Complete Hausa Novels

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 50

*BABI NA GOMA SHA UKU DA NA GOMA SHA HUD'U*

WATTPAD:Hassana3333

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*FARKON LABARI*

***Tana zaune a tsakar gida kan kujera Y'ar tsuguno,dankali ne na turawa a gabanta da wuk'a a hannun ta tana feraye wa,motsin da taji ya sa ta d'ago kai tana kallon bakin k'ofar parlour'n ta.

Tsaye yake ya d'aga labule yana kallonta,idanuwan sa da alamun bacci ya farka,yayi mik'a yana salati kafin ya sauke kallonsa a kanta,a hankali ya ta ko ya fito tsakar gidan ya nufo in da take,yayin da ta dakata da ferayar ta na kallon sa cikin kulawa da murmushi akan fuskarta.

Yana isowa gabanta ya tsuguna ya mik'a Hannu ya karb'i wuk'ar hannun ta,sannan ya d'auki dankalin ya cigaba da ferayewa,a lokacin ne kuma yayi magana.

"Haba Umma,maimakon ki tashe ni nayi Aikin da kaina,ai bai kamata ni ina bacci ke kuma kina aiki ba,ni ya kamata nayi aiki ke kuma ki huta,gashi ma har yamma tayi sosai ban san lokacin da baccin ya kwashe ni ba bayan na idar da sallar la'asar"

Umma tayi murmushi ta dubeshi da kulawa tace.

"Haba HAMZA!wannan ai Aikina ne ba naka ba,gani nayi yau kamar Azumin yana baka wahala shiyasa ma na k'yaleka ban tashe ka a baccin ba,saboda na san shi kansa baccin mai Azumi ibada ne,yanzu nake shirin da na kammala ferayar dankalin nan na taso ka domin kaje bakin titi ka samo mana kayan marmari da dabino da za mu yi bud'e baki da su".

Hamza ya jinjina kai yana cigaba da ferayar dankalin.

" To Umma,bari na kammala wannan sai na fita na nemo mana,ni na zaci ma akwai ragowar dabinon ai?

"Babu ya k'are wallahi,jiya da yara suka shigo wasa na rarraba musu ragowar"
Umma ta amsa tana k'ok'arin tattara b'awon dankalin za ta kwashe,ganin har ya kammala ferayewa.

Da sauri ya amshi tsintsiyar ya tattara,ita kuma Umma ta karb'i dankalin ta d'auraye ta nufi kitchen domin d'orawa.

Bayan ya zubar da b'awon a shara,ya nufi Famfon da ke tsakar gidan ya d'auraye hannayensa ,d'akin sa ya nufa ya cire jallabiyar jikinsa,sannan ya saka wani yadi na kufta me kyau da ya sake fito masa da asalin kyawun zatinsa,babu Wanda zai kalleshi yace bai haura shekaru Ashirin da wani abun ba,amma a lokacin yana da shekaru goma sha takwas kacal a duniya ne,tsantsar kamalar sa da haibarsa ke sawa Mutane na yi masa kallon Babban mutum.

Yana fitowa daga d'akin sa Umma na fitowa daga kitchen da flask d'in shayi a hannun ta,ta dubeshi tana jin dad'i a ranta sosai,har ta kasa had'iye wa sai da ta furta.

"Ka yi kyau Hamza,yadin nan yana yi maka kyau Sosai"

Yayi murmushi kansa a k'asa yace.

"Asalin kyan ai naki ne Umma,Hamza ke ya gado a fagen kyawu"

Tayi dariya tace.

"Anya kuwa?ai ni na tsufa,kyawun ya fara gushewa kwamanda"

Ya d'ago idanuwan sa ya kalleta da kyautatawa yace.

"Wai Umma menene kwamanda?wataran sai naji kina ambato na da kwamanda"

Ta sauke numfashi tace.

"Sunan ka ai sunan Kwamandan Yak'in uhudu ne,wato sayyadina Hamza,shugaban masu shahada na musulmai,shiyasa wataran nake maka alkunya da kwamanda"

Ya lumshe idanuwan sa ya bud'e yana jinjina kai,a hankali ya furta.

"Allah ya k'ara yarda da aminci ga sahabban manzon Allah (S A W)"

Umma ta amsa da "Ameen" sannan ta zarce da cewa.

"Bari na d'auko maka kud'in da zaka siyo kayan marmarin"

Da hanzari ya tare ta.

"Ki barshi kawai Umma,ina da kud'i fa"

Ta waiwayo ta k'ura masa idanu,kafin tace.

"Kana da kud'i ?ina ka samu kud'i?

Ya D'an Sosa k'eya yana murmushi,ya langab'e kai yana dubanta yace.

" Tun Wanda KHALEEL ya turo min ne fa,har yanzu basu k'are ba Umma akwai ragowa da yawa"

Umma ta girgiza kai tana murmushi tace.

"Ayya!Allah sarki Ibraheem,Allah dai ya saka masa da alkairi,Ubangiji ya bar amintarku har zuwa Aljanna,yadda yake taimakon ka Allah ya taimaka shi a dukkanin lamuran sa shi ma"

Hamza ya amsa cikin shauk'i.

"Ameen Umma,ai khaleel jinin jikina ne Umma,ni da shi tamkar Jini da hanta ne"

Sannan ya zarce da cewa.

"Bari naje nayi sauri na dawo Umma,yamma na dad'a yi bana son Magriba tayi ban dawo ba"

Yayi hanyar fita daga gidan,Umma nayi masa fatan alkairi da dawowa lafiya.

****************

A cikin wani kango suke zaune su biyu,wata mata me kyakkyawar sura tana kwance a k'asa tayi matashi da wata jaka, ga Yarinya da bata wuce shekaru takwas ba zaune a gabanta rik'e da hannayen ta,da doguwar Riga a jikinta Y'ar kanti mai d'ankaren kyau,kanta ba d'ankwali sai kalba da ta zubo har kafad'unta an mata adon duwatsu a kanta,yarinyar siririya ce k'warai,sai dai tana da kyawu dai dai gwargwado.

Yarinyar tana rik'e da hannun Uwar tana girgizawa da ambatar sunanta.

"Mummy!mummy!mummy ki tashi mu tafi daga nan,nan fa bashi da kyau,ki tashi mu koma gida kinji mummy…!

Uwar ta D'an bud'e idanuwanta da suka yi jajir alamun tana cikin tsaka mai wuya,da k'yar ta iya magana tana kallon yarinyar.

" Hidaya bamu da wata hanya da zamu fita daga nan!nan shine mafakar mu!nan shine rufin asirin mu!ko ni ban tsira ba ke ina son ki tsira Hidaya,rayuwar ki tana da amfani a gaba da yardar Allah!shirun nan da kika ga nayi addu'a nake yi Allah ya kawo Wanda zai taimake mu Hidaya"

Hidaya tayi shiru tana kallon mahaifiyarta,bata da wayo sosai da za ta gane maganganun mahaifiyar ta,ta k'urawa bakin ta idanu tana ganin yadda ya bushe da alamun tana buk'atar ruwa,ta kai Hannu ta shafa leb'en mahaifiyar ta ta,tayi magana cikin Yarin ta.

"Mummy kina jin k'ishirwa ko?za ki sha ruwa?

Tayi murmushi ta yi tari, sannan ta gyad'a kai tayi magana cikin nishi.

" Idan Allah yayi nufin shayar da ni zan sha Hidaya,idan kuma shan ruwa na na duniya ya k'are Allah ya shayar da ni na alkausara tare da Mahaifin ki"

Hidaya tayi kasak'e bata fahimta ba,kawai sai ta saki hannun mahaifiyarta ta ta mik'e tana cewa.

"Bari na samo miki Ruwa ki sha kinji Mummy"

Ta d'aga Hannu tana k'ok'arin dakatar da ita akan kar ta fita daga kangon,amma tari ya sark'afeta,ita kam Hidaya tuni ta zura da gudu ta fice daga kangon domin nemowa mummyn ta Ruwan da za ta sha.

*************

Sauri yake ta yi sosai ganin magriba ta kusa,hannunsa rik'e da ledoji da ya siyo kayan marmari,bai bi ta hanyar da ya bi da farko ba sai ya canja hanya,a ganinsa wannan hanyar da ya biyo za ta fiye masa sauk'i wajen isa gida tunda sauri yake yi.

Yana yanko layin da ke gaban sa yaji layin tsit babu hayaniyar mutane,haka nan babu yawaitar gilmawar mutane da yawa a layin,kansa a k'asa ya zo zai gifta ta gefen wani kango,kamar an ce ya d'ago kansa,karaf!ya ci karo da k'aramar Yarinya tsaye a bakin kangon sai zare idanu take yi tana kalle kalle,har zai wuce sai kuma ya D'an tsaya yana duban ta yana nazarin ta,kamar yadda yake kallonta haka ita ma ta k'ura masa idanu tana kallon sa,can kuma ta maida kallon ta kan ledar da ke hannunwan sa.
Har ya kuma juyawa zai wuce ganin Ummansa tana can jiransa,sai kuma wata zuciyar take k'issima masa me yarinyar take yi tsaye a gaban kango?kuma daga ganin ta kamar a tsorace take,ko d'ankwali babu a kanta ga magariba ta matso,in da take tsaye bakin kangon kuma duk bola ne.

Waiwayo wa yayi ya ta ko a hankali zuwa gabanta,ya tsaya suna kallon juna,ya D'an durk'usa gabanta ya kalli idanuwan ta yace.

"Ke!Me kike yi tsaye a bola kanki babu d'ankwali?maza ki tafi gida magariba tayi kinji ko"

Tayi shiru kanta a k'asa tana kallon ledar hannunsa.
Ya k'ura mata ido jin bata yi magana ba yace.

"Ba kya magana ne?

Sai ta girgiza kai,sannan ta cigaba da waiwaye tana kallon gefen ta da cikin kangon.

Yayi mamaki,amma ya shanye ya sake tambayar ta.

" me kike nema ne?

"Ruwa" ta ambata cikin k'aramar murya da yarinta.

Yayi shiru yana nazari,sannan yace.

"Ruwa?me za ki yi da Ruwa?

Tayi rau rau da ido tana murtsika idon da hannun ta.

" Mummyna zan kaiwa,tana jin k'ishirwa ne..!

"Ina mummyn ta ki?

Ya tambaye ta,haka kawai yaji ba zai iya tafiya ya bar yarinyar ba ba tare da ya ji dalilin tsayuwar ta a Gun ba duk da saurin da take yi,a yadda Zamani ya lalace abubuwan b'arna suka yi yawa akwai tsoro kaga Yarinya k'arama a bakin kango da magariba.

Hannu ta sa tayi masa nuni da cikin kangon tace.

" tana cikin nan..!

Gabansa ya fad'i!k'irjinsa ya buga!tsoro ya fara kamashi,ko dai yarinyar nan Aljana ce?daman gata kyakkyawa ga gashi mai tsawo!sannan ga idanuwan ta wasu iri!amma duk da hakan sai ya samu zuciyarsa da son shiga kangon domin ya ganewa idanunsa abin da ke ciki!

Hakan ya sa ya mik'e tsaye yana duban yarinyar yace.

"Muje ciki naga Mummyn ta ki,sai na bata Ruwan ta sha kinji"

Da hanzari ta saki murmushin murna har da D'an tsallen ta,tayi gaba da sauri,ya bita a baya zuciyar sa na dokawa,haka nan bakinsa na ambatar .

"حسبنا اللہ و نعمل وکیل"

Comments
Share
Vote
Pls

*TYPING*📲

✌️💔 *GARKUWA BIYU* 💔✌️

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*DA KUMA*

GARKUWA BIYU

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.