Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 17 of 50
*BABI NA TALATIN DA UKU DA NA TALATIN DA HUD'U*
WATTPAD:Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
Lumshe idanuwa yayi yana jin wani sanyi a Zuciyar sa,sak'on daga Khaleel yake,kamar ya san cikin buk'atar kud'i yake,godiya yayi wa Allah yana ta fad'in "Alhamdulillah" har bai san iya adadin da ya fad'a ba.
Da sauri ya nufi pharmacy d'in,me wajen ya gane shi,nan da nan ya tare shi cikin fara'a suka gaisa,Hamza yace yazo ne akan maganar maganin nan,sai dai bashi da kud'i Cash a Hannu,shin zai iya yi musu transfer ta bank?
Mutumin yace ba damuwa zai iya,ya bashi acc number nan da nan Hamza yayi masa transfer yana daga tsaye,mutumin yana jin shigar kud'in cikin acc number d'in sa ya had'awa Hamza maganin ya bashi,sai lokacin Hamza ke tambayar sa in da zai samu ragowar maganin,mutumin yace ya shiga cikin asibitin akwai wajen siyar da magunguna ya duba ba zai rasa ba.
Hamza yayi masa godiya sosai ya fito rik'e da ledar maganin,ya tsallaka titi ya shige cikin asibitin,bai sha wahala wajen gane pharmacy d'in asibitin ba,ya D'an tarar da layi kad'an,ya jira aka sallame su sannan ya mik'a na sa katin,cikin ikon Allah aka ce akwai maganin da yake ne ma guda biyun,nan ma ya rok'i alfarmar yayi musu transfer suka ce eh zai iya babu komai,nan ya tura musu kud'in dubu takwas da d'ari uku,aka bashi maganin ya had'a da na hannunsa ya fito .
Sanda ya koma d'akin Umma har ta taimakawa Hidaya tayi wanka ta sauya kaya,sai yaga tayi fari sai dai ta rame,ya dubeta yaga duk k'asusuwa a wuyan ta yace.
"An ya Hidaya za ki yi k'iba kuwa?irin wannan rama haka?"
Umma tace.
"Hmmmm!irin lalurar su ai bata barin su k'iba,sai dai su murmure"
Ita kam Hidaya murmushi ta yi tana shafa wuyan ta,ya mik'awa Umma ledar magungunan ,ta karb'a ta duba tana cewa.
"Duka an samu kenan?
" Eh Umma an samu duka,bari nayi wa likitan magana ko?"
Umma tace.
"To babu laifi,Allah yayi maka Albarka Hamza"
"Ameen Umma na"ya amsa yana k'ok'arin ficewa daga d'akin yaji muryar Hidaya ma cewa.
" Allah sarki Ya Hamza,duk ka kashe kud'in ka wajen siyo min magani ko?insha Allahu zan siyi banki idan na samu kud'i in ta tara maka kana amfani da su"
Murmushi kawai yayi ya fice bai ce komai ba,yana jin Umma nan dariya tana fad'in.
"Ah lallai su Hidaya Ashe za a tara kud'i da yawa".
************
Lokacin da likitan yazo ya dubata sannan ya bata magungunan tasha,sai da Hamza ya dinga lallab'ata sannan ta karb'a har da Kuka,saboda Hidaya bata son magani ko kad'an,likitan yana ta tsokanar ta yana dariya.
Nan da nan Hidaya ta ware sosai kamar ba ita ce ta lallank'washe jiya ba,likitan ya dinga bawa su Umma shawarwari akan yadda za su kula da lafiyar Hidaya,da yadda ciwon yake,ya fad'a musu a dinga bawa Hidaya kulawa sosai,saboda ciwon ta yana buk'atar kulawa,ya dinga fad'a musu yadda masu ciwon sikila suke jin azaba a jikinsu,yace musu shi kansa yana da sikila,kuma ba k'aramar wahala ya sha ba,yana kan sha ma,yace saboda hakan yayi karatun likita b'angaren cutar domin ya taimakawa masu ciwon,saboda duk yadda za a fasalta maka yadda suke shan wahala ba zaka gane ba in dai ba cutar gareka ba.
Nan Umma da Hamza suka sake tausayawa Hidaya da duk wani mai fama da lalurar,suka yiwa likitan godiya sosai da sosai,a ranar haka Hamza ya shashance a asibitin ko makaranta bai jeba,gashi karatu ya d'au zafi sun kusa fara exam.
Yana ta lallab'a Hidaya sai abin da take so yake mata,har da su tatsuniya sai k'yalk'yala dariya take yi,Umma dai na kallon su tana jin farinciki a Zuciyar ta ganin yadda suke kulawa da junan su,sai lokacin ya tuna da Khaleel yace idan yazo asibitin ya kira shi.
Da sauri ya gyara zama yana k'ok'arin zaro wayar sa cikin Aljihun wandon sa yace.
"Subhanallah,Umma nayi mantuwa fa,d'azu mun yi magana da Khaleel har yace min idan nazo asibitin na kira shi za ku yi magana ke da shi,sannan ya duba jikin Hidaya,shaf na manta sai yanzu,Ashe shirun da naji daga gareshi bashi da lafiya ne Umma,ciwon sa ne ya tashi wallahi"
Umma ta jinjina cike da jimami take nemar wa Khaleel sauk'i a wajen Allah,Hamza yayi masa flashing,cikin minti uku sai ga Khaleel ya kira Video call,Hamza ya amsa sai ga Khaleel zaune akan wata farar kujera a bakin beach,k'afafun sa zube cikin ruwan ,sanye yake da k'ananan kaya da suka yi masa masifar kyau tamkar D'an turawa,yayi haske sosai ga kwantacciyar suma da saje da ya k'a wata fuskar sa,fuskar sa d'auke da wadataccen murmushin da ya k'ara masa kyau,suka haske juna da murmushi shi da Hamza,Khaleel ya D'an harari Hamza,cikin muryar sa mai dad'i yace.
"Ni fa ba da kai zan yi magana ba Aboki,ka fara bani Umman mu naga mahaifiyata,daga nan sai na gaisa da K'anwar mu Hidaya"
Hamza yayi murmushi ya D'an tab'e baki yace.
"To ai ga Umman a kusa dani ….in kuma ka cika min baki sai na hanaka magana da ita malam"
"Afuwan Aboki…don Allah bani Umman mu,na jima ban ganta ba balle naji muryar ta"
Umma na daga gefe tana ta murmushi tana jin maganar Khaleel,Hamza ya kai mata wayar ya zauna ya jingina da kafad'ar ta ,Umma ta kalli fuskar wayar idanuwan ta suka yi arba da Khaleel,wani farinciki ya kamata,Khaleel ya harari Hamza cikin wasa yace.
"To ka kauce mana,ko a gabanka zan gaisa da Uwa ta?
Umma tayi dariya yayin da Hamza yayi masa gwalo ya matsa gun Hidaya,shi kuma Khaleel ya fara gaida Umma cikin tsantsar nuna kulawa da biyayya.
Umma ta amsa tana yi masa ya jiki,har tana k'orafin tsananin ramar da taga yayi,yayi murmushi kawai,a lokacin ya kwantar da murya ya fara tsara Umma da maganganu masu dad'i akan k'udurin sa akan Hamza,babu yadda Umma za ta yi saboda kwarjinin da Khaleel yayi mata tunda suna kallon juna,gashi sai magiya yake surfa mata,tilas Umma tace ta amince,sannan ta dinga yi masa godiya,amma tayi k'orafin ya dinga rage wasu abubuwan Hidimar tayi yawa,Khaleel farinciki tamkar ya zuba ruwa a k'asa ya sha,ya dinga godiya,a lokacin yake tambayar Umma jikin Hidaya,Umma tace da sauk'i,tana mamakin Ashe har Hamza ya bawa Khaleel Labarin Hidaya kenan?
Sun gama magana da Umma sannan Hamza ya karb'i wayar,suka kalli juna da murmushi akan fuskokin su,Khaleel na tsokanarsa wai ya yaga ya k'ara kyau?me Umma take bashi yana ci?Hamza yayi dariya yace" kai da kake k'asar turawa ai Kaine kayi kyau Khaleel, kalli fatarka fa,ni kuwa ina Nigeria jaga jaga muna fama,Khaleel ke k'orafin ai shi a dole yake zaune England, Dan dai babu yarda zai yi ne,amma yafi son zaman k'asar sa Nigeria,Nigerian ma kuma Kaduna kusa da Hamzan,domin baya son zaman Abuja gurin daddyn sa,shi dai Hamza dariya kawai yayi.
A lokacin Khaleel ke cewa Hamza ya bashi Hidaya ya ganta su gaisa,kuma yayi mata sannu,a hankali Hamza ya matsa kusa da Hidaya ya kalleta yana ce mata.
"Hidaya ga Uncle Khaleel za ku yi magana kinji"
Fuskarta na kallon Hamza tayi murmushi cikin zumud'i tace.
"Da gaske ya Hamza?don Allah da gaske ka ke?
Ya jijjiga mata kai yace.
" Eh da gaske!kin ganshi ma fa yana kallonki"
Duk tattaunawar da ake tsakanin Hidaya da Hamza khaleel na kallon su yana murmushi,a lokacin ne Hidaya ta juya a hanzarce ta kalli wayar cikin slow,idanuwan Khaleel da na Hidaya suka yi arba da juna….wata irin fad'uwar gaba Khaleel yaji wadda bai tab'a jin irinta a fad'in duniyar sa ba a lokacin da idanuwan sa suka sark'afe cikin na Hidaya,wani Abu yaji yana masa yawo a jikinsa yana zagayawa jini da tsokarsa yana huda shi,bai san ko menene ba!amma tabbas a lokaci guda yaji Hidaya ta gama zagaye jinin jikin sa.
Yadda yake kallon ta haka take kallonsa tana doka masa murmushi,tayi maza ta juya ta kalli Hamza tace.
"Wannan ne Uncle Khaleel Ya Hamza?
Gyad'a mata kai yayi yana murmushi, Khaleel kam wani sanyi sanyi yake ji a jikin sa,cikin wata irin murya da bai san yana da ita ba ya D'an d'agawa Hidaya yatsun sa guda biyu yace.
" Hi!K'anwar mu ya kike? Ya jikin na ki?
Tayi dariya cikin k'ank'anuwar murya tace.
"Jikina da sauk'i Uncle Khaleel, Ya Hamza yana ta bani Labarin ka ina so na ganka,kullum ina cewa ya nuna min hoton ka sai ya k'i,yau dai gashi na ganka ko?
Ya lumshe idanu yana kad'an kai yace.
" Aikuwa yau Hidaya taga Uncle d'in ta,shi kam Ya Hamza sai mun hukunta shi tunda ya hana Hidaya ganin Uncle Khaleel ko?"
Tayi dariya ta kalli Hamza da ke ta murmushi tace.
"Ah ah a k'yaleshi,bana son a tab'a min Ya Hamza na fa"
Hamza da khaleel suka yi dariya,suka cigaba da hira su uku,Umma kam toilet ta shige tana wanka,sai da Hidaya ta fara Hamma tana jin barci har tana langab'ewa kafad'ar Hamza,sannan Khaleel ya hak'ura yace zai sake kira da daddare suyi hira,yayi wa Hidaya fatan samun sauk'i,lokacin Hamza ya fara yi masa godiya kan kud'in da ya turo masa d'azu,Khaleel bai tsaya jin godiyar ba ya kashe wayar sa saboda baya son godiya.
Hidaya kam har tayi bacci,Umma ta fito daga toilet a dai dai lokacin da Hamza ke k'ok'arin ficewa daga d'akin ta ambaci sunan sa cikin wata irin murya,da hanzari ya juyo ya dubeta yana amsawa,yanayin da ya gani a fuskarta yasa k'irjinsa ya tsananta bugawa……..!
Comments
Share
Vote
Pls
*TYPING*📲
✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR* 👇
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)
*DA KUMA*
GARKUWA BIYU
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.