Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 30 of 50

BABI NA HAMSIN DA TARA DA NA SITTIN

***Umma ta rungume Hidaya tana jin tausayin ta a ranta,a hankali ta shiga yi mata nasiha tana kwantar mata da hankali,Hidaya tayi kuka sosai a jikin Umma kafin hawayen ta ya lafa,ta d'ago ta dubi Umma cikin rauni tace.

"Umma duk mutumin da zai kyautata muku a rayuwa ya so ku to tilas nima na so shi,duk mutumin da zai k'i ku ya tsane ku tilas nima na tsane shi,a yanzu na ji a raina na k'ara son Uncle Khaleel, amma kuma ina jin tsanar Mahaifin sa"

Umma ta rufe mata baki ta girgiza kai tace.

"Kul!kar na sake jin hakan daga gareki,na baki wannan labari ne ba don ki tsani Daddy ba,sai don ki san yawan k'aunar da Khaleel ya nuna wa Hamza,wadda ta cancanci shi Hamzan ya saka wa Khaleel da mafiyin ta,ma'ana ya hak'ura da ke ya barwa Khaleel, kuma a yanzu Daddy ya shiryu,duk yayi nadamar abubuwan da ya aikata marasa kyau a baya,don haka shi ma ki kalleshi a matsayin uba ko domin darajar Khaleel da ya ke son zama GARKUWAR ki"

Hidaya ta jijjiga kai tana rik'o hannun Umma, ta kalleta tace.

"Umma duk wata GARKUWA da zan samu a bayan ki take ke da Ya Hamza,ni dai kune GARKUWA ta"

Umma tayi murmushi ta sauke numfashi tana k'ank'ame hannun Hidayan,sannan tace.

"Mutum biyu ne GARKUWAR ki Hidaya,wato Hamza da Khaleel, ni kai tsaye kawai ki d'aukeni matsayin mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeki"

Sai Hidaya ta k'ara jin k'aunar Umma sosai,ta matsa ta kwanta a kafad'ar ta hawaye na sake ratsowa fatar idanunta,Umma ta sake rungume ta tana cigaba da fad'a mata alkairan da Khaleel yayi musu a rayuwa,bata gushe ba har sai da Zuciyar Hidaya ta fara aminta da cewar za ta karb'i Khaleel amma a rashin Hamza…..!

A haka ta samu barci ya kwasheta a jikin Umma, sai da baccin yayi nisa sannan Umman ta zame ta ta gyara mata kwanciyar ta fice daga bedroom d'in zuwa parlour.

Bata jima da zama ba Hamza ya shigo, ya nemi waje ya zauna,Umma ta dubeshi tana tambayar sa Khaleel, sai Hamza yace.

"Ya shiga toilet ne zai yi wanka,wai zafi yake ji"

Umma ta gyad'a kai,suka yi shiru na mintuna,sannan Hamza ya muskuta ya dubi Umma yace.

"Wai yarinyar nan ta ci abinci kuwa?"

Umma ta dubeshi kamar bata gane ba tace.

"Wa fa..!?

" Hidaya" ya ambata a tak'aice.

Umma ta girgiza kai tace.

"Bata ci ba,bacci ma take tana d'aki"

Ya D'an yamutsa fuska yana shafa kai,sannan ya dubeta yace.

"A tashe ta taci Umma,na lura yanzu bata wani cin abinci sosai,kuma zama da yunwa bashi da amfani"

Umma ta gyara zama tayi murmushi tace.

"Ai ita ba Yarinya ba ce Hamza,ta san yunwar cikinta,dole idan ta tashi zata nemi abincin da kanta"

Ya kawar da kai yayi magana a hankali cikin jan numfashi.

"To Umma ba gara Yarinya akan ta ba ma,kina ganin fa yanzu ta maida kuka da damuwa sana'ar ta,duk ta k'warzabi kanta ta hanawa ranta sukuni"

"Duk jirgi d'aya ne ya kwasoku ai,da kai da itan D'an juma ne da D'an jummai" inji Umma kenan tana kallon sa.

Sai kawai yayi shiru kansa a sunkuye,can kuma ya mik'e ya fice daga parlour'n, Umma ta bi shi da kallo kawai.

Tana nan zaune ya sake shigowa,ta d'aga kai ta kalleshi,rik'e yake da plate ya zubo abinci a kitchen, da alamun Hidayan ya zubo wa tunda d'aki ya nufa,Umma bata ce masa komai ba har ya shige.

Cikin bacci Hidaya taji ana ambatar sunan ta a hankali,ta fara bud'e idanuwa tana dafe kanta da ke ciwo,tana daga kwancen ta bi Hamza da kallo da jajayen idanuwan ta,dire abincin yayi kan dressing mirror ya juyo ya dubeta.

"Tashi zaune" abin da yace kenan idanuwan sa a kanta, da k'yar ta fara k'ok'arin mik'ewa,yabi kwantaccen gashinta da kallo sanda ta jawo D'an kwalin ta ta d'aura,sannan ta kalleshi suka had'a idanuwa,ya lumshe idanuwan sa yayi magana fuska babu walwala.

"Ki shiga toilet ki wanko bakin ki da fuskar ki kizo ki ci abinci"

Ta D'an marairaice fuska tana shirin magana,yayi hanzarin dakatar da ita da hannun sa sannan yace.

"In dai ba amsar " To" ce zata fito daga bakin ki ba bana son jin komai, tashi kiyi abin da nace kawai"

Tilas ta tashi tana b'ata rai ta shige toilet d'in,wani haushi take ji,d'azu a gaban Khaleel ai nunawa yayi bai damu da cin abincin na ta ba,shine yanzu tana baccinta zai zo ya tada ta,Kuma sai wani d'aure mata fuska yake.

Haka ta kuskure bakin ta ta wanke fuskar ta,sannan ta fito,yana tsaye inda ta barshi kansa a k'asa,ta k'araso ta zauna bakin gadon,ya juya ya d'auko abincin ya mik'a mata,karb'a tayi tana kallon sa,ya karya wuya yana kallon ta k'asa k'asa yace.

"Maza ki cinye shi,yawan wasa da cin abinci shiyasa har yanzu kika kasa yin kumari,haka kike so in d'auke ki in bawa Khaleel d'in jiki duk k'ashi?

Wannan magana ba k'aramin b'ata mata rai tayi ba,bata san lokacin da tayi masa wani irin kallo ba,ba tare da shawara da zuciyqrta ba kawai ta ji bakinta na furta masa cewar.

" To ai irin mu ake yayi,shi ma Uncle khaleel d'in ba zai so in yi k'iba ba domin kar na dinga cika masa Hannu "

A razane Hamza ya dubi Hidaya yana mamakin fitowar wannan kalamin daga bakin ta, bakin sa a sake,zuciya ta tunzuro shi,yana niyyar magana ya jiyo muryar Khaleel a parlour'n Umma,kawai sai yayi wa Hidaya wani kallo mai tarin ma'anoni ya kad'a kai ya fice,ta bishi da kallo a ranta tana cewa "nima na rama" sai kuma taji hawaye ya zubo mata,musamman da ta fuskanci maganarta ta b'ata ran Ya Hamzan ta,gefe tayi da abincin ta fad'i kwance kan gadon tana sharar hawaye.

*****************

Khaleel dai da k'yar ya iya juyawa Abuja a ranar da magriba,saboda a yammacin sai da ya d'auki Hamza da Hidaya suka fita a motarsa domin zaga gari,da k'yar ma Hamzan ya bi su don dai Umma ta saka baki ne,Hidaya ta nemo rakiyar Sumayya suka tafi tare su hud'u.

A wannan fitar Khaleel ya kashewa Hidaya kud'i sosai kamar ba gobe,har sai da Hamza ya dinga yi masa fad'a,amma yace shi a barshi ai matarsa ce,komai yayi a kanta dai dai ne,sai Hamza ya share shi bai kuma bi ta Kansu ba ya shiga Hidima da wayar sa.

Shi kam Khaleel kulawa da soyayya ya dinga nunawa Hidaya,kalamai na soyayya masu dad'i kuwa babu adadi a bakinsa,har sai da Hidaya ta k'ara tabbatar wa lallai Khaleel D'an love ne na hak'ik'a,ya iya soyayya k'arshe.

Ita kanta Sumayya sha'awar su ta dinga yi,har tana jin Ina ma ta samu saurayi irin Hamza ko Khaleel, da ta gama morewa a duniyar ta.

Ko da Khaleel ya koma gida bai bar Hidaya ta huta ba,wayar safe daban ,ta rana daban,ta dare daban,tun Hidaya bata saba ba har ta fara sabawa ita ma,ta kan mayar masa da amsa idan yana maganganun sa,

Tuni soyayyar Khaleel da Hidaya ta fantsama,a dangin Khaleel babu Wanda bai san da soyayyar ba,hatta Daddyn sa,kuma abin mamakin shine kwata kwata Daddyn bai nuna k'yamar abin ba,kasancewar ya fara canja d'abi'arsa mara kyau ta k'in talakawa,sannan an sanar masa Hidayan d'iyar Umman Hamza ce,ga yadda Khaleel gabad'aya ya haukace akan son yarinyar,ya san ko me zai yi da wuya Khaleel d'in ya hak'ura da Auren ta,dalilin da ya sa ya amince kenan ba wai don yaji a Zuciyar sa yana son abin ba.

Cikin wata biyu maganar Auren Khaleel da Hidaya tayi k'arfin gaske,an kawo kud'i da sa rana wata biyu masu zuwa,Umma dai sai siyen kaya take tana ajiyewa,tana so ta nunawa Hidayan gata sosai,bata son tayi kukan rashin wani Abu,shiyasa ta dage sosai.

Yayin da Khaleel ke Cikin farinciki yana jin ba ya shi a fad'in duniya,a lokacin ne kuma Hamza ke rama da k'ek'ashewa kamar kud'in guziri, shi dai ya san ya fawwalawa Allah komai,kuma ya hak'ura da Hidayan,amma bai san abin da yasa ya kasa cire ta a ransa ba,kullum tunaninta da mafarkinta yake,idan suka kasance guri d'aya kuma ya kan rasa ya zai yi,musamman yanzu da take k'ara nane masa,duk wasu shirye shiryen bikin shi ta d'orawa,wai shine zai yi komai,yace mata ta nemi Hansa'u da su Sumayya sune mata k'awayen ta da suka san komai,amma shi namiji ne bai sani ba,sai tayi murmushi tace masa.

"Ya Hamza bani da K'awar da ta fika a duniya,dole kai zaka zamo babbar K'awata a biki na"

Ramar da Umma ta ga yana yi sai ta d'aga hankalin ta, ta zaunar da shi tayi masa nasiha iya nasiha,da maganganu masu dad'i,da hak'urk'urtar da Zuciyar sa,ya dinga share hawaye yana gyad'a kai ya kasa magana,ita kanta Umma ranar sai da tayi hawaye,saboda mugun tausayin da Hamzan ya bata,tabbas Maryam kabir mashi tayi gaskiya da tace (so babbar cuta ne).

Lokacin biki na matsowa a sanda Hidaya ke Cikin fargabar rabuwa da Umma da Hamza,har ta kai bata iya barci saboda damuwa,sai kuka Cikin dare,kafin me ta kuma ramewa sosai,bata son nuna damuwarta saboda kar Umma da Hamza su damu,sannan bata son Khaleel ya fuskanci damuwar ta Dan kar ta saka shi Cikin wani hali,don tuni ta fara koyawa zuciyarta yadda za ta so Khaleel, ganin shine zai zama mijinta babu yadda zata yi,in dai nuna kulawa da tsantsar soyayya da nuna tausayawa ga mace na sa mace ta so namiji, to tabbas dole ta so Khaleel saboda babu ta in da ya Gaza,sai dai ta san Son Hamza a jininta yake,ba zai tab'a fita ba har ranar da numfashin ta zai bar gangar jikinta.

*****************

Sati biyu da yin candy d'in Hidaya aka kawo lefenta,Wanda fad'ar kayan da aka jibga k'auyanci ne,kuma duk kayan zab'in Hamza ne,Khaleel ne ya saka ya zab'ar mata komai,saboda a cewar Khaleel d'in Hamzan ya fi shi sanin abin da ya dace da Hidayan sa masoyiyar sa.

A satin da za a fara biki kuwa gabad'aya Khaleel ya tattaro ya dawo Kaduna,saboda zirga zirga ta mishi yawa,gashi yana cuku cukun fara aiki a babbar kotun Abuja bayan bikin su.

Hamza ma b'angaren aikin sa na tafiya dai dai,babu abin da ke damun sa kamar yadda y'ammata suka saka shi a gaba da sunan soyayya,har gidan redio kai masa ziyara suke,waya kuwa har rasa wadda zai d'auka yake,gashi shi a ransa ba wata soyayya,yana ganin yayi rashin ta tunda ya rasa Hidaya a fad'in duniyar sa.

K'anwar Umma da ke kano ce takanas ta dira a Kaduna, da kayayyakin gyaran amare,domin sana'arta ce,nan da nan ta fara gyaran Amarya Hidaya,wadda cikin kwana uku da wuya ka shaida ta idan ka ganta,tsabar kyawun da tayi,ga matsanancin k'amshin da ya ratsa jikinta,ko ya ya ta gifta sai guri ya jima yana k'amshi.

Ango Khaleel ya rud'e matuk'a,burin sa kawai a shafa fatiha Hidaya ta zama mallakin sa.

Da yake Hidayan ustaziya ce babu wani shiri na rak'ashewa da tayi,duk da kuwa Khaleel yaso a yi biki na kece raini,amma Hamza da Hidaya suka k'i amincewa,tilas ya hak'ura,domin farincikin mutanen nan guda biyu ya fiye masa komai.

Babu dinner balle wani party,illa walima k'ayatacciya da aka shirya iya mata kawai,yayin da maza ma za su yi tasu daban,an yi abubuwa kadaran kadahan kamar yadda Hamza ya nunar a yi,babu fariya ko almubazzaranci na kud'i.

Duk shagalin bikin kuma da ake yi Daddy baya nan,ya tafi k'asar China akan business d'in sa,shi kansa bai san dalilin da yasa baya d'okin Auren D'an sa da yake matuk'ar so ba,Daddy bai dira a Kaduna ba sai ana saura kwana d'aya d'aurin Auren Khaleel da Hidaya,da yake gabad'aya suka tattaro daga Abuja zuwa Kaduna domin a gama bikin a nan,cikin tsohon gidan su Khaleel d'in da suka bari,tuni aka k'ara gyara shi domin a gabatar da bikin,in da Hidaya da Khaleel za su zauna a b'angare guda da aka ware musu tsawon sati d'aya,daga nan su d'unguma zuwa Abuja domin cigaba da zama a can.

A Daren ranar da Daddy ya sauka Kaduna, yana zaune shi da Anty kubra a bedroom d'in sa,suna magana akan d'aurin Auren da za a yi gobe,sai Daddy yaji k'arar wayar sa,nan da nan ya d'auka yana murmushi yayi magana.

"Alhaji Maude manyan gari,ina fatan ka iso kadunan dai,domin fa da safe k'arfe goma ne za a d'aura Auren"

Anty Kubra ta b'ata rai jin mijinta ya ambaci sunan Alhaji Maude, haka kawai bata son alak'arsu duk da dai tare ta gansu,Alhaji Maude ba mutumin kirki bane kwata kwata,tana wannan tunanin ta jiyo muryar Alhaji Maude na bawa Daddy amsa murya a cushe.

"Mudassir me ya shiga kanka ne?yaushe har ka yi lalacewar da za ka bari Khaleel ya auri yarinyar da ba a san asalinta ba?Y'ar tsuntuwa !tsintacciyar mage wadda bata mage!mara asali!shegiya wadda bata da uwa da uba!me kuma lalurar sikila….!

Zumbur Daddy ya mik'e tsaye cikin tsananin fad'uwar gaba,a tsorace yana zare idanu yace.

" Wace irin magana ce wannan Alhaji Maude? Me maganganun ka suke nufi?kana nufin yarinyar da Khaleel zai aura ce take da duk wannan tawayar?K'anwar abokin sa Hamza ce fa"

Anty Kubra ma dafe k'irjinta tayi jikinta na tsuma da tsananin tsoro,domin duk ta ji maganar da Alhaji Maude yayi,shi kam Alhaji Maude a fusace ya sake yin magana.

"K'warai kuwa,domin naji yo maganar ne daga majiya mai tushe,shi kansa Khaleel d'in ya san ba K'anwar Hamza ba ce,ya san bata da Asali,tsintar ta suka yi har ta rayu da su,kai kana ina har hakan ke shirin faruwa baka yi bincike ba?wane irin uba ne kai?

Daddy duk ya rud'e a gigice yake gabad'aya,cikin wata irin murya yake cewa.

" Ban sani ba Maude, wallahi ban sani ba,ni fa nan ko yarinyar ban sani ba,ban tab'a sha'awar ganinta ba balle har nayi bincike a kanta,tunda dai an ce min k'anwar Hamza ce,ni gabad'aya daman ba son Auren nake ba,kawai don naga Khaleel d'in ya makance akan son yarinyar ne,amma ai ba sa'ar aurensa ba ce,ni da nake son Khaleel ya samo Y'ar manya wadda ta dace da shi,innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yanzu menene abin yi Alhaji Maude? "

Anty Kubra jikinta na mazari duk ta jik'e da zufa tsabar tashin hankali,ta k'ara zaro idanuwa a sanda taji muryar Alhaji Maude na fad'in.

"Abin yi zai wuce ka hana Auren gabad'aya ne,domin muddin ka bari akayi wannan Aure to ina rantse maka da Allah sunanka zai b'aci!darajarka zata zube!k'imarka zata fad'i k'asa warwas!zaka barwa bayanka abin fad'e,ina shawartarka ka gaggauta d'aukan matakin dakatar da wannan Aure kafin a d'aura shi gobe,idan ba haka ba zaka yi danasani mara amfani Mudassir"

Alhaji Maude na kaiwa nan ya kashe wayarsa ya bar Daddy da waya a Hannu baki a sake,jikinsa na karkarwa tamkar mai jin sanyi,a hankali ya zame ya zauna bakin gado yana sakin gwauron numfashi, hannunsa dafe da kansa,ya d'ago ya dubi Anty Kubra da tayi mutuwar tsaye,da k'yar ya fizgo magana ya ce.

"Kubra kinji wani bala'i kuma?da me Khaleel yake ji da yake Neman janyo min wannan tarangahuma haka?da mutuncina da komai ya rasa wadda zai aura sai shegiya Y'ar tsuntuwa?

Anty Kubra ta janyo salib'ab'b'en jikinta zuwa kusa da daddyn ta zauna,da k'yar ta saita kanta daga razanar da tayi,cikin k'arfin hali ta fara magana.

" Daddyn Khaleel kar ka rud'a kanka,wannan magana tana buk'atar bincike Sosai, ka daina yarda daga an fad'a maka magana ka d'auka,wani abin k'arya ne ba gaske ba,idan ma kuma gasken ne k'ila akwai wani b'oyayyen al'amari,domin na tabbatar Khaleel yadda yake da hankali ba zai auri mace me aibu ba,sai dai idan k'addarar sa ce haka,ka kwantar da hankalin ka zuwa Safiya sai kayi bincike kafin d'aurin Auren kaji"

Daddy ya share zufar goshin sa idanunsa jajir tsabar b'acin rai,sannan yace da Anty Kubra.

"Idan nayi binciken maganar Alhaji Maude ta zama gaskiya fa?ya za a yi kenan?"

Anty Kubra tayi shiru jiki a sanyaye ta rasa abin cewa,Daddy ya runtse idanu ya cigaba da cewa.

"Na tabbatar abin da yafi dacewa shine na hana wannan Auren,to amma K'alubalen shine Khaleel, banga ta in da zai iya hak'ura da yarinyar nan ba Kubra,tunda har ya san aibun ta amma ya gwammace ya aureta a haka saboda tsananin son da yake mata,na san Khaleel zai gwammace ya rasa ransa a kanta,ni kuma ina son rayuwar d'ana,Kubra kin sani ina matuk'ar son Khaleel, ta ya ya kike ganin zan b'ullowa wannan al'amari"

Anty Kubra ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Daddy tace.

"Ina ganin tunda lokaci ya k'ure ka hak'ura a d'aura Auren kawai,bayan an d'aura duk wani bincike sai ya biyo baya,kafin nan mun yi tunanin hanyar da za a biyo wa lamarin,amma yanzu idan aka ce wata magana mai kama da hana Auren za ta b'ullo to za a b'ata goma d'aya bata gyaru ba,zamu iya shiga mugun hali Alhaji,domin zamu iya rasa Khaleel, don Zuciyar sa ba lafiya ne da ita ba,sannan a zo mata da wannan babban gib'in abin akwai razanarwa gaskiya,ka hak'ura a d'aura kawai,in yaso sai a san yadda za a b'ullowa lamarin kafin mu wuce Abuja"

Daddy yayi baya ya fad'i akan gadon cikin matsanancin tashin hankali,kansa na sarawa kamar ya tsinke,ya rasa tudun dafawa,shin dakatar da Auren zai yi ya hana amma kuma ya rasa D'an sa da Ya fi so?ko kuma hak'ura zai yi a d'aura Auren D'an sa da shegiya Y'ar tsuntuwa sunan sa da record d'in sa ya b'aci…..???

comments
share
vote
pls

*GARKUWA BIYU*

BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.