Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 26 of 50
BABI NA HAMSIN DA D'AYA DA NA HAMSIN DA BIYU
***Sauke hannun sa yayi bai maretan ba,ganin yadda ta tsorata,musamman da ya kasance bai cika yi mata tsawa ba,sai dai yau ta matuk'ar b'ata masa rai akan munanan kalaman da ta dangana kan ta da su.
Fuska a d'aure,a fusace yake wani irin kallon ta yace.
"Idan har kika sake ambatar kanki da wannan munanan kalaman ranki zai b'aci,domin zan iya dukan ki wallahi Hidaya,wane irin hargitsewa k'wak'walwarki tayi har kike fad'in wannan kalaman …!?
Cikin fitar hayyaci tace.
" Yanzu Ya Hamza fad'ar gaskiyar da nayi shine alamun hargitsewar k'wak'walwa?k'arya nayi?shin baka sona d'in ne?ko kuwa zaka rantse babu b'urb'ushin sona a Zuciyar ka..!?
Ya wani kauda kai cikin dukan zuciya,yayi magana a hankali.
"Kin tab'a ganin in da Yaya yak'i K'anwar sa?fad'in ina son ki ko bana son ki ai gidadanci ne Hidaya..!?
Ta girgiza kai cikin hawaye.
" Kar ka kufcewa maganata Ya Hamza,ka gane abin da nake nufi,ba irin wannan son ba,so na soyayyah,so na Aure nake nufi Ya Hamza….
Yayi mata wani kallo da ya k'ara hargitsa ta,sannan ya kawar da kai yace.
"Ni da bakina na tab'a furta miki cewar ina yi miki irin wannan son ne..!?
" Ko baka furta ba idanuwan ka sun fallasa ka,fuskar ka ta nuna ka,Labarin zuciya a tambayi fuska,ni na san kana sona,in kuma ba haka ba ka rantse cewar baka sona…!?
Ya d'aga mata Hannu yana dafe kansa,da k'yar yayi magana.
"Please Hidaya mu bar maganar nan,ko ina son ki ko bana son ki Abu d'aya kawai na sani,shine,ba zan so kaina domin na k'untata wa wani ba,wanin ma kamar Khaleel, muddin ina da yadda zan yi to zan yi domin na sa ma masa farinciki,Manzon Allah (S A W) yace.
" ka sowa D'an uwanka abin da kake sowa kanka"
Dan haka mu rufe maganar nan iya ni da ke,bana son wani ma ya ji ta,Khaleel da ke ya dace,kuma insha Allah zan yi Iya k'ok'ari na domin ya zama miji a gareki,sai dai kuma idan kin watsa min k'asa a idanuwana kin k'i amincewa ne"
Hidaya tayi wani murmushi na takaici,ta goge hawayen ta tsaf ta kalli Hamza tace.
"Allah kar ya nuna min ranar da za ka bani Umarni na k'etare shi,tunda har ka zab'i farincikin khaleel akan farincikina da naka shikenan Ya Hamza,ni kuma na amince zan maka biyayya,zan auri Khaleel ko da ba shi zuciyata take so ba,zan zauna da shi har na rabauta da soyayyar sa"
Wannan magana ta tara ma'anoni kala kala a Zuciyar Hamza,Wanda ke son sadaukar da farincikin sa akan abokin sa Khaleel, Khaleel d'in da ya nuna masa so iya so,ya gwammace ya b'ata da kowa akan Hamza,shiyasa yake son sakawa Khaleel da gingimemiyar sadaukarwa….
Daga wannan maganar Hidaya bata sake cewa komai ba,illa maida kanta da tayi jikin kujera ta kwantar,sannan ta runtse idanuwan ta,tana ta ambaton Allah a ranta ko za ta ji salama.
Hamza kam da k'yar ya tashi mota suka fara tafiya,k'wak'walwar kansa gabad'aya ta cushe,burinsa su isa gida ya samu ya kwanta ko zai samu nutsuwa,amma tabbas yana cikin tashin hankali.
******************
A maimakon Umma taga sun dawo cikin farinciki sai taga akasin hakan,dukkan su a hargitse suke,Hidaya tunda ta shige d'aki ta kwanta ko motsinta Umma bata sake ji ba,haka ma Hamza,Wanda ya shige d'akin sa ya kwanta lamo yana jinyar Zuciyar sa,mamaki ya ishi Umma,tai ta tambayar Hidaya ko wani Abu ya faru ne amma Hidaya ta kafe akan babu komai,kawai kanta ke ciwo,Umma dai ta san ba haka bane,amma ta k'yaleta da fad'in idan tayi tsami ai za ta ji.
A Daren ranar Khaleel ya addabi Hidaya da turo sak'onni na soyayya,wai ya kasa zaune ya kasa tsaye tunda har yanzu baiji amsarta ba,ta taimakawa numfashinsa da Zuciyar sa ta bashi amsa,ko zai samu ransa ya kai safiya a jikinsa,ita Hidaya ma gabad'aya abin d'aure mata kai yayi,ganin yadda lokaci guda Khaleel duk ya rikice mata,kalaman k'auna da soyayya kamar an masa gori,sai zazzago mata su yake.ta rasa da wane Abu ta burge Khaleel ta k'ayatar da shi har yake mata wannan son,ya fita kyau,ya fita Asali,ya fita kud'i da d'aukaka,gata nakasasshiya mai fama da ciwon sikila da maza ke gudun mata idan suna da shi,to ita kuwa menene abin so a tare da ita…!?
Da ta zurfafawa Zuciyar ta tunani sai kawai taga dacewar amsawa Uncle Khaleel k'udurin sa,ko domin yadda ya kawar da kansa wajen hangen ita d'in ba kowa ba ce face Y'ar tsuntuwa me lalura,amma ya runtse idanuwan sa daga hakan ya zab'o ta cikin dubban mata da suka fita komai,sannan kuma ya kasance zab'in Ya Hamzan ta,Hamzan da take jin sa can cikin k'ololuwar Zuciyar ta…
Tana gama yanke shawara da Zuciyar ta ta d'auki wayar ta,ta rubutawa Khaleel gajeran sak'o Wanda ke bayyana amincewar ta ga soyayyarsa,da bashi amanar kanta gabad'aya,tana turawa ta kashe wayar ta cillata k'ark'ashin pillow, Dan ta san muddin Khaleel yayi katarin ganin wannan sak'on to ba zai barta ta huta ba,zai iya kaiwa har wayewar gari yana yi mata sambatun soyayya…
Wani kuka mai cin rai ya tawo wa Hidaya,ta cusa kanta cikin pillow ta dinga kuka da hawaye tana jin ciwo a Zuciyar ta,ciwon son Ya Hamza,Wanda ta tabbatar a yanzu yayi mata nisa,haka ta shafe tsawon Daren babu bacci sai kuka da ciwon k'irji..
Da asuba bayan sun yi sallah ita da Umma a gida,sai Umman ta waiwaya ta kalleta ta ambaci sunan ta,Hidaya ta amsa a hankali muryarta duk ta dusashe tsabar kuka,idanuwan ta kam sun kumbura suntum,Umma ta girgiza kai ta k'ura mata idanuwa tace.
"Na yi na yi ki fad'a min abin da ke faruwa kin k'i ko?duk da na san baki cika tattauna matsalarki da ni ba amma ya kamata na san wannan,domin na hangi tarin damuwa a tattare da ke Hidaya,ba ma ke kad'ai ba har da yayan na ki shi ma na hangi damuwa a tattare da shi,amma dukkan ku kun k'i fad'a min damuwar ku a matsayi na na mahaifiyar ku,jiya ina jin ki kwana kika yi kina kuka babu bacci,shi ma Hamzan fitilar d'akin sa a kunne ta kwana alamar bai yi barci ba,kuma ko sallar Asuba bai fita ba yau a gida yayi abarsa,na kuma tabbatar duk abin da zai hana Hamza fita masallaci to babba ne,kuma na san kin san komai,Dan haka ki bud'e bakin ki ki fad'a min menene yake faruwa da ku…..!?
Hidaya tayi shiru,tuni hawaye sun sake tsinke mata,ta sunkuyar da kanta kan cinyoyin ta tana kuka,Umma tayi sakato tana kallon ta cikin tashin hankali,babu yadda bata yi akan Hidaya ta fad'a mata ba amma Hidaya tak'i,sai kuka kawai take tana shesshek'a….
Ganin haka sai Umma ta mik'e da sauri ta fice daga d'akin zuwa d'akin Hamza,tun daga bakin k'ofar take jiyo kamar yana kakarin amai,da hanzari ta bankad'a k'ofar ta shiga,yana tsugune yana ta kakari aman ya k'i fitowa sai kad'an,saboda babu komai a cikinsa,tsawon ranar jiya zuwa Daren bai iya cin komai ba tsabar damuwa,yana jin shigowar Umma yayi sauri ya d'auraye bakinsa da fuskar sa ya fito.
Tana tsaye tana kallon sa har ya zauna bakin gadon sa a hankali jikinsa babu k'wari,ta bishi da kallo taga kwana d'aya duk ya zabge,fuska babu walwala cikin kulawa tace.
"Wai ciwon cikin ne ya saka amai…!?
Ya gyad'a kai yana yamutsa fuska yayi magana a hankali.
" Eh Umma,aman ma ya k'i fitowa har k'irjina ya fara ciwo"
Tayi masa wani kallo,Sannan ta girgiza kai tace.
"Kai ciwon k'irji,Hidaya ciwon k'irji,to me yake faruwa haka..!?
Ya d'ago kan sa da sauri ya kalli Umma,ganin kallon da take masa yayi saurin sunkuyar da kansa k'asa,lumshe idanuwan sa yayi kafin yace.
" Umma ai ni yunk'urin amai ne ya saka k'irjina ciwo,ita kuma ai kin san ciwon k'irjin ta yana da nasaba da lalurarta,tunda ba yau ta fara yi ba…"
Umma tayi murmushin takaici tace.
"Hamza….!
Ya d'ago kan sa a hankali yana amsawa.
" Na'am Umma na…!
Ta nemi wata kujera da ke gefe ta zauna,sannan ta maida hankalin ta kansa tana duban sa ta fara magana.
"Jiya lafiyar Allah ka d'auki Hidaya kuka tafi Abuja tare,a maimakon naga kun dawo cikin murna da farinciki sai naga akasin hakan,kun dawo cikin damuwa,Hamza jiya Hidaya bata yi bacci ba,kwana tayi tana kuka,kaima kuma naga alamun baka yi baccin ba,domin ko sallar asuba baka fita ba,ina son sanin meke faruwa,na tambayi Hidaya ta k'i sanar da ni komai sai kuka,tilas kai ka sanar da ni,idan ba haka ba ranka zaiyi mummunan b'aci,me kayi wa Hidaya…!?shin ko ka cutar da marainiyar Allah ne…!?
A rikice Hamza ya d'ago kansa jin maganar Umma,kawai sai ya zame k'asa ya rarrafo gabanta ya kama hannuwan ta ya rik'e,idanuwan sa a kan ta cike da rauni ya fara magana.
" Umma ai kin fi kowa sanin halina tunda ke kika haifeni,kin sani a duniya babu wani da zai cuci Hidaya ina kallo na barshi,balle ni na cuceta,wallahi Umma da ina da hali ko sauro ba zan bari ya ciji Hidaya ba,ni d'in GARKUWAR HIDAYA NE kin sani…
Idanuwanta a kansa tace.
"Eh na sani,to amma ina son sanin menene mak'asudin kukan ta..?menene ya sakata cikin wannan halin..!?
Ya runtse idanu,sai yaga gara ya fad'awa Umma gaskiya kawai,shiyasa yayi k'asa da kai yayi magana cikin rawar murya.
" Mun fara kewar rabuwa da juna ne Umma,saboda a jiya da muka je Abuja Khaleel ya bayyana wa Hidaya cewar Yana son ta,yana son ya aureta..shine abin da ya saka ta…..
Ya kasa k'arasawa saboda yadda yaga Umma ta zabura kamar wadda taga abin tsoro,ta k'ura masa idanu cikin fitar hayyaci da gigicewa tace.
"So kuma?Ibraheem d'in ne ke son Hidaya?to kai kuma fa?ya za ka yi da son da kake mata?
Ta jero masa tambayoyi a hargitse,ya sunkuyar da kai yana k'ok'arin maida hawayen sa da ke son fitowa,ya girgiza kai yace.
" Ai ni Umma ban tab'a furtawa cewar ina sonta da Aure ba,ban ji hakan a zuciya ta ba,Hidaya matsayin k'anwata na d'auke ta"
Cikin fushi da k'unan rai Umma tace.
"Ni za ka yi wa k'arya Hamza….!?
Yayi saurin girgiza kai yana rik'o hannun ta,a kid'ime yace.
" ah ah,kiyi hak'uri Umma"
Ta fizge hannun ta ta mik'e tsaye tana kallon sa fuska babu walwala tace.
"Kai zan bawa hak'uri Hamza,domin ka tafka kuskuren da za ka yi danasani,kana son Abu ka kasa yardarwa kanka hakan,har ka bari wani ya rigaka furtawa, wanin ma Wanda ba za ka iya hanashi komai ba,kowa ya kalleka ya san kana son Hidaya,haka duk Wanda ya dubi yarinyar nan ya san tana sonka,amma shine kake son cutar da zukatanku,shikenan aikin gama ya gama,domin ko ni ba zan iya hana Khaleel Hidaya ba,domin bani da hujjar hakan,duk wasu Abubuwa da na dinga yi a kwanakin nan domin ku nake,ina so ne ku bayyana wa juna kuna son junan ku,a maimakon hakan sai kuka juya baya,kuka yi nauyin baki,musamman kai da ka kasance namiji,kai ne mai laifin Hamza,ina cike da bak'incikin ba kai za ka auri Hidaya ba,domin a yanzu bani da wani buri da ya wuce hakan, kai ne kafi kowa sanin Hidaya,kai ne ka raineta,kai ka san halayen ta,Hidaya tarbiyyarka ce,kai mahaifiyarta ta dank'awa amanar ta,kai ne Wanda baka gajiyawa da ita idan lalurarta ta tashi,kai ne Wanda za ka iya yarda ka rasa komai Dan ka tallafi rayuwar Hidaya,Hidayan da bata da kowa sai kai sai ni,kai ne Wanda za ka zauna da ita ba tare da ka yi mata gorin wani abin ba,me ya sa hankalin ka ya gushe har ka kasa gane hakan Hamza,wane namiji ne kake tunanin zai iya yiwa Hidaya duk wad'annan abubuwan da na lissafa?Na yarda Ibraheem mutumin kirki ne, mai imani da tausayi ne,amma Mahaifin sa kuma fa?kana tunanin Hidaya ba za ta samu k'alubale da shi ba?ko dangin sa?ka dawo cikin hankalin ka Hamza…lallai ka tafka babban kuskure Wanda ba zai gyaru ba….
Kawai sai Hamza ya fashe da kuka,maganganun Umma sun k'ara d'aga masa hankali,wata gingimemiyar soyayyar Hidaya ta taso masa,k'ok'arin dannewa yake amma ya kasa,ya matsa ya rungume k'afafun Umma yana wani irin kuka na tashin hankali,cikin wata irin murya yace…
"Umma na k'addara ce,Umma na jarrabawa ce,Na shiga uku ya zan yi….!?
Hawaye ya ratso ta idanuwan Umma,wani mugun tausayin Hamza ya rufe ta ganin yadda maganganun ta suka rud'a shi,ita kuma ta yi su ne domin ya gane kuskuren da ya tafka,ba wai don ta tayar masa da hankali ba,duk da ta san haka Allah ya k'addara,komai nufi ne na Allah,amma tabbas da sakacin Hamza,kenan akwai yiwuwar ta zauna ta taushi Zuciyar sa saboda kada dukan yayi masa yawa..
Zama tayi a in da ta tashi,ta rik'o hannuwan sa ta na duban yadda yake kuka da hawaye sosai,sai ta dafa kansa ta sanyaya murya tace.
" Tabbas k'addara da jarrabawa sun same ka Hamza,to amma ina son sake tuna maka cewa,shi Allah mai buwaya da d'aukaka,mai hikima ne cikin jarrabarsa ga bayin sa,da abin da yake jarrabar su da shi.Ya kan jarrabi bayin sa wani lokaci da abin farinciki,wani lokacin kuwa da tsanani,duk wannan jarrabawar da gwadawar domin ya bayyana godiyar mai godiya da hak'urin mai hak'uri ne.Allah mai girma da d'aukaka yana cewa.
"و لنبلونکم حتیٰ نعلم المجھدین منکم والصبرین و نبلوا أخبارکم"
Ma'ana (Kuma wallahi za mu jarrabe ku don mu san masu jihadi daga cikinku,da masu hak'uri,kuma don mu jarrabar hak'ik'anin lamarinku).
Ni yanzu babu abin da zan hore ka da shi sai hak'uri,ka yi hak'uri Hamza, kuma ka ambaci "Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un" saboda masifar da ta sameka,domin Allah ya ce Annabi (S A W)yayi wa masu hak'uri bushara,cikin suratul bak'ara….
"وبشر الصٰبرین،الذین إذا أصٰبتھم مصیبة قالوا إنا للہ و إنا إلیہ ر ٰجعون،أولٸک علیھم صلو ٰت من ربھم ورحمہ،و أولٸک ھم المھتدون"
(Kuma ka yi wa masu hak'uri bushara.wad'anda idan masifa ta same su sai su ce.daga Allah muke,kuma zuwa gare shi muke komawa.Wad'annan suna da tsoran daga ubangijinsu da rahama,kuma wad'annan sune shiryayyu).
Ka yi hak'uri Hamza, sannan ka ambaci wannan ayar,Allah zai sauk'ak'a maka,sannan ya mu sanya maka da mafi alkairi a rayuwar ka….
Sai Hamza ya matsa ya kwantar da kansa a kan cinyar Umman sa, hawayen sa na sauka suna jik'a jikinta,da wata irin murya yake ta nanata "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dinga fad'arta sau ba adadi yana kuka,yayin da Umma take shafa kansa ta na hawayen tausayin sa……!
Comments
Share
Vote
Pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.