Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 33 of 50
BABI NA SITTIN DA BIYAR DA NA SITTIN DA SHIDA
***Dab da kunnen Daddy Alhaji Maude ya sunkuya a rikice,yayi magana a hankali yadda ba Wanda zai iya jin abin da ya fad'a.
"Mudassir har an d'aura Auren ne…!?"
Da k'yar Daddy ya iya jijjiga kansa cikin dukan zuciya da Alhini,Alhaji Maude bai fahimci jijjiga kan Daddy ba shiyasa ya k'ara rage murya Dan kar a jiyo shi yace.
"Kuma da Khaleel d'in aka d'aura…!?"
Daddy ya kasa magana tsabar k'uncin da yake ciki,yayin da hayaniyar mutane tayi yawa kowa cikin fara'a ana ta gaishe gaishe,Alhaji Maude ya damk'i hannun Daddy da ke zaune gumi na yanko masa,da k'yar ya daddafa ya mik'e ya bi bayan Alhaji Mauden da ke jan sa zugui zugui tamkar rak'umi da Akala,Mutane sai gaisuwa da fatan Alkairi suke kawowa Daddy yana amsawa cikin yak'e tamkar Wanda aka yi wa dole,sai da suka fice daga cikin jama'a har zuwa in da Alhaji Maude yayi parking motar sa ya bud'e suka shiga.
Cikin matuk'ar fusata Alhaji Maude ya dubi Daddy ya zuba masa harara kafin yayi magana.
"Tabbas Mudassir ka bani mamakin da baka tab'a bani ba!yaushe ka zama sahorami sullutu haka?kana ji kana gani D'an ka ya d'auko kara da kiyashi amma ka kasa d'aukar mataki har ka bari aka d'aura Auren?wallahi Mudassir ka gama da rayuwar ka!ka yi wa rayuwar ka tabon da ba zai tab'a goguwa ba har abada!ka had'a jininka da jinin shegiya Y'ar zina Y'ar kwararo!duk wani tarihin samuwar yarinyar nan ina da shi a tafin hannuna ! Wai ina ka kai taurin kanka na baya da har ka yi sanyi haka?ina ka kai muguntar ka da bak'ar zuciyar ka da har a wannan lokacin ka kasa juya Khaleel ?Me ya sa a wannan lokacin ka kasa d'aukar shawarata ?bayan duk wasu Abubuwa da kake gabatarwa a rayuwar wa nine k'ashin bayan su ! Kuma kana ganin nasara idan har na baka shawara"
Kamo hannun sa Daddy yayi idanuwan sa jajir !yayi masa nuni da can nesa in da Khaleel da Hamza da sauran Abokanan su ke tsaye,kowannen su bakin sa a bud'e tsabar murna da farinciki,musamman Khaleel da tsananin farincikin da yake ciki ba zai misaltuba,hannuwan sa sark'afe da na Hamzan suna nane da juna,cikin rawar baki Daddy ya fara magana.
"Dubi yawan farincikin da Khaleel yake ciki Maude !So kake na katse shi na maida shi bak'inciki?tun Khaleel yana yaro nake juyashi yadda nake so a matsayina na Ubansa mai tutiyar ina k'aunarsa !ko baya son Abu haka yake biye min yayi min biyayya,Zuwa wannan lokacin da ya girma ya mallaki hankalin sa ya kamata nima na barshi ya shak'i iskar y'anci !Alhaji Maude duk wasu Abubuwa da muka shuka a baya a yau ina danasanin su,kullum k'ara girma muke mutuwa na doso mu !ya kamata muyi hankali musan duniya ba matabbata ba ce !abin da baka sani ba jiya wallahi kwana nayi banyi bacci ba,amma da na rufe idanuwan babu abin da nake gani Sai (Taufik' )….
Cikin zaro idanuwa Alhaji Maude yace .
" Taufik' kuma..!? Taufik' d'in da ya riga yayi nesa da rayuwar mu…!?
Daddy ya jijjiga kai hawaye na ciko idanuwan sa..
"K'warai kuwa! Na rantse maka da Allah a kwanakin nan shine kawai yake dawowa cikin zuciyata da kwakwalwata,ban San dalilin hakan ba !sai dai ina tunanin kamar sakayyar sa ce take dumfaro mu Maude ! Wannan kad'ai da wasu dalilan ya sa na kasa maida hankali kan hana Auren Khaleel, domin kar na sake tafka wani kuskuren a rayuwa ta, Wanda nayi ma a baya ina rok'on Allah ya yafe min,kuma a yanzu babu abin da yake raina irin son ganin TAUFIK' domin na nemi yafiyar sa kan manak'isar da muka shirya masa a baya tsawon shekaru ….!"
Wani irin murmushi Alhaji Maude ya saki,Wanda duk wani mai saurin fahimta yana ganin wannan murmushi ya San na mugun ta ne !cikin ransa yana cewa"Har abada ba zaka sake ganin Taufik' ba Mudassir !kuma yadda naga bayansa da sunan ka kai ma a shirye nake da naga bayanka !sai na rusa duk wata soyayya da alak'a da ke tsakanin ka da D'an cikinka !sai nayi maka tabon da sai ka gwammace baka zo duniya ba !Sai na sa D'an ka na cikin ka ya gujeka ! Ya k'yamace ka !ya tsane ka !Yadda ka rusa min target a wannan lokacin har ka bari aka yi wannan Auren to sai na lullub"e rayuwar ka da musibu na sharri wad'anda baka isa ka kufce musu ba,Mu zuba mu gani …..!?
K'wank'wasa glass d'in motar da aka yi shine ya katse tattaunawar su,Abokan Daddy ne da y'an uwa masu Neman sa domin yi masa fatan Alkairi akan Auren D'an sa Khaleel da aka d'aura.
********************
Rana ce mai matuk'ar d'unbun tarihi da soyuwa a zuciyar Khaleel, a lokacin da ya tabbatar an d'aura Auren sa da Hidaya Sai hawayen murna ya zubo masa,ya kwantar da kansa jikin Hamza ya rungume shi k'am yana hawaye yana ta fad'in "Alhamdulillah ala kulli halin" Shi ma Hamzan tarbarsa yayi ya rungume shi yana runtse idanuwa da sakin ajiyar zuciya mai girma, shikenan komai ya k'are,Hidaya ta zama ta Khaleel, Allah ubangiji ya cigaba da ba shi hak'uri da k'arfin Zuciyar.
An cigaba da hidimar biki a ranar,Wanda Khaleel babu yadda baiyi ba akan yaga Hidaya bayan d'aurin Aure hakan ya gagara,su Hansa'u da Sumayya suka dinga Ja masa rai suna masa dariya,ya marairaice masu kamar zai yi kuka yana rok'onsu,amma suka dage akan ya hak'ura tunda yau ne za a kai ta gidan sa,sai ya cinye ta ma k'arewar Kallo,har Hamza sai da yaji Haushin b'oye Hidayan da ake yi ya kalli su Sumayya fuska kadaran kadahan yace.
"Ku bashi matarsa ya ganta mana,menene abin b'oyo haka tunda har an d'aura Auren ai kuma komai ya k'are"
Sumayya ta D'an yi dariya cike da ladabi ta dubi Hamza tace.
"Ya Hamza mu fa a ka'ida ba zai ganta ba har sai mun kaita gidan sa ya sa yi baki tukun"
Ya yamutsa fuska yana tab'e baki yace.
"Meye siyan baki kuma?au wai daman har yanzu ana wannan al'adar ne?
Hansa'u tayi caraf tace.
" Sosai ma Ya Hamza ana yi,kuma mu bakin tamu amaryar tsada ne da shi sosai sai an wahala kafin a siye shi"
Wani miskilin murmushi Hamza tayi yace .
"Allah ko? To kar ku manta fa ita kanta gabad'ayan ta mallakin Khaleel d'in ce balle wani bakinta"
Ya waiwaya yana duban Khaleel da ya langab'e yana sauraren su,ya kanne ido d'aya yana d'aga girarsa yace .
"Ka San shawarar da zan ba ka?
Khaleel ya jijjiga kai yana murmushi, Hamza ya dafa kafad'ar sa ya matsa dab da kunnen sa yana masa rad'a,Khaleel ya d'ago yana kwashewa da dariya yana ruk'unk'ume hannun Hamza,fad'i yake cewa.
" Exactly Aboki…Na rantse sai na cinye bakin nan tassssssss….Aboki komai ma sai na cinye….bazan bar ragowar komai ba….."
Dariya Hamza yayi suka tafa, yayin da su Sumayya suka bi su da kallo basu fahimci dariyar da suke ba.
Tun da aka d'aura Auren Hidaya ke faman kuka da hawaye sharaf sharaf,tun Umma na lallashin ta har ta rabu da ita ta shiga sabgar ta da mutane,kafin wani lokaci zazzab'i ya rufe ta Sai rawar sanyi take yi,da taji za a dame ta ma d'akin Hamza ta gudu tayi kwanciyar ta a can,saboda baya d'akin yana tare da su Khaleel.
Sai wajen Azahar da ya shigo canza kaya sannan ya tarar da ita k'udundune kan bed d'in sa,Sosai ya rud'e yana tabayarta me ya faru?babu magana sai hawaye !da ya fahimci zazzab'i take da sauri ya fita ya nemo mata maganin ta,saboda baya son ciwonta ya tashi,sun samu an dad'e bai motsa ba,har abinci yayi wa Sumayya magana ta kawo mata,ya tasata a gaba tana kuka sai da ta ci sannan ya bata maganin ta sha,Yace ta shiga toilet tayi alwala,haka ta mik'e jiki ba k'wari zuciyar ta cike da tausayin Ya Hamzan ta,ta d'auro alwala ta fito,yana zaune har tayi sallah,Sai yace ta kwanta ta huta zuwa la'asar saboda hayaniyar mutane tayi yawa,sai Neman Amarya ake yi kowa sai ace masa bata jin dad'i.
Ta sha baccinta sai k'arfe hud'u da mintuna na yamma sannan Hamza ya kira Umma a waya yace a tashe ta tayi sallar la'asar,Umma da kanta ta je d'akin Hamzan ta tashe ta,cikin ikon Allah sai ta tashi ragau da ita ba zazzab'in,Umma ta sa ta sake wanka tayi Sallah,sannan Hansa'u ta rangad'a mata kwalliya,nan da nan Amarya Hidaya ta fito ras da ita sai walwali da d'aukar ido take yi,Shagali ya sake b'arkewa a cikin gida,y'an kid'an k'warya sai cashewa ake mata na tik'ar rawa da lik'i, Sai da aka fara kiran sallar magriba sannan aka dakata.
K'arfe takwas dai dai Hidaya durk'ushe cikin d'akin Hamza a gaban sa tana kuka,yayin da Hamzan ke ta lallashin ta da kalamai kyawawa masu cike da ilimi,yana karanta mata darajar Aure da martabar sa,Sannan ya umarceta da ta tsare Salla da karatun alk'ur'ani, da yawan ambaton Allah da istigfari,Sannan ya fad'a mata maganar da ta sake raunata zuciyqrta da sakata hawaye mara misali,domin cewa yayi.
"Hidaya a da nine GARKUWAR ki,amma yanzu baki da wani GARKUWA da ya wuce Khaleel, ki bishi ki masa biyayya fiye da kowa a Duniya,wallahi idan kika aikata haka za ki tsira har ki samu Aljanna mad'aukakiya"
Yana gama wannan jawabin K'anwar Umma ta shigo d'akin domin fita da Hidaya,har sun je k'ofar fita Hamza ya yayi magana cikin sanyin murya.
"Ina takardar da na baki jiya?
Hidaya ta waiwayo ta d'ago kanta ta kalli Hamza fuska duk hawaye,ta d'ago tafin hannun ta nuna masa takardar,cikin muryar kuka tace .
"Ina tare da ita Ya Hamza"
Yayi murmushi ya russunar da kansa k'asa saboda hawayen da ke shirin zubo masa,yayi magana a hankali.
"Shikenan ki rik'e ta Hannu bibiyu,kuma idan za ki duba ta ki ringaji a Zuciyar ki kamar Mummyn tana gabanki,kuje Allah yayi miki Albarka ya sa ki shiga a sa'a"
Mik'ewa yayi ya shige toilet da sauri,yayin da Hidaya ta sake fashewa da kuka mai k'arfi,da k'yar K'anwar Umma ta ja ta suka fita daga d'akin.
An kai ruwa rana kafin a b'amb'are Hidaya daga jikin Umma,Sosai ta ruk'unk'ume ta tana shirgar kuka har da birgima,Umma kanta sai da tayi kukan rabuwa da Hidaya,shekara da shekaru suna tare amma yau sun rabu!ta San da Hamza ta aura babu abin da zai raba su,amma ya za su yi da hukuncin Ubangiji?
Haka aka rankaya domin kai Hidaya gidan ta,wadda tsananin kuka da yadda zuciyar ta ke tafasa take jin kamar ta mutu ta huta da d'acin rabuwa da Umman ta da Ya Hamzan ta.
****************
D'aki ne na alfarma da aka shirya shi da k'ayatattun kayan d'aki na musamman,duk da kasancewa ba nan ne muhallinsu da zasu dawwama ba,amma duk da hakan Khaleel yayi Namijin kokari wajen k'ayata wannan Muhallin.
Kowa ya fashe aka bar Hidaya kad'ai ita da Hansa'u da Sumayya,wad'anda suke ta lallashin ta ganin yawan kukan da take,Hansa'u cewa take.
"Ki rage kukan nan Hidaya,Auren soyayya kuka yi ke da Uncle Khaleel ba Auren K'iyayya ba,Don Allah kiyi hak'uri kar ki janyo ciwon ki ya tashi ! domin kin san yawan damuwa tana tayar da ciwon,wannan rana kamata yayi ki d'auketa ta farinciki ba akasin hakan ba,Ki bud'e idanuwa ki dubi baiwar da Allah yayi miki Hidaya,kin samu Miji na gari wanda bai rasa komai ba ! Me tsananin sonki da k'aunarki da begen ki, kamata yayi ki godewa Allah ba kiyi ta kuka ba......
Sumayya ta sauke tagumin da tayi ta saki ajiyar zuciya,fuska cike da jimami ta fara magana.
"Hmmm ! ke dai bari Sister Hansa'u, ni gabad'aya Hidaya ta sanyayar min da jiki na,wannan kuka da take kamar wadda aka kawo ta gidan mak'iyin ta?"
Sai lokacin Hidaya ta d'ago kai ta kallesu da kumburarriyar fuskar ta da tasha kuka,cikin dusashewar murya tayi magana hawaye na sake b'ullowa.
"Ba zaku fahimci kukan da nake ba k'awayena,abinda nake so kawai ku sani shine,ban riski wata rana a rayuwata da ta kasance min cikin yanayi guda biyu ba kamar wannan,ma'ana farinciki da akasin sa"
Da sauri Summaya ta tare ta da cewa.
"kamar ya ya ?fahimtar da mu Hidaya"
Hawaye na zirarowa tace.
"Yau d'in ranar farin cikina ce,haka nan ranar bak'in cikina ce!
A hanzarce suka dubeta suna shirin magana,motsin shigowa da sallama da k'amshin wani daddad'an turare ya dakatar da su.
Khaleel ya bayyana cikin k'ayatacciyar shigar da ta sake fito masa da asalin kyawunsa da haibarsa,kamalarsa ta cika gurin tsaf,Haske da walwali ne kawai suke fitowa a fuskarsa mai d'auke da k'ayataccen murmushi,idanuwansa akan Hidaya da kanta ke sunkuye tana sharar hawaye,Su Hansa'u suka bishi da kallo suna amsa sallamar sa,a zuciyar su suna fad'in "Gaskiya Hidaya kin dace da samun miji irin Khaleel"
A tare suka gaishe shi,ya amsa cike da kulawa da fara'a,Sannan ya zarce da cewa.
"Aboki yace in sanar da ku cewa dare ya fara yi,dan haka yana waje yana jiranku domin ku k'arasa gida tare dan duk an fashe babu kowa"
Hidaya na jin ya ambaci Aboki tayi zumbur ta d'ago kanta,ashe daman Ya Hamzan ta ya rakota gidanta kenan?to amma me ya sa yak'i shigowa?kamar Khaleel ya san tambayar da ke ranta taji yana cewa da su Sumayya.
"Na yi na yi ya shigo tunda shine babban Aminin Ango amma yak'i,wai cewa yake a wane k'auyen na tab'a ganin yayan Amarya ya halarci gurin siyen bakin k'anwarsa?na ce yazo a matsayin Aminin Ango mana,amma yace ba za a yi wannan zubar da girman da shi ba"
Su Sumayya suka yi dariya shi ma yana taya su,suna mik'ewa dan shirin tafiya sai gani zumbur ni ma na mik'e na rik'o hannun Hansa'u dake gab da ni,Uncle Khaleel ya waiwayo ya tsura min idanuwansa yana min wani gajiyayyen kallo me tafiya da numfashin mutum,da k'yar ya iya motsa bakinsa yayi magana a hankali kamar zai had'iyeni don kallon da yake min.
"D'an saketa kinji my love ! Aboki na jiransu dare yana sake yi kuma"
Fashewa nayi da wani irin kuka kamar zuciyata zata fito,Hansa'u tayi tayi ta k'wace hannunta amma ta kasa saboda rik'on da nayi mata me k'arfi kamar zan b'allata ina kuka,ban ma san lokacin da Uncle Khaleel ya zagayo ta bayana ba,kawai jina nayi a jikinsa yayi min wata shegiyar runguma ya dabaibayeni,bakinsa dab da kunnena ya fara yi min wata irin magana da zak'inta ya so juyar min da kaina.
"D'an cika ta ! Sakar mata hannu kar ki b'allata kinji my love ! saketa ! saketa don Allah !
Ban ma san lokacin da hannuna ya saki hannun Hansa'u ba,saboda tasirin da jikinsa yayi wa jikina,tamkar jik'ak'k'en tsumma haka na lafke a jikinsa yana rungume dani,ina ji ina gani su Hansa'u da Sumayya suka fice daga d'akin,a lokacin da Uncle Khaleel yake sake k'ank'ameni jikinsa yana sauke ajiyar zuciya me tsananin k'arfi a jejjere.....!
Comments
share
vote
pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.