Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 50

*BABI NA GOMA SHA TARA DA NA ASHIRIN*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

Ya D'an runtse idanu saboda yadda kanta ya bugi k'irjinsa,a gigice ya D'an kauce yana niyyar janye ta,ta k'ara matsawa jikinsa tana ruk'unk'ume shi sosai tana kuka,ya rik'o hannun ta yana shirin b'amb'areta a jikin shi amma ta rik'e shi gam,mamakin k'arfin ta yayi duk da ta kasance siririya matuk'a,ganin yadda yake kokawa da ita tak'i tsayawa sai kuka take tana rirrik'eshi,Umma kam tsayawa tayi kallon ikon Allah ta kasa magana.

A hankali ya waiwayo a gajiye ya dubi Umma,ya narke fuska yace.

"Umma ki mata magana ta sakeni,kinga dai ba wani Abu naci ba duk ta sake gajiyar da ni"

Umma tayi murmushi tace.

"Ai yanzu fa dole sai kayi hak'uri domin kai ta sani,ba Lallai ta yarda da ni ba dole kai za ta mak'alewa Hamza"

Fuska cike da Alhini yace.

"To ni yanzu ya zan yi da ita Umma?ina so naje na ci abinci,Sannan na fita masallaci sallar isha'i,kuma kin san k'arfe Tara ina da waya ni da Khaleel"

Umma ta sauke numfashi ta na kallon Hidaya da ta lafe jikin Hamza tace.

"Lallab'ata za ka yi ta ci abincin,na tabbatar idan ta k'oshi da kanta za ta koma baccin'

Ya D'an girgiza kai,to shi ta ya ya ma zai lallab'ata?gaba d'aya bai ma san ya zai yi ba,ya kalli Umma duk a daburce yake,kukan Hidaya na damunsa duk ta jik'a masa gaban riga da Hawaye da majina,kamar me tsoran magana haka ya daure ya fara ambatar sunanta yana d'ago ta daga jikin sa.

" Hidaya…ke Hidaya tashi kiji wata magana kinji…za ki gun mummyn ki ko?"

Ta na ji ya ambaci Mummyn ta tayi sauri ta d'ago ta kalleshi tana jijjiga kai,har da murmushin ta,fuskarta duk zanen hawaye,ya kalleta yana rik'e hannun ta.

"Za ki je gun Mummy ko?"

Ta gyad'a kai.

Ya D'an sakar mata Murmushi yace.

"Mummy ta je unguwa za ta dawo,in kuma ba ta dawo da wuri ba zan kai ki gun ta,amma idan kina so na kai ki sai kin daina kuka,kuma sai kinje gun Umma na ta ba ki abinci kin ci kinji"

Ya nuna mata Umman,ta waiwaya ta kalli Umman,Umma tayi mata Murmushi, Hidaya ta kau da kai ta kalli Hamza ta mak'e wuya alamar ba zata ba,ya D'an dafe kansa,sannan ya d'ago ya kalleta yace.

"Ba za ki je gun Umman ba?"

Ta gyad'a kai tana k'ok'arin sake fashewa da kuka,da sauri ya girgiza mata kai yana k'ok'arin zaunar da ita kusa da shi,tak'i yarda sai nane masa take,yana ji yana gani haka ta matseshi kamar zata koma cikin sa,Umma dai ta na ta kallonsu ba tayi magana ba.

Janyo plate d'in dankalin yayi ya fara d'ebowa yana kai mata bakin ta,ba musu ta karb'a ta fara taunawa a hankali,ya sauke ajiyar zuciya ya dubi Umma yana marairaice fuska,Umma tayi masa alamar yayi hak'uri na D'an lokaci ne,ya jijjiga kai ya mayar da hankalinsa kan Hidayan yana bata dankalin,ba taci da yawa ba ta daina karb'a alamar ta k'oshi,Umma ta mik'e ta kawo ruwa,ya karb'a ya bata tasha,yadda ya lura ko kallon Umma bata son yi,da sun had'a ido sai tayi saurin kau da kai ta matsa jikin sa,ko me ya sa oho!ya D'an tab'e baki.

Kiran Sallah ya fara jiyowa a masallaci,yana mik'ewa sai ga Hidaya ma tsaye tana rik'o hannunsa,ya rasa ya zai yi,a lokacin Umma dariya ta fara yi masa ganin duk ya rud'e Yarinya ta nane masa,da k'yar ya zaunar da Hidaya ya fara share mata hawayen da yake zubo mata,ya tausasa murya yana kallon ta yace.

"Hidaya ki zauna wajen Umma yanzu zan dawo,masallaci zani in yi sallah,kuma zan yi addu'a Umman ki ta dawo da wuri ko?

Ta D'an yi shiru,sai kuma can tace" Eh".

Yaji dad'i har yayi Murmushi yace.

"Ko in baki waya ta kiyi game?kin iya game?"

Tayi magana da sanyin murya.

"Eh na iya,ina yi da wayar Mummy na"

Ya fara k'ok'arin zaro waya a aljihun sa yana dariya.

"Da kyau HIDAYA, bari na baki to kiyi,yanzu zan dawo ba zan jima ba,kar kiyi kuka kinji"

Ta girgiza kai,ya kamo mata game ya mik'a mata wayar,ta haye kujerar d'akin har da kashingid'a ta fara buga game tana dariya,mamaki ya kama shi,ya tsura mata idanu yana murmushi,haka kawai yaji dad'in ganin yadda take farinciki,Umma tayi sakato ganin yadda ya shagala da kallon Hidaya har za a ta da sallah a masallaci,sai da ta yi masa magana sannan ya Ankara,kunya ta kama shi,da sauri ya juya ya fice daga parlour'n domin tafiya masallaci,ya bar Hidaya na b'angala dariya ba ta lura da fitar sa ba.

*****************

Loakacin da ya dawo gidan sai ya tarar Hidaya har tayi bacci,ga wayar sa nan a gefen ta ita kuma sai bacci take,Umma na zaune tana cin abinci daga gefen ta,zama yayi kusa da Umma ya tsoma Hannu cikin kwanon suka cigaba da cin abincin tare, yayi loma d'aya sannan ya kalli Umma yace.

"Wannan Y'ar rigimar har tayi bacci kenan?"

Umma ta girgiza kai ba tayi magana ba,sai a sannan ya tuna da gargad'in Umma akan magana idan ana cin abinci,saboda za a iya k'warewa,hakan yasa yayi shiru,suka cigaba da ci,lokaci lokaci yana d'aga kai ya kalli Hidaya har suka kammala cin Wanda ke gaban su,Umma ta nemi a dad'o yace ya k'oshi ,ya tattara kwanukan ya fita da su ya wanko hannun sa.

Ya D'an jima suna hira da Umma duk akan Hidaya,sannan ya kalli Agogo yace.

"Umma bari na gudu d'akina,kar Khaleel yayi ta jirana ban kira shi ba"

"To Hamza Allah ya tashe mu lafiya,bari na kai Hidayan cikin bedroom, Allah dai ya sa kar ta farka cikin dare tayi kuka" Umma ta ambata tana niyyar mik'ewa.

Hamza ya amsa da "To ameen Umma".

Yana kallo har Umma ta ciccib'i Hidaya,duk da bata da wani nauyi saboda sirantakar ta,suka wuce bedroom, sai da yaga shigewar su sannan ya sauke numfashi ya girgiza kai,a salub'e ya fice daga parlour'n zuwa d'akin sa.

Sai da ya kammala komai na al'adar sa ,ka ma daga wanka zuwa shirin bacci da sleeping dress masu kyau,sannan ya nemi waje ya zauna ya lalubo wayar sa da Hidaya ta jefar a parlour'n Umma,sunan Khaleel ya kamo Wanda ya rubuta (JININ JIKINA).

flashing yayi a lambar,wadda ta kasance ta k'asar waje,minti biyu wayar sa ta fara ruri alamar Khaleel ya kira shi,yayi murmushi yana jin wani sanyi a kansa,sannan ya d'aga wayar yayi sallama da k'ayatacciyar muryar sa.

Daga can Khaleel ya sauke numfashi cikin marairaicewa ya fara magana.

" Wai yau ina ka shiga ne Aboki?saura kad'an fa na rusa kuka saboda rashin jin muryar ka akan lokaci"

Hamza ya k'yalk'yale da dariya yace.

"Wane irin kuka kuma Khaleel?wallahi wasu Abubuwa ne yau suka yi min rubdugu sai hamdala kawai,to ya kake? Ya karatu?"

Khaleel ya amsa cikin shagwab'a tamkar mace.

"Gani nan dai kawai Aboki,rayuwar da babu kai a cikin ta ai lami ce,nan d'in babu wani dad'i sai hak'uri kawai"

Hamza yayi murmushi yace.

"To ya za a yi?kowa da in da Allah yake ajiye shi ya tsara masa rayuwa,ba ya yiwuwa daman mutum ya samu duk abin da yake so Khaleel,ka k'ara hak'uri akan Wanda kake yi,gani na ne kawai baka yi fa,amma kullum muna jin muryar juna,kuma kullum kana raina dai dai da second d'aya bana mantawa da kai"

Khaleel yayi ajiyar zuciya har Hamza ya jiyo shi,a hankali yayi magana.

"Shikenan Aboki na hak'ura,tun da babu yadda zan yi da daddy,wai ina Umma ne?ko har ta kwanta?

Hamza ya amsa.

" Eh ta kwanta,da yake yau tayi Azumi duk ta gaji ne"

Khaleel yace.

"Aboki kuna ta Azumi kai da Umma kuna samun lada,ni kuwa na kasa daurewa na dinga na litinin da Alhamis d'innan,gashi yana da falala sosai ko?"

Hamza yayi murmushi yace.

"Sosai ma kuwa!da za ka daure ka dinga yi,yana k'ara lafiya sosai ga jikin D'an Adam,yana durk'usar da zuciya,domin yawan k'oshi da abinci ya kan gadarwa zuciya girman kai da tak'ama da gafala,amma zama da yunwa na wani lokaci kan haskaka zuciya ta zama mai taushi,gami da gusar da k'ek'ashewar ta,ta zama killatacciya da tunani da zikirin Ubangiji,sannan Azumi kan k'untata magudanar jini,wad'anda sune magudanar shaid'an a jikin D'an Adam,domin shaid'an yana gudana a jikin D'an Adam a magudanar jini,haka nan yana k'ara kusanci ga Allah"

Khaleel yana sauraran bayanin Hamza Zuciyar sa na k'ara k'aunar sa,babu ranar da zai yi hira da Hamza bai samu wani Abu da ya k'aru da shi ba,Hamza ai kyakkyawar zuciya ne,yana jin sa tamkar Wanda suka fito ciki d'aya,ya lumshe idanu ya k'ara k'ank'ame wayar yace.

"Nagode Aboki,hak'ik'a kai d'in wani b'angare ne na jikina,Allah ya barmu tare,Ina sonka Hamza"

Hamza ya gyara kwanciya yana runtse idanu,sannan yace.

"Na fi sonka Khaleel,ka yi min abin da na zan manta da kai ba,ka yarda dani ka amince dani,na zama wani sirrinka,kai na daban ne a rayuwata Khaleel, komai kake so idan har ina da shi zan maka"

Khaleel yayi murmushi yace.

"Ina jin bacci,duk da ban gaji da jin muryar ka ba,me za ka fad'a min Wanda zai haskaka zuciyata Aboki na gari?

Kai tsaye Hamza yace.

" Sai dai in maka Nasiha,Nasiha akan tsoran Allah,wadda aka yi mana ranar juma'a yayin hud'uba a masallaci"

Da sauri Khaleel yace.

"Eh ina so Aboki,nima kayi min….

Hamza yayi murmushi yace…….!

" Ina yi mana wasiyya da ni da kai da mutanen duniya a kan muji tsoron Allah,domin tsoron Allah shine matattarar dukkanin alkairi gabad'aya,babu wani alkairi na nesa ko na kusa face tsoran Allah yana zaburarwa a kansa,haka nan,babu wani sharri na kusa ko nesa,a fili ko a b'oye,face tsoran Allah yana ba da Katanga don kariya daga gareshi.
Kuma hak'ik'a tsoran Allah shine Abu na farko da Allah yayi wa mutane farko da k'arshe wasiyya da shi.Allah yana cewa:

"ولقد وصینا الذین أوتوا الکتب من قبلکم و إیا کم أن اتقوا اللہ "

(Hak'k'a mun yi wasici ga wad'anda a ka ba wa littafi gabaninku da kuma ku,a kan ku ji tsoron Allah)

Hakan nan y kamata mu san siffofin masu tsoran Allah,domin muyi k'ok'ari muyi koyi da su.Kad'an daga cikin siffofin sun had'a da:
Imani,da tsayar da Sallah,da ciyarwa domin Allah,da yarda da abin da Allah ya saukar,da sakankancewa da ranar Lahira.
Yana daga cikin alfanun tsoron Allah :Allah yana karb'ar aikin mai tak'awa ne,kamar yadda yace,

"إنما یتقبل اللہ من المتقین"

(Kad'ai Allah yana karb'a ne daga masu jin tsoron sa).

Yana daga cikin amfanin tsoron Allah,ubangiji zai ba wa mai shi kaso biyu na rahamarsa,kuma ya sanya masa haske da zai rik'a tafiya a cikin sa,kuma ya gafarta masa zunubansa,kamar yadda Allah yace,

"یأیھا الذین ءامنوا اتقوا اللہ و ءامنوا برسولہ یٶتکم کفلین من رحمتہ ویجعل لکم نورا تمشون بہ و یغفر لکمؒ واللہ غفور رحیم"

(Ya ku wad'anda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku yi imani da manzansa,zai Baku kaso biyu daga cikin rahamarsa ,ya sanya muku haske a cikin rayuwarku,ya gafarta muku,hak'ik'a Allah mai yawan gafara ne mai jin k'ai).

Sannan Allah yana sanya wa mai tsoron sa mafita daga duk wani K'unci da damuwa,kamar yadda yace,

"و من یتق اللہ یجعل لہ مخرجا"

(Duk Wanda yaji tsoron Allah,to Allah zai sanya masa mafita)

Dan haka ya kamata muyi guziri da tsoran Allah,domin mu rabauta a rayuwar mu ta duniya da Lahira,domin tsoron Allah shine mafi alfanun abin da bawa zai yi guziri da shi,saboda fad'in Allah ta'ala.

"و تزودوا فإن خیر الزاد التقویؒ واتقون یٰأولی الألبٰب"

(Ku yi guziri ,hak'ik'a mafi amfanin guziri shi ne tsoron Allah, kuma ku ji tsoro na ya ku masu hankula).

Khaleel babu abin da yake rik'e tsoron Allah ,ya kafe shika shikan sa a Zuciyar mumini sai yawan Ambaton Allah a kowane lokaci,a kowane hali,Dan haka babu makawa a dawwama akan zikirin Allah,da tasbihi,tare da godiya ga Allah,ko domin mutum ya samu ya murk'ushe abokan gabarsa guda biyu,(shed'an da son zuciya).

Ina fatan wannan wasiyya za ta shiga Zuciyar mu khaleel,kuma mu zama daga cikin masu aiki da ita.

Zuciyar khaleel tayi sanyi,hawaye ya zubo masa,sosai yaji maganganun Hamza sun ratsa shi,shiyasa ya dinga yiwa Hamza godiya mai tarin yawa,kafin suka yi sallama da juna Zuciyar su cike da kewa.

Hamza ya gyara kwanciyar sa domin ya D'an samu ya runtsa,ko domin ya samu tashi tsakar dare ya gabatar da ibadar sa kamar yadda ya sa ba…..!

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.