Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 50
*BABI NA ASHIRIN DA BIYAR DA NA ASHIRIN DA SHIDA*
WATTPAD:Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
A hanzarce suka waiwayo suna duban ta saboda basu san da zuwan ta ba,ta na tsaye bakin k'ofar jikinta jagab duk ta jik'e da Ruwan wanke wanke,jikinta na D'an rawa kad'an alamar ta fara jin sanyi,Umma ta dubeta ta k'ak'aro murmushi tace.
"Yanzu haa kika jik'a jikinki da ruwa Hidaya?to muje na sauya miki kaya saboda naji ana cewa ba a son masu irin lalurarki suna zama da jik'ak'k'un kaya"
Mik'ewa tayi tana kama hannun Hidayan za su fice,ta waiwayo ta dubi Hamza da ke zaune kansa a k'asa tace.
"Ka dai cigaba da dubawa ko za a dace a ganta,bari na sauyawa Hidayan kayan jikinta"
Ya jijjiga kai ba tare da yayi magana ba,kuma bai d'ago kansa ba,har suka fice Hidaya na waiwayen sa tana kallon sa.
Kafin Umma ta sauyawa Hidaya kaya tuni Hamza ya birkita d'akin sa Neman takarda,amma ko mai kalarta bai gani ba balle ita,duk ya gigice ya rasa ya zai yi ma,haka ya tattara ya hak'ura ya nufi cikin gida parlour'n Umma domin a san mafita.
Yana sallama Hidaya na zurowa da gudu tana nuna masa kayan da aka sauya mata,tana tambayar sa wai tayi kyau?yayi malalacin murmushi yana jinjina mata yace.
"Kin yi kyau K'anwata sosai"
Ta fara murna tana biye da shi har ya zauna kan kujera,ta fara k'ok'arin hayewa cinyar sa,da hanzari ya hanata hakan ya nuna mata kusa da shi yace.
"Zauna a nan kinji Hidaya"
Ta yi shiru tana duban sa k'uri da idanu,ya sake magana babu walwala a kan fuskar sa.
"Ki zauna a nan nace ko"
Ta tafi a hankali ta zauna,tayi kasak'e duk ranta a jagule ganin babu fara'a a fuskar Ya Hamzan ta,ganin yadda tayi shiru har da D'an tagumin ta sai yayi murmushi ya kalleta yace.
"Hidaya…..
Ta d'ago ta kalleshi tana k'ifk'ifta idanuwa,ya karya wuya yace.
" Fushi kika yi da yayan ki ne?"
Girgiza kai tayi ,Hamza yace.
"To D'an yi murmushi na gani mana"
Aikuwa sai ta saki murmushi mai kyau da ya sa Hamza cikin nishad'i,har bai san lokacin da ya zaro wayar sa a aljihu ya k'yasa mata photo ba,ya d'auketa wajen kala shida,ita kam Hidaya sai canja salo take tana wani iyayi,shi kuma yana dariya.
A lokacin Umma ta fito daga bedroom tana kallon su,sun shagala cikin nishad'i sosai,sai da tayi gyaran murya sannan suka Ankara,Hidaya da tafi da gudu da wayar Hamza a hannun ta ta na nunawa Umma hotunan da ya d'auketa ,Umma ta karb'a ta na dariya tace.
"Iyen ba,Aikuwa y'ammatan nawa tayi kyau sosai"
Ta k'yalk'yale da dariya ta na zama a jikin Umma bayan Umman ta zauna,Hidaya ta maida hankalin ta kan wayar tana wasa,Umma kuma ta dubi Hamza tace.
"Ka ga takardar kuwa?"
Ya girgiza kai cike da damuwa yace.
"Banganta ba Umma,na yi iya duba amma ko k'yallinta ban gani ba,abin ya d'aure min kai sosai"
Umma ta yi shiru,sai can tace.
"To yanzu ya za a yi kenan Hamza….
Ya jefa hannuwa yace.
" Ban sani ba Umma,wallahi ni duk kaina ya kulle ma"
Tayi ajiyar zuciya da tunani iri iri a ranta,tun jiya take addu'ar Allah yasa Hidaya ta zauna tare da su,Hamza ne kad'ai rabon da ta samu a duniyar ta,Wanda ya kasance maraya tun yana cikinta D'an wata biyar,Hamza ne komai na ta kamar yadda ta zama ita ce komai na sa,Ruwa da iska,zafi da sanyi,bazara da damuna duk suna tare,komai shi yake mata,idan bata da lafiya shine mai lura da ita,wani abin ma bai kamata yayi mata ba a matsayin sa na namiji,duk da kasancewar sa D'an cikin ta,amma wani abin dole sai Y'ar uwarta mace,duk wata mace tana buk'atar Y'ar uwa mace ko d'iya mace domin tallafawa juna a bisa wasu larurorin,shiyasa taji a ranta tana buk'atar zaman Hidaya tare da su,haka nan tana tausayawa Hidayan a bisa rayuwar da ta tsinci kanta,ga lalura ga kuma rashin dangi,kulawar da za a bata a gidan Marayu ba Lallai ta gamsheta ba,duk da su d'in ma ba wani k'arfi ne da su ba,amma tana tunanin da taimakon Allah za su iya rik'e Hidayan domin ta rayu da su,bata sani ba ko Allah ne yayi nufin amsa mata rok'onta shiyasa aka nemi takardar aka rasa,wadda kuma tilas sai da ita za a kai Hidayan gidan Marayun,ba tare da b'ata lokaci ba kawai Umma taji Zuciyar ta ta yarje mata su zauna da Hidaya har zuwa lokacin da Allah zai bayyana gaskiya akan lamarin ta.
Hamza dai yana ta kallon Umma ganin ta yi shiru bata ce komai ba,hakan ya sa yayi magana cikin sanyin murya.
"Umma kinyi shiru baki ce komai ba,yanzu ya za mu yi kenan? Ko komawa kangon zan yi ma gani ko har yanzu Mummyn Hidayan tana wajen?
Umma ta sauke numfashi ta dubi Hamza,cikin karsashi tace masa.
" Ni fa ina ganin Allah yayi nufin bamu kyautar Hidaya ne domin mu rayu tare da ita na wani lokaci,abin da nake ganin zai fi kawai shine,mu rik'e Hidaya mu zauna tare da ita a gidan nan,duk ma Wanda ya tambayeni a kanta zan shaida masa cewar Y'ar k'anwata ce aka bani ita daga nesa domin na raineta,tunda dai bani da wasu y'an uwa a kusa sai na nesa,ko ya ya ma gani…?"
A razane Hamza ya d'aga kai ya dubi Umma jin maganganun ta,Abubuwa biyu suka had'e masa lokaci guda,tsananin fargaba!da kuma mad'aukakin farinciki!
Ya dad'e a haka Zuciyar sa na kai komo bisa ga zab'in Umma,cikar farincikin sa shine zaman Hidaya tare da su,amma kuma Alk'awari ya d'aukar wa mahaifiyarta cewa zai kai ta gidan Marayu,bai sani ba ko akwai babban dalilin da ya sa ta nemi hakan gareshi,idan har bai kai ta ba ya karya alk'awari kenan?shikenan ya shiga sahun munafukai?to amma idan maslaha da kyakkyawar rayuwa yake nemawa Hidaya an ya ta cancanta da za ma gidan Marayu?wad'annan tunane tunane su ne suka damu ran Hamza har ya ji kansa ya fara ciwo,amma da ya tuna Allah mai bada mafita ne akan komai sai ya sauk'ak'awa ruhin sa,yayi wa Umman sa kyakkyawan kalami ta hanyar dubanta da cewa.
"Hanzarin ki mai kyau ne Umma na ,Sai dai akwai k'alubale tattare da hakan,abin da nake gani zan yi istihara akan lamarin,duk abin da yafi alkairi Allah ya zab'ar mana,idan zaman ta alkairi ne a garemu da ita kanta Allah ya tabbatar, idan kuma babu alkairi Allah ya musanya da mafi alkairi"
Umma ta ji dad'in abin da Hamza yace,cikin farinciki tace.
"Ameen ya Allah Hamza,zab'in Allah kam shine zab'i mai kyau ba son zuciyoyin mu ba"
Da wannan suka rufe maganar.
**************
Kwanan Hidaya Uku a gidan,tuni ta sake tamkar gidan su tana walwala sosai,yaran layin da suke shigowa har sun zama k'awayen ta,mamakin su Umma bai wuce yadda Hidaya ta fara mantawa da zancen Mummyn ta ba,ba ta cika tunawa da ita ba.
Hidaya Yarinya ce mai hankali da nutsuwa,sai dai akwai yawan shagwab'a da son wasa,wani zubin Hamza har gajiya yake da wasan ta,in dai yana gidan
bata da abokin wasa sai shi,wani zubin ficewar sa yake ya gudu ya bar mata gidan,idan ya dawo kuwa ta dinga shagwab'a kenan har da kuka,sai ya sha aikin lallashi tukun take shiru.
A tsawon wannan kwanakin da Umma da Hamza suna ta addu'a da istihara,babu abin da zuciyoyin su ke kai irin k'ara jin son zaman Hidaya tare da su,shiyasa kawai suka barwa ransu cewar su cigaba da rik'on Hidaya a wajen su.
Umma bata da yara,amma kuma gidan ta akwai farinjinin yara ko Dan Hamza yana da son yara,kuma ita ma Umman haka,musamman da yake ta iya kitso,yara suna shigowa tana yi musu musamman na layin,kuma bata karb'ar kud'i,domin Umma akwai karamci da mutumci,hakan yasa take zaune da mutane lafiya a unguwar,kuma tana da jarinta a Hannu Wanda Khaleel ya bata,tana saro atamfofi da laces da dai kayan mata duk tana siyarwa,gidajen masu kud'in layin duk suna siyan kayan ta,hakan yasa asirin su yake a rufe.
Satin Hidaya biyu a gidan idan ka ganta za ka d'auka tayi shekara ne,matuk'ar Sabo suka yi ta yadda suke ganin ba za su iya rabuwa da ita ba,a lokacin Hamza ya samu Umma da zancen yana so ya nemarwa Hidaya School wadda za ta dinga zuwa saboda cigaban karatun ta,saboda ya lura yarinyar tana da k'ok'ari sosai,kuma kullum sai tayi masa maganar makaranta,musamman idan taga ya shirya zai tafi ta sa makarantar,lokacin Hamza yana jami'a level 100 yana karantar mass communication.
Lokacin da ya samu Umma a parlour'nta tana zaune tana ware wasu atamfofi da zata aiki Hamza ya kai mata tasha,za a tura su gurin wata Costomer d'in ta a Gombe state,sai da ta kammala sauraren sa sannan ta amsa masa da cewa.
"Hakan na da kyau,sai a nemi makaranta mai kyau a sakata,amma Mara nisa wadda za ta iya zuwa da kanta ta dawo da kanta ko?"
Ya jijjiga kai yana taya ta zura kayan a Leda.
Ta sake magana tace.
"To yanzu nawa kake gani zai isa ayi hidimar karatun ta da su?in yaso sai na ware kud'in na baka,domin babu laifi watan nan na samu riba da yawa Hamza"
Yayi murmushi yace.
"Alhamdulillah haka akeso Umma,Allah ya k'ara sakawa kasuwancin ki albarka,amma ki bar kud'in ki zan yi wa Hidaya komai insha Allah"
Ta tsare shi da idanu da kallon tuhuma tace.
"Me yasa baka son na dinga yiwa Hidaya Hidima ne?komai nace zan mata sai kace kai za ka yi?a sanina kai d'in karatu kake ba wata Sana'a ba,har yaushe za ka iya d'aukar d'awainiyar wani a kanka?"
Da sauri ya tare ta cikin tausasawa.
"Ba haka bane Umma na,bana son na yi ta saka ki kashe kud'i ne akan abin da bakiji ba baki gani ba,ni ne na d'auko Hidaya na kawota gidan nan,ni ya kamata naji da d'awainiyar ta kar na d'ora miki,amma kiyi hak'uri don Allah Umma"
Tayi murmushi tace.
"Ai duk abin da ka kawo tamkar ni ce na kawo Hamza,ka daina kokonto akan hakan,ni Hidaya jin ta nake a raina tamkar kai, babu abin da babu zan mata ba"
"Na gode Umma na" ya fad'i hakan cikin k'ayatacciyar fara'a da ta fito da kyawunsa fili,Sannan yace da Umman.
"Ina Hidayan ne na ji ta shiru?"
Ta nuna masa bedroom tana cewa.
"Tana ciki tana kwalliya,wai yau Hansa'u take partyn Y'ar tsanarta,shine take ta kwalliya wai don tafi kowa kyau….
Hamza yayi dariya yana mik'ewa da fad'in.
" Lallai Ashe yau za mu sha party kenan?bari na lek'a na gano kwalliyar y'ammata"
Umma tayi dariya tana cigaba da had'a kayan gaban ta,shi kuma ya nufi bedroom d'in Umma ya d'aga labulen yana sallama.
Can kan kujerar gaban dressing mirror ya hangota zaune tana kwalliya,ta damb'ara powder duk tayi dabbara dabbara,ga jambaki duk ya b'ata mata gefen baki,kwalli kuwa har k'asan idanuwa da gefe wai tayi hawayen masoya,tun shigowar sa bata lura da shi ba ta na ta sake lamb'ata Abubuwa a fuskar ta,kallon fuskar ta yake yi yana k'unshe dariya,kamar wadda za ta dandali gad'a,bai san lokacin da dariyar ta sub'uce masa ba,k'arar dariyar sa yasa ta waigowa a hanzar ce……..!
Comment
Share
Vote
Pls
*TYPING*📲
✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR* 👇
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)
*DA KUMA*
GARKUWA BIYU
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.