Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 43 of 50

BABI NA TAMANIN DA BIYAR DA NA TAMANIN DA SHIDA

***Mummy ta cigaba da ba su labari da ce wa.

"Wannan shine gani na na farko ga Alhaji Mudassir,da kuma aminisa mai suna Alhaji Maude,wad'anda dukkansu y'an kwangila ne,kuma sun zo wajen Oga Taufik' ne domin ya bud'a musu hanya,su cigaba da samun kwangilolin da za su samu kud'i sosai.

Zama mai dad'i da armashi ya cigaba da wanzuwa tsakani na da mijina,har zuwa lokacin da Allah ya saukeni lafiya na haifi d'iya ta mace,wato Fad'imatul Hidaya,zan iya ce muku Oga Taufik' ya fimu farinciki da murnar samun wannan haihuwa,shine yayi komai da ake wa mai jego da jaririya,gata dai mun sha shi fiye da in da bakwa zato,kyautattuka kuwa Oga Taufik' yayi mana su har sai da muka gaji da amsa,saboda shi yana da yawan kyauta da sadaka,haka nan duk lokacin da zai fitar da zakka yana yin ta yadda Allah yake so,shiyasa arzik'in sa yake hab'aka kullu yaumin.

Sai da Hidaya tayi wata shida sannan muka san ita sikila ce,wani dare da ta dinga kuka ta hanamu barci,musamman idan na tab'a k'afarta sai ta tsandare da ihu,hankalin mu ya tashi,washe gari kuwa da wurwuri muka nufi asibiti da ita,anan aka yi mata gwaje gwaje,daga baya aka sanar da mu cewar ita d'in sikila ce.

Muka shiga tashin hankali,saboda mun sani lalurar sikila babban ciwo ne mai matuk'ar wahala,amma da muka yi tunani muka ga ai Allah ne mai d'ora cuta kuma shine mai yaye wa,kuma ba kanta farau ba haka nan ba kanta k'arau ba,sai muka fallawa Allah kawai,muka shiga addu'a da nemar mata magani.

Wata rana muna zaune ni da Hidayan,lokacin shekarar ta biyu har da watanni,tuni bakinta ya bud'e ta fara magana,shiyasa na zaunar da ita ina koya mata karatun Suratul Fatihatul kitabi,nan da nan naga tana d'aukewa,hakan ya faranta raina Allah Allah nake Abbanta ya dawo na bashi labarin Hidaya ta iya karatu.

Da ya dawo sai na lura da ba shi da walwala sosai,sai naji hankali na ya tashi,nayi masa dukkan abin da ya kamata nayi masa,abinci ma kad'an ya ci yace min ya k'oshi,na d'auke na mayar ktcheen,ina dawowa sai na tarar suna ta labari shi da Hidaya yana dariya,na zo na zauna gefen su ina kallon sa,sai ya waiwayo ya kalleni da murmushi kan fuskarsa yana d'ora Hidaya kan cinyarsa ya ce da ni.

"Mummyn Hidaya yaushe Hidayana ta fara iya karatu baki min albishir ba?"

Ni ma nayi murmushi na langab'e wuya nace.

"Ina ta so ka dawo na fad'a maka,to kuma na ganka ba yadda na saba ganinka ba shiyasa nayi shiru da bakina dan kar na dame ka"

Ya girgiza kai yace min.

"Ai wannan abun farinciki ne bai kamata ki b'oye min ba,bakiji yanda naji dad'i ba wallahi,ai gobe zanwa Abba albishir cewa amaryarsa ta iya karatun alk'ur'ani"

Nayi dariya kawai,yayin da ya cigaba da kallon Hidaya yana fad'in"Princess d'ina sake karanta min in ji"

Ita kuwa ta tak'ark'are tana karanta masa Fatiha,shi kam yana ta jin dad'i.

Sai dare da muka zo kwanciya nake tambayar sa dalilin canjawar yanayin sa d'azu,da dai kamar ba zai fad'a min ba sai kuma ya janyoni jikinsa sosai yana gyara min kwanciya,sannan yayi ajiyar zuciya ya ce da ni.

"Wato a rayuwa wasu mutanen ba sa tsoron Allah Zainab,ha'inci da son zuciya yayi wa wasu katutu a zuciya,rashin imani ya yawaita,d'azu Abbana ya kirani,da naje sai na iske shi cikin damuwa,shine hankalina ya tashi na tambaye shi damuwarsa,sai yake shaida min cewar akwai aminan sa guda biyu da suke harkar kwangila da su,ina jin ma ai kin san su,wad'anda suka tab'a zuwa nan gidan lokacin kina da cikin Hidaya har kika yi musu girki,to shine fa yake shaida min cewar baya jin dad'in aiki da su,saboda suna da son zuciya,yana nemo musu kwangiloli ya basu saboda ya fisu hanyoyi na samun kwangiloli ko a wajen gwamnati ma,to amma duk lokacin da hakan ya faru ba sa yin aiki da gaskiya,ayyukansu ba sa yin k'arko,su kan fi maida hankali akan abinda za su samu fiye da aikin da za su yi,yace min a kwanakin nan ya sama musu wata kwangila daga gwamnati mai tsoka,duk don ya kyautata musu ya hana kansa ya ba su,kuma ya rok'e su suyi aiki mai nagarta,amma basu yi hakan ba,kwata kwata a kud'in da aka basu ko kaso goma cikin d'ari basu kashe ba,su dai burin su su azurta kan su ba suyi aiki mai kyau ba,Abba yace min hakan sai da ya janyo masa matsaloli daga gwamnati,shine yake neman shawarata akan ko dai ya daina nemo musu kwangiloli ta b'angaren sa,ya barsu su nema da kansu,ni kam take na bashi shawarar cewar hakan ne ya kamata,kawai ya daina nema musu tunda sun cika zuciyarsu da mugunta,kuma yayi musu gargad'i sau ba adadi amma sun k'i dainawa,take Abba ya amince da shawara ta,yace min zai kira su gobe ya fad'a musu abin da ya yanke a kansu"

"To kinji dalilin b'acin raina har na dawo gida,saboda ni bana son huld'a da irin wad'annan mutanen da basu san kowa ba sai kansu,gara Abba ya fita sabgarsu saboda kar su dinga janyo masa zargi da b'atanci gun jama'a da abokan huld'ar sa"

Ajiyar zuciya na sauke mai k'arfi,ina jinjina maganar a raina,tabbas gara Abba ya fita harkar su,tunda ba za su gyaru ba,nan na cigaba da kwantarwa da mijina hankali,har bacci yayi nasarar d'auke mu mai dad'i.

*****************

Lokacin da Abba ya kirawo Alhaji Mudassir da Alhaji Maude sun tsorata da jin batun sa,domin sun san kusan shine silar arzik'in su,ya bud'a musu sosai a harkokin su,hakan ya sa suka rud'e suka gigice,suka rasa yadda za su yi,nan sukai ta rok'on Abba akan ya basu dama ta k'arshe in sha Allahu za su gyara.

Da yake Abban yana son cigabansu sai ya hak'ura,ya sake basu dama suka cigaba da harkokin su,sosai suke samun kud'i mai yawa,Abba ya fad'awa Sulaiman cewar sun rok'i a basu dama ta k'arshe kuma ya basu,Sulaiman yace shikenan babu damuwa Allah ya sa su rik'e alk'awari.

Tafi tafi aka cigaba da buga harka,har Hidaya ta fara girma ta kai shekaru biyar kan ta shida,don har an sakata a school,kuma ta tashi da basira sosai,gashi mun yi sa'a lalurarta bata cika tashi sosai ba,saboda Oga Taufik' yana k'ok'ari wajen siya mata magani akan kari,d'awainiya yake da Hidaya sosai,haka nan son da yake wa Sulaiman shine ya shafi Hidaya.

Ba zan manta wata rana da Hidaya ta zo na d'aya ba lokacin da suka yi exam,Abba dan murna sark'ar gwal ya siya mata,ni ma kuma ya siya min dank'areriya mai kyau,yace saboda ni na d'ora Hidayan akan turba ta gari,ni ce nayi mata foundation mai kyau har take k'ok'ari a makaran ta.

Ana cikin hakan kawai watarana muna zaune sai Abba ya kira Sulaiman,da hanzari ya tafi amsa kiran,da ya dawo min gabad'aya ransa a jagule yana ta masifa har na tsorata,saboda na san Sulaiman yana da hak'uri bai cika fushi ba,da k'yar ma ya sanar da ni cewar ai abokan Abba ne halin tsiyarsu ya motsa,sun aikatawa Abban babban laifi,kuma daman ai ance mai hali baya fasa halin sa.

Nan na tattaushe shi na kwantar masa da hankalu,sai yake ce min shidai ya fad'awa Abban sunyi na farko kuma na k'arshe,ba za a sake basu wata dama ba kuma.

An yi hakan da kwana biyu sai Sulaiman yake bani labarin wai sun same shi har office d'in sa,wato Alhaji Mudassir da Alhaji Mauden,akan ya lallab'a Oga Taufik' ya basu wata damar,saboda sunga shine mashawarci a gareshi,shine na kusa da shi sosai,take Sulaiman yak'i yarda da batun su,yace ba ruwansa ba zai saka baki ba,domin dai suna cutar da Abban sa saboda sunga yana da hak'uri,shine fa sukai fushi suka dinga zagin Sulaiman d'in suna aibata shi,suna ce masa matsiyaci d'an tsuntuwa wanda bai gaji arzik'i ba,sun so su had'a kaine yadda za su bawa Sulaiman kud'i mai yawa dan a cuci Abba,amma Sulaiman ya gaza hakan ya fatattakesu duk da sun girme masa,take Alhaji Mudassir ya furta wata magana cikin fushi,domin cewa yayi.

"Kai Sulaiman baka isa ka ja damu ba,ko shi marik'in naka yayi kad'an balle kai k'aramin k'waro wanda bashi da ko sisi,kuma mu zuba da kai mu gani,wallahi sai munga bayanka daga kai har uban gidan naka tunda ka ja da mu"

Tunda Sulaiman ya bani wannan labari sai na kasa nutsuwa,tsoro ya cika raina fal,har ma Sulaiman d'in ya dinga mun dariya wai na cika tsoro,babu abinda zai faru basu isa suyi komai ba,mu dogara ga Allah kawai.

Da naji haka sai na share batun,washe gari aka yo min waya daga gida Mahaifina ba lafiya,hanakali na a tashe na tafi GOMBE,ni da Hidaya babu Sulaiman,saboda aiki yayi masa waya yace min zai zo daga baya ko nan da kwana biyu ne ya duba Babana,da naje ma sai na tarar Baban ya samu k'warin jiki sosai,ya dinga murnar ganina da y'ar jikar sa.

Kwanana biyu ina ta jiran Sulaiman shiru bai zo ba,sai gashi ya kirani a waya wai in yi hak'uri aiki ne ya masa yawa,ya nemi in bashi Baba a waya na bashi suka gaisa,yayi masa ya jiki tare da bayar da hak'urin rashin zuwan sa,Baba yace babu komai ai ya ji sauk'i ba sai ya zo ba,sannan yayi masa godiyar d'awainiyar da yake da su,haka nan yace a yiwa Oga Taufik' godiya ma .

Washe gari sai Baba yace na haad'a komatsaina na koma d'akina bai ga amfanin zamana ba na bar mijina shi kad'ai,ba da son raina ba na kama shirin tafiya,Babana ya zaunar dani ya dinga min nasiha kan zaman aure da biyayya wa miji,yace in yi hak'uri zan ci riba,haka Ummana ma tai tayi min Nasiha,na nemi ta bani Sajida mu tafi tayi min hutu amma Ummana ta k'i,tace min in bar mata d'iyar ta tunda gashi nan ni ma na samu tawa,ba zai yiwu in had'a biyu in barta ba ko d'aya ba,tilas haka na hak'ura nayi sallama da su cikin yanayi mara dad'i da kewarsu,na bar Gombe na dawo Abuja.

Kwatsam kawai sai ganina Sulaiman yayi,ya sha mamaki sosai saboda baiyi tunanin zan dawo kusa ba,nace masa ai Baba ne ya koroni,ya dinga dariya yana shiwa Baba albarka,wai Baba yayi masa dai dai daman kewarmu yake ni da Hidayan sa,a ranar har b'angaren Abba naje na gaishe shi tare da kai masa tsarabar Gombe,Abba ya dinga murnar ganinmu tare da sa albarka,ni dai nan na fito ma na bar Hidaya a wajen sa tana ta ba shi labarin Gombe yana dariya.

A washe gari kawai sai muka tashi Abba ba lafiya,babu k'afa babu baki babu ido,ma'ana baya iya tafiya,haka nan baya gani kuma baya magana,ya zama dunkun dukumanu,batun tashin hankali ma baki yayi kad'an wajen zayyana shi,a haka muka kwashe shi zuwa asibiti,duk wani gwaje gwaje an masa amma aka kasa gano lalurar da take damun sa balle a bashi magani,sai uban drip da kullum suke sanya masa.

Abba duk ya rame saboda wahalar da yake sha,shi kansa Sulaiman yayi bala'in rama,kullum cikin kuka yake da neman hanyoyin da zai nemarwa Abba magani amma an rasa,tunaninsa gabad'aya ya toshe ya rasa mafita.

A haka aka sallami Abba daga asibiti muka dawo gida babu wani cigaba,da muka dawo ne ma hankalina ya kai kan in dinga karanta masa alk'ur'ani da ayoyin karya sammu ko sihiri,take kuwa muka fara ganin alfanun abun,domin idanuwan Abba sun bud'e yana gani,sai dai ba magana,amma yana iya motsi har ya karb'i abinci me d'an ruwa ruwa.

Wata rana da ba zan manta da ita ba muna zaune muna karantawa Abba alk'ur'ani,da ni da Sulaiman,sai Hidaya ma ta zo ta zauna ta na karatun,Abba yaji dad'i sosai har ya dinga hawayen jin dad'i,sai da muka kammala sannan ya d'ago hannun sa ya kirawo Sulaiman,Sulaiman ya tashi ya je gareshi,ba bakin magana amma haka ya dinga nunawa Sulaiman godiyarsa gare mu,sannan ya nunawa Sulaiman wata akwatu y,ya nunar masa ya d'auko masa ita.

Sulaiman ya d'auko ya kai masa,sannan ya d'aga shi ya jingina da gadon,sai ya nuna wa Sulaiman yadda ake bud'ewa ya umarce shi kan ya bud'e masa,take kuwa Sulaiman ya bud'e,sai ga tarin takardu kala kala sun bayyana.
Takardun filaye ne da na gidaje,da dai kadarori da dama,ya raba su gida uku,sannan ya umarci Sulaiman da ya bashi biro da takarda zaiyi rubutu.

Sulaiman ya tashi ya binkito takarda da biro ya kawo,shine ya rik'ewa Abban hannu yayi rubutu saboda yadda jikinsa yake wani irin rawa,Abba yayi rubutu kamar haka.

*D'ana wannan sune kadarorin da na mallaka,ka sani cewar ni ma maraya ne mara uwa da uba tamkar kai,bani da d'a haka nan bani da jika,haka nan bani da d'an uwa na kusa sai y'an uwa na nesa,to ga dukiyata nan na rabata gida uku,ka d'auki kaso d'aya na mallaka maka,kaso d'aya kuma a bawa dangina na nesa,ragowar kaso d'ayan kuma a rabawa mabuk'ata wato marasa k'arfi ko kuma marayu,saboda ni na san tawa ta zo k'arshe,na bar wannan wasiyya ne saboda inaji a jikina mutuwa zanyi*

Da Abba ya gama rubutun sai yayi wa Sulaiman alamar ya karanta,Sulaiman yana karantawa sai ya fashe da kuka,hawaye yayi ta malala akan fuskar sa,na matso ina tambayar sa abin da ya faru,sai ya mik'o min wannan takarda nima na karanta,sai nima na fashe da kuka,mukai ta kuka Abba na girgiza mana kai alamar mu daina kuka,yana ta shafa kan Sulaiman,kuma shima hawayen yake yi.

Da dare yayi sai Sulaiman ya umarceni akan in tafi part d'in mu ni da Hidaya mu kwanta,shi zai zauna wajen Abba domin ya kwana da shi,haka kuwa aka yi,na d'auki Hidaya muka wuce sashen mu,kafin mu tafi ma sai da Abban ya nemi in kawo masa Hidayan gabansa,da na kai masa ita ya d'ora hannu a kanta yayi shiru alamar addu'a yake mata,sai da ya kammala sannan yayi min nuni da na d'auketa,haka na d'uketa jiki a salub'e muka bar sashen na sa.

Cikin dare wajen k'arfe d'aya da rabi Sai ciwon k'afa da k'irji ya hana Hidaya bacci,tai ta kuka har tana shirin fita daga hayyacin ta,hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi,ina tsoron fita in nufi sashen Abba a wannan daren,tilas na janyo waya ta na kira Sulaiman ina kuka na shaida masa halin da muke ciki,nan take Sulaiman yace min gashi nan yanzu zai zo tunda Abba ya samu bacci.

Can kuwa sai gashi ya fad'o d'akin a rud'e,ya zo ya karb'i Hidaya daga hannuna,ya tambayeni na bata magani?cikin rud'ewa na girgiza kaina alamar ban bata ba,saboda gabad'aya na rud'e ma,ya umarce ni naje na d'auko na kawo masa,ya bata maganin ina kallo tana ta kuka tana cewa"Abbana k'afa na ciwo zata cire"lallashinta ya dinga yi cike da tausayawa,bayan tasha maganin sai ya dinga yi mata addu'a yana shafawa a k'afar ta ta,cikin ikon Allah sai ta samu salama har bacci ya kwashe ta a jikinsa,lumshe idanu yayi ya jingina da allon gado yana shafa bayanta,a haka baiyi aune ba kawai sai bacci ya kwashe shi shima,saboda a kwanakin baya samun bacci dalilin lalurar Abba,ni kuma ganin yayi bacci sai na kasa tashin sa ya koma gun Abba,a ganina gara na barshi ya d'an huta ya rama baccin da bai samu ba a kwanakin,nima rab'awa nayi gefen su na kwanta,nan da nan nima baccin ya kwashe ni.

Kiran assalatu ne ya tayar da mu,Sulaiman ya farka yana salati sannan ya dube ni yana tambayata wai ya akayi har bacci ya kwashe shi anan?bai koma wajen Abba ba?bai ma tsaya jiran amsawa ta ba ya mik'e yana kwantar da Hidaya gefe guda sannan ya fice daga d'akin da sauri ya nufi sashen Abba.

Har na shiga toilet zan d'auro alwala kawai naji dawowar Sulaiman a firgice yana k'wala min kira,da hanzari na fito a lokacin har Hidaya ta farka a firgice saboda k'arar muryarsa ta razanata,nan da nan ta fashe da kuka,bai bi ta kan Hidayan ba ya nufo ni a gigice yana fad'a min wai yaje sashen Abba amma bai ganshi ba,baya in da ya barshi a kwance,kuma shi dai ya san Abba ba iya mik'ewa yake ba balle ace tashi yayi da kansa,kuma duk ya duba sashen amma ko mai kama da shi bai gani ba,nan da nan nima na rud'e,muka fita muka fara binciken gidan a wannan asubar,amma duk in da muke tunanin ganin Oga Taufik' bamu ganshi ba,sai gashi muna kuka da idanuwan mu duk mun firgice,musamman Sulaiman da kamar yayi hauka dan rud'ewa da gigicewar da yayi,sai nice ma nace ya kamata muje wajen mai gadin get d'in gidan mu tambaye shi ko ya san abin da ya faru,da gudu Sulaiman ya kwasa yayi bakin get,yayin da na rufa masa baya,muna zuwa muka ga mai gadin a sheme a k'asa a sume,ga kuma alamun duka nan a gefen fuskar sa,ga kuma get a bud'e han hai,wani irin tashin hankali ya rufto mana da bamu tab'a tsammani ba,shikenan shigowa akayi aka sace Oga Taufik' kenan?kafin ka ce me Sulaiman ya fad'i ya suma,Zuwa wayewar gari kuwa tuni zan ce ya cika gari cewar an nemi Oga Taufik' an rasa,ma'ana dai ba a san in da yake ba.😭

Comments
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.