Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 50

*BABI NA ASHIRIN DA UKU DA NA ASHIRIN DA HUD'U*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

Yana daga kwancen ya D'an waiwayo da kansa yana duban ta,ga mamakin sa sai ita ma yaga hawayen a idanuwanta suna shirin zubowa,ya yunk'ura ya mik'e zaune bakinsa d'auke da salatin Annabi,ya kai Hannu ya murje ragowar hawayen da ke fuskarsa,sannan ya dubeta da D'an murmushi yace.

"Ya dai Hidaya?

Ta kai Hannu ita ma ta goge na ta hawayen,ta turo baki gaba tace.

" Me ya sa ka ke kuka?"

Ya girgiza kai.

"Babu komai Hidaya,kawai na tuna wani abokina ne da yayi tafiya mai nisa,shine kewarsa ta saka ni Hawaye"

Ta rik'o hannun sa tana wasa da yatsun sa,ta kalle shi tace.

"Amma zai dawo ko Ya Hamza"

Ya jijjiga kai alamar eh,sannan ya zarce da cewa.

"Amma dai zai jima bai dawo ba,gashi bani da wani Aboki sama da shi,shi kad'ai me babban Aboki na"

Ta d'an yi dariya kad'an ta zura masa idanu tace.

"To ba gani ba Ya Hamza,tunda baya nan ai ni sai na zama k'awarka kawai"

Yayi murmushi yace.

"Hidaya kenan!ai babu abota ko k'awance tsakanin Namiji da mace,ai ni yayanki ne ke kuma k'anwata ce ko?"

Ta jijjiga tana kallon sa tace.

"Eh kuwa, shiyasama zan dinga ce maka Ya Hamza,shi kuma Abokin ka ya sunan sa?"

Kai tsaye ya amsa mata da cewa, "Khaleel".

Tayi tsalle tana cewa.

" Ya Hamza zan dinga kiransa Uncle Khaleel ka ji,Mummy na tace idan mutum ya girme ni na dinga ce masa Yaya ko Uncle, idan mace ce kuma Anty ko Adda"

Ya zame hannun sa cikin na Hidaya yana amsawa da.

"Hakan na da kyau yarinyar kirki,ke kuma k'awayen ki guda nawa ne?"

Ta d'aga kanta sama kamar tana tunani har da sa d'an yatsanta a hab'ar ta,ya bita da kallo cike da birgewa,sai can ta sauke kallonta kan fuskar sa ta kamo yatsun ta ta na k'irgawa da su,har ta k'irga guda uku,cikin murmushi tace.

"Ka ga k'awayena haka ne Ya Hamza,Amma na yi fad'a da guda biyu,saura d'aya nake kulawa?"

Ya d'an zaro ido yace.

"Fad'a kuma?Ashe k'anwar ta wa mafad'aciya ce kenan?me yasa kika yi fad'a da su?"

Ta b'ata fuska saboda tuno abin da suke mata tace.

"To Ya Hamza ba su bane sai su yi ta tsokana ta wai k'ashi da rai,ko su ce min k'anjamammiya me ciwon sikila,ko su ce min me idon mage"

Tausayin ta ya kamashi,ta tab'e fuska kamar za ta yi kuma,nan da nan ya fara lallashin ta da cewa.

"Rabu da su kinji my k'anwa,Ai Allah ne ya jarrabeki kuma zai yaye miki tare da duk wani mai ciwon,kuma ke ba k'anjamammiya bace,za ki yi k'iba nan gaba kad'an insha Allah"

Ta saki fuska sosai sannan ta dubeshi tace.

"Kuma idan suka sake tsokana ta za ka rama min ko?za ka doke su ko?"

Ya gyad'a kai yana murmushi yace.

"K'warai kuwa,insha Allah zan zama GARKUWAR ki,babu Wanda zan bari ya tab'a ki Hidaya"

Tayi wani irin tsalle da juyi na murna,bai aune ba yaji ta fad'o kansa tana tuntsira dariyar murna,shi ma sai ya samu kansa da dariyar,da k'yar ya b'anb'areta a jikinsa,sannan ya zaunar da ita kusa da shi suka cigaba da hirar su cikin farinciki.

Umma dai ta ji su shiru ba su tawo ba,amma tana jiyo hayaniyar su musamman Hidaya da take ta zuba masa hira kala kala da zance,shi ba gwanin magana ba ma amma haka ya daure ya biye mata,tana ta d'akko Abubuwa a d'akin tana masa tambaya a kai,shi kuma bai k'osa ba yana ta bata amsa da kulawa.

Sai da Umma ta k'wala masa kira sannan ya mik'e yana amsawa yayi hanyar fita,Hidaya ta cillar da tsintsiyar da ta d'auka wai za ta yi shara,ta bishi a baya da gudu har ta cimmasa ta rik'o hannun sa suka jera har gaban Umma da ke ktcheen ta kammala had'a break fast, ya d'an Sosa k'eya yana murmushi yace.

"Ayya Umma na kiyi hak'uri ban zo na tayaki aiki ba yau"

Tayi murmushi tana rufe flask d'in tea tace.

"Ina za ka tuna dani ka samu Hidaya?ai tun d'azu ina ta jiyo shewar ku,Aiken ta na yi fa tayi kiranka kuzo ku karya shine ta shantake a can"

Ya mik'a Hannu ya karb'i flask d'in,Hidaya kuma ta d'auki wani tire da aka jera cups guda uku a kai,Umma tana cewa "Ajiye Hidaya ba za ki iya ba" ita kuma Hidaya na cewa"Allah zan iya Umma,ni fa ina da k'arfi sosai"

Umma tayi dariya a ranta tana cewa.

"A wannan Lange langen jikin na ki ina wani k'arfi?"

A parlour suka baje suna karyawa su Uku,Hidaya na ta wasanni ta k'i maida hankali kan cin abinci,Hamza ta na fama da ita dai Umma na tayashi har suka Kammala,shi da Hidaya suka kwashe kayan suka fita da su,Hidaya tace alambur ita za ta yi wanke wanken cups da spoon d'in da suka b'ata,Dan kar tayi rigima Umma ta k'yaleta,ta had'a mata Ruwan kumfa ta barta a tsakar gidan ta dawo parlour gun Hamza.

Zaune ta tarar da shi yana danne danne da wayar sa,ta zauna ta dubeshi cikin kulawa tace.

"Ya kamata ka tashi kayi shirin da za ka yi,nima a shirye nake,domin mu wuce mu mik'a yarinyar nan yanzu ko?"

Da wani irin hanzari ya d'ago ya kalli Umma,fuskarsa cike da tashin hankali mara misali,ganin yadda Umma ta zubo masa idanu shiyasa yayi saurin waskewa ya sunkuyar da kai,a hankali yace.

"To Umma,bari na d'auko takardar da za mu kaita da ita,tana cikin aljihun wando na na ranar da na saka,tare da envelop d'in da mummyn Hidayan ta bani akan na ajiyewa Hidaya sai ta girma sai na bata"

A hankali ya mik'e,jikin sa a sanyaye ya fito daga parlour 'n,Umma ta bishi da kallo tana girgiza kai cike da damuwar rabuwa da Hidaya.

Hidaya na kallon fitowar sa ta fara d'aga Hannu tana yi masa magana.

"Ya Hamza zo ka tayani wanke wanke,sai kayi min d'auraya ko?"

Ya tsaya cak! ya waiwayo yana dubanta cikin wani yanayi,duk ta jik'a jikinta da ruwa,kumfar omo kuwa har a fuskarta tayi faca faca,ya k'ura mata idanu sosai,wata kewa ta mamaye ruhinsa,yaji tamkar ya rusa ihu,Hawaye ya ciko idanuwan sa,da sassarfa ya juya da hanzari ya wuce d'akin sa ko gabansa baya iya gani.

**************

Yana shiga d'akin sa ya kife kansa a bango yana sakin numfashi, idanuwan sa a runtse k'irjinsa na zafi sosai,ya rasa dalilin da ya sa yake jin wani matsanancin ciwon tafiyar Hidaya,bai santa ba !bai sa ba da ita ba!rana d'aya ta shigo rayuwar sa tana son hargitsa masa lissafi!Yarinya k'arama da ita!kuma ya san matsanancin tausayin ta ke d'awainiya da shi! Ya sake lumshe idanuwan sa hawaye na taruwa,a hankali bakinsa ya motsa yana addu'a domin nemawa kansa sauk'in da yake ji a fad'in k'irjinsa,domin ya tabbatar Allah ba ya nufin bayin sa da tsanani sai sauk'i,kamar yadda ya fad'a a cikin littafinsa mai Girma.

"یرید اللہ بکم الیسر ولا یرید بکم العسر"

(Allah yana nufin sauk'i gare ku,baya nufin tsanani)

Haka nan Annabi(S A W)Yana cewa sahabbansa:"Ku sassauta kada ku tsananta,kuyi bushara kada ku Kore" Bukari da Muslim ne suka rawaito shi.

Yana tuna hakan ya sauke numfashi da k'arfi,ya cigaba da addu'a sosai,sai yaji k'uncin Zuciyar sa ya fara yaye wa,musamman da ya tuna cewa,Allah yana sane da Hidaya,domin shine mahaliccinta,shine mai zab'a mata rayuwa a duk in da ya so,haka nan Allah yana jin sa da ganin sa,kuma yana da yak'inin zai amsa masa addu'ar sa wadda yayi Daren jiya,akan Idan zaman Hidaya gidan Marayu alkairi ne Allah ya tabbatar, idan kuma babu alkairi to Allah ya sauya mata da mafi alkairi a rayuwar ta,Ubangiji mabuwayin sarki shi yace mu rok'e shi zai amsa mana mu bayin sa,domin shi makusanci ne a garemu,kuma yana amsa addu'ar duk Wanda ya kira shi .Allah ta'ala yace.

"و إذا سألک عبادی عنی فإنی قریب،أجیب دعوة الداع إذا دعان،فلیستجیبوا لی ولیٶمنوابی لعلھم یرشدون"

(Kuma yayin da bayina suka tambayeka game da ni,to ni makusanci ne,ina amsa addu'a idan ya kirani).

A take yayi Hamdala ga Allah,sannan ya k'ara da salatin Annabi,sai ya ji jikinsa yayi k'wari,Zuciyar sa cike da jarumta,k'afafuwansa da suka yi sanyi suka soma k'arfafa,ya ta ka ya nufi wardrobe d'in sa ya bud'e ya zaro wandon kuftar da ya sa ka jiya da k'addara ta had'ashi da Hidaya,ya zauna a gefen gado ya zira hannuwan sa cikin aljihun wandon da nufin zaro takardar,cikin ikon Allah ya zaro ta ya fito da ita,ga mamakinsa sai yaga iya envelop d'in ce kawai babu takardar da za a kai gidan Marayu, ya ajiye envelop d'in gefen sa ya juya wandon d'aya b'arin yana duba d'aya aljihun,amma sai baiji komai ba,haka yai ta caje aljihun yana zazzagewa amma takarda tace d'aukeni in da ka ganni,ya cika da matsanancin mamaki,saboda shi dai ya san lokacin da Mummyn Hidaya ta ba shi takardun da kansa ya cusasu cikin aljihun sa,to ya akayi yaga d'aya bai ga d'aya ba,wannan takardar kuma ita ce jigon kai Hidaya gidan Marayu, idan babu takardar bai san ya ya zai yi ba,tunda bai san komai ba,bai da masaniya akan abin da ke cikin takardar balle yayi musu bayani da baki,bayani da baki ma ba zai gamsar ba.

Haka ya mik'e yayi ta binciken takardar amma Allah bai sa ya ganta ba,har gwiwar sa ta sare ya fara gajiya,ya zauna bakin gado ya dafe kansa cikin tunanin in da takardar ta yi kamar wata aljana,ya jima a zaune har bai san lokaci na ta tafiya ba,kawai sai jin sallamar Umma yayi a kansa.

Ya d'ago yana amsa wa idanuwan sa sun sauya kala,Umma taji gabanta ya fad'i ganinsa cikin wannan yanayin,da hanzari ta matso ta zauna gefen sa tana kamo hannunsa,cike da kulawa take ambatar.

"Lafiya kuwa Hamza?me ya faru ne tun d'azu ina jiranka?

Bai san lokacin da ya d'ora kansa kan kafad'ar Umman ba,ya saki Numfashi a hankali yayi magana.

" Umma na an samu matsala ne….

Ta d'ago kansa da sauri ta dubeshi,suka had'a idanu,ta ga duk ya wani marairaice,ta k'ura masa ido tace.

"Matsala kuma?wace matsala kenan?"

Ya sunkuyar da kai ya fara magana cikin rauni kamar zai saka kuka.

"Wallahi Umma banga takardar da za a kai Hidaya gidan Marayu da ita ba,tun d'azu nake dubawa amma ban ci nasarar ganinta ba,na rasa in da ta yi,kuma fa a aljihuna na sakata,kuma wallahi Umma ita ce shaidar da za mu kaita da ita,idan babu ba zai yiwu mu kai Hidaya gidan Marayu ba"

Umma na shirin magana suka ji Hidaya a bayansu na ambatar.

"Ya Hamza ni za a kai gidan Marayu?Umma ina ne gidan Marayu kuma …?".

Comment
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.