Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 50

*BABI NA GOMA SHA BAKWAI DA NA GOMA SHA TAKWAS*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*FAN'S INA GODIYA DA FATAN ALKAIRIN DA KUKE MIN A KULLUM,ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI* 👏🥰

*** Umma ta na zaune a tsakar gida kan dadduma ta idar da sallar magriba,carbi ne a hannun ta tana salati da hailala,a gefe guda zuciyar ta cikin tsananin mamaki take sosai da rashin dawowar Hamza gida har magariba tayi,ta san halin Hamza duk wani Aike da za ta yi masa ya kan hanzarta yaje ya dawo akan lokaci ba tare da jinkirtawa ba,to menene dalilin dad'ewar sa haka?anya kuwa lafiya?duk cikin damuwa take jin ranta ta kasa ko da shan ruwa duk da lokacin shan Ruwan ma ya wuce,har lokacin da azumin ta a bakin ta na ranar Alhamis,kamar yadda suka saba yin Azumi a duk wata ranar litinin da Alhamis ita da Hamza.

Ta na nan zaune taji Sallamar sa ya shigo gidan,da Hanzari ta waiwaya ta dubeshi tana amsa sallamar,kuma shigowar sa yayi dai dai da kawo wutar NEPA wadda ta haskake tsakar gidan sosai,Umma ta bi Hamza da kallo ganin sa da Yarinya akan kafad'arsa,ga k'atuwar jaka a hannun sa,kansa a sunkuye ya zo ya gifta ta gabanta ya shige cikin parlour'n ta,kan kujera ya nufa ya sauke Hidaya a hankali Dan kar ta farka,ya gyara mata gashin ta da ya ba zo ya rufe mata fuskarta,ta D'an motsa a hankali tana tura yatsanta guda d'aya a bakin ta tana tsotsa,ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta,tausayin ta na ratsa shi,Yarinya k'arama amma har shafukan k'addararta sun fara bud'ewa,an ambaceta da marainiya mara Uba,ta rabu da mahaifiyarta a shekaru na yarinta,babu dangi na nesa balle na kusa!ga lalura me wahalar da Numfashi.

Hak'ik'anin gaskiya Hidaya ta cancanta a tausaya mata,ajiye jakar ta yayi a k'asa daga gefe,ya sake sunkuyawa ya tofa mata addu'o'i,ya rage yawan iskar fanka,sannan ya juya ya fito tsakar gidan jikin sa a sanyaye.

Umma na nan in da ya barta ko motsi bata yi ba,shi ma wucewa yayi zuwa kitchen ya d'akko wankakken plate,ledar sa ta kayan marmari na hannunsa,ya kwance ta ya juye kayan marmarin a cikin plate d'in,ya d'auka ya fito da su ya k'ara so gaban Umma ya ajiye,a hankali yayi magana cikin sunkuyar da kai.

"Umma ki D'an yi min Afuwa na gabatar da sallar magariba ,saboda kar lokacin ta ya tsere mini"

Yana fad'in hakan ya mik'e tsaye ya nufi toilet d'in tsakar gidan,ya d'auki buta da ke cike da ruwa ya shiga ya gabatar da tsarki,ya fito ya tsuguna ya gabatar da cikakkiyar alwala a nutse,Umma dai sai kallon sa take yi,har ya kammala ya kuma komawa parlour'n ya d'auko wata daddumar ya fito ya shimfid'a ya ta da sallah,kasancewar ko yaje masallaci tuni an idar,shiyasa bai fita ba yayi abarsa a gida,har ya idar yayi addu'oin sa sannan ya waiwayo ya dubi Umma,ganin kallon da take masa sai yayi Murmushi ya matso kusa da ita ya kamo hannun ta ya rik'e,yayi magana yana duban kayan marmarin da ke gabanta da ko kallon su bata yi ba.

"Umma ya ba ki sha ba?Bismillah ki sha mana"

Ya fad'a tare da k'ara turo plate d'in gabanta.

Tayi shiru bata tanka ba sai kallon sa kawai da take yi,haka nan bata da niyyar sha,fuskantar hakan da yayi ya sa ya kuma magana cikin tausasawa yana kallon ta da murmushi akan fuskar sa.

"Umma kiyi hak'uri banyi miki sannu da shan ruwa ba,dafatan kin sha ruwa lafiya?kuma kiyi hak'uri da b'ata lokacin da na yi ban dawo ba,abin da kika hore ni da aikatawa naci karo da shi a hanyata ,shine dalilin rashin dawowa ta akan lokaci"

"Me kenan Hamza?" Umma ta tambayeshi,karo na farko kuma da tun shigowar sa tayi magana kenan.

"Taimako Umma,wani taimako na tsaya yi"ya bata amsa cikin karsashi.

Tayi ajiyar zuciya idanuwanta a kansa tace.

"Wane irin Taimako ne Hamza,wacece wannan da naga ka shigo da ita har ka wuce d'aki da ita?wacece ?ina ka samo ta?

Ya sauke numfashi,cikin Y'ar fargaba yace.

" Wata baiwar Allah ce Umma,mai tsananin rauni da Neman taimako"

Umma tace.

"Mu ma bayin Allah ne Hamza,kuma masu Neman taimako a wajen Allah,kawai ka fayyace min wacece ita?"

Ya kuma sauke ajiyar zuciya sannan yace.

"Zan gaya miki Umma na ,amma don Allah kiyi min alfarma ki fara saka wani Abu a cikin ki kafin na sanar da ke komai,kinga Azumi kika yi,ya kamata ace zuwa yanzun kin ci wani Abu"

Ta yi Murmushi tana yabawa da kulawar da yake bata,ta mayar masa da amsa da cewa.

"Kai ma ai Azumin kayi,kuma har zuwa yanzun ba ka ci komai ba,ta ya ya zan ci alhali kai baka ci ba Hamza"

Yayi Murmushi mai k'ayatarwa har fararen hak'oran sa suka bayyana,cikin jin dad'i yace.

"To mu sha wannan tare Umma,idan muka kammala nayi alk'awarin sanar da ke komai da ya faru daga fita ta d'azu har zuwa dawowa ta".

Umma ta girgiza kai cike da gamsuwa,tayi bisimillah ta saka hannun ta ta fara d'aukar kankana ta kai bakinta,sai da yaga ta sha sannan shi ma yayi bisimilla ya d'auka ya kai bakin sa ya tauna,ya lumshe idanu a hankali yana jin dad'in yadda suke shan Abu a kwano d'aya shi da mahaifiyar sa.

******************

Umma ta jima cikin k'urawa Hamza idanu bayan ya kammala fad'a mata abin da ya faru!wani irin mugun tausayin Hidaya na ragargazar zuciyar ta,ka sa hak'uri tayi ta mik'e daga tsakar gidan ta shige parlour'n ta,taje dab da Hidaya da ke kwasar bacci ta tsaya ta tsura mata idanu,a hankali Hamza ya d'aga labulen parlour'n shi ma ya shigo,ya tsaya dab da Umma suka tsurawa Hidaya idanu suna ta kallonta ,Umma ta waiwayo fuskarta cike da alhini ta kalli Hamza,tayi magana a hankali gudun kar Hidaya ta farka.

" Yanzu duk abin da ka fad'a min akan yarinyar nan da gaske ya faru Hamza?"

Ya sauke numfashi ya jijjiga kai yace.

"Abin da mahaifiyar ta ta sanar da ni nima shi na fad'a miki Umma,gaskiyar faruwar abin ko akasin hakan wannan Allah ne masani,sai dai a iya kallon da na yi mata na hango gaskiya cikin idanuwan ta,kuma na kyautata mata zato"

Ta nemi kujera ta zauna,yayin da Hamza ya zauna a k'asa ya tank'washe k'afafuwan sa yana kallon ta,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi magana.

"Wani kokonto ne ya shiga zuciyata Hamza,ka tara hankalinka guri guda ka hango abin da na hango,ta ya ya Uwa mahaifiya za ta bawa Wanda bata sani ba d'iyar da ta haifa?kuma har tayi masa umarnin kai yarinyar Gidan Marayu?ni fa zuciyata a tsorace take Hamza!na fara zaton wani mummunan al'amari akan hakan…..

Da sauri ya fara girgiza kai,fuskar sa cike da alhini ya fara magana.

" Ah ah Umma,kar kiyi mummunan zato akan lamarin wannan Yarinya,domin bamu san komai a kanta ba,abin da yafi gara mu kyautata zato a kanta,sannan yawaita zato babu kyau,musamman mummunan zato,ko domin fad'in Allah mad'aukakin sarki.

"یأیھا الذین ءامنوا اجتنبوا کثیرا من الظن إن بعض الظن إثم"

Ma'ana:(Ya ku wad'anda suka yi imani,ku guji yawancin zato,domin wani b'angare na zato zunubi ne).

Haka nan a wani Hadisi ,Annabi (S A W) yana cewa."ku guji zato ,domin zato shine mafi k'aryar zance"

"Dan haka Umma mu kyautata zato akan Hidaya da mahaifiyarta ,kar muyi musu mummunan zato"

Umma ta sauke numfashi ta k'urawa Hamza ido tace.

"Haka ne Hamza,tabbas ka tunasar da ni abin da na manta,shikenan babu komai,Allah ya kai mu goben da kaina zan shirya na raka ka gidan marayun domin mu kaita,Allah ya kyautata rayuwar ta".

" Ameen Umma"Hamza ya amsa yana murmushi.

Suka yi shiru suna kallon Hidaya,sai can Umma ta kuma cewa.

"Ya kamata a tashi yarinyar nan a bata abinci,dole za ta ji yunwa fa"

Ya jinjina kai ya D'an tara gira yace.

"Amma Umma ina tsoron a tashe ta bata ga mahaifiyarta ba tayi kuka! Tunda mu dai ba sanin mu tayi ba"

Umma ta D'an yi murmushi tace.

"Insha Allahu babu abin da zai faru,ba zata yi kuka ba,bai kamata a barta da yunwa ba Hamza,kuma ai kai ta riga ta sanka,tunda har ta nemi kaje ka bawa mahaifiyarta Ruwa"

Hamza ya D'an yi dariya yana sunkuyar da kai,yace.

"To babu laifi Umma,a tashe ta d'in ta samu ta ci abincin,ni fargabata ma ko ya ya mahaifiyarta ta take a yanzu?saboda gaskiya na barta cikin mawuyacin hali,ina jin tamkar na koma inga halin da take ciki a yanzu wallahi"

Fuskar Umma ta nuna Jimami sosai!tace.

"Insha Allah tana cikin Aminci,Allah ya dubeta ita ma,Zo ka tashe ta,bari na had'o mata tea da wancan dankalin da na soya,zai fi mata sauk'in ci"

Umma ta ambata sannan ta mik'e ta fice daga parlour'n.

A hankali ya rarrafa kusa da Hidaya da ke ta bacci hannun ta cikin bakin ta,ya rasa ta ya ya ma zai tashe ta,kawai ji yake k'irjinsa na bugawa fat fat,da k'yar ya iya d'aga hannunsa ya kai kan nata hannun ya zare daga bakin ta,yana zare hannun kamar wadda aka daka ta tsandara wani ihu tana k'ok'arin bud'e idanu,a gigice ya mik'e tsaye yana zare idanuwan sa saboda ihunta ya zo masa a bazata…….!

Ihunta ne ya shigo da Umma parlour'n da sauri,hannun ta d'aya rik'e da kofin shayi,d'ayan plate ne ta zubo dankali,tana shigowa Hamza ya dubeta a firgice yace.

"Wai fa Umma kawai hannun ta da ke bakin ta na cire mata,shine tayi wannan ihun"

Umma tayi murmushi ta ajiye kayan hannun ta,ta matsa kusa da Hidaya da take k'ok'arin komawa bacci bayan ta mayar da hannun ta cikin bakin ta,ta kai Hannu za ta d'ago ta,da sauri Hamza yayi magana.

"Umma ki k'yale ta kawai,kar ki tab'a ta ta sake yi mana ihu"

Umma tayi Y'ar dariya tace.

"Kai dai wani zubin matsoraci ne Hamza,yanzu D'an wannan ihun ne ya sa ka firgice haka?

Ya D'an Sosa kansa yayi murmushi yace.

" Allah Umma ihun ne ya zo min a bazata,kawai fa daga cire mata Hannu a bakin ta shikenan ta zunduma ihu"

Umma tace.

"Ai yara masu tsotsan Hannu ba sa son a na cire musu hannun idan suna tsotsa,kuma da alama tana da hak'uri,saboda yara masu wannan d'abi'ar ta tsotsan Hannu suna da hak'uri ,ba su cika rigima ba"

Umma tana kammala maganarta ta juya ta ciccib'o Hidaya ta d'ora ta kan cinyar ta,a hankali ta fara shafa fuskarta tana ambatar Sunan ta"Hidaya…ke Hidaya bud'e idanuwan ki kinji…"

Hamza yana ta kallon su yana son ganin yadda Hidaya za ta yi idan ta farka,Umma kuma na ta ambatar sunanta tana D'an jijjigata,sai Hidaya ta fara bud'e idanuwan ta masu cike da barci,Umma tana ganin haka ta mik'e tsaye ta dire ta,sannan ta ja hannun ta suka shige bedroom d'in ta,toilet d'in d'akin ta ta kaita ta tsugunar da ita tayi fitsari,tayi mata tsarki,ta wanke mata fuskarta da bakinta,sannan ta kamota suka sake fitowa parlour 'n.

Har lokacin Hidaya bata gama wartsakewa ba,Hamza na tsaye suka fito,Umma ta zauna ta jawo Hidayan jikinta,ta kalli Hamza tace.

"Mik'o min tea d'in nan ka wani tsaya k'erere a tsaye,ka nemi waje ka zauna mana"

Da hanzari ya d'auko kofin ya mik'owa Umma,sannan ya durk'usa gaban su,ta karb'a tana k'ok'arin bawa Hidaya a baki, babu musu Yarinya ta karb'a ta fara k'walk'wala saboda babu zafi,Umma ta fifita ya huce.

Sai da ta gama sha tas,Umma tace wa Hamza"Mik'o dankalin ka ga har ta shanye shayin,k'ila daman tana jin yunwa fa"

A lokacin ne Hidaya ta fara dawowa hayyacin ta daga sakin da bacci yayi mata,ta d'aga kanta ta k'urawa Umma idanu,Umma na yi mata murmushi,har Hamza ya mik'o dankali yana fad'in.

"Ga shi Umma" a lokacin Hidaya ta d'auke kallonta daga kan Umma ta mayar kan Hamza,k'ura masa idanu tayi,shi ma ya zuba mata ido,ta kuma mai da kallonta kan Umma,sai kuma ta mik'e da hanzari daga kan cinyar Umma ta nufi Hamza ta fad'a k'irjinsa ta ruk'unk'ume shi ta fasa wani gigitaccen kuka da kiran "Mummy naaaaaa……!

Comment
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.