Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 39 of 50

BABI NA SABA'IN DA BAKWAI DA NA SABA'IN DA TAKWAS

***Da k'yar Mummy ta iya d'ago kan Hidaya daga k'irjinta,ta tsura mata idanu tana kallon yadda hawaye yayi mata kaca kaca a fuskarta,hannu ta kai tana share mata,a yayin da wasu suke sake b'ullowa kamar ana tunkud'o su,girgiza mata kai Mummy tayi tana mayar da nata hawayen da ke k'ok'arin sake zubowa,Hidaya ta kasa jurewa,ta sake afkawa k'irjin mahaifiyarta tana sake k'ank'ameta kamar za ta gudu,wani irin dad'i mara misali na kwarara a ruhinta,wai yau ita ce rungume jikin Mummyn ta,me yafi wannan dad'i a duniyarta?

Da k'yar Mummy ta iya janye Hidayan suka zauna bakin gado,amma duk da hakan Hidayan tana manne da ita,sai faman kallonta take tana rik'e mata hannu da kwanciya kan kafad'arta,murna duk ta ishe ta,sai can ta waiwaya tana duban Hamza da ke k'ok'arin bud'e k'ofa ya fita daga d'akin,a hankali cikin dasasshiyar murya Hidaya ta ambaci sunan sa,tasayawa yayi cak sannan ya waiwayo suna duban juna,da sauri ya kawar da kai saboda baya son kallonta sosai,a hankali tayi magana tana murmushi.

"Ya Hamza kaga Mummy na ta zo ....yau ta tuna dani ta zo gareni"

Shi ma murmushin yayi wanda ya k'ara masa kyau,sannan ya mayar mata da amsar maganarta.

"Na ganta Hidaya,har ma na riga ki ganinta fa,kuma ina tayaki murna"

Sakin hannun Mummy tayi,sannan ta taso a hankali ta nufo in da yake tsaye,tana zuwa gabansa ta tsaya tana kallonsa,d'ago kansa yayi ya dubeta,hawaye ya gani sun cicciko idanuwanta,cikin wata irin murya ta karya wuya ta fara magana.

"Ya Hamza ai na sani...wallahi na san babu wanda zai taya ni murna a duniya sama da kai...Ya Hamza ka fad'awa kowa...ka fad'a da babbar murya cewar Mummyn Hidaya ta bayyana...ina so kowa ya tayani murna...murnar saduwa da Mahaifiyata...Ya Hamza har Uncle Khaleel ina so ka fad'a masa domin ya tayani murna....!"

A hanzarce ya zuba mata idanu jin ta ambaci sunan Khaleel,da mugun mamaki yake kallonta,sai yaga ta girgiza kai hawaye ya sake zubo mata,ta saka bayan hannunta ta share,sannan ta cigaba da magana cikin raunin murya.

"Ka yi mamaki da na ambaci Uncle Khaleel ko?ai ba zan tab'a fushi da shi ba har na daina numfashi,saboda shi GARKUWA ta biyu ne a gareni,kaje wajensa ka fad'a masa cewar yau Mahaifiyata ta bayyana,kuma na yafe masa duk abin da yayi min,ba ma shi kad'ai ba,duk wanda ya san ya tab'a yi min wani abu mara dad'i ,ko na zalunci,ko na ha'inci,ko ya zage ni ,ko ya aibatani,a yau duk su sani na yafe musu,darajar Mahaifiyata,mutum d'aya ne ba zan iya yafe masa ba a duniya wato DADDY"

Tana fad'in hakan ta juya,ta bar Hamza tsaye yana binta da idanu,kafin ya lumshe idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya.

****************

Sai a washe garin ranar sannan Khaleel ya fara dawowa hayyacinsa sosai,idan ka ganshi ba zaka shaida shi ba saboda tsananin ramar da yayi,tunda ya dawo hankalinsa kuma bashi da aikin komai sai kuka da zubar hawaye,Aunty Kubra tana iya k'ok'arinta wajen lallashi da yi masa nasiha akan hak'uri amma ya gaza,sosai zuciyarsa ta tab'u akan abin da ya faru,bashi da wani buri a yanzu illa ganin Hamza da Hidaya,to amma da wane idanuwan zai dube su?

Bud'e k'ofar d'akin akayi,Daddy ne ya shigo jikinsa a salub'e yana tafiya da k'yar,bayan sa Alhaji Maude ne rik'e da ledoji ya zo duba Khaleel,Khaleel na ganinsu yayi maza ya juya musu baya hawaye na zubo masa,baya son ko kallon Daddyn sa kwata kwata,a lokacin ne Aunty Kubra ta bud'e k'ofar toilet d'in d'akin ta fito,ita ma kanta ganin Alhaji Maude sai da taji ba dad'i a ranta,ta tsani mutumin k'warai da gaske,anan ta tarar Daddyn sai magana yake wa Khaleel amma yayi banza da shi yak'i juyowa ya dube shi sai kuka yake yi,matsawa tayi sosai tana lek'a fuskar Khaleel d'in,cikin tausayi ta girgiza masa kai tayi magana.

"Khaleel wannan ba d'abiarka ba ce,kana ji mahaifinka na magana kana share shi?tare da abokinsa yake fa,me yasa hakan?"

Cikin kuka Khaleel yayi magana da k'yara.

"Bana son ganinsa Aunty...Don Allah ki ce ya fita daga d'akin nan...zuciyata za ta buga idan ina kallonsa"

A gigice Daddy ya dubi Aunty suka had'a idanu,cikin fushi Aunty ta juya tana duban Khaleel zata yi magana,da hanzari Daddy ya dakatar da ita,sannan ya sunkuyar da kai jiki a sanyaye,muryar sa na rawa ya dubi Khaleel ya ce.

"Shikenan zan tafi Khaleel tunda baka son ganina,kayi hak'uri"

Yana fad'in hakan ya juya yana kallon Alhaji maude,cikin sanyin murya yace masa.

"Mu je Alhaji Maude"

Alhaji Maude ya dire kayan hannunsa,sannan ya juya yayi gaba zuciyarsa k'al da tsananin murna,Daddy ya biyo shi jiki a sanyaye,yana tafe yana waiwayen Khaleel da ke ta faman kuka,hawaye ya cicciko idanuwan sa,da hanzari ya fice daga d'akin yana goge idanuwan sa da gefen babbar rigar jikinsa,ya bar Aunty Kubra da binsa da kallo bakinta a sake.

Yana ficewa Aunty Kubra ta mayar da kallonta kan Khaleel,cikin b'acin rai ta ce da shi.

"Amma ka bani mamaki Khaleel,wannan wane irin tozarci ne kai wa mahaifinka haka a gaban abokinsa?me yayi maka da ya cancanci irin wannan sakayyar Khaleel?Mahaifinka ne fa da yayi silar zuwanka duniya"

Da k'yar Khaleel ya iya k'arfin halin mik'ewa zaune,hawaye na zuba a idanuwansa,kallon Aunty yayi da ta zuba masa idanu tana kallonsa,sai ya sunkuyar da kai ya fara magana a hankali cikin rauni.

"Da gaske bana son ganinsa Aunty,kuma nayi hakan ne saboda gudun fad'awa halaka,domin muddin idanuwa na za su dinga ganinsa zan iya yin wani abu wanda ya sab'awa Allah Aunty"

Aunty ta nemi kujerar gefen gadon ta zauna tana fuskantarsa,idanuwanta cike da tsananin mamaki take duban Khaleel,kafin ta girgiza kai tayi k'arfin halin yin magana.

"Me yake faruwa ne Khaleel?Na kasa gane kan abubuwan da suke faruwa tun daga jiya zuwa yau,me ya faru da kai ne a jiyan?kuma ina matarka take?

Runtse idanuwa Khaleel yayi da k'arfi kafin ya sake fashewa da wani irin kuka me cin zuciya,cikin wata irin murya yace wa Aunty Kubra.

"Aunty na sake ta,wai na sake ta da bakina,wai nine na saki matata Hidaya har saki uku kwana d'aya da auren mu"

A zabure Aunty Kubra ta mik'e tana salati,maimaita salati take da innalillahi bakinta na karkarwa,duk ta gigice tana jin maganar na mata kuwwa a kunne,Khaleel ya bud'e idanuwan sa hawaye na zuba kamar famfo,ya cigaba da kallon Aunty Kubra,ya kai hannunsa ya dafe k'irjinsa saboda yadda yaji ya motsa masa da azabar ciwo.

"Aunty hak'ik'a naci amanar Aboki da Hidaya,na d'aukar masa alk'awarin zan rik'e masa ita amana,zan zama GARKUWARTA,amma na gaza hakan tun ba a je ko'ina ba,Aunty jiya da hannuna na dinga dukan Hidaya ina marinta,banji tausayinta ba,ban duba rauninta ba,ban duba lalurarta ba,ban fasa dukanta ba har aboki ya shigo ya ganni,Kuma a gaban idanuwan sa nayi wurgi da ita ina ambata mata saki" yana zuwa nan ya sake rushewa da kuka.

Aunty ta kuma saka salati hawaye na cicciko idanuwan ta,jikinta babu in da baya rawa,a hankali ta kuma neman waje ta zauna jin tana shirin fad'uwa k'asa,cikin gigita ta sake duban Khaleel tayi magana a rud'e.

"Saki uku fa naji ka ambata Khaleel...me tayi maka haka..?me ya jawo hakan ?

Cikin kuka ya ce.

"Daddy ne Aunty...Daddy ne ya janyo komai"

Aunty ta sake rikicewa,hannayenta dafa da kuncin ta ta ce.

"Bangane ba Khaleel,ban fahimta ba,kamar ya ya Daddyn ka shi ya janyo komai?shine ya saka ka sake ta?"

Khaleel yayi shiru ya kasa magana ya cigaba da kuka,idanuwan sa har wani janyewa suke tsabar bala'in kukan da yake yi,mugun tausayin sa ya cigaba da ratsa zuciyar Aunty,tana jin kukansa da damuwarsa na tab'a ruhinta,a hankali ta sassauta murya ta dube shi ta ce.

"Khaleel ka daina wannan kukan don Allah,wallahi ba k'aramin d'aga min hankali yake ba,yadda zanji damuwar Sameer da Sameera a raina kaima haka nake jin taka,domin duk d'aya na d'auke ku kamar yadda ka d'aukeni a matsayin mahaifiya,ka bud'e bakinka ka fad'a min abin da ya faru har ya janyo saki tsakaninka da matarka kwana d'al tal da aure,kuma sakin ma irinna bidi'a mara kyau Khaleel,wanda ko Allah shine ya halatta shi amma baya son sa,ni ban san abin da ya faru ba tun jiyan,amma zuciyata tuni take fad'a min wani abu mara dad'i ya faru,duk da ban za ci girmansa ya kai haka ba,bayan kun fito da Daddyn ka da kaje gaishe shi da safe,baku jima sosai ba ya dawo min a firgice wai na zo na tayashi lallashinka yayi maka laifi,shine ka shige d'aki ka kulle kanka,da muka zo shine muka ganka cikin mawuyacin hali kana aman jini har ka fita daga hayyacinka,shine muka rud'e muka kwasoka zuwa asibiti,ni gabad'aya ma na manta da zancen matarka sai da komai ya fara lafawa sannan na tuna,shine na tambayi Daddyn ka ita,shi kuma yak'i cemin komai akanta har zuwa yanzu,don Allah Khaleel ka fad'a min,shin mahaifinka ne ya umarceka da ka saki Hidaya ko kuwa?domin zuciyata ta fara zargin hakan saboda wasu abubuwa da suka faru tun kafin a d'aura auren ku"

Khaleel ya d'ago kansa ya dubi Aunty,yayi wata irin ajiyar zuciya,Numfashi na masa wahalar shak'a,a haka ya daure ya fara magana yana kallon Aunty Kubra,wadda ta zuba masa idanu kamar ta cinye shi saboda k'aguwar jin maganar da zai fad'a.

"Aunty na rantse miki da Allah ban tab'a ganin bak'ar rana irin jiya ba,ranar da tazo da abubuwa na tarin bak'inciki a gareni da sauyin rayuwa,kin sani Aunty ina tsananin yiwa mahaifina biyayya tun ina yaro,komai ya umarceni ina aikatawa ko da ni bana son abun,ba kuma komai ke sa hakan ba sai yawan Nasihar da Abokina Hamza yake min akan girmama iyaye da fifita buk'atarsu akan ta kowa,matuk'ar bata sab'awa Allah da manzonsa ba,Hamza ne kullum yake k'ara cusa min k'aunar Mahaifina da kare masa mutuncinsa,dalilin da yasa kenan jiyan na aikata abin da ban ma san nayi ba,na saki matata wadda nake tsananin so da k'auna,saboda ta zagi mahaifina a gabana,ta ci mutuncinsa ta tozarta shi,shine na zame masa GARKUWA,na kare shi na kare masa martaba da mutuncin,nayi abu cikin rashin sani wanda yafi dare duhu,domin ban sani ba ashe Hidaya tana da dalilinta na aikata hakan ga mahaifina,dalili kuwa mai k'arfi wanda nake bak'incikin sanar miki da shi a halin yanzu"

Yayi shiru yana maida numfashi yana jin kamar ya mace a wajen dan bak'inciki da k'uncin da yake ji ya dabaibaye ruhinsa,Aunty ta tsura masa idanu cikin numfarfashi da dukan zuciya tana shirin jin dalilin da yasa Hidaya ta aikata hakan akan Daddy,wanda ya janyo mata saki uku kwana d'aya rak da d'aura auren ta.

Runtse idanuwa Khaleel yayi hawaye ya gangaro da gudu,yana shesshek'ar kuka ya cigaba da magana.

"Aunty....Aunty...Aunty ashe Daddy ne ya kashe mahaifin Hidaya...ashe Daddy ne ya zama silar barin Mahaifinta duniya....shine ya zama ajalinsa...shine ya kashe mata ubanta mahaifi....Daddy ne....Daddy ne Aunty....!

Sai ga Aunty rigijib ta fad'o daga kan kujerar da take zaune tsabar tsoratar da tayi,hannuwanta akan ta ta saka saka salati da k'arfin gaske,wani mugun kuka ya kufce mata tana ambatar "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ita kuka ,Khaleel Kuka, har kukan Khaleel ya fara yawa ya fara wani irin tari da shak'uwa kamar zai mace.

******************

Tana kwance lamo akan gadon Umma,ba bacci take ba illa tunanin da ya addabi ruhinta,tunani guda biyu,tun bayan dawowarsu daga asibiti take son su zauna ita da Mummyn ta suyi maganganu a tsakanin su,amma hakan ya gagara,gabad'aya Mummyn tak'i ce mata komai,sai dai taji suna ta hirarsu da Umma da Aunty Sajida,sai kuma tunanin Uncle Khaleel da ya addabi ruhinta,da ta runtse idanuwanta shi take gani,ko bacci take mafarkinsa take,kewarsa take ji sosai a ranta,idan ta tuna soyayyar da ya nuna mata daren da aka kaita gidansa har wani hawaye take yi,so take ta ganshi duk da akwai katanga tsakaninta da shi,tana jin k'iyayyar mahaifinsa amma shi tausayi da soyayyarsa ne suka sami matsuguni a ranta,ta san k'ila yana cikin wani hali,ina ma za ta ganshi,ina ma za su yi ido biyu da juna,wallahi da ta furta masa kalmar yafiya da afuwa,domin ta san yana can yana zargin kansa da cutar ta ,da cin amanar ta,yana can yana tuhumar kansa da kasa zame mata GARKUWA kamar yadda ya so,bata tab'a sanin akwai wata soyayya mai zak'i da dad'i a filin duniya kamar wadda Khaleel ya nuna mata ba,sai gashi Soyayyar ta katse a dai dai lokacin da take cikin tsananin buk'atar ta,ita kuma k'addararta kenan! karb'ar tikitin saki uku kwana d'aya tal da zamantowar ta matar aure,shikenan yanzu sai dai a kirata BAZAWARA,kalmar da ko a baki bata da dad'in fad'a,to amma ya zata yi da hukuncin ubangiji?wanda shine mai tsara komai yadda yake so akan wanda yake so kuma,a maimakon ta dinga jin zafin Khaleel a ranta,sai aka samu akasi take jin wata irin soyayyar sa a ranta wadda bata tab'a ji ba,da yawan mutane ta kanji suna cewa "idan namiji ya saki mace,to dukkansu sukan samu kansu cikin nadama da tsananin son juna,musamman wanda saki uku ya shiga tsakani" ashe kuwa hakane! tunda gashi tana jin hakan a filin zuciyar ta,idanuwan ta na mararin ganin Uncle Khaleel ! kunnuwanta na son jin muryarsa da dad'ad'an kalamansa ! hancinta na d'okin jin k'amshin jikinsa ! ilahirin jikinta na buk'atar Uncle Khaleel gabad'aya...!

Lokaci d'aya ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ! ta wawuri pillow ta matse a k'irjinta gam hawaye na sharara da gudu,kuka take haik'an tana furta wasu irin maganganu cikin gushewar hankali da k'wak'walwa.

"Me ya sa ka guje ni Mijinahhhh...?me yasa ka tafi ka barni lokacin da nake buk'atar ka...? me yasa ka nisanceni bayan na mallaka maka komai...?har ma ka cinye komai...! Don Allah Allah da manzon sa Uncle Khaleel...Don Alk'awarin da kayi min na zamo wa GARKUWATA ka zo gareni....! ka zo na ganka Uncle Khaleel....wallahi INA TSANANIN SONKA"

Kalamanta suka sauka a kunnuwan Ya Hamza ! wanda ya shigo da nufin bata magungunanta domin ta sha,domin sai ya sakata a gaba sannan take sha,wani irin bugawa k'irjinsa yayi da k'arfi,kukan da take yi cikin rauni da kalaman da take furtawa sunyi matuk'ar sanyaya jikinsa,hajijiya ya ji tana kwasar sa kamar ya fad'i,a hankali ya dafa bango yana ambatar"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" a zuciyar sa.

*Idan bakwa comeents zan ajiye alk'alamina,bana jin dad'i ma amma hakan nake daurewa in muku saboda yadda kuke son littafin,amma sharhi ya dinga gagararku haba*🙄🙄🙄

Comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.