Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 50
*BABI NA TALATIN DA D'AYA DA NA TALATIN DA BIYU*
WATTPAD:Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke jin muryar Khaleel na Sallama cikin sanyin murya,kasa amsawa yayi saboda hawayen da ya ratso fuskar sa,jikinsa har wata rawa rawa ya fara,daga can b'angaren Khallel yaji Hamza bai amsa masa sallamar sa ba,hakan ya sa yayi magana a hankali cikin k'ank'anuwar murya tamkar ta marasa lafiya.
"Aboki……kana tare da ni…..?
Hamza ya zame ya zauna bakin gado yana numfarfashi,duk da yaji matuk'ar farincikin jin muryar Khaleel amma cike yake da jin haushin k'in Neman sa da yayi,kuma shi ma idan ya nemeshi baya samun sa,da k'yar Hamza ya sauke numfashi yayi magana murya na rawa.
" Khaleel…! fushi nake da kai Khaleel"
Cikin rauni Khaleel yayi saurin tare shi da cewa.
"Bani da lafiya ne Aboki…..Kayi hak'uri..!?
Hamza ya lumshe idanu k'irjinsa na bugawa saboda tunowa da Hidaya da yayi,cikin alamun tausayawa yace.
" Laifinka ya k'aru kenan Khaleel,kayi fushi da ni kak'i fuskanta ta tsawon lokaci,kayi rashin lafiya ta tsawon kwanaki amma baka sanar da ni ba?ko da bana tare da kai ai zan iya yi maka addu'a Khaleel,me yasa hakan?ka san irin tashin hankalin da na shiga kuwa?ka san irin yadda zuciyata tayi rauni akan tunanin halin da kake ciki kuwa?ban ji dad'in abin da kayi min ba ko kad'an Khaleel, zuciyata tana fushi da kai "
Khaleel ya marairaice murya ya fara bayani .
"Tsaya kaji Aboki,wallahi a ranar da muka yi sa'insa ni da kai akan siyen mota,ka san na kashe wayar cike da b'acin rai saboda ka k'i yarda,to bayan na kashe ne naji k'irjina yana zafi sosai saboda b'acin rai,shine fa ciwon Zuciya na ya motsa,sai James ne da muke zaune gida d'aya ya kwashe ni muka tafi Hospital saboda na fara fita hayyacina,kwana na biyu ban san in da kaina yake ba,a lokacin ne aka nemi daddy na a waya aka sanar da shi yazo hankalin sa a tashe,a nan daddy ya nemi sanin abin da ya tayar min da ciwon,shine James yake fad'a masa cewar bai sani ba,shi dai kawai ya ji sanda nake waya,daga nan kuma sai tari na da nishi na ya jiyo,shine ya kawo ni asibiti,a lokacin daddy ya karb'i wayata ya kasheta ma gabad'aya ya b'oyeta,shine dalilin da ko ka kira ba zaka samu ba,kuma da na dawo hayyacina babu yanda banyi da daddy ya bani na kira ka ba amma ya k'i,wai sai na warware gabad'aya,har kuka nayi masa saboda na san na barka cikin damuwa ba ka jin murya ta,amma daddy ya k'i fuskanta ta,yau kwanana goma da fitowa daga Hospital amma daddy bai koma Nigeria ba sai yau,yana tare dani yana lura da ni har na murmure,yau d'in ma Anty Kubra ce ta ishe shi da waya shine ya tafi,shine fa na samu na kira ka yanzu…ka ji abin da ya faru Aboki,don Allah kayi hak'uri…….
Hamza ya sauke nannauyar ajiyar zuciya saboda jin bayanin Khaleel,tausayin sa ya kamashi sosai,wannan ciwo yana wahalar da Khaleel,Allah ya yaye masa,Hamza yayi magana cikin nuna kulawa.
"Ayya Khaleel ban sani ba ne,nayi kiranka sau ba adadi bana samun ka,nayi tunanin ko har yanzu fushi kake dani akan maganar shiyasa kak'i kulani,ni zan baka hak'uri Khaleel tunda b'acin ran da na saka ka a ciki ne har ciwon ka ya tashi….kayi min Afuwa ka yafe min Khaleel"
Khaleel yayi murmushi,ya mak'e wuya kamar yana gaban Hamza,yayi magana cikin shagwab'a.
"Ni ba zan hak'ura ba sai ka yarda da wata magana da zan fad'a maka yanzu…
Da sauri Hamza yace.
" Na amince Khaleel…idan har za ta sa ka yafe min laifina"
Khaleel ya D'an yi tsalle ganin ya ci gari ,yace.
"Maganar siyen mota tilas ka amince da ita,sannan shagon nan na Gidan ku da k'ofar sa ke kallon waje za a zo a gyara shi a zuba kantoci,na saro maka wayoyi na zamani sai ka dinga siyarwa,idan kaje lectures ka dawo sai ka bud'e ka zauna,lokacin da baka nan ka samu yaro ya dinga zauna maka,y'an kud'ad'en da zaka dinga samu za su to she maka wata kafar,bana son zaman ka haka babu sana'ar yi Aboki,wad'annan Abubuwa biyun idan ka amince da su to ni kuma zan yafe maka dalilin su"
Tunda ya fara magana Hamza ke jinjina lamarin ,da ya san abin da zai ce kenan da baiyi alk'awari ba sam,yanzu ya zaiyi kenan?hidimar ta yi yawa,Khaleel baya tausayawa kud'i idan yaso kashewa,ko Dan yaga Allah ya hore masa su?domin ko iya kadarorin da mahaifiyar sa ta mallaka masa kafin ta rasu suna da yawa,har da kamfanoni,bayan ta rasu kuma ya samu gado mai d'umbun yawa…..
Jin Hamza yayi shiru yasa Khaleel ya sake magana.
"Karfa kace min ah ah Aboki,domin kayi alk'awari ya kamata ka cika,Idan kuma kana son kuma b'ata min rai ne na koma gadon Asibiti to shikenan "
Hamza ya sauke ajiyar zuciya, babu abin da yake tsoro irin daddyn Khaleel yaji wannan hidimar da zai masa,tunda ba k'aunar abotar su yake ba,haka nan ga Umma nan a gefe, ita ma ya san ba zata amince ba,hakan yasa yace da Khaleel.
"Ba k'i nayi ba Khaleel, amma Umma bai zata amince ba,hidimar tayi yawa Khaleel…sannan ka tuna daddy ma…
Ya katse shi da sauri.
" Babu abin da zan maka yayi yawa a rayuwa,Hamza baka san yadda kake da k'ima a tare da ni ba ne,ba kuma zaka gane ba,ni dai na san ina sonka Hamza,zuciyata kullum k'ara k'aunarka take,kai Aboki ne nagari,irin Wanda manzon Allah (S A W)ya kwad'aitar da mu akan mu samu,batun Umma ka jingine shi gefe,zan mata bayani da kaina yadda zata fuskanceni…ko ba kai ba ni na riga na saba da kyauta Aboki,in dai ina da shi nafi son nai ta bayarwa,hakan yana sa wa ina jin dad'i idan ina taimakawa Wanda bashi da shi,sannan ka k'yale batun daddy ,ba kud'in sa nake d'iba ina amfani da su ba,nawa ne,halal d'ina ne Aboki,ra'ayin daddy na k'in talakawa daban,ra'ayi na na son taimako daban,shi ma daddyn ina nan ina ta addu'a akan Allah ya shiryar da Zuciyar sa ya gane dai dai"
Hamza yayi shiru har ya kammala jin bayanin Khaleel, sannan yayi magana.
"Duk abin da ka fad'a Hakane Khaleel,na kuma gode da nuna k'auna,yadda kake jina a ranka haka nake jin ka a raina,fiye ma da hakan,na kuma yarda da abin da kake so,sai dai a bisa wani sharad'i guda d'aya"
"Menene sharad'in..?Khaleel ya tambaya.
Hamza yace.
" Na yarda da batun bud'e shago,amma duk ribar da za a dinga samu sai dai mu raba biyu,d'aya taka d'aya tawa,sannan kayan ciki da ka zuba suna nan a matsayin naka ba mallaka ta ba,kawai zan kasance kamar yaron gun mai lura da shi,sannan batun mota ka ajiyeshi gefe,ka sauya min da mashin,ban isa hawa mota yanzu ba,komai da limit d'in sa Khaleel, idan aka ganni da mota yanzu idanu za su yi yawa a kaina,tunda an san talaka ne ni,don Allah ka fahimce ni ka yarda dani da maganata"
Khaleel ya sauke numfashi yace.
"Na ji na amince Aboki tunda haka kake so…
A lokacin Hamza ya d'aga kai ya dubi Agogo,yaga lokaci ya ja sosai, ya san Umma nan can na jiran shi,ga maganin Hidaya da zai siya ya kai,da sauri yace da Khaleel.
" Khaleel muyi sallama haka,Umma na can asibiti ita da Hidaya suna jirana…"bai san lokacin da ya furta hakan ba.
Cikin mamaki Khaleel yace.
"Umma na asibiti?waye ba lafiya?wacece Hidaya Aboki?
Ya jero masa tambayoyi,sai lokacin Hamza ya tuna b'aranb'aramar da yayi,domin kwata kwata Khaleel bai san da maganar Hidaya ba,bai kuma da niyyar fad'a masa a tsukin har sai wani lokaci na daban,amma yanzu tilas ya sanar da shi komai,tunda bakinsa yayi azarb'ab'in furtawa.
Cikin wani irin yanayi Hamza ya fayyacewa Khaleel abubuwan da ya sani game da Hidaya tun daga ranar da ya fara ganinta har yau,da yake Khaleel yana da matuk'ar tausayi sai gashi yana hawayen tausayin Hidaya,ji yake a ransa ina ma yaga Hidayan da idanuwan sa,Aikuwa tilas insha Allah zai taimaki Hidaya,zai tsaya a kan al'amuranta ya zama GARKUWAR ta,zai to she mata duk wata k'ofa da zata wargaza rayuwar ta,haka kawai yaji a ransa yana son Hidaya,duk da bai tab'a ganin ta ba,Lalurar Hidaya ta tab'a ransa,saboda yana ganin yadda masu ciwon sikila suke shan wahala,nan Khaleel ya rok'i Hamza a kan idan yaje asibiti yayi masa flashing,shi kuma zai kira domin su gaisa da Umma,sannan yayi wa Hidaya ya jiki.
A haka suka yi sallama duk zuciyoyin su ba dad'i,sannan Hamza ya mik'e ya fara tattara abubuwan da ya san zai tafi da su asibiti…..
*****************
K'arfe Bakwai da y'an mintuna na safe mota ta sauke shi bakin Asibitin,ya waiwaya yana kallon pharmacy d'in da zai siyi maganin Hidaya,sai ya ganshi a kulle basu bud'e ba,ya fito da ledar da ya zubo kayayyaki da flask d'in Ruwan zafi, sannan ya sallami mai adaidaita sahun,da hanzari ya d'ebi kayan zuwa cikin Asibitin.
Ya tura k'ofar a hankali da sallama, Umma na zaune gefen gadon tana mammatsawa Hidaya k'afafuwanta da suke mata ciwo,Hidayan na kwance hankalin ta a kan k'ofar shigowa,tana ganin Hamza ne ta saki wani k'ayataccen murmushi da ya fito da asalin kyawun fuskar ta,cikin dasasshiyar murya ta marasa lafiya tayi magana tana k'ok'arin mik'ewa zaune.
"Oyoyo Ya Hamza na….."
Wani farinciki ya mamaye ruhin sa ganin Hidaya ta fara warwarewa,da sauri ya k'arasa ya ajiye kayan hannun sa,ya nufi bakin gadon ya sunkuya yana kallonta fuskarsa cike da murmushi yace.
"Sannu K'anwata…ya jikin na ki?
Ta rik'o hannunsa tana Murmushi tace.
" Da sauk'i Ya Hamza,ina ta Neman ka ban ganka ba,Umma tace min kana gida"
Ya amsa yana damk'e siririn hannun ta a na sa hannun.
"Eh ina can tunaninki ya ishe ni,Ashe har kin fara warwarewa?Alhamdulillah Addu'a tayi aiki kenan,to yanzu menene yake miki ciwo?" Ya zarce da tambayarta.
Ta amsa tana D'an yamutsa fuska..
"K'afata ne Ya Hamza,kamar ana tsira min allura,amma yanzu Umma ta na matsa min ina jin dad'i"
Ya girgiza kai cike da tausayi yana jera mata sannu ba adadi,ita kam sai amsawa take tana kallonsa,zuwan sa yanzu taji dad'in ganin sa,tunda ta farka take son ganin sa daman,ita dai tana son Ya Hamzan ta.
Waiwayawa yayi yana duban Umma da ke had'awa Hidaya tea a k'aramin Kofi,sai lokacin ya tuna Ashe bai gaisheta ba,duk hankalin sa ya tafi kan Hidaya,cikin kunya ya soma gaishe ta,ta yi murmushi tana cewa.
"Sai yanzu ka tuna da ni Hamza..?
Ya Sosa k'eya yana sunkuyar da kai,Umma ta cigaba da juya tea d'in yayin da Hidaya ke cewa Hamza ya cigaba da mammatsa mata k'afarta,haka ya zauna a gefenta ya kai Hannu yana mammatsa mata a hankali,sosai take jin dad'in hakan har da lumshe idanuwa.
Umma ce ta taimaka mata ta yi brush,sannan Hamza ya fara bata tea d'in da k'aramin cokali,tana sha tana shagwab'a shi kam sai biye mata yake,wai ita ya tsefe mata kanta sai Umma ta yi mata kitso,kan ya ishe ta haka,da k'yar ya lallab'ata akan ta bari su koma gida tunda yanzu bata da lafiya.
Yana kammala bata yace da Umma bari ya fita ya siyo maganin,ita kam Hidaya saboda son yawo wai zata rakashi,yayi dariya Yana cewa .
" Da wace k'afar za ki rakani?
Umma da yake ta san akwai kud'i a hannun sa sai bata tambaye shi yadda zai siyo maganin ba,kuma bata san maganin Yana da tsada ba,haka ya fita cikin tunanin yadda zai siyi maganin,dubu Ashirin d'in acc d'in sa ba zata isa komai ba,amma ya san Allah ba zai kunyata shi ba,ya rok'eshi ya hore masa,kuma ya san hanyoyin Allah suna da d'umbun yawa.
Babu abin da ya fad'o a ransa irin yayi maza yaje ya saida wayar sa,in yaso ko k'arama sai ya siya,hakan zai sa ya samu kud'in maganin.
Yana fitowa bakin Asibitin ya kalli pharmacy d'in ya ganshi a bud'e sun fito,Yana shirin tsaida mota domin tafiya kasuwar sayar da wayoyi kawai yaji wayar sa ta yi k'ara alamar shigowar sak'o,a hankali ya zaro ta daga aljihun sa ya duba,zaro idanu yayi k'irjinsa na bugawa saboda ganin alert d'in dubu d'ari cas an tura masa cikin acc d'in sa……!
Comments
Share
Vote
Pls
*TYPING*📲
✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR* 👇
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)
*DA KUMA*
GARKUWA BIYU
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.