Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 48 of 50
BABI NA CASA'IN DA BIYAR DA NA CASA'IN DA SHIDA
*SHAFIN YAU ME YAWA NE,IDAN KUNJI DAD'INSA TO KUYI SHARHI ME MA'ANA*👇😉
***Ranar haka ta kasance musu babu Wanda ya samu nutsuwa a cikinsu,kowa da abinda ya addabi zuciyar shi,Daddy yayi nadama sosai,har yake ji a zuciyarsa ina ma bai san Alhaji Maude ba,ina ma bai biyewa son zuciya ya aikata abubuwan da suka faru a baya ba,da yana da yadda zaiyi da ya goge tarihin baya,amma babu yadda zaiyi,alk'alami ya riga ya bushe.
Kwana biyu da hakan Mummy da Aunty Sajida suka yi shirin tafiya Gombe,kuma tare da Hidaya za su tafi,hakan yasa Umma da Hamza su ma suka ce da su za a yi wannan tafiyar,ko domin suje suga kakar Hidaya,amma Umma ta k'udure a ranta ko sunje Gombe tare da Hidaya zata dawo,zata rok'i Mummy alfarmar ta bar mata Hidaya a wajenta,ko domin sabon da tayi da ita,duk da tana ji a zuciyarta anya idan ta aikata hakan tayi adalci kuwa?kamata yayi ta bar Hidaya da mahaifiyarta su zauna tare,ko domin dad'ewar da suka yi ba tare da juna ba,ta san dole ne za su yi mararin juna,kuma za su so kasancewa tare da juna a koyaushe.
A motar Hamza suka yi tafiyar,shine zai tuk'a motar yayin da Hidaya ke zaune a gefensa,sai kuma Umma da Mummy da Aunty Sajida da ke zaune a gidan baya,Khaleel ya so ya bisu,abubuwa biyu suka yi masa shamaki,na farko yana son zama domin kammala bincike kan Alhaji Maude da kuma shigar da k'ara da yake son yi a kotu,na biyu kuma nesanta kansa da yake so yayi da Hidaya,domin tabbas ganinta yana tayar da hankalinsa ba kad'an ba,wani irin sonta yake ji a cikin zuciyarsa,kuma ita ma ya lura tana jin soyayyar shi a ranta,sai dai Soyayyar ba zata yi musu amfanin komai ba,wannan dalilin ya sa ya hak'ura da bin su,illa fatan alkairi da ya bisu da shi.
Cikin ikon Allah suka isa garin Gombe,suka tarar da tarba mai kyau daga kakar Hidaya,domin kamar ta goya su,ta rik'e Hidaya k'am a jikinta tana hawayen jin dad'i da murna,sai ga dangi na nesa da na kusa duk sun hallara domin ganin Hidaya,sai ga Hidaya na kuka sosai,kukan ganin danginta,kukan godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana mai matuk'ar muhimmanci a tare da ita.
Kwanansu uku a Gombe,sunji dad'in garin sosai saboda karamcin mutanen garin,haka Aunty Sajida da yaranta suka dinga zagayawa da Hidaya da Umma cikin gari gidajen y'an uwa da abokanen arzik'i,tabbas Hidaya taga gata,kuma taji dad'in hakan,ta samu kanta cikin walwala sosai,duk da akwai abinda yake mintsinin zuciyarta,wato soyayyar Khaleel da ke addabarta,duk dare ba ta iya bacci sai tunaninsa da kuka,gashi ba ganinsa take ba,ko muryarsa ma bata ji,har gwada kiran wayarsa take ko domin taji muryarsa amma kullum wayar bata shiga,mamaki ya kan baibayeta ,burinta ta samu Ya Hamza ta tambayeshi dalilin da yasa bata samun lambar Uncle Khaleel d'in.
A kwana na biyar ne da zuwan su Hidaya ta shiga d'akin da aka sauki Hamza da sallamar ta,fura Mummy ta dama masa shine ta bawa Hidayan ta kai masa,zaune ta tarar da shi da waya a kunnensa yana magana fuskarsa d'auke da murmushi mai k'ayatarwa,ajiye furar tayi ta nemi gefe ta zauna tana kallonsa,ambatar sunan Khaleel da yayi shine ya saka ta zabura jikinta na rawa alamar murna,ta tsurawa Hamza idanu tana wani irin murmushi mai kyau,cikin azarb'ab'i da saurin magana ta ce.
"Lah ! Ya Hamza da Uncle Khaleel kake magana?Don Allah Ya Hamza ina son jin muryar shi,bani shi mu gaisa"
Sanya mata ido kawai Hamza yayi ganin yadda jikinta ke rawa duk ta wani firgice,sai mik'a masa hannu take tana yarfewa alamar ya bata wayar,lumshe idanuwa yayi ya sauke ajiyar zuciya kafin cikin sanyin murya ya ce wa Khaleel.
"Khaleel ga Hidaya a kusa da ni,bari na bata wayar ku gaisa"
Daga can Khaleel ya d'auke wuta gabansa na tsananin fad'uwa,ambatar sunanta kad'ai sai da ya sanya shi cikin wani yanayi,ya san yana jin muryar ta to sai ta tono masa mikin da ke zuciyarsa,k'ila ko bacci ba zai samu a daren ba,hakan ya sa cikin sauri yace wa Hamza.
"Aboki wani aiki ya taso min yanzu na hanzari,idan nace zan tsaya gaisawa da ita zan b'ata lokaci,kawai mik'a min gaisuwa ta zuwa gareta tare da fatan alkairi" yana fad'in hakan kafin ma Hamza yayi wani yunk'uri tuni ya kashe wayar sa,ya bar Hamza da waya a kunne yayi sakato da shi.
Hidaya na jiran ya mik'o mata waya sai gani tayi ya sauke wayar ya ajiye ta gefe yana sauke numfashi,bin shi da ido tayi alokacin da shima ya d'ago kansa suka had'a idanu,ganin yadda take kallonsa sai ya d'an lumshe idanu yana shafa kansa ya ce.
" Ya kashe wayar" Zaro idanuwa tayi,sai ga hawaye sun cicciko idanun,kautar da kai Hamza yayi yana cewa," Amma ya ce min in gaisheki...kuma yana miki fatan alkairi..wani d'an uzuri ne ya taso masa da ya hana ganawarku a yanzu"jijjiga kai Hidaya tayi Hawayen na sakko mata,ta sanya bayan hannunta ta goge,sannan ta mik'e a hankali domin barin d'akin,har ta kai bakin k'ofa taji muryar Hamza ta kira sunan ta.
"Hidaya" tsayawa tayi cak kafin ta waiwayo duk jikinta a sanyaye, " Zo nan kinji" abinda yace da ita kenan yana gyara zamansa kan daddumar da yake zaune,takowa tayi a hankali ta iso gabansa,sannan ta tsuguna kanta a sunkuye tana wasa da yatsun hannun ta idanuwan ta cike da hawaye.
Kallonta yake sosai kafin ya k'ara ambatar sunanta,ta d'ago idanuwan ta ta jefa cikin na sa,saiga hawaye yarrrrrr sun biyo kuncinta,k'irjinsa yayi wata irin harbawa,har ga Allah baya son damuwar wannan baiwar Allah,cikin muryar jimami da rauni ya ce mata.
"Me ya saka ki kuka?ko wani abu na damun ki ne?"
Girgiza kai tayi hawaye na yarari a fuskarta,sai shi ma ya girgiza kan,ka na ya sake cewa.
"Ah ah Hidaya,tabbas akwai abinda yake damun zuciyarki,kawai dai ina tunanin kin sauya min matsayi ne,kin canja ni a matsayin wanda kike fad'awa damuwarki har ya baki shawarar da ta dace ko?Hidaya duk wani yanayi da zaki shiga ina fuskantar sa,kin sani tun kina yarinya na gama karantarki,ko motsi kika yi na kan gane abinda yake nufi,yanzu ma fuskarki da yanayinki sun karantar da ni damuwar da kike ciki,da zaki taimaka da kin fad'a min,k'ila akwai wani abu da zan iya taimakawa da shi domin kawar da damuwar"
Kawai Sai Hidaya ta fashe da kuka jin maganganun Hamza,ta sanya kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka me had'e da shesshek'a mai tab'a zuciya,to ita yanzu me zata ce masa?bud'e baki za ta yi ta fad'a masa cewar Soyayyar Khaleel ce ke addabarta?ko ce masa za ta yi tunanin Khaleel ke damun ta?ko kuwa kewar Khaleel na neman hallakata?duk ciki babu wanda zata iya kallon tsabar idanun Hamza ta fad'a masa,domin ita kanta ta san akwai babban shinge tsakaninta da Khaleel,wani shinge mai matuk'ar girma da zai hana wanzuwar komai a tsakaninsu.
Kukan da take sosai yake tab'a ruhin Hamza,yayi shiru yana sauraren ta tare da runtse idanuwan sa,ta d'auki tsawon lokaci tana ta kuka ba tare da ya dakatar da ita ba,ya barta tayi abinta ta k'oshi,a ganinsa kukan zai yaye mata wata damuwar,shiyasa baiyi k'ok'arin hanata ba,sai dai shima yana jin tamkar ya fashe da kukan,saboda raunin da zuciyarsa tayi,sai da yaji ta d'an tsagaita sannan yayi magana cikin sanyin murya.
"Hidaya kiyi hak'uri...kiyi hak'uri...kiyi hak'uri...ita rayuwa daman haka take,ba ko yaushe mutum yake jin dad'i a cikinta ba,akwai tarin k'alubale da k'addarori da jarrabawa,hak'uri da juriyar da mutum zai yi matakin nasara ne,taki damuwar kawai kika sani Hidaya,amma wallahi da zaki san damuwar wasu to tabbas za ki ga taki k'arama ce akan ta su,na san zaki ta cewa shi wannan Hamzan kullum bashi da magana sai ta Hak'uri,to kar kiyi gajen hak'uri ki dai k'ara hak'urin,wallahi duk wanda yayi hak'uri ya had'a da addu'a ba zai tab'a tab'ewa ba Hidaya,tashi kije,kuma ki cigaba da hak'uri da addu'a"
Share hawayen ta tayi,sannan ta mik'e a hankali ta fice,maganganun Ya Hamza na yawo a kanta,har ta fice idanuwan sa a kanta,sannan ya lumshe idanuwa yana d'an sakin wani murmushi k'arami,a ransa yake cewa"Hidaya kenan ! damuwarta kad'ai ta sani,bata san damuwar da ke ran wasu ba"bud'e idanuwan sa yayi ya k'urawa sili ido,a hankali ya furta cewar.
"Allah ka magancewa duk wani musulmin duniya damuwar da take ransa....!"
****************
Kwanansu Bakwai da zuwa Gombe suka yi shirin komawa Kaduna,ko dan saboda aikin Hamza da yake ta fashin zuwa,dan ma ya d'auki uzuri a wajen aikin shiyasa bashi da wata damuwa,Umma ta kasa yiwa Mummy magana akan tana so Hidayan ta bisu,ita ma kuma Mummyn bata yi mata zancen ba,hakan yasa Umma da Hamza ne kawai ke shirin komawa babu Hidaya da zata zauna na wani d'an lokaci domin shak'uwa da danginta da kuma mahaifiyar ta.
Har bakin mota suka yi musu rakiya,godiya dai da fatan alkairi Umma da Hamza sun sha a wajen dangin Hidaya har kunya suka dinga ji,haka nan sun samu alkairai masu yawa wasu ma k'in karb'a suka yi saboda yawan abubuwan,sai ga Hidaya na kukan rabuwa da su,shi Hamza ma kasa tsayawa yayi yaga kukan ta ya shige mota ya zauna,sai Umma ce ta dinga lallashinta ita ma har da nata hawayen,ta dinga lallab'ata akan tayi hak'uri ba dad'ewa zata yi a Gombe ba,da zarar komai da Khaleel yake yi ya kammala dole su tattaro su dawo Kaduna ko domin fuskantar Shari'ar da ke gabansu,hakan ya sa Hidaya ta rage damuwarta har tayi murmushi,Umma taji dad'i ta rungumeta,daga nan kuma suka saki juna Umma ta zagaya ta shiga mota,sai Hidaya ta matsa inda Hamza ke zaune b'angaren tuk'i ta d'an lek'a shi,yana zaune wayarsa na hannunsa yana danne danne,sai da ta ambaci sunansa sannan ya waiwayo a hankali ya amsa yana duban ta,sai tayi k'asa da kanta tace masa.
"Ya Hamza Allah ya tsare hanya,Allah ya sauke ku lafiya,don Allah a mik'a min gaisuwata zuwa ga Uncle Khaleel kafin na dawo"
Murmushi me kyau ya sub'uce masa,ya tura wayarsa cikin aljihu ya jinjina kai yana fad'in.
"Sak'onki zai isa in sha Allah,amma banji kin ambaci Hansa'u da Sumayya ba,ko su kin manta da su ne?"
B'ata fuska tayi tana marairaicewa kafin ta kalleshi tace," To ai su fushi nake da su Ya Hamza,munyi fad'a na daina kula su ma"
Hamza ya d'anyi dariya,har sai da Hidaya ta k'ura masa idanu saboda kyawun da taga ya k'ara a idanuwan ta,jerarrun hak'oransa farare tas sun bayyana sai d'aukar ido suke,cikin dariyar ya ce.
"Da alama sun miki wani laifi kenan?to ina neman musu afuwa da yafiya,kiyi hak'uri ki yafe musu"
Sai ta jijjiga kai tare da matsawa daga jikin motar,domin ta basu damar tafiya,a hankali tana kallonsa ta ce," Sun ci darajarka Ya Hamza,wallahi da zan jima ban k'ara duban wata yarinya a cikinsu ba"
Dariya ya sake yi yana k'ok'arin tashin mota da hannu d'aya,d'aya hannun kuma ya d'ago shi yana mata jinjina irin ta sarakai,fuska a washe yake ce mata "Sannu Babba,Allah dai ya k'ara Girma" Maganarsa ta bawa Hidaya dariya,take kuwa ta fashe da dariya tana rufe fuskarta,Umma ma na gefe zaune kusa da Hamza tana murmushi,har Hamza ya tashi motar yana murmushi suka soma tafiya,yayin da Hidaya take ta d'aga musu hannu murmushi d'auke akan fuskarta,sai Hamza yake ta jin dad'i akan ya tafi ya barta cikin nishad'i ba cikin damuwa ba.
***************
Cikin ikon Allah kwanakin da suka shud'e tuni Khaleel ya kammala shirye shiryen komai da had'a bayanai,kuma har an shigar da k'ara kotu,in da Mummy ta so jagorantar Shari'ar,amma Hamza ya ce ta bari wani Alk'alin yayi,saboda ita dole zata kasance lamba ta farko wajen bayar da shedar duk wasu abubuwa da suka faru a zamanin na baya da ya shud'e.
Rana d'aya Alhaji Maude da Alhaji Mudassir suka samu takardar sammaci daga kotu,take kuwa Maude ya kira Daddy yana zayyana masa wai an kawo masa sammaci daga kotu,Daddy da ke jin haushinsa sosai yace masa shima ya samu sammacin,dan haka sai suyi shirin shiga kotu kawai,domin a bajeta a fai fai,ya kashe wayar ya bar Maude da waya a hannu baki a sake.
Ana saura kwana d'aya shiga kotu,sai ga tawagar mutanen Gombe sun iso,Mummy ce da Aunty Sajida,sai kuma Mahaifiyar su,tare da Hidaya da tayi wani mugun kyau kamar wadda taje k'asar waje,jikinta har wani shek'i yake yi tayi b'ul b'ul da ita,duk da bata yin k'iba amma ta murje sosai,har k'ofar gida mota ta kawo su ta dire,suka firfito suna sakko da kayansu,Hidaya murna duk ta cika ranta,ko tsayawa kwasar kayan baya yi ba ta ruga domin shiga gidan da d'an gudunta.
Lokacin ne Hamza da Khaleel ke k'ok'arin fitowa daga cikin gidan,Khaleel na korawa Hamza bayanin yanda Shari'ar za ta kasance a gobe,suna sanyo kansu cikin zauren Hidaya ma na shigowa da d'an gudunta,su za su fito ita kuma za ta shiga,saura kad'an su zabga karo suka ankara suka yi baya da sauri idanuwan su a waje,ita ma ja baya tayi tana sauke wani irin numfashi kafin ta d'ago kanta idanuwan ta su fad'a cikin na Uncle Khaleel,take taji wani irin abu ya tsirga mata,musamman da taga yayi wata muguwar rama yayi duhu,duk ya sauya mata saboda ta d'auki tsawon lokaci bata ganshi ko ta ji muryar shi ba,a k'alla kuwa za a yi wata biyu kan na uku,domin a yanzu mutuwar auren su suna cikin wata na uku ne,wani irin kallo suke wa juna tamkar za su had'e,Khaleel na had'iyar wani yawu me d'aci da ya cika bakinsa,kai gaskiya ya tafka babbar asara,rashin Hidaya a gareshi ba k'aramin gib'i ba ne,shi kad'ai ya san halinda zuciyarshi take ciki.
Abin da ya d'agawa Hamza da Khaleel hankali bai wuce ganin Hidaya da suka yi ta dafe kanta da hannu d'aya ba,d'aya hannun kuma ta rufe bakin ta tana wani irin yunk'uri,cikin firgita Hamza ya dubeta a rikice yana fad'in " Ke lafiya..?me ya sa m....
Kafin ma ya kai k'arshen maganarsa sai gani suka yi Hidaya tayi k'asa ta durk'ushe,take ta fara kelaya wani irin amai na tashin hankali tana yunk'uri kamar ta amayo y'ay'an hanjinta,matsowa suka yi gareta dukkansu suna sunkuyawa zuwa gareta cikin tashin hankali,sannu kawai suke jera mata yayinda ta kasa amsawa sai yunk'uri take tana kelaya amai,tuni hawayen wahala ya wanke fuskarta saboda rad'ad'in da take ji a k'irjinta na yunk'urin da take yi,a lokacin ne kuma su Mummy suka k'araso cikin zauren,sai suka tsaya turus suna duban Hidaya da ke durk'ushe tana amai,ga kuma Hamza da Khaleel tsugune gabanta sai jero mata sannu suke yi.
Hamza ke tambayar Mummy a rikice"Wai daman Hidaya bata da lafiya ne?" Aunty Sajida ce ta bashi amsa da cewa"Lafiyar ta k'alau muka tawo wallahi" Mamakinsu bai wuce yadda aman yak'i tsayawa ba,sai wani irin yunk'uri take yi ga juyawar da kanta ke yi,wani irin jiri take ji kamar za ta kife a wajen,ganin haka sai suka tsorata sosai,Khaleel yace gara a tafi asibiti a duba halin da take ciki,irin wannan mugun amai lokaci guda akwai tashin hankali.
Aunty Sajida ko hutawa bata yi ba ta rik'e Hidaya da idanuwan ta ke lumshewa tsabar wahala,suka yi waje,yayin da Hamza da Khaleek suka rufa mata baya,Khaleel ya janyo motarsa cikin rawar jiki,ya bud'ewa Aunty Sajida bayan motar suka shiga ita da Hidaya sai jera mata sannu yake yi,shi da Hamza suka shiga gaban motar,nan da nan Khaleel ya figi motar cikin hanzari suka nufi asibiti.
Ita dai Umma sai ganin su Mummy tayi kawai,ta tare su cikin murna da kulawa,sai da suka zauna take tambayar Ina Hidaya da Sajida?nan Mummy take fad'amata dukkan abinda ya faru yanzu daga zuwansu,take hankalin Umma ya tashi ta fara neman hijab wai za ta bisu asibitin,sai da Mummy ta dinga tausarta akan tayi hak'uri ta zauna tunda sun tafi,ta tabbatar ba za su jima ba yanzu za su dawo,kuma in sha Allahu Hidayan za ta samu lafiya.
*********
Zaune suke a gaban Likitan suna jiran jin bayaninsa,bayan zuwan su an d'auki jinin Hidaya da fitsarin ta domin a gwada,Sannan kuma an jona mata drip saboda yawan aman da tayi,tana kwance a d'akin da aka jona mata ruwan bacci ya kwasheta cikin wahala,yayin da Aunty Sajida take lura da ita,su kuma suna can office d'in likita zaune suna jiran sakamakon ya fito dan sanin abinda yake damunta.
Cikin lokaci kad'an kuwa sai ga shi an kawowa likitan sakamakon,ya karb'a ya sanya glass d'in sa yana dubawa,take suka hangi fuskarsa d'auke da tarin murmushi mai k'ayatar wa,su kam a rikice suke,har rige rigen tambayarsa suke yi wai shin me yake damun Hidayan?
D'agowa yayi yana murmushi,kafin ya dube su yana fad'in" Alhamdulilla" Sannan ya zarce da cewar " Wanenw mijin na ta a cikin ku?" Sakato suka yi suka rasa abin da za su ce,Sai Khaleel ne yayi k'arfin halin magana"Ni ne mijinta Doctor,wani abu ne ya faru?me yake damunta ne? ya k'arasa da jero masa tambayoyi,Hamza ya bi Khaleel da kallo kawai,Sai Likita ya mik'owa Khaleel hannu ya kama hannun Khaleel d'in yana girgizawa cike da fara'a,murya a sake ya ke cewa.
"Congratulation....Ina taya ka murna matarka tana d'auke da cikin wata Uku...shine ya sabbaba mata shiga cikin wannan yanayi"
A take Khaleel ya zabura ya mik'e cikin d'imaucewa da gigicewa idanuwan sa a warwaje yake kallon Likita da kuma Hamza......!
************
A firgice Aunty Sajida ta juya jin an turo k'ofar d'akin da k'arfi an shigo,Khaleel na ya shigo da sauri ya nufi in da Hidaya ke kwance tana baccin wahala,yana zuwa ya zube gaban gadon ya kwantar da kansa gefen da take kwance tare da fashewa da wani matsanancin kuka,sai surutai yake cikin gigicewa da d'imaucewar k'wak'walwa.
"Ki yafe min matata hak'ik'a nayi nadamar abinda na aikata...kuma zan kasance cikin nadama har lokacin da zan bar duniya...shikenan ba zan cigaba da rayuwa da ke ba?ba zan kasance muhalli d'aya tare da ke da tsatsona da ke jikin ki ba?hak'ik'a na tafka asara...na san abinda zai fito daga jikinki ba zai tab'a yafe min wulak'anta masa mahaifiya da nayi ba...tabbas Allah mai hikima ne da basira cikin dukkan abin da ya tsara...
Sai ya sake fashewa da kuka yana cigaba da surutai kala kala,Aunty Sajida dai a tsorace take,ta tsurawa Khaleel idanu k'irjinta na bugawa,juyawa tayi ta dubi Hamza da shima ya shigo d'akin jikinsa a sanyaye,idanuwansa cike suke da tarin k'wallar tausayin Khaleel,har gaban gadon yaje ya sunkuya ya d'ago Khaleel d'in ya mik'ar da shi tsaye,hannu ya kai yana share masa hawaye tare da girgiza masa kai,wani hawayen ya sake kwararowa Khaleel,ya bud'e baki cikin kyarmar murya ya cewa Hamza .
"Aboki ya zanyi?"
Hamza ya ce "Godiya ga Allah za ka yi ,ba kuka ba,murna ya kamata kayi Khaleel domin mun samu k'aruwa a lokacin da bamu yi zato ba"
Sai Khaleel ya sa kansa a kafad'ar Hamza hawaye na tsiyaya,cikin tabbatarwa ya ce wa Hamzan "Ina murna Aboki,tabbas ina jin duk duniya yau babu wanda ya kaini farinciki,domin na samu abinda ban tab'a tunanin zan samu a rayuwata ba,kuma na sameshi ne daga wacce nake matuk'ar so da k'auna,sai dai kuka ya zama dole a gareni Aboki,k'addara ta rabani da ita a lokacin da yafi dacewa ace ina tare da ita,ko domin in bata kyakkyawar kulawar da ta dace akan nauyin da na d'ora mata,Aboki na zalunci yarinyar nan,ban kyauta mata ba,ya zanyi?don Allah ka fad'amin ya zanyi?
Rungumeshi Hamza yayi k'am yana runtse idanu,yana jin kamar tausayin Khaleel zai kasheshi,jin muryar Aunty Sajida suka yi cikin rud'u tana fad'in "Wai menene ya faru ne?menene ya faru Hamza?"
Hamza ya zaunar da Khaleel gefen gadon da Hidaya ke kwance,saboda jin da yayi jikin Khaleel d'in na rawa sosai,Khaleel ya jingina kansa jikin bangon d'akin idanuwansa kan Hidaya yana kallon yadda take sauke numfashi,ya dinga kallon lafaffen cikinta yana mamakin wai akwai ajiyarsa a ciki,tabbas Allah mai hikima ne,bai san lokacin da wani kukan ya b'alle masa ba.
Shi kam waiwayawa yayi ya dubi Aunty Sajidasannan yayi k'asa da kai yayi magana A hankali.
"Aunty Doctor ya sanar da mu cewa Hidaya na da juna biyu,ma'ana tana d'auke da cikin Khaleel na wata uku"
Dafe k'irji Aunty tayi tana salati,ta juya tana kallon Khaleel da ke kuka sai taji mugun tausayinsa wanda bata tab'a ji ba,hawaye ya kwararo mata,bata ma san lokacin da ta dubi Hamza ta jefa masa wata tambaya ba a d'imauce.
"Hamza kaine malami...wai shin babu ta yadda za a yi a gyara auren Khaleel da Hidaya su koma ne?Wallahi tausayinsu nake ji,yana son matarsa ita ma tana son mijinta,k'addara ce kawai tayi musu shigar sauri,wallahi tunda suka rabu bata da sukuni ko a Gombe bacci ma bata iya yi sai yawan tunani da kuka,wataran ma idan ta samu baccin sai dai kawai kaji tana ambatar sunansa kamar mai mafarki alamun dai shine a ranta,ka duba Hamza idan da akwai wani hadisi ko aya da suka yi bayani akan irin wannan sakin da yadda za a gyara shi don Allah ka taimaka,kar yaran nan su rasa hankalinsu domin damuwar tayi yawa" ta k'arashe maganarta da kuka sosai.
Hamza yayi shiru,kafin ya d'ago idanuwansa da suka sauya launi suka yi jajir,hawaye ya kwanta a cikinsu,a sanyaye ya ce wa Aunty Sajida.
"Ni ba Malami ba ne Aunty,sai dai na kasance d'alibi mai neman sani musamman akan harkar addini,na karanta Alk'ur'ani da sauran litattafai na musulunci,tabbas a gabana kuma a gabanki Khaleel ya saki Hidaya,kuma ba saki d'aya yayi mata ba saki uku yayi mata,har maimaitawa ya dinga yi a lokacin,to akwai malamai da suka rabu gida biyu akan irin wannan sakin, wad'ansu suna cewa wanda ya saki matarsa saki uku a kalma daya ko majlisi daya to saki daya ne yake afkuwa.
Wannan shi ne ra'ayin da aka samu daga Ibn Abbas, kuma ita ce fatawar irinsu Ibn Taimiyya da dalibinsa Ibnl Kayyim da sauransu.
Amma abin da jumhur na malamai suka tafi a kai shi ne, idan mutum ya saki matarsa da irin wannan siga to ta saku saki uku, ba zata sake halatta gare shi ba har sai ta yi tabbataccen aure kuma mijin ya d'and'anta, kamar yadda Allah madaukaki yake fada:
*"فإن طلقها فلا تحل له من بعد حتى تنكح زوجا غيره، فإن طلقها فلا جناح عليهما أن يتراجعا إن ظنا أن يقيما حدود الله"*
(Idan ya sake ta (saki na uku) to ba ta sake halattuwa a gare shi har sai ta auri wani mijin ba shi ba, idan kuma ya saketa (shi mijin na biyu) to babu laifi a kansu su yi kome.......).
Wannan k'aulin dukkanmu akansa muke,kuma shi muke bi,Khaleel ya saki Hidaya saki uku,dan haka ba zata sake halatta a gareshi ba har sai bayan ta auri wani mijin ya d'and'ana zumarta,daga nan ne kuma idan sun rabu da mijin,to ta halatta a wajen Khaleel,a wannan lokacin za su iya komawa auren su.
Aunty ta share hawayenta ta cigaba da duban Hamza,tabbas ta gamsu da bayaninsa,to amma tunda akwai mafitar da ya fad'a ko ita za a gwada?shiyasa ta sake cewa Hamza.
"Na fahimta Hamza,to amma tunda akwai mafita me zai hana mu sami wani ya auri Hidayan, ko bayan ta haihu ne,in yaso ko wata d'aya tayi sai ya saketa ta dawo hannun Khaleel d'in ko?ina ga hakan zai fi ko dan mu ceto rayuwarsu Hamza"
A tsorace Hamza ya dubeta,cikin mamaki yace .
"Aunty Auren KISAN WUTA kenan fa"
Ta jinjina kai tare da cewa "Eh shi nake nufi Hamza,ai wai dan mu ceto rayuwar wad'annan masoyan"
Hamza ya ce.
"Mu ceto rayuwar su ko mu k'ara dilmiyar da su cikin halaka? Aunty Sajida bud'e kunnuwanki kiji ni.
Auren kisan wuta d'aya ne daga cikin lalatattun aure da addini ya haramta, Manzon Allah (S.A.W) Ya la'anci wanda yake yi da wanda aka yiwa, a cikin fad'in sa Annabi (S.A.W) ya ce:
*"لعن الله المحلل والمحلل له"*
(Allah Ya la'anci mai halattawa (Auren kisan wuta) da wanda aka halattawa)
Idan aka yi shi to matar ba ta halatta ga duka mazan, na farko da na biyun.
Ko da daga baya mijin ya canja niyyarsa daga auren kisan wuta sai dai ya saketa a sake sabon aqadi, idan kuma ya sadu da ita to sai ta yi cikakkiyar idda ta jini/tsarki uku ga wacce take ala'ada, ko wata uku ga wacce ba ta yi.
Idan kuma mijinta na farko yana son mayar da ita to sai ta sake yin wani auren da shari'a ta amince da shi kuma mijin ya kwanta da ita, idan ya saketa ta yi idda to sai ya shiga zawarci a sake sabon aqadi.
Wallahu a'alam.
Don haka Auren kisan wuta ba abune me kyau da addini ya yarda da shi ba,babu kyau aikata shi,babu wata hanya da za su bi tilas suyi hak'uri da k'addararsu,kamar yadda duk wani mutumin k'warai yake wa Allah biyayya akan jarrabawar da ya d'ora masa.
Take Aunty Sajida ta sake gasgata Hamza,ta tabbatar Hamza d'an baiwa ne,bawan Allah ne na gari wanda baya bin son zuciyarsa sai abinda Allah da manzonsa suka umarce mu....
***************
Lokacin da suka koma gida su Umma suka ji Labarin Hidaya na da ciki ba k'aramin kad'uwa suka yi ba,sun tausayawa Khaleel da Hidaya sosai a bisa wannan babbar k'addara da ta afka musu,ita kanta Hidayan tunda taji labarin tana da juna biyu ba k'aramin firgita tayi ba,ta yi kuka ta gode Allah,tausayin Khaleel na cin zuciyar ta,Khaleel kuwa ranar sai da ya sha maganinsa na ciwon zuciya,jin yadda k'irjinsa ya rik'e sosai,kowa dai ya tausaya musu,sai dai ta wani b'angaren ana murna da samun cikin da Hidayan tayi,a matsayin kyauta daga Allah.
Khaleel ya cigaba da k'arfafa zuciyar sa saboda Shari'ar da za su fuskanta a washegari,daren baiyi bacci ba sai salloli da addu'a kan samun nasarar ubangiji akan shari'ar,bashi ba ma hatta Hamza da ragowar mutanen gidan babu wanda yayi cikakken bacci a wannan daren,sun rayashi da salloli da addu'o'i bisa rok'on ubangiji kan samun nasara,saboda ita shari'a sab'anin hankali ce sai an had'a da addu'a.
*************
K'arfe Goma sha d'aya na safiyar washegari sun hallara a Kotu,inda Daddy da Alhaji Maude ke tsaye wajen amsa tambayoyi bisa ga manyan Laifukan da suka aikata,aka fara bata kashi tsakanin Lauyan da ke kare Alhaji Maude da Lauya Ibraheem Khaleel mai kare b'angaren masu k'ara,shi kam Daddy ma bai d'auki wani Lauya ba,ba tare da kuma b'ata lokaci ba ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su,amma Alhaji Maude yak'i amsawa ya k'aryata cewar shi bashi ne ya kashe Sulaiman da Taufik' ba,sharri kawai Mudassir yake masa,cike da k'warewa Khaleel ya dinga jerowa Alhaji Maude tambayoyi wad'anda suka firgitashi ya dinga inda inda,Alhaji Maude ji yake tamkar ya shak'e Khaleel ya mutu,aka kirawo sunan Mummy nan da nan ta fito,ta bayar da shaida akan dukkan abinda ta sani,sai lauyan Alhaji Maude yayi mata tambaya akan cewa a labarinta da takardar da wannan mutumi ya bata ai sunan Alhaji Mudassir ta gani,to ya akayi ta jingina kisan akan Alhaji Maude,anan ne Mummy tayi shiru tana tunanin amsar da zata bayar,take alk'ali ya d'aga shari'ar zuwa wata Uku masu zuwa,kuma yayi umarni a tafi da Alhaji Maude da Daddy gidan ajiya a ajiye su har zuwa lokacin da kotu za ta cigaba da zama,kuma alk'ali ya bada umarnin a kamo mutanen da ake zancen sune suka yi kisan,haka nan yayi umarnin a tafi da Mummy da jami'an tsaro domin a binciko wannan jakar kud'i da ke b'oye tsawon shekaru,da wannan aka tashi daga zaman kotu na wannan rana.
Y'an sanda na shirin tafiya da su Daddy sai Khaleel ya nemi yana son yin magana da mahaifinsa,da k'yar ma suka yarda dan dai sunga Lauya ne,suka koma gefe guda suka tsaya,Khaleel ya dubi mahaifinsa cikin rauni ya ce.
"Daddy kayi hak'uri da duk abinda zai faru,gara ka karb'i hukuncinka tun a duniya kafin a je lahira"
Daddy ya jijjiga kai cike da k'aunar d'an sa ya ce" Na shiryawa hakan Khaleel,kuma zan baka duk wani goyon baya dan ganin ka samu nasara a wannan shari'a in Allah ya yarda"
Khaleel yayi murmushi sannan ya ce "Na gode Daddy,yanzu ma wani taimako nake son kayi min,zan baka wata y'ar na'ura y'ar k'arama ce sosai dan girmanta ko rabin d'an yatsa baiyi ba,zaka sakata a aljihunka kullum ka kasance tare da ita,a duk lokacin da zaka yi magana da Alhaji Maude ya kasance ka latsa ta,za ta d'auki dauki duk wata magana da za ku yi,wannan shaida ce me k'arfi da muke son mu sameta a wajenka,domin na tabbatar Alhaji Maude zai nemeka da maganar,kuma ina so ka biye masa domin kuyi ta,ta nan za mu samu wasu abubuwan da za su taimaka mana"
Daddy ya dafa kafad'ar Khaleel ya saki murmushi,sannan yace masa "Kar ka samu damuwa Khaleel,ka bani na'urar,kuma in sha Allahu za ka samu duk wasu bayanai da kake so a tare da ni"
Khaleel ya d'auko na'urar ya dank'awa Daddy a b'oye,Daddy ya karb'a ya zura cikin aljihunsa,sannan suka rungume juna kamar ba za su rabu ba,a lokacin ne y'an sanda suka k'araso domin sun gaji da jira suna so su tafi da Daddy,ba tare da b'ata lokaci ba Daddy ya saki Khaleel tare da yi masa kyakkyawan murmushi,y'an sanda suka saka shi a gaba har zuwa wajen motar su,sai lokacin Daddy ya juyo ya kalli Aunty Kubra da ke gefe tana hawaye,ya girgiza mata kai ya ce mata.
"Kiyi Hak'uri Kubra" Iya abinda yace mata kenan aka kad'ashi cikin mota,take motar ta tashi aka wuce da Alhaji Maude da Daddy.
************
A washe gari ne kuma jami'an tsaro da Mummy da Khaleel da Hamza suka nufi Abuja,tsawon shekarun nan gidan Alhaji Taufik' yana nan inda yake,babu abinda ya tab'a shi,yana dai k'arkashin kulawar gwamnati ne,sai dai gidan sosai yayi k'ura da datti ta inda sai da suka sa face marks suka rufe bakin su da hancin su,ko ina k'ura da datti da yana da k'wari kala kala,a haka suka turmutsa suka shiga har cikin d'akin Mummy wanda ta barshi tsawon shekaru,Mummy bata tsaya ba har sai da ta dangana da su cikin vantlation d'in da ta bunne wannan jaka.
Mutum biyu ne suka hau fasa gurin,yayin da su Mummy suke tsaye a gefe suna kallo,cikin mintoci sai gashi an hak'o wannan jaka a inda aka binneta,mamaki sosai su Hamza da Khaleel suka shiga lokacin da suka yi arba da jakar,suka kalli Mummy suna jinjina mata,yayinda ganin wannan jaka ya tonowa Mummy mikin da ke zuciyarta ta dinga zubar da hawaye mai tsananin zafi su Hamza na lallashin ta.Sai da suka kammala komai jakar tana hannun ma'aikata sannan suka kulle gidan suka dawo Kaduna a ranar.
Abubuwa sun cigaba da faruwa na farinciki da akasin haka,inda Hidaya ke cikin wani irin yanayi,sai dai ta fawwalawa Allah komai ta mayar da hankalinta kan rainon abinda ke cikinta,dan ma bata wani laulayi sosai sai d'an abinda ba za a rasa ba,haka Khaleel yake daurewa zuciyarsa yana zuwa ganinta da duba halinda take ciki,duk da kullum idan ya ganta baya samun nutsuwa sai sunyi kuka sun zubda hawaye,har cikin ta ya isa wata hud'u da kwanaki a lokacin da ta fara zuwa Awon ciki a asibiti,duk wani nauyinta kuma Khaleel ne ya d'auke,baya barin Hamza da Umma suyi mata komai,tuni kuma su Mummy suka koma Kaduna ko domin aikinta,Aunty Sajida kuma ko domin mijinta da yaranta,sai dai ba a cikakken sati biyu su kan zo Kaduna domin a ga juna a sada zumunci,amma ita Hidaya tana Kaduna wajen Ummanta,bata koma Gombe ba.
Khaleel yana zuwa ganin Daddynsa,da shi da Aunty Kubra,har ma da Hamza da Umma,Hidaya ma ba a barta a baya ba,kuma duk lokacin da suka je indai Daddy yaga Hidaya ya dinga hawaye kenan yana bata hak'uri,har sai ita ma ya sakata hawayen,Daddy yana tausayawa Khaleel da Hidaya akan rabuwar su,gashi sun samu k'aruwa a lokacin da zama ya haramta a gare su.
Lokaci na ta tafiya har wata uku ta cika cif,ana shirye shiryen komawa kotu domin zama na biyu,saura kwana uku su shiga kotun Khaleel ya ziyarci gidan Umma domin ya ga lafiyar Hidayan,sai ya tarar Umma bata nan,Hamza ma baya nan sai Hidaya kawai a gidan,tana zaune a tsakargida tana wanke wanken kwanuka,Sallamar Khaleel ta sa ta juya tana amsawa cikin fara'a sannan ta zarce da cewa.
"Sannu da zuwa Uncle Khaleel"
K'arasowa yayi gabanta ya tsuguna yana janye kwanukan,sannan ya kalleta yana d'an b'ata rai ya ce "Ba na hanaki yawan aikace aikacen nan ba?kina fama da kanki amma ba zaki dinga hutawa ba,ni fa idan na ganki kina aiki hankalina tashi yake yi Hidaya"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa,sannan ta ce "Babu fa wani abu da yake damuna Uncle Khaleel,haka ma Ya Hamza sai yai ta hanani yin komai,kuma a asibitine ake ce mana mu dinga motsa jikinmu,saboda idan haihuwar ta zo mana zamu samu sauk'i sosai"
Jijjiga kai yayi ya gamsu da bayaninta,sai ya sanya hannu a ruwan wanke wanken yana taya ta,tana ta cewa ya bari kar ya b'ata jikinshi amma yak'i,har tattare hannun rigar yayi ya cigaba,sai da ya kammala mata sannan ya bari,a hankali ta mik'e daga kujerar da take zaune da k'yar,saboda cikin ya soma girma sosai yayi tsini kamar ta kusa haihuwa,da yake Hidaya siririya ce bata da k'iba sai cikin yake rinjayarta,sai a dinga ganin kamar yayi mata nauyi,ita kuma bata jin wani nauyi sosai,yanzun ma da ta mik'e kallonta kawai Khaleel yake yi yana jin tausayin ta,sai faman ce mata yake "Sannu ...sannu da ibada kinji Hidaya..Allah ya saukeki lafiya ya rabaku lafiya" Kunya ta kamata,sai ta sunkuyar da kai tana amsawa cikin zuciyarta,ta fara kwashe kwanukan tana kaiwa ktcheen,yayinda Khaleel ya sanya tsintsiya yana share wajen da suka yi wanke wanken.
Kusan ranar a gidan ya yini,yana ta tayata aikace aikacen gidan,da zarar ya ga zata yi wani abun sai ya karb'e yace shi zaiyi,sosai ranar tayi musu dad'i kamar kar ta wuce,suna ji a zukatansu ina ma suna da aure,da kulawar da za su bawa juna sai ta ninka haka sau ba adadi,haka Khaleel ya isheta da zancen Babyn da zata haifa masa,har yana cewa idan ta haihu karb'an babyn zaiyi dan ya dinga ganinsa yana jin dad'i,tunda ya san cewar ita aure za ta yi,wannan maganar ita ta b'ata ran Hidaya ta dinga kumburi har da hawaye,wai akan me zaice za ta yi aure?ita ba wani aure da za ta yi,hakan yasa ya dinga bata hak'uri har ta sakko suka cigaba da hirar su,sai da ta kammala girkin dare da yamma da taimakon Khaleel,sannan tayi shirin shiga wanka domin taji dad'in jikinta,sai Khaleel yaji a ransa da suna da aure fa shine zai mata wankan ma,da hanzari ya kawar da wannan tunanin daga ransa,hawaye ya ciko idanuwan sa amma ya shanye dan kar Hidaya ta gani.
Da za ta shiga wankan sai Khaleel ya karb'i mukullin d'akin Hamza yace zai bud'e ya zauna a can har ta gama shiryawa,kuma zai jira Hamzan ya dawo domin akwai abinda za su tattauna da shi,Hidaya dai tana bashi mukullin ta shige ta tafi domin yin wanka,shi kuma ya bud'e d'akin Hamzan ya shige abunsa,yana shiga kan gadon Hamza ya fad'a ya kwanta rigingine yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwansa,ya jima a haka kafin ya bud'e idanuwan yana gyara kwanciyar shi,sai idanuwansa suka kai kan wani littafi k'arami mai kyau,d'auka yayi yana kallon littafin,bai san ko na meye ba amma yaji a zuciyarsa yana son ya ga abinda ke ciki,hakan ya sa ya bud'e littafin yana daga kwance ya fara duba shafin farko,ba rubutun kowa ba ne a jiki illa rubutun Hamza,hakan ya sa ya fara bin shafin farko yana karanta abin da ke jiki,a take ba da shiri ba sai ga Khaleel ya mik'e a matuk'ar razane,idanuwansa kamar su fad'o k'asa ya cigaba da karanta abinda ke cikin littafin shafi bayan shafi,cikin lokaci k'ank'ani sai ga Khaleel yayi rud'ewar da ya jima baiyi irinta ba,zuciyarsa kamar ta faso k'irjinsa ta fito,hawaye ya b'alle masa kamar an bud'e famfo,kuka Khaleel ke yi sosai har bai san lokacin da gaban rigarsa ya jik'e da hawaye ba.
Bai kai k'arshen littafin ba yaji kansa na juyawa,ba zai iya cigaba da karanta abinda ke rubuce ba,hakan ya sa ya ajiye littafin inda ya ganshi sannan ya mik'e cikin layi da cushewar tunani zai fice daga d'akin,waiwayowa yayi yaga takarda da biro akan bedside drawer,sai ya sunkuya ya d'auka yayi rubutu kad'an a jiki ya nannad'e,fitowa yayi daga d'akin Hamzan har lokacin hawaye ne ke sintiri kan kyakkyawar fuskarshi,yasa mukulli ya kulle d'akin,sannan ya nufi parlour'n Umma ya lek'a,baiji motsin Hidaya ba,hakan yasa yayi zaton ko har lokacin tana wanka bata fito ba,ajiye mata takardar yayi kan kujera,ya d'ora mata mukullin kan takardar yadda zata gani,sannan ya fice ya bar gidan ma gabad'aya zuciya cike da rauni.
Sai da Hidaya ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar shadda,sai taga cikinta ya k'ara fitowa sosai,hakan ya sa ta d'auko hijab ta sanya ta rufe jikinta,sannan ta fito parlour'n.
Da mukullin d'akin Hamza ta fara cin karo,ga kuma takarda a k'asan mukullin,hakan yasa ta sanya hannu ta d'auki mukullin ta ajiye gefe,sannan ta d'au takardar cikin mamaki ta warware tana dubawa.
*Ko da kin fito kin tarar bana nan ba wani abu bane,na samu kiran gaggawa ne shiyasa na tafi bamu yi sallama ba,kiyi hak'uri*
*UNCLE KHALEEL*
Iya abinda ta gani kenan,ta sauke ajiyar zuciya ta d'an lek'a tsakar gidan tana duban d'akin Hamza,sai kuma ta saki labule ta koma parlour'n tana zama kan kujera zuciyarta cike da sak'e sak'e,bata jima da zama ba kuma taji muryar Umma na sallama alamun ta dawo......!
Comments
Share
Vote
pls
08080049548
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.