi kuma ya tako a hankali zuwa kusa da ita ya zauna gefenta,a hankali kuma ya kai Hannu ya d'ago fuskarta da ke sunkuye yana son su had'a ido,tsigar jikinsa ta wani mik'e yarrrrr!ganin yadda idanuwanta suka yi ja sosai alamar taci kuka ba da wasa ba,ta bishi da kallo hawaye na k'ara ziraro mata,ya kai D'an yatsan sa ya share mata,sannan ya jata jikinsa a hankali ya rungumeta tsam yana ajiyar zuciya,hannunsa d'aya ya kai kan lallausan gashin kanta Wanda bai cika tsawo da yawa ba yana shafawa,d'aya hannun bisa gadon bayanta yana mata messaging.
Sai da suka d'auki tsawon lokaci a haka kafin ya d'agota daga jikinsa,ya tallabo kumatunta yana k'ok'arin jefa idanunwansa cikin nata,suna had'a idanu ta runtse nata idon,bata fiye son kallon k'wayar idon sa ba saboda maganad'isun dake fizgarta , shi kuma ya lumshe nasa idanun ya bud'e,a hankali kuma cikin maganar rad'a yace.

" Kullum na ganki cikin wannan yanayin sai nai ta tuhumar kaina anya kuwa na cancanci a kirani da GARKUWAR ki?bana son ganinki cikin damuwa ko kad'an,ki taimakawa numfashi na ki daina yawan damuwa domin nima kina sakani a damuwar,ba iya ni kad'ai ba har D'an mu da muka Haifa, me ya saki kuka a yau HIDAYA?kin tuna da k'addarar rayuwarki ne?

Ta girgiza kai a hankali hawayen ta ya kuma gangarowa,ya D'an dafe kai yace.
"Oh my God"

Sannan ya d'ago k'afafuwanta zuwa kan cinyarsa yana duba su yana mammatsawa a hankali,ya d'ago ya kalleta.

"K'afarki tana ciwo ne?ban ga kumburi a tare da ita ba,ko wani wajen nayi miki ciwo ne?

Nan ma ta girgiza kai babu magana.

" Hidaya" ya ambaci sunanta ya na mai k'ura mata idanu,ta d'ago kanta ta kalleshi.

"Menene? Don Allah ki fad'a min"Ya tambayeta idanuwansa cikin nata,ta fara k'ok'arin sunkuyar da kai,da hanzari ya tallabo ta ya marairaice.

" Idan baki fad'a min ba wallahi zan yi Kuka Hidaya ,a yanzu baki ji yadda k'irjina yake ciwo ba ganin hawayen ki"

Ta kwantar da kanta kan kafad'arsa tana ajiyar Zuciya,a hankali tayi magana muryarta na shak'ewa.

"Duniya cike take da mutane mabanbamta,kuma kowa da irin tasa k'addarar,wani Mummuna wani kyakkyawa,wani jarrabawarsa mai tsananin zafi ,wani kuma mai sauk'i,kowa da yadda tasa take zuwar masa a yadda Allah ya k'addara masa,ba kuma wai don ba ya son bayinsa ba yake jarrabarsu,illa domin ya gwada imanin su"

Ta D'an yi shiru tana maida numfashi,shi kam ya k'ura mata idanu,ta gyara zaman ta a jikinsa ta cigaba da magana.
"Wannan kukan da kaga ina yi k'addarar wasu na tausayawa,shiyasa nake zubar musu da hawaye"

Yayi mamaki sosai har ya kasa b'oyewa,da hanzari ya magantu.

"K'addarar wasu kuma Hidaya?yanzu akwai k'addarar da zaki tausayawa wadda ta wuce taki Hidayaa?kin manta jarrabawar ki a rayuwa ne?shin kin manta da taki k'addarar ne?wad'annan su waye da kike tausayawa k'addarar su?

Tayi murmushi mai ciwo.

" A yayin da wasu zasu tausayawa k'addarata da jarrabawata,a lokacin ne ni kuma idan naji ta wasu zan tausaya musu"

"Su wanene"? Ya tambayeta kai tsaye.

Ta amsa cikin girgiza kai.
" Ban san su ba,ban tab'a ganin su ba,Labarin su kawai na karanta ya tab'a ruhi na,kai ma kayi mamaki ko?

Ya d'aure fuska kad'an.

"Wai kina nufin daman kukan da kike yi akan karatun littafi ne?kina nufin labarin wasu kika karanta na k'arya kika zauna kina kuka?ba na hanaki zama ki karanta littafin da kika San zai saki kuka ba?yau kuma na wace marubuciyar kika karanta?

Ta bishi da kallo.

" kamar Kullum,yau ma littafin HASSANA D'AN LARABAWA na karanta mai suna SANADIN HOTO,hak'ik'a labarin ya tab'a min zuciya sosai,kamar yadda sauran litattafanta na HASSANA DA HUSSAINA DA CIN AMANAR RUHI suka tab'a min zuciya"

Haushi ya kamashi,ya fara fad'a a zafafe.

"Na rantse da Allah da zanga marubuciyar nan sai nayi shari'a da ita,akan me zata dinga saka min ke kuka?haka kawai ta zauna ta dinga rubuta k'arya tana saka ku kuka,saboda rashin aikin yi,ku rasa me zaku yiwa kuka wai sai littafi?

Yayi D'an tsaki yana zamewa ya jingina da kujerar.

Zahra tayi murmushi.

" Ba zaka gane ba ne,Abin da baka sani ba shine,ya wanci litattafan HASSANA D'AN LARABAWA Gaske ne sun faru,sannan tana duba abubuwan da suke faruwa a zamanin da muke ciki tayi rubutu a kai,Wanda zai fad'akar kuma ya nishad'antar da mutane,ni dai ina sonta,kuma ina son karanta litattafan ta domin mutum zai k'aru da wasu Abubuwan,duk da ban Santa ba ban kuma tab'a ganinta ba amma zan karb'i Numbarta wajen Sumayya domin muyi magana ni da ita,da man Sumayyan ce ta turo min litattafan na karanta"

Ya D'an yi mata kallon k'asan ido sannan ya lumshe su,a hankali kuma yasa tattausan hannunsa ya rik'o nata hannun mai kama da Auduga don laushi,ya matse a cikin tafin hannunsa,ta d'ago idanuwanta wad'anda basu kasance farare tas ba,saboda akwai wani sirki a tare dasu na lalura,ta dubeshi, fuska babu walwala idanuwansa a kanta ya fara magana.
"Zan b'atawa Sumayya rai My Hidaya,sanin kanta ne cewa duk duniya bana son ganin abin da zai saki kuka ko ya b'ata miki rai,akan me zata baki littafin da zaki karanta kiyi kuka?

Ta jawo jikinta kusa da shi ta zame ta kwantar da kanta kan yalwataccen k'irjinsa ta D'an rungumeshi ta na sauke ajiyar zuciya tace.

" Don Allah kar kaga laifinta,ni na dameta akan ta bani saboda yadda naji ana cewa litattafan sun yi dad'i,wallahi ma hanani tayi nai ta takura mata da naci shine ta bani na karanta,kuma wallahi na k'aru sosai dasu,Don Allah kayi hak'uri kar kayi wa Sumayya komai"

Yayi shiru bai ce komai ba,ta d'ago kanta tana kallon kyakkyawar fuskarsa idanuwansa a rufe,ta D'an shafi fuskarsa cikin sanyin murya tace "ka ji" yayi wal ya bud'e idanun ya sauke akan ta,ya D'an d'aga gira yayi magana a hankali"Menene?

"Kar ka yiwa Sumayya komai" ta ambata cikin shagwab'a.
"OK,ya fad'a yana yunk'urawa ya mik'e da ita a jikinsa.
" Muje bedroom wanka nake so nayi,za ki tayani ko Hidaya na?

Tayi murmushi ta na gyad'a kai sannan ta sak'alo wuyansa ta rad'a masa wata magana.
Shi ma yayi murmushi ya tsuguna gabanta yace.

"Abu mai sauk'i kenan Hidaya na,maza ki hau bayan mijinki Garkuwar ki"

Ta haye bayansa ta kwanta luf tana murmushi,shi kuma ya mik'e yana zunkud'ata suka shige bedroom suna dariya.

Hamza da ke d'akin sa yana karatu jin dariyar da iyayen sa ke yi sai yayi murmushi,hankalin sa ya kwanta,domin damuwar mahaifiyar sa ta na damun sa,ya kuma tabbatar Mahaifin sa yana k'ok'ari sosai wajen tafiyar da da uwar Ammin sa a duk lokacin da ta shiga damuwar,ya lumshe idanu ya mai da kan sa kan alk'ur'anin gaban sa ya cigaba da karatun sa cikin kwanciyar Hankali.

Comment
Share
Vote
Pls

*TYPING* 📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI(SABON SALO)

*DA KUMA*👇

GARKUWA BIYU

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.