Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 18 of 50

*BABI NA TALATIN DA BIYAR DA NA TALATIN DA SHIDA*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

Jikinsa a sanyaye ya juyo ya dawo d'akin,Umma ta nemi gefen gado ta zauna,shi kam tsugunawa yayi a gabanta ya rik'o hannun ta yana kallon fuskarta da babu walwala ko kad'an,hankalin sa a tashe yayi magana.

"Gani Umma na…."

Ta k'ura masa ido ta ambaci sunan sa.

"HAMZA…

" Na'am Umman Hamza"ya amsa mata.

Ta sauke numfashi ta fara magana cikin wani yanayi.

"Khaleel ya sanar da ni abubuwan da kuka tattauna,amma me yasa baka fad'a min da kanka ba?me yasa ka saka shi ya gaya min da bakinsa?saboda ka san zan ji kunyar sa har na amince masa ko?to ai shikenan Hamza ka yi nasara,na amince masa ne saboda kwarjinin da yayi min,gashi sai magiya yake min,amma gaskiya hankalina bai gama kwanciya da hakan ba,mutane ba za su dubi domin Allah yake mana Hidima ba,za su dubi mune kwad'ayayyu da muka nace masa har yake kashe mana kud'ad'e da hidindimu,Hamza wannan rayuwar ta sauya,kiwon mutum ake ba dabba ba,ina tsoron kar a kaiwa Mahaifin sa gulmar hidimar da yake mana,kasan ba sonmu yake ba,babu abin da ya tsana irin alak'ar ka da D'an sa,ni tun farko ban so har ka amsa masa cewar ka amince da abin da yace ba Hamza,zuciyata tana kokonto akan hakan,bana son abin da zai zo ya tab'a mutuncin mu muna zaune lafiya Hamza"

Ya rud'e ganin damuwar Umma,da sauri ya sake damk'e hannun ta ya d'ora kansa kan kafad'ar ta ya fara magana a hankali cikin ladabi.

"Ki gafarceni Umma,wallahi na rasa yadda zan yi da nacin Khaleel ne shiyasa har na amsa,kuma shi yace zai gaya miki da kansa ba ni na yarje masa hakan ba,amma ni ma ba da son raina ba,kuma dalilin da yasa na amince masa saboda kar na kuma saka masa damuwa a ransa har ciwon sa ya tashi ne,kin san Khaleel da saka Abu a rai Umma,amma don girman Allah ki yafe min idan na b'ata miki rai,bana son ganinki cikin damuwa ko kad'an Umma,kuma insha Allahu babu abin da zai biyo baya sai alkairi"

Umma ta yi shiru ba tace komai ba,ganin yadda Hamza ya shiga damuwa har da k'wallarsa yana ta rok'onta Afuwa sai taji tausayin sa,tayi masa murmushi ta shafa kansa tace.

"Shikenan babu komai ya wuce,Allah ya tabbatar da alkairi"

"Ameen Umma na,Na gode Allah ya k'ara miki Lafiya da Nisan kwana mai amfani" ya fad'a cike da murna.

*********************

Kwanan Hidaya biyu a asibitin aka sallameta,cikin ikon Allah ta warware sosai,daman shi ciwon sikila haka yake,idan ya motsa mutum kamar ba zai rai ba,amma idan ya lafa sai kaga kamar mutum bai tab'a ciwon ba ma(Allah ka k'ara mana lafiya).

A wad'annan kwanakin Hidaya ta yi mugun Sabo da Khaleel ta waya,kusan kullum sai ya kira Hamza ko kuma video call domin su sha hira shi da Hidaya da Hamzan,sai Khaleel ya sake shiga Zuciyar Hamza sosai saboda nunawa Hidaya k'auna da yake yi…

Da aka sallamosu haka Gidan Umma kullum a cike da masu zuwa duba Hidaya,y'an unguwar sun yi matuk'ar Sabo da ita,k'awayen ta su Hansa'u kuwa suna manne da ita,hatta y'an uwan Umma daga kano sai da suka zo duba Hidaya.

Hidaya ta cigaba da zuwa makaranta,shak'uwar ta da Hamza na k'ara hab'aka,bata da abokin shawara sai shi,bata da wani makusanci da ya zarce Hamza,duk abin da ya shige mata duhu Hamza take fad'awa,ko Umma bata san wasu abubuwan game da Hidaya ba kamar yadda Hamza ya sani,Hamza shine sirrin Hidaya.

Cikin ikon Allah tuni har an kammala gyaran shagon yayi fes da shi,an zuba wayoyi da charger da condom da earpiece masu tsananin kyau da sauk'i,ga kuma gallelen mashin d'in Hamza Sabo dal na zamani,lokacin da aka kawo mashin d'in kamar Hidaya zata shid'e don murna,haka suka wuni yana zagaya unguwa da ita akan mashin,Hidaya an samu abin hawa,ko makaranta zata sai tace sai ya kaita,duk da makarantar babu nisa,haka zata haye baya ya kaita ya direta,in yana da lecture ya wuce makaranta,idan babu kuma ya dawo gida ya bud'e shago yayi zaman sa.

Sosai ciniki ya bud'e masa sai Hamdala,har da generator Khaleel ya siya masa,yana kunnawa ana kawo chaji sosai a wajen,da yake Hamza na mutane ne,akwai kuma abokan sa guda biyu y'an mak'otan su,Faisal da Anas,idan baya nan sune suke jire masa shagon sa.

Wata uku da bud'e shagon wata ranar lahadi bashi da lecture,Hidaya ma babu makarantar boko,misalin k'arfe sha d'aya na safe bayan ta kammala taya Umma aikin gida tayi wakan ta fes da kwalliya,ta k'ara girma kamar ba ita ba,ta dubi Umma da ke zaune parlour tana hutawa tace.

"Umma ina Ya Hamza ne?

Umma tayi Hamma saboda gajiya tace.

" Yana shago,bai jima da fita ba kina wanka"

Hijabin ta ta d'auka ta saka tayi hanyar fita tana cewa.

"Umma bari naje na goggoge masa kantocin shagon nan,naga jiya duk sunyi k'ura da yawa"

Umma ta d'aga murya tace.

"Kinyi wanka fa,amma zaki kuma shiga aikin k'ura?

Ta fice da sauri tana cewa.

" Na sake wani wankan idan na gama"

Umma ta girgiza kai ta maida kanta ta kwanta gyangyad'i na d'iban ta.

Bakin shagon cike da mutane masu kawo caji da masu siyen abubuwan da suke so,suka matsa mata suka bata hanya,ta d'aga kantar da ta kare tsakanin Hamza da mutane ta shige cikin shagon,Hamza na tsaye yana d'aukowa wani mutum condom da yazo siya,ya waiwayo ya kalleta yayi murmushi yace.

"Har kin shirya?na neme ki ai Umma tace kin shiga wanka"

Ta jijjiga kai tana murmushi tace.

"Eh Ya Hamza, yau fa sanitation zan wa shagon nan duk yayi k'ura"

Ya D'an zaro ido yace"Ayya Hidaya ai zaki b'ata wankan ki"

"Babu komai sai na canza wani Ya Hamza"

Haka ya k'yaleta ta d'au daster ta fara goge goge,shi kuma ya cigaba da sallamar mutane,sai dai Abu d'aya ya dame shi ganin yadda mazan da suke zuwa suka ishi Hidaya da kallon k'urilla,nan da nan yaji ransa ya b'aci, ko me suke kallo oho musu.

Ita kam bata san ma suna yi ba,hankali ta na kan aikin ta tana zubawa Hamzan surutu,ba kuma hirar komai take masa ba sai ta khaleel,yana jinta yana bata amsar maganar da take masa.

Fitsari yaji ya matse shi,Dan haka yace da Hidaya ta bar goge gogen ta kula da shagon zai shiga cikin gida ya fito yanzu,ta amsa da to ,shi kuma ya d'aga Kantar ya fice daga shagon.

Yana shiga ya wuce d'akinsa da sauri,toilet ya shiga saboda jin fitsarin ya matse shi sosai kamar ya zubo a wando,bayan ya gama uzurin sa sai ya fito,ya lek'a d'akin Umma ya ganta kwance a parlour bacci ya kwasheta.

A dai dai wannan Lokacin wata dank'areriyar mota me azabar kyawu ta tsaya dai dai k'ofar Gidan,driver'n motar yana tsayawa ya fito da hanzari ya zagayo ya bud'e k'ofar Gidan baya,wani Hamshak'in mutum ya sako k'afafuwan sa ya fito,jikinsa sanye da kaya na alfarma,daga ganinsa kasan naira ta zauna,ALHAJI MUDASSIR Kenan,Mahaifin Khaleel.

Babu Neman izini ko sallama haka ya taka cikin izza da gadara ya kutsa kansa cikin Gidan,driver kam tsayawa yayi a gindin motar yana jiran sa.

Ita Hidaya bata lura da zuwan su ba ma,hankalin ta ya d'auke kan sallamar mutanen da suke zuwa.

ALHAJI mudassir yana kutsawa tsakar Gidan ya ci karo da Hamza yana k'ok'arin fitowa,da sauri Hamza yayi baya yana duban daddy k'irjinsa na wani irin bugawa da tsananin k'arfi, fuskar daddy tamkar gobara saboda fushi,zubewa Hamza yayi a gaban daddy cikin rawar baki yace.

"Barka …da zuwa daddy…ya …ya hanya..?

Wani matsiyacin kallo daddy ya watsawa Hamza,cikin kakkausar murya ya fara magana da k'arfi yana nuna Hamza da Hannu.

" Kai ka kiyaye ni?bana buk'atar gaisuwar ka,matsiyacin yaro D'an Gidan talakawa jikan mayu,so nawa zan gargad'eka akan mak'alewa yarona ne,wai kai maye ne?nace kai maye ne?haka kawai ka mak'alewa d'ana sai zuk'e masa jini kake,D'an arzik'in da yake da shi wato sai ka k'arar da shi ko?wai kai baka da zuciya a cikin k'irjinka ne?wane irin jarababben yaro ne kai?me za a yi da halin talaka a rayuwa?talaka shegen kansa ne,na tsani talakawa a rayuwa ta domin bak'ar Zuciyar su,ba zan tab'a sonka ba Hamza,idan ka cika D'an halak cikin uwarka da uban ka ka rabu da d'ana,ka fita daga rayuwar d'ana,ka barshi ya sake yayi min biyayya,kai warware asirin da kayi masa,idan ba haka ba wallahi sai Na d'auki mummunan mataki a kanka, asararre kawai……

Hamza kansa a k'asa yana jin duk cin mutuncin da daddy ke masa,K'unci ya mamaye ruhinsa,idanuwan sa suka yi jajir,a dai dai lokacin hargagin daddy ya tashi Umma daga baccin da ta fara,ta taso da sauri ta d'aga labulen parlour'nta tana duban daddy tsaye yana zazzagawa Hamza cin mutunci,Hamza durk'ushe kansa a k'asa Hawayen sa na d'isa,daddy ya waiwaya ya dubi Umma,suka had'a idanu a lokacin da daddy ya cigaba da magana yana mata kallon banza.

"Yawwa fito kiji da kunnuwanki kema,d'anki ya zama kaska rab'i mai jini,to ki ja masa kunne ya fita daga harkar d'ana,ya daina mak'ale masa,bana buk'atar sa a cikin rayuwar d'ana,idan ba haka babu sai na mayar da shi abin kwatance a garin nan,talakawan banza talakawan wofi,na d'aukeshi ma daga k'asar amma kuna bibiyarsa kamar mayu, wannan shine gargad'ina na k'arshe a gareku,Idan kunne ya ji jiki ya tsira…….

Yana kaiwa nan ya saki mugun tsaki ya juya zai fice daga Gidan,yana kaiwa soro suka yi kacib'us shi da Hidaya da ke k'ok'arin shigowa soron a dai dai lokacin,sakamakon man inji ya k'are ta rufe shagon ta shigo ta kirawo Hamza domin a zuba wani,tun daga waje take jiyo hargagi da masifa amma bata san ko muryar waye ba,bangaje Hidaya daddy yayi ya wuce a fusace,Hidaya ta tsorata saosai ta kauce,ta bi k'eyarsa da kallo saboda bata yi nasarar ganin fuskar sa ba,a hankali ta tab'e baki ta nufi cikin gidan.

Hamza ya d'ago yana duban Umma da ta yi mutuwar tsaye,irin wannan ranar take gudu daman,ranar da Mahaifin Khaleel zai sake yi musu tijara a karo na barkatai,shin wai menene laifin su ne?Khaleel ne ya mak'alewa Hamza ba Hamza ne ya mak'alewa Khaleel ba,amma me yasa Mahaifin Khaleel ya kasa gane hakan?shin menene laifin talaka a rayuwa?talaka da ya kasance bawan Allah…!

Hawaye mai zafi ya zubo mata,a dai dai lokacin da Hamza ya d'ago ya kalleta,k'irjinsa ya buga ganin Umma na kuka,ya nufeta hankali a tashe kamar ya kifa,zubewa yayi a gabanta ya rik'e k'afafuwanta ya fashe da kuka mai cin rai yana magana cikin rauni.

"Ki yafe min mahaifiyata,fushin ki gareni babbar masifa ce umma na,nine na jawo miki,daman an ce D'an kuka mai jawa uwarsa jifa,da banyi abota da Khaleel ba da ba a zo an ci mutuncin ki ba,don Allah ki yafe min Umma na,hawayen ki ya bar zuba a kaina,ban san me zan fad'awa ubangijina akan hakan ba,ina kwad'ayin samun aljanna Umma,idan hawayen ki yana zuba a kaina ba zan tab'a samunta ba Umma,don Allah ki yafe min Mahaifiyata"

Kuka sosai Hamza yake mai cin rai,ita ma Umma hawayen ta na d'isa,cikin wata irin Murya a shak'e ta kirayi sunan Hamza.

"HAMZA…..

Ya kasa amsawa saboda kuka sai kallonta da yake yi kawai yana shesshek'a da nishi,ta runtse idanu tace.

" Idan har da gaske ni ce Mahaifiyar ka,ni na tsuguna na haifeka,ni ce na raineka,nice na shayar da kai,ni ce na d'auki d'awainiyar ka tun daga haihuwarka har zuwa girman ka,ni ce uwarka ni ce ubanka,to ina so a yau kayi min alfarmar cire Khaleel daga ranka,ka shafe babin tarihinsa a rayuwar ka,ka manta da shi da duk wani Abu da ya shafe shi,ka mayar masa da duk wani Abu na sa da ke wajen ka,ina so abotarku ta zo k'arshe a yau ba gobe ba……

A dai dai lokacin da Hidaya ta k'araso kalaman Umma na shiga kunnuwan ta,a gigice ita da Hamza suka dubi Umma…k'irjin su ba bugawa,Kansu kamar ya fashe saboda razanar jin kalaman Umma…….!

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU...!* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.