Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 50
*BABI NA ASHIRIN DA D'AYA DA NA ASHIRIN DA BIYU*
WATTPAD:Hassana3333
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
K'arfe biyu na dare ya farka,bayan ya shiga toilet d'in d'akin sa yayi tsarki sai ya d'auro alwala,sallolin Nafila raka'a goma sha biyu ya gabatar,bayan ya idar yayi karatun alk'ur'ani,sannan yayi addu'o'i masu tarin yawa,har ya samu kansa da yiwa Hidaya addu'a ta fatan alkairi da samun sassauk'ar Rayuwa a gidan Marayu,haka nan yayi wa Mahaifiyarta addu'a akan duk in da take Allah ya tsare gabanta da bayan ta,sai wajen k'arfe uku da rabi sannan ya koma barci,bai jima da kwanciya ba aka fara kiraye kirayen sallah,haka ya mik'e bacci cike fal a idonsa,ya d'aura alwala yayi raka'atanil fijri,sannan ya bud'e d'akin sa ya fito.
Har k'ofar Umma yaje ya D'an bubbuga mata,bai jima ba ta taso ta bud'e tana muttsika idanu,yayi murmushi ya kalleta yace.
"Umma barcin bai isheki bane?ga shi har za a ta da sallah a masallaci"
Tayi Hamma ta dubeshi tace.
"Ashe har lokaci ya tafi haka,bari to nayi hanzarin d'aura alwala,Masallaci za ka tafi ne?"
Ya amsa yana gyara zaman dadduma a kafad'ar sa.
"Eh Umma Masallaci za ni,dafatan dai Y'ar rigimar nan bata hanaki bacci ba?
Tayi murmushi tace.
" Wai Hidaya?Ai yadda kasan matacciya saboda bacci,ko motsawa bata yi ba baccinta take cikin kwanciyar hankali wallahi"
Ya jinjina kai yana jin dad'i sannan yace.
"Alhamdulillah naji dad'in hakan Umma,ina ta fargabar kar tayi miki kuka Ashe ita baccinta ma ta sha,Lallai ta kyauta da bata wahalar min da Umma na ba"
Umma tayi murmushi, Yayi mata sallama ya wuce masallaci,ita kuma ta koma bedroom domin sallatar Asubahi.
Ya dad'e a masallaci yana Lazimi,sai da gari ya fara haske sannan ya dawo gida,ya koma d'akin sa ya D'an kwanta, bai ma san lokacin da barci ya sake d'auke shi ba.
K'arar kukan Hidaya ne ya farkar da shi,ya mik'e yana salati da addu'ar tashi daga barci,da k'yar ya mik'e ya fad'a toilet yayi brush ya wanke fuskar sa sannan ya fito,bai zauna ba sai ya wuce tsakar Gidan in da yake jiyo kukan Hidaya.
Tana tsaye d'aure da tawul a jikinta,da alamun wanka Umma tayi mata,fuskarta ta k'ara haske sosai,sai dai idanuwanta sun sauya kala duk sun yi ja saboda kuka,sai shesshek'ar Kuka take yi,bata kula da shi ba har ya k'ara so bayanta,lokacin Umma ta fito daga parlour'n ta da man shafawa a hannun ta,tana ganin Umma ta fito ta kuma fasa kuka kamar wadda aka ciza,ta juya da sauri tana kuka,kawai sai tayi arba da Hamza yana k'arasowa,ta ja wata ajiyar zuciya ta tafi da sauri ta rik'eshi tana kwantar da kanta a jikinsa,ya tsaya sakato suna kallon juna shi da Umma.
Umma tayi murmushi ta nufo su tana cewa.
"Yawwa ai gara da ka ta so,tunda ta tashi take Neman ka tana kuka,da k'yar ta yarda nayi mata wanka,nayi nayi mu shiga ciki na shafa mata mai ma amma tak'i,shine na shiga na d'auko na shafa mata a nan kawai"
Yayi murmushi yana rik'o kafad'un Hidaya ya rabata da jikinsa,sannan ya tsuguna gabanta ya kai Hannu ya share mata hawaye,ita kam sai k'ok'arin b'oye fuskarta take a jikinsa,yak'i bata damar hakan,ya dubi Umma fuskar sa da jimami yace
"Na rasa yadda akayi yarinyar nan ta sanni haka Umma,daga had'uwa da ita jiya tayi min wani mugun sani kamar Wanda muka shekara"
Umma ta k'ara sakin murmushi ta jawo kujera Y'ar tsuguno ta zauna,sannan ta dubi Hamza da Hidaya ta lafe a gefen sa tace.
"Ai dole ne Hamza,kai fa kana da shiga rai,nan da nan da mutum yayi maka gani d'aya yake jin ka kwanta masa a rai,kuma ba wai don kai d'in d'ana bane nake fad'in hakan a kan ka,ah ah,kawai gaskiya na fad'a,kuma kai kana da farinjinin yara,kaga dai yadda yaran layin nan suke cika Gidan nan saboda kai,ko Dan Nasiha da tarihin Annabawa da kake musu kullu yau min,Hidaya kuma tilas ta mak'ale maka,tunda kai kad'ai ta sani a halin yanzu,Ni wallahi har tausayin ta nake yadda za ta yi Rayuwar Gidan Marayu, ga ta ba wata ishasshiyar lafiya ce da ita ba,Rayuwar Gidan Marayu kuma ba wata gamsasshiyar kulawa za ta samu ba,saboda ciwonta yana buk'atar kulawa gaskiya,na ga yadda Maman Salma take fama da Salma akan wannan cuta ta sikila,wallahi Hamza ina tausayawa wad'anda Allah ya jarraba da wannan cuta mai wahalar da Numfashi.
Ya sauke numfashi duk ransa a jagule,ba komai yasa hakan ba sai wata gingimemiyar kewar Hidaya da ya fara ji a ransa,sai yaji baya son rabuwa da ita kwata kwata,amma ya zai yi ?tilas ya rabu da ita ya cika umarnin mahaifiyarta ,tausayin ta yake ji sosai,jin ta yake a jininsa tana yawo tamkar wadda suka fito ciki d'aya.
Ita kanta Umma ta fuskanci halin da Hamza ya shiga,kuma ita ma tuni ta fara jin kewar rabuwa da Hidayan,duk da Hidayan ba wani sakin jiki tayi da ita ba amma tana jin ta a ranta sosai tamkar d'iyar ta,lokaci guda taji ta zauna a Zuciyar ta daram.
Da wayo da dabara sannan Hidaya ta yarda Umma ta shafa mata mai,sai da Hamza ya bata wayar sa yace ta rik'e masa zai je yayi wanka ya dawo,a haka Umma ta shirya ta,sai ta rasa kayan da za ta saka mata,hakan ya sa ta jira har Hamza ya kammala shiryawa cikin shadda fara tas me aikin blue d'in zare,ya taje sumar sa da ta D'an fara taruwa,ya fito sai k'amshi yake zubawa yayi fes da shi ainihin zatin kyawun sa ya dad'a fitowa.
Ko Hidaya sai da ta bishi da kallo k'uri har ya iso gabanta ya tafa hannayen sa dai dai fuskar sa,sai ta D'an firgita kad'an,sai kuma ta fashe da dariya har jerarrun hak'oranta suka bayyana,kawai sai shi ma ya tsinci kansa da dariya yana kallonta,lokacin Umma ta fito daga bedroom tana wa Hamza magana.
"Hamza ya za a yi ne?Hidaya tayi wanka babu kayan sakawa"
Ya d'ago ya dubi Umma har lokacin fuskar sa da walwala yace.
"Ai ina jin kayan cikin jakar nan fa kayan ta ne,amma dai duba ki gani Umma"
Umma ta girgiza kai tare da komawa d'akin ta sungumo jakar ta fito da ita,zama tayi ta zuge jakar tana duba kayan,sai ta tarar duk kayan Hidaya ne masu kyau sosai kuwa,yawan ci y'an kanti ne dogayen riguna da riga da siket,sai lace da atamfa da shadda har ma da material su kam basu da yawa,ga takalma wajen kala shida,sai yarirrika da sark'ok'i da abin Hannu da ribbons iri iri na gayu,ga k'ananan pant dai dai jikinta.
Umma ta tsurawa kayan idanu tana mamaki,gaskiya duk in da Hidaya ta fito to daga gidan arzik'i ta fito,domin a cikin sark'ok'in ta har da sark'ar gwal guda biyu,kuma manya ne ba laifi,hakan yasa ta tasa kayan a gaba tayi shiru kawai.
Shi kam Hamza yana can hankalin sa na kan Hidaya da ya kamo mata cartoon a wayar sa tana kallo tana dariya yana taya ta,sai can ya waiwayo ya dubi Umma ya ga tayi kasak'e da kayan a gaban ta,gyara zama yayi yace.
"Umma babu kayan ta a ciki ne?"
Ta sauke numfashi tace.
"Duk ma kayan ta ne a ciki fa"
"To Umma d'auko mata guda d'aya ta saka kawai,sai tayi break fast,kar tai ta zama da towel a jikin ta" ya fad'a a sanda yake k'ok'arin mai da hankalin sa kan Hidaya da take ta nuna masa wayar hannun ta tana cewa "kalli kaga".
Umma ta zaro mata wani d'an d'asheshen material ja mai duwatsu ,d'inkin doguwar riga ne mai kyau,da flowers milk a jiki,ta d'auko mata takalmi milk color da sarka,sannan tayi mata magana akan ta taso ta sanya kaya a jikin ta.
Ita kam hankalin ta na kan waya har sai da Hamza ya sake yi mata magana sannan ta waiwayo ta kalleshi ta k'ura masa idanu,ya sake mai maita mata maganar sa.
" ki tashi ki sanya kayan ki,ko ba kya so mu tafi na kai ki wajen Mummyn?
Sai ta jijjiga kai ta b'ata fuska,ya zaro idanu yace.
"Ba kya so?me yasa hakan Hidaya?"
"Ni ma ba zani ba tunda ta gudu ta barni" ta fad'a da shagwab'a.
Yayi murmushin yace.
"Ayya Hidaya ki mata Afuwa kinji,wani uzuri ne ya sa ta tafi ta barki,kiyi hak'uri"
Ta D'an yi shiru,sai can ta kalleshi ta rik'o hannun sa tace.
"Amma dai idan ka kaini kai ma za ka zauna a wajen mummy ko?"
Ya kalli Umma k'irjinsa ya buga,Umma tayi murmushi tana kallon su,sai ya girgiza wa Hidaya kai yace.
"Ah ah Hidaya,ni ma zan dawo wajen Umma ta ne mu zauna tare ni da ita"
Bai aune ba yaga hawaye ya fara sintiri a idanuwan ta,ta fara buga k'afa tana kuka wai ita in dai ba zai zauna gun mummy ba ita ma ba zata tafi ba,hankalin sa ya tashi ya rasa ya zai yi ,gashi baya son kukan ta,da ta fara kuka yake Neman nutsuwar sa ya rasa,ya kalli Umma idanuwan sa sun fara sauyawa yace.
"Ya zan yi Umma?"
Tayi ajiyar zuciya ta jawo Hidaya ta rungume ta,abin mamaki sai bata k'i ba,ta kwanta luf a ji kin Umma tana ajiyar zuciya da hawaye,Umma ta dinga Shafa kanta ta kalli Hamza tace.
"Hamza na lura yarinyar nan tana sonka,kuma ba ta son rabuwa da kai"
Ya shafa gashin kansa da ke kwance yana k'yallin gyara,fuska babu walwala yace.
"To ya za mu yi Umma?haka nan za ta yi hak'uri mu rabu……
Bai k'arasa ba yaji muryar sa tayi rauni,da sauri ya mik'e ya fice daga parlour'n hawaye na ciko idanuwan sa.
Umma da ta hango damuwarsa sai taji duk na dad'i,ita kanta ba ta son rabuwa da Hidaya ko kad'an,musamman yanzu da take kwance a jikinta sai take jin k'aunarta na ratsata,da k'yar Umma ta daure ta dinga lallashin Hidaya har tayi shiru,kayan da ta d'auko mata kam k'in sakawa tayi,wai ita irin kayan Ya Hamza za ta saka,Umma ta dinga dariya tace.
" To ban da abin ki Hidaya ina mace ina sa kayan maza?
Kawai sai Umma taji Hidaya ta fara koro zance.
"Ai Umma akwai kayana kalar na sa a nan,ni dai su zan saka muyi iri d'aya kinji"
Haka tilas Umma ta birkice jakar ,sai daga can k'asa ta ci karo da wasu y'an kanti riga da siket,rigar fara me tutoci blue,sai siket d'in kuma blue color, Hidaya ta dinga Murna ta d'auki kayan ta saka da kanta,Umma ta d'auko mata wata farar hula ta bata ta saka,jelan gashinta duk sun bazo kafad'un ta,sai tayi wani irin kyawu na ban mamaki.
Sai lokacin ta fara cigiyar Hamza,Umma tace .
"Yana d'akin sa k'ila,je ki ki kirawoshi ya zo kuyi break fast"
Hidaya tayi tsalle ta tafi da gudunta Umma tana nuna mata k'ofar d'akin,Umma tayi murmushin ganin yadda Hidayan ta fara sakewa,ta shige kitchen domin fito da kayan break fast.
Shi kam Hamza na kwance rigingine akan bed d'in sa,kan sa a sama ya fad'a cikin tunani,duk a jagule yake jin ransa,Zuciyar sa na k'unar Rabuwa da Hidaya,rabuwa ta biyu da yake jin tana tab'a ruhin sa,ya rabu da abin da ya fi so cikin rayuwar sa wato (Khaleel) da k'yar ya jure ya daure wa wannan rabuwa kafin ya samu Zuciyar sa ta sake,kullum yana kukan rashin (Khaleel) kusa da shi,to ga Hidaya ta shigo rayuwar sa cikin kwana d'aya tak!amma yana jinta a Zuciyar sa kamar wadda suka shafe tsawon shekaru da dama.…
Wani Hawaye mai zafi ya tsiyayo masa yana gangarowa ta gefen fuskar sa,tattausan Hannun Hidaya kuma k'arami,shi yaji akan fuskar sa tana goge masa Hawaye,cikin raunin murya kuma yaji tayi magana a shagwab'e..
"Ya Hamza me yasa ka ke Kuka…?"
Comments
Share
Vote
Pls
*TYPING*📲
✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️
*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA
*MARUBUCIYAR* 👇
SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)
*DA KUMA*
GARKUWA BIYU
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.