Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 46 of 50

BABI NA CASA'IN DA D'AYA DA NA CASA'IN DA BIYU

Ban bar wannan kangon ba sai da duhun magariba yayi,sannan na daddafa cikin k'arfin hali na fito,babu komai a tare da ni sai sark'ar gwal d'ina da na d'auka a cikin kayan Hidaya na k'ulle ta a bakin zani na,sai kuma kud'in da wannan mutumin ya bani akan na siyawa Hidaya abincin rana,a haka na fito ina walagigi har zuwa bakin hanya wajen titi,sai a lokacin na tsaya na tambayi wani mutum in da zan sami motar da zata kaini Gombe,yace min ai dole sai naje tasha,a tak'aice dai wannan mutum shine ya sakani a hanya har zuwa tasha,nayi masa godiya sosai,sai dai kuma wani jidalin babu motar da zata tashi a daren wai sai zuwa safiya,haka na hak'ura nayi kwanan tasha,dan ma naga da mutane sosai,da sassafe kuwa mota ta d'aga damu zuwa Gombe,wannan kud'i da mutumin nan ya bani su suka zame min GARKUWA,domin da su na samu na biya kud'in mota.

A maimakon da na isa Gombe na samu salama sai na tarar da wani tashin hankalin,mahaifina ya rasu ana shirin kaishi makwancinsa,ana ta neman wayata da ta mijina an rasa,take na fad'i a tsakar gidan mu na suma tsabar tashin hankali.😭

Kwana na biyu ban san in da kaina yake ba,nasha wahala matuk'a da gaske a lokacin,na dinga ciwo kamar ba zan kai labari ba,abubuwa biyu suka had'e min,rashin miji da rashin mahaifi lokaci guda,in ban da Allah waye zai maka wannan?ganin halin da nake ciki shiyasa Ummana bata tambayeni Hidaya da mahaifinta ba,har sai da aka d'auki kwana tara da rasuwar mahaifina,lokacin mutane sun baje y'an zaman makoki,na rame na k'ok'ale tamkar allura,ko mik'ewa tsaye nayi jiri nake ji sai an rik'eni,bana iya ci balle sha,kullum kuka nake me soya k'irji da zuciya.

Ranar kwana goma da zuwa na Gombe Ummana ta sameni har d'akinta in da nake kwance ina sana'ar kuka na,ta zauna ta d'agoni ta tasheni zaune,sannan ta tsura min ido ta dinga lallashina da kalamai masu dad'i tare da yi min nasiha da hak'uri akan rashin mahaifina,sannan ta tambayeni shin ina mijina?ina Hidaya?kuma ya akayi na zo Gombe a ranar ?kamar ina da masaniyar mahaifina ya rasu?haka ta dinga jeromin tambayoyin da suka sake tayar da hankalina,na dinga wani irin kuka me tayar da hankali da ban tausayi,har ita ma nasa ta fashe da kukan ,tana ta rok'ona akan na fad'amata abinda ya faru,domin wannan kuka da damuwar da nake ta shallake hankali da tunani,da k'yar na iya bud'e baki cikin kuka na fayyacewa mahaifiyata dukkan abinda ya faru,abu d'aya na b'oye mata,shine barin Hidaya da nayi a Kaduna,sai nace mata wad'annan mutanen sun tafi da Hidayan da gawar mahaifinta,kuma ban san in da suka tafi ba,saboda na san in dai na fad'amata Hidaya na Kaduna tilas zata ce sai an karb'o ta,shiyasa nace mata haka,sannan na k'ara mata da cewa mutanen sun ce muddin na bibiyesu ko na fallasa su gun hukuma to nima sai sun kasheni,kuma sai sun k'arar da kaf zuri'ata dake doron k'asa,dan haka na kiyaye. Wannan bayani da nayi wa mahaifiyata ya sakata cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa,tayi kuka mara iyaka tare da mamakin yadda mutanen duniya suka lalace,zalunci da mugunta ya mamaye zukatan al'umma,wanda mumini na k'warai ba zai tab'a aikata wannan mummunan aiki ba,haka muka had'u muka dinga kokawa da jajantawa juna.

Ummana ta k'ara bani hak'uri tare da min nasiha akan gara mu hak'ura kar muce za mu d'au wani mataki,tunda ba k'arfi garemu ba,ga yadda k'asar ta mu ta zama manya suna taka talakawa yadda suke so kuma babu yadda za a yi,idan ma muka ce zamu shigar da k'ara bamu da wata babbar shaida,reahe ma zai iya juyewa da mujiya,idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kama ka caraf,gara mu barwa Allah komai zaiyi sakayya lokacin da bamu zata ba,tashin hankalinta d'aya ne wato bamu san halin da Hidaya take ciki ba,ko tana raye ko tana mace Allah masani,kullum zancenta baya wuce na Hidaya tana addu'ar duk in da take in tana raye Allah ya cigaba da kare ta,kuma Allah ya bayyanata.

Ni da yake na san Hidaya na raye bana damuwa da hakan,sai dai kullum ina mata addu'a,ban tab'a mantawa da ita ba,haka nan mahaifinta da Oga Taufik' kullum sai nayi kuka idan na tuna su da rayuwar da muka shimfid'a mai dad'i,yau komai ya wargaje dalilin azzalumai,ba mijina,ba mahaifina,babu y'ata sanyin idaniyata a tare dani,sai inji wani bak'inciki kamar na mutu,sai in tuna da wad'anda basu da kowa,wad'anda suka tashi a gidan marayu basu da dangi,sai in ga ashe ni Allah yayi min lud'ufi ma da ya barni da uwata ina ganinta ina jin dad'i,ga y'ar uwata Sajida ma akusa dani,sai in godewa Allah abisa jarrabawar da yayi min,Amma tabbas a lokacin nan na shiga tashin hankali mara misali,babu ranar da zata fito ta wuce ban zubar da hawaye ba,abinda yake sanyaya min raina kawai shine yawan mafarkin Hidaya da nake,cikin rayuwa ingatacciya da kyawun yanayi,wannan kad'ai ya kan sani naji farinciki mara misaltuwa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin k'alubale,kwana bayan kwana,sati bayan sati,wata bayan wata,shekara bayan shekara,har aka d'auki wasu shekaru kafin na fara manta wasu Abubuwan da suka faru da ni,amma ban tab'a mantawa da Sulaiman da d'iyata Hidaya ba,da kuma Oga Taufik'kullum ina musu addu'a,rayuwa dai muna yin ta kadaran kadahan,mu ba masu k'arfi bane amma akwai rufin asiri,abin da mahaifinmu ya mutu ya bari shi muka dinga juyawa da jalautawa muna rufawa kanmu asiri da shi,a lokacin ne kuma mane ma auren Sajida suka fara bayyana kasancewar ta girma sosai har tayi candy,sai Ummana tace min nima ya kamata na fitar da miji nayi aure zamana haka baida wani amfani,nan fa hankalina ya tashi sosai domin banga ta in da zan iya wani aure ba a halin da nake ciki,duk da Sulaiman ya mutu amma shine kawai a raina,na dinga kuka ina ce mata nifa ba zan yi wani aure ba har abada,ganin tashin hankalin da na shiga sai Ummana ta rabu da ni da zancen fito da miji,akayi bikin Sajida aka gama aka kaita gidan mijinta nan Gombe a unguwar Arawa.

Bayan bikin ne nake fad'awa Ummana ina son komawa makaranta domin na rage zaman gida da yawan tunani,Umma ta bani k'warin gwiwa sosai,sai dai tunaninta ta ya ya zan dinga samun kud'i ina biya a makaranta?tunda bamu da wani k'arfi?a lokacin ne na d'auko sark'ar gold d'ina da na tawo da ita,na cewa Ummana ita zan siyar nayi hidimar makaranta,ragowar kud'in kuma sai mu ja jari mu kama sana'a,haka kuwa akayi,muka saida sark'a kuma tayi daraja sosai da sosai,wani d'an uwan mahaifina Kawu Muttak'a yayi min cuku cuku har na samu shiga jami'ar GOMBE domin cigaba da karatuna,wanda na d'auki b'angaren shari'a a matsayin abin da zan karanta,ko domin cimma wani k'uduri na wa.Ragowar kud'in kuma muka fara sana'ar sayar da abinci a cikin gida,Umma ta d'auki ma'aikata guda biyu suna taya ta aikin,nima duk randa bani da lakca ina zama ayi da ni,da yake Umma mai tsafta ce kuma ta iya abinci sosai nan da nan muka samu kasuwa sosai da sosai,abinci har k'arewa yake ayi ta zuwa nema.

Cikin lokaci k'ank'ani Allah ya sakawa sana'ar mu albarka,sai gashi mun tara kud'i mai yawa,harkar karatuna kuma na tafiya yadda ake so,na dage sosai karatu nake ba da wasa ba,kullum Hidaya na raina,ina jin sha'awar zuwa Kaduna domin na binciki halin da take ciki.

Wata rana kawai na tashi da son ganin Hidayan,zuciyata sosai take azalzalata akan son ganinta,ji nake in banje Kaduna a lokacin ba kamar wani abu zai faru da ni,hakan ya sa na samu Ummana na tsarata akan cewa Za mu yi wata tafiya a makaranta zuwa Jami'ar Kaduna, Jami'ar Kaduna ta gayyaci Jami'ar GOMBE domin k'arawa juna sani akan wasu abubuwa da suka shafi harkar karatu,Umma ta amince sannan ta bini da addu'ar samun nasara da kiyayewar ubangiji.

Na shirya nayi wa Umma sallama na fice sai tasha,na nemi motar Kaduna na d'ane,direba ya kwashi mota ya dinga falfala gudu,ni dai bakina d'auke da addu'o'i kala kala har muka isa Kaduna lokacin kusan k'arfe d'aya na rana,da na sauka daga mota sai na d'akko nik'ab d'ina a cikin jaka na d'aura,kamar me gudun kar na had'u da wanda ya sanni,cikin ikon Allah ban manta da sunan unguwan Tudun wada ba,sai gani a cikinta ina bin layi layi har na zo kan layin da kangon nan yake,wanda muka zauna ciki randa na bawa Hamza Hidaya,sai naga kangon ma tuni har an gine shi ya zama gida, dan ma dai ina da gane guri shiyasa ban b'ata ba.

Na d'an jima ina tsaye ina k'arewa gurin kallo kafin na cigaba da tafiya na b'ulla wani layin,sai lokacin naji zuciyata na tambayata wai shin ma ina zanga Hidayan?tunda ba sanin gidansu Hamzan nayi ba,shin ma har yanzu Hidayan tana hannun Hamzan?kuma shin har yanzu Hamzan suna wannan garin cikin wannan unguwar?ina zan gansu?take k'wak'walwata ta shiga yi min wad'annan tambayoyin .

Ina tsaye daga gefe nake wannan tunanin,wallahi kamar an ce min kalli d'aya gefenki kawai na juya,me zan gani?Hamza ne da Hidaya suke tafe,yana rik'e da jakar ta ta makaranta da alama ko islamiyya zai raka ta,suna tafe suna hira fuskokinsu da murmushi,Hamza ya k'ara girma sosai,Hidayana tayi girma ta k'ara kyau fes da ita kamar ba mai lalura ba,ban san lokacin da Hawaye ya kwararo min ba,kamar na ruga da gudu na isa wajensu,amma k'afafuwana suka gaza hakan,ban san me zance musu ba idan naje gare su,kwata kwata ma ban shirya hakan ba,ba zan tab'a iya manta kamannin Hamza ba balle y'ar da na haifa a cikina,ta gabana suka wuce lokacin Hidaya na dariya k'ila wata maganar Hamza ya fad'amata,kuma a lokacin da suka zo dab dani naga Hidaya tana waige waige k'ila ko wani yanayin taji a jikinta,da naga haka sai nayi hanzarin juya baya har suka wuce,sannan na juyo na cigaba da kallon bayansu har suka k'urewa ganina,hawaye sosai na dinga zubarwa a wajen,nafi k'arfin rabin awa kafin na share hawaye na na matsa d'an can gaba kusa da wani mai siyar da manja da man gyad'a,yana zaune a rumfarsa ta langa langa,nayi masa sallama ya masa yana tasowa da hanzari ko yayi zaton mai zan siya,sai na gaishe shi,sannan na tambaye shi dan Allah ina neman gidan su Hamza,an ce min a layin nan yake,sai ya tambayeni Hamzan babbane ko k'arami?nace masa babba ne dan har ma ya fara zama saurayi,sai yayi murmushi yace min .

"HAMZA GARKUWAR HIDAYA za ki ce min kawai Hajiya"

Nace masa "Au haka ake kiransa?"

Ya jijjiga kai da fad'in.

"K'warai kuwa,idan ba haka kika ce ba ba lallai a gane ba,saboda akwai Hamza da yawa a layin nan har da yara,amma kina cewa GARKUWAR HIDAYA to za a shaida shi "

Sai nace masa "Ayya ! to me yasa ake kiransa da hakan,wacece kuma Hidayan?"

Sai naga ya kalleni sosai kafin ya kuma murmushi yace min.

"Da alamun dai ke ma baki san Hamzan sosai ba ko Hajiya?dan duk wanda ya san Hamza to dole ne ya san Hidaya, ita Hidayan kuma k'anwarsa ce,dalilin kiransa da GARKUWAR HIDAYA kuma saboda tsananin sonta da yake da kareta,baya barin kowa ya tab'a ta,ya zame mata GARKUWA SOSAI,ko yanzu ma basu dad'e da wucewa ta nan ba ya tafi rakata makarantar islamiyya,da alamun dai ke bak'uwa ce baki ma san su Hamzan sosai ba ko"

Nan da nan na girgiza kai ina fad'in.

"Tabbas ban san su ba,kwatance akayi min aka ce idan naje gidan su Hamzan na shiga na fad'i gidan da nake so a kaini to za a kaini,yanzu dai gidan su Hamzan za ka taimaka ka nuna min"

Babu b'ata lokaci kuwa ya d'aga yatsan sa yana nuna min gidan da ke d'an can nesa da mu kad'an,nayi masa godiya ina kallon k'ofar gidan,na zaro d'ari biyar na bashi,ya dinga yi min godiya,sannan na wuce shi kuma ya koma runfarsa ya zauna.

Ta k'ofar gidan su Hamzan na wuce,na jima a tsaye ina kallon gidan da Hidaya take rayuwa a ciki tamkar a gidan aka haifeta,nayi kuka sosai ina jinjina k'addarar da ta rabani da gudan jini na,kamar na shiga gidan haka na dinga ji,sai kuma na taurara zuciyata kawai,ina ji ina gani na wuce daga k'ofar gidan na koma bakin titi na nufi tasha,take na samu motar da za ta tashi zuwa Gombe ana jiran mutum d'aya,ba tare da jinkiri ba na haye direba ya d'aga da mu zuwa Gombe,zuciyata cike da raunin ganin Hidayata,sai dai cikin farinciki nake da murna matsananciya ganin yanayin da ta samu kanta na kulawa wanda ko ni sai haka,zuciyata kuma ta k'ara girmama HAMZA GARKUWA,tare da k'ara jin wata k'aunarsa mai girma ta mamaye ni.

Tun daga lokacin sai na samu kwanciyar hankali sosai,kuma daga ranar ne duk lokacin da naji mararin ganin Hidaya na kan tsara Ummana na tawo Kaduna kawai don na ga Hidaya,na kan lab'e tare da rufe fuskata,wataran na ci sa'ar ganinta ko za ta tafi makaranta ko kuma ta dawo,wataran na ganta a shagon da ke jikin gidan nan na sai da wayoyi da yin chaji,wataran ma har naje na dawo bana cin karo da ita,sai dai duk da hakan na kanji dad'i saboda na san tana samun kulawa sosai.

A haka shekaru suka dinga ja har na kammala karatuna na fito da babban kwali,haka nan na dinga ziyartar wurare daban daban dan k'ara ilimi akan harkokin shari'a,har kuma lokacin burina na na a raina na ganin bayan Alhaji Maude da Babban mak'iyina wato Alhaji Mudassir,wanda kaf fad'in duniya bani da mak'iyin da ya fishi.
Lokacin Hidaya ta girma sosai,kuma ina da yak'inin sak'on da na bar mata ya kusa isa gareta,duk da na san zata ga bak'ina sosai akan gujemata da nayi,amma na san wannan ita ce hanyar da yafi kamata na bi,domin cimma k'udurina.

A ranar da Hamza ya ganni a airport tabbas ni ya gani,shi ban san abin da yaje yi ba,amma ni zan yi tafiya ne zuwa wata k'asa akan harkar Shari'a,wanda gwamnatin Gombe ta d'auki nauyi na saboda k'wazon da nake da shi a harkar,wannan tafiya da nayi ita ce musabbabin da na daina jin labarin ku ko bibiyar lamarinku,har aka yi shirin aurar da Hidayan ba tare da na sani ba,tunda yawanci abubuwan da suke faruwa da ita ina sanin wasu,ta hanyar zuwan da nake da kuma wasu hanyoyin da nake bi don bincike akan ku.

Mun d'auki lokaci mai tsawo a tafiyar,domin kwana na biyu da dawowa garin Gombe kawai na dinga jin wata muguwar kewa wadda ban tab'a ji ba,zuciyata na azalzalata kan naje naga Hidaya,saboda wasu irin mafarkai da nake da ita,kullum na ganta a mafarki sai na ganta tana kuka sosai tana mik'o min hannayen ta domin na kama,sab'anin baya da duk lokacin da zanyi mafarki da ita na farinciki ne,zan ganta tana walwala da nishad'i,amma yanzun mafarkina ba haka yake nuna min ba,nan na tabbatar k'ila ko tana cikin damuwa ne ko b'acin rai,shiyasa hankalina ya gaza kwanciya.

A firgice na tashi saboda wani mugun mafarki da nayi da Hidayan,kuka nake sosai ina ambatar sunanta har ban san lokacin da Ummana ta taso ta zo gareni ba,ta rik'eni ganin ina zabur kamar zan ruga da gudu,addu'a ta dinga yi min har na samu nutsuwa,sai kuma na dinga kuka kafin na tashi da hanzari in ce mata ni Kaduna zan tafi,cikin tsananin mamaki take tambayata me zan yi a kaduna a tsohon daren nan?wajen wa za ni a kaduna?wa na sani a can?cikin gigita nake ce mata ni wajen Hidaya zan tafi,y'ata zanje na gani,so nake na san halin da take ciki kawai a yanzu,Umma cikin tsananin mamaki ta kamoni ta zaunar da ni,tana tambayata wai Hidayan da shakara da shekaru ba a tab'a jin d'uriyarta ba ta ya ya na san cewar tana kaduna,waye ya fad'a min?ko dai a mafarkina na gani?Sai lokacin na fara dawowa hayyacina na tuna she fa Umma bata san Hidaya na kaduna ba,ashe fa na b'oye mata komai,to amma yanzu ba zan iya b'oyewar ba,bayyanawa a wannan muhallin ita tafi dacewa da ni,a hankali na bud'e bakina na fad'awa Ummana komai da ya faru cikin kuka matsananci,ban tab'a sanin Ummana tana da fushi sosai ba sai lokacin,domin har marina tayi,ta rufe idanunta ta dinga min fad'a kamar ta cinyeni,wai ni mahaukaciyar ina ce da akan wannan dalilin na banza da wofi zan rabu da y'ata,a wane garin mahaukatan na tab'a ji an yi haka?kai ranar naga fushin Umma wanda ban tab'a gani ba,ta dinga kuka sosai tana fad'in ban kyauta ba na cutar da Hidaya,ni ma na dinga kuka ina kawo mata uzurina akan hakan,saboda na tsorata da su Alhaji Mudassir na san komai za su iya aikatawa,ranar dai haka muka kwana cikin kuka,da assssuba kuwa Umma ta d'auki waya ta kirawo mijin Sajida akan tana son ya kawo Sajida a lokacin tana son ganinta,yace shima har ya shirya zai yi wata tafiya shi da ubangidan sa da asubar, za su yi sati biyu ne a tafiyar ,amma bari ya kawota ita da yara sai ya wuce kawai,haka kuwa akayi,yana kawo su ita da yaran ta shi kuma ya wuce ya tafi,Umma ta zayyanewa Sajida komai,hankalinta ya tashi itama har da kuka tana min fad'an abin da na aikata,ni dai hak'uri na ba su akan duk abin da ya faru,sai kuma Umma tace tilas mu tashi mu nufi Kaduna a wannan asubar dan zuwa mu gano Hidaya,kuma tilas in bayyana mata kaina.

A wannan Asubar muka tawo Kaduna ni da Sajida,Umma ta dage sai ta bimu muka tausheta akan ta zauna tare da yaran Sajida mu kad'ai ma mun isa muje,da k'yar ta yarda ta bi mu da addu'a,shine fa muka dira Kaduna a wannan ranar kuma da wuri,saboda muna zuwa tasha muka samu motar da za ta tafi Kaduna ba da b'ata lokaci ba,

Ba k'aramin mamaki Hamza da Mahaifiyarsa suka shiga ba a lokacin da suka yi arba da ni cikin gidansu ina bayyana musu kaina,Hamza yayi kukan farinciki da murna yana kallona,da na nemi ganin Hidaya sai aka sanar dani jiya aka d'aura mata aure tana gidan mijinta,take kuma Umman Hamza ta bawa Hamza umarni kan yaje ya tawo da Hidayan da mijinta domin su ganni,shine Sajida ta bishi suka tafi,take kuma suka je suka tarar da abin da ya fallasa komai.

Umma ta sauke Numfashi tana kallon mutanen falon kowa kukan jin labarinta yake yi,yayin da Hidaya ta mik'e da hanzari ta nufeta ta fad'a kanta tana wani irin kuka tana kiran Abban ta,Khaleel kam k'urawa mahaifinsa ido yayi cike da tsantsar tsana da k'yama,Mummy har shid'ewa take saboda tsananin kuka,kafin ta d'ago kai tana rungume da Hidaya ta kalli Daddy ido cikin ido,wanda yake had'a uwar zufa cike da mad'aukakin tashin hankali mara misali,cikin tsana da k'yama ta ce masa.

"ALHAJI MUDASSIR,yau k'aryarka ta zo k'arshe! k'ila Allah yayi nufin tona asirinka ne shiyasa ya had'a auren d'an ka da y'a ta,kuma ya raba auren a dai dai lokacin da komai zai fallasa,kaine ka aikata komai! kaine ka kashe min mijina ! kaine ka sa na rabu da y'ata ta cikina tsawon shekaru! wannan duk sharrinka ne ! don haka na shirya tsaf domin yin shari'a da kai,duk da cewa d'anka Khaleel LAUYA NE,to zan gani zai bi bayanka ne ko zai bi bayan GASKIYA,ko a yanzu burina na farko ya cika,domin kuwa na tabbatar kud'in nan da kuke hank'oro har yanzu baku same su ba,suna in da na b'oye su tsawon shekaru,in da babu wani mahaluk'i da ya sani da ga ni sai ubangiji na,a yanzu kuma nake fatan burina na biyu ya cika,wato ganin bayanka da kai da azzalumin abokin ka wato MAUDE,dukkan abubuwan nan da suka faru kaine silar su MUDASSIR,kai ne ka kashe min MIJINA ka rabani da shi,bud'e baki kayi magana ko ba kai ba ne......?" Mummy ta k'ara she da daka masa wata muguwar tsawa.

Take Daddy ya mik'e a firgice ya rik'e kansa ya fashe da wani irin gigitaccen Kuka yana fad'in.

"Ni ne.....Tabbas Ni ne....Wallahi Ni ne na ......! 😳

Comments
Share
Vote
pls

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.