Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 36 of 50
BABI NA SABA'IN DA D'AYA DA NA SABA'IN DA BIYU
***Wata irin muguwar zufa ce ta yankowa Ya Hamza ,gabad'aya jikinsa babu in da baya rawa yana rik'e da Hidaya tsabar tashin hankali mara misali wanda ke d'awainiya da shi,idanuwansa akan ta yana duban fuskarta da idanuwanta a rufe babu numfashi a tare da ita,d'agowa yayi cikin matuk'ar tashin hankali ya dubi Khaleel da ke tsaye hannayen sa dafe da kansa,domin maganar da Hidayan tayi kafin ta sume ta kai k'urewa wajen d'aga hankalin sa,me Hidaya take nufi da cewar Daddyn sa ne ya kashe mahaifinta? shin wanene mahaifin na ta?ya akayi Daddy ya san mahaifinta har ya kashe shi?ya aka yi Hidayan ta san haka?tambayoyi da yawa ne suka cika k'wak'walwarsa ,wanda kuma bashi da mai ba shi amsa cikakkiya sai Hidayan da furucin ya fito daga bakinta.
Bai san lokacin da ya zabura yayi kan Hidaya da ke kwance jikin Hamza a sume ba,yana isa dab da su kawai sai k'afafuwansa suka kasa d'aukarsa ya zube a gabansu,hannun sa na karkarwa ya d'aga yana niyyar aza shi jikin Hidaya,a fusace Ya Hamza ya d'ago kansa cikin matuk'ar fushi,idanuwan sa kamar gauta saboda jan da suka yi,zuciyarsa kamar ta faso k'irjinsa ta fito,ya rasa yadda zai kwatanta wannan d'umbin tashin hankalin da ya zo ya tarar,shi da ya tawo cikin farinciki da annashuwa,amma ya zo ya tarar da tashin hankalin da bai tab'a gani a duniyarsa ba.
Dab da hannun Khaleel zai isa jikin Hidayan Ya Hamza ya daka masa tsawa me bala'in k'arfi cikin hargowa,cak Khaleel ya tsaya yana bin Hamza da kallo baki a sake kamar wani shashasha,idanuwan sa a birkice,Hamza ya sake rik'e Hidaya gam a jikinsa yana wa Khaleel wani kallo mai cike da fassarori iri iri,kafin ya bud'e baki cikin matuk'ar fushi da b'acin rai ya ce.
"Idan har ka sake hannuwanka suka sauka a jikinta wallahi nine ajalin hannuwan,domin sai na kakkarya su nayi makamashin wuta da su,daman haka ka ke?daman kai azzalumi ne?daman ba son Hidaya ka ke ba kasheta ka ke son yi?Khaleel kaine yau ka fitarwa da Hidaya jini a jikinta?kaine yau ka wulak'anta Hidaya mafi munin wulak'anci?ka manta alk'awarin da kayi min?ka manta cewar ka fad'a min za ka rik'e min ita amana ko k'uda ba za ka bari ya hau kanta ba?ka manta kace min za ka zama GARKUWAR ta? ka manta kace min ba za ka bari tayi kuka ba?ka manta kace min aurenku mutuwa ce za ta rabaku?duk ka manta da wad'annan abubuwan har ka samu damar tab'a min lafiyar jikinta,ka manta ita d'in me rauni da lalura ce Khaleel?yau a gaban idona kayi wa Hidaya wannan tozarcin da ko a mafarki ban tab'a tunaninsa ba?ka saketa cikin kwana d'aya rak da aurenku,kayi mata saki mafi muni da wulak'anci,Khaleel ko kad'ai za ka rage min a duniya daga yau na barka,kuma wallahi duk da kasancewarka Lauya sai na bi kadin abin da kayi wa wannan baiwar Allah ko komai nawa zai k'are.......
Wani irin zazzafan hawaye ya zubowa Hamza,bai tab'a ganin tashin hankali irin na lokacin ba,ya kau da kai daga kallon Khaleel da ke sandare a gabansa,ya runtse idanuwa da k'arfi kafin ya fashe da wani irin kuka yana rungume Hidaya a jikinsa,cikin wata irin murya yake magana harshen sa na sark'ewa.
"Ummana kinyi gaskiya ! daman kin fad'a min babu wanda ya san mutuncin Hidaya kamar ni,babu wanda zai rik'eta amana sama da ni,babu wanda zai jure rauninta da lalurarta kamar ni,Hidaya ki yafe min,na cutar da ke da na had'aki da wanda bai san darajarki ba,wanda yayi min k'arya yace min zai zama GARKUWAR ki....ashe yayi hakan ne domin ya cim ma wanni k'udurinsa a kanki.....kwana d'aya da aurenki yayi miki saki irin na bidi'a har saki uku....!
Hawaye ya cigaba da kwarara a idanuwan Ya Hamza yana kuka sosai,yayin da ya saka gefen rigarsa fara tas da ke jikinsa yana gogemin jinin da ya b'ata min fuskata zuwa jikina....
Kamar wani gunki haka Uncle Khaleel yayi kasak'e ya zubawa Ya Hamza idanuwa,shi sam ma baya wani fahimtar abubuwan da Hamzan ya ke fad'a,abu d'aya ne ya ke ta yawo cikin kwanyar kansa yana sake hargitsa shi,wato yadda Hamzan ya ke fad'in wai ya saki Hidaya,wai da bakinsa ya furta cewar ya saketa,shi sai yake jin ma abin tamkar almara,domin shi dai bai ma san lokacin da ya furta sakin ba,Khaleel bai sake shiga tashin hankali ba sai da yaga Hamza ya juya cikin kuka yana kallon matar da ke bayan sa a tsaye hannuwan ta aka,ita ma d'in fuskarta jage jage da Hawaye,a hankali cikin raunin murya yace mata..
"Aunty za ki iya d'aukar Hidaya mu tafi ko na d'auke ta...?
Cikin Hawaye ta ce.
"D'auke ta Hamza,hannaye na ba za su iya rik'onta ba"
Hamza ya sake rungumota jikinsa ya mik'e tsaye da ita a hannayensa tamkar wata jaririya,ya cigaba da kallon fuskarta da ta kumbura yatsun Khaleel kwance kan kumatun ta,ga gefen kanta ma ya kumbura saboda yadda ya garata da garu,nan da nan wani bak'inciki da tsanar Khaleel ta kuma d'arsuwa a zuciyar Hamza,sosai yake jin ciwo a k'irjinsa da tsananin zafi..
A salub'e Khaleel ma ya mik'e yana rik'o hannun Hamza da ke d'auke da Hidaya,cikin wani irin yanayi na tamkar mai tab'in hankali da rashin nutsuwa yayi magana yana nishi.
"Aboki .....ina za ka kai min matata...!?
Wani irin matsiyacin kallo Hamza ya dank'arawa Khaleel,idanuwansa tamkar su fad'o k'asa,cikin matuk'ar fusata da gigita yayi magana .
"Sakar min hannu"
Da yake Khaleel bai tab'a ganin Hamza cikin irin wannan fusatar ba sai ya tsorata,a hankali ya saki hannun Hamzan yana ta had'iyar zuciya idanuwansa jajir hawaye ya cika su,ya k'urawa Hamzan idanu kansa tamkar ya fashe yake ji,Hamza ya kawar da kai yana jin k'unci a ransa,ya dubi matar da ke tsaye ya ce.
"Mu tafi Aunty"
Ta juya ta nufi k'ofa tana share hawayen fuskarta,yayin da Hamza ya rufa mata baya yana tafiya a hankali hannuwansa d'auke da Hidaya,sai da yaje bakin k'ofa sannan ya tsaya ya waiwayo a hankali ya dubi Khaleel da ke tsaye yana kuka da nadamar rayuwa,a hankali ya cigaba da kallonsa yana ayyana abubuwa kala kala a zuciyar sa,kafin ya girgiza kai su k'urawa juna idanuwa,Hamza yayi magana cikin wata irin murya"
"Zan cigaba da amsa sunan GARKUWAR HIDAYA a ko yaushe ! zan tabbatar da cewar nayi shari'a da dukkan wanda ya zalunceta ! ba zan bari a zalunceta ba domin amanata ce ! ni bana zalunci kuma bana shiri da duk wani azzalumi ! ina so ka sani cewa a yanzu Hidaya bata da wani had'i da kai...komai da ke tsakaninku ya k'are domin saki uku k'warara kayi mata...idan saki d'aya ne ko biyu zan barta cikin d'akinta ta kammala iddarta kamar yadda Allah (S W A)ya umarta,amma yanzu fa?komai ya k'are tsakaninka da ita Khaleel...yanzu tsakani na da kaine...ba zan d'auki hukunci da hannuna kamar yadda ka d'auka ba...amma ka sani akwai k'aramar hukuma,sannan akwai babbar hukuma wato Allah (S W A).
Sannan ya juya ya dubi Daddy da ke tsaye kai a sunkuye yana hawaye,wani bak'in Daddyn yake gani a idanuwan sa ,cikin wata irin murya ya fara magana bayan ya kautar da idanuwan sa daga kallon Daddyn zuwa kan fuskar Hidaya da take cikin rai kwakwai mutu kwakwai.
"Har yanzu ina kallonka a matsayin uba Daddy ! amma muddin na tabbatar da abin da Hidaya ta fad'a a kanka to zanyi yak'i da kai,duk da kana tak'ama da k'arfin dukiya ! to ni kuma zanyi tak'ama da Allah mahallicina da cikar izzarsa da buwayarsa domin na yak'e ka,domin ko Allah baya son zalunci ! kuma ya haramta shi a tsakanin sa mu bayinsa kada wani ya zalunci wani ! Don haka ka jira ni Daddy....!
Iya nan maganar Hamza ta tsaya,ya juya ya fice da Hidayan sa d'auke a hannunsa yana hawaye,ya bar Khaleel a tsaye yana kuka kamar ya zauce,yana jin danasanin zuwan wannan rana a duniyarsa da babu ranar da ta kaita bak'i a idanuwan sa,domin hankalinsa ya gushe bai ma san abinda ya aikata ba,Daddy kam k'afafuwansa ne suka kasa d'aukarsa,sosai jikinsa ke rawa yana neman zubewa a k'asa,kafin ya kai k'asan sai ganin Khaleel yayi yana k'ok'arin fad'uwa hannayensa dafe da k'irjinsa dai dai zuciyarsa,idanuwansa na lumshewa yana wani irin nishi mai k'arfin gaske kamar ransa zai fita,da wani irin hanzari Daddyn ya rik'o shi jikinsa yana rungume shi yana ambatar sunasa a rikice.
Khaleel ya dinga cije lab'b'ansa yana nishi saboda azabar da yake ji a k'irjinsa,idanuwan sa suna son rufewa amma k'ok'ari yake ya bud'e su,bakinsa na mugun rawa yana son yin magana amma ya rasa abin da zai cewa Daddyn,bai san ta ina zai fara ba,bai san wane kalami zai furta ba,sai dai zuciyarsa cike take da d'okin sanin shin da gaske abin da Hidaya ta fad'a gaskiya ne?shin da gaske Daddyn sa ne ya kashe mata mahaifi?
Duk wani k'arfinsa ya tattaro ya rik'e kafad'un Daddy,kallon fuskar Daddy yake wadda ta tattare tsabar tashin hankali da shiga rud'u,ga hawaye sosai yana zuba,shi tunda yake ma a rayuwarsa bai tab'a ganin Daddyn cikin irin wannan yanayin ba.
Ganin Khaleel ya kasa magana duk da yunk'urin da yake ta faman yi wajen maganar,shine dalilin da yasa Daddy ya tallabo fuskar Khaleel d'in ya zuba masa idanu,kallon idanuwan Khaleel d'in yake da suka birkice suna fidda wani irin hawaye mai zafi suna gangarowa,cikin wata irin murya me rauni Daddy yayi masa magana,kafin yasa hannun sa d'aya ya shiga share masa hawayen da suke zuba.
"D'ana Khaleel,bud'e bakin ka ka furta min duk abin da yake zuciyar ka,ni kuma nayi maka alk'awarin fad'a maka gaskiya a duk yadda ta zo "
Khaleel yayi wani irin murmushi hawaye na sake zubowa akan fuskarsa,ya rik'e hannuwan Daddy yana girgiza kai,can ya fara magana yana d'an tari,maganar bata fitowa sosai.
"Daddy kai mahaifina ne...wanda na baiwa matsayi guda biyu..wato matsayin uwa da uba tunda bani da uwa...bayan kai bani da wani makusanci da nake jin sa a zuciyata kamar Hamza...kafin kuma Hidaya ta shigo rayuwata... Daddy kullum Hamza na fad'a min darajar iyaye da matsayin su a wajen mutum...kullum shine yake umarta ta da yi maka biyayya...Hamza yana fushi dani idan na sab'a umarnin ka...kullum yana nanata min bani da kamar ka duk duniya musamman ma da ya kasance kai kad'ai nake da shi..babu mahaifiyata a fad'in duniya... A yau na yanke wannan hukunci mai zafi ne akan Hidaya dalilin ta tab'a k'imar ka...ta tab'a min mutuncinka...ni kuma ba zan iya jurewa ba...saboda kullum Hamza yana fad'a min in yi fito na fito da duk wanda zai tab'a min iyaye..domin ban da tamkar su...Sai dai a yau na manta da abu d'aya...wanda shi ma Hamza ya kan tunasar da ni akansa...ya kan ce min "Khaleel a duk lokacin da kaji ranka ya b'aci ko kana cikin fushi to kar ka yanke wani hukunci,ka ambaci (Hasbunallahu wa ni'imal wakeel)sannan kayi istigfari kace(Astagfirullah wa atubu ilaihi)to Allah zai sanyaya maka ruhinka da salama har ka samu farinciki,a lokacin ne za ka yanke hukunci abisa abinda ya dumfaroka,amma muddin baka yi haka ba,to duk hukuncin da ka yanke daga baya sai kayi danasani akan sa" Daddy ina tuna ranar da Abokina Hamza ya fad'a min wannan maganar..yau gashi na rasa shi...haka nan na rasa rabin rayuwata...
Yayi shiru yana maida numfashi hawaye na zuba,shi dai Daddy kallonsa yake yi shima yana hawayen sosai,Khaleel ya sake damk'e hannun Daddyn ya cigaba da magana cikin wahala
"A wata rana da ta shud'e Abokina Hamza ya tunasar dani azabar da Allah yake wa mak'aryata,har ma yayi min nuni da ayar nan da Allah yake cewa.
"فنجعل لعنت الله على الکذبين"
(Sannan kuma mu sanya tsinuwar Allah akan mak'aryata).
Sannan Hamza ya fad'a min cewar babu kyau iyaye suyi wa y'ay'ansu k'arya,saboda addininmu ya nuna cewa dole ne a guji yin k'arya a cikin tarbiyyar y'ay'a,domin su tashi a cikin gaskiya kuma su saba da ita,hakan zai sa y'ay'a su saba da fad'ar gaskiya da aiki da ita,to a yau ina so ka fad'a min gaskiya mahaifina,domin ka zama cikin wad'anda Allah yake sakawa gaskiya da gaskiyar su.
"ليجزي الله الصدقين بصدقھم"
"Daddy ina so ka fad'a min gaskiya...me ka sani game da Hidaya...?shin da gaske kaine ka kashe mahaifinta...?shin wanene mahaifin na ta...?Don Allah Daddyna ka fad'a min kafin ruhina ya bar gangar jikina....!
Wani irin fashewa da kuka Daddy yayi,hawayensa na sauka akan fuskar Khaleel da ke tallafe da shi.
Comments
share
vote
pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.