A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 24
EPISODE1️⃣
FREE PAGE1️⃣2️⃣
TYPING 📲📲📲
*Announcement*
Ina tunatar daku A mafarki nasanta ba free book bane,yanzu muna kan free pages ne da mungama free pages za,a fara payment......gamasu bukata👌
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Yana gama maganar sa ya figi motar da karfi jikake tana wani k'uuw,suma yaran sa dake bayan sa ahankali suka tada nasu motocin bayan fitar sa gate suka duk da sun hango gate man yana kokarin rufe k'ofa.....
Suna isowa bakin d'in suka dakata,d'aya daga cikin su ne ya furta sir bude muna gate d'in ,saboda dukansu ya girme su,shiyasa aka bashi tsaron gate...
A hankali wannan tsohon gate man din ya mayar musu da amsa cikin yaren india domin shi baya jin turanci,ya furta Dr.yace kar wanda yabisa,jin wannnan magana tasa ta tayar musu da Hankali,shi bai ma san yadda abun yake ba sai da suka sanar dashi,an aiki enuch da mota yakaiwa Dr.Aj amma har yanzu bai je ba,kuma meeting din na gaggawa zaije....
Dan danan hankalin sa yatashi,dan dukkansu sun san muhimmancin wannan meeting da uwayen gidansu zasuje,saboda meeting ne daya tara manyan likitoci na kasashe daban daban,gashi d'ayansu bai je ba tun da in d'aya yaje a wani lokacin ya isar sai d'aya yayi attending a system live ta hanyar comference call da ake hadawa ga wayenda basu samu damar halarta ba..
Jimami suke atsakaninsu,d'aya daga cikin sune yayi k'arfin halin furta guys muna cikin matsala idan wani yasamu Dr.bazamuji dad'i ba domin munyi ma gwamnati rantsuwar karemata su,kuma munyi rantsuwa ga abun bauta shiva,dan haka dole mu daure hakan nan mubisa duk da yayi warning namu ......Ga ra nasa fushin da wanda lord shiva zai yi damu
......Kunsan indiyawa da rikon Addini.....
Allah yakyauta,yakara tsare muna imanin mu🙏
Bayan sunyi na,am da maganar ta dan uwansu sai suka nemi gate man da ya bud'e musu gate din wanda shima yayi na,am da shawarar tasu duk da shi musulmi ne,duk da kuma ta wani gefen yana jin shakku,wanda suma sauran duk hakance azukatansu.....
......nima dai anan alkalamina yakara k'aimi wajen dauko muku rahoto.....Ku cigaba da bibiyata.......
💫Fa'eeh Bg💫
Ficewa sukayi atsare cikin gidan a cikin manyan2 motocinsu kirar hillux da wasu daga cikin normal car nasu bakake wulik,bayan wangale musu gate d'in da yayi..
*************************
Suna fita ya rufe gate din yana jimamin Abinda zai biyo baya.
A bangaren Dr.Ammar kuwa bayan fitar sa bai zarce ko ina ba sai inda Dr aj sukayi parking na motocinsu,Domin gudu ne yayi ba d'an kad'an ba, ta hanyar amfani da Gps tracking ya isa inda suke, A hankali ya tunkari motar da Aj yake ciki duk da yaji gaisuwar da yaran suke masa amma ba wanda ya tankama,Dr aj dake cikin mota har sakon zuwan Dr.Ammar ya iso masa ta hanyar Babban yaronsa dake gefen motar atsaye....
A hankali yaron Dr aj dake atsaye kusada murfi motar ya bu'de masa murfin bayan motar ,mai makon ya shiga sai yayi tsaye yana k'arewa cikin motar kallo,Bayan kamar minti biyu yasanya yasanya k'afarsa d'aya a hankali ya zauna yana mai k'ara tamke kyakkyawar fuskarsa,A hankali itama dayar leg dinshi ya janyeta zuwa cikin motar kamar wanda ankayiwa dole shiga,shiko Dr.Aj duk da yasan da zuwansa kuma yaga shigowarsa bai nuna masa ba yamai da hankalinsa kan meeting d'in da yake kallo live a yar madaidaiciyar tvn dake makale akujerar driver,wanda ake gudanarwa ahadadden hall na garin mumbai mai suna......
( MUMBAI EXPENSIVE HALL )
wanda shine Babban hall wanda gwamnatin india ta zube mak'uddan kudade gurin ginshi,wanda yaji kayan more rayuwa ta ko ina....
Shima Dr.Ammar baice masa uffan ba kawai yayi joining meeting din ta hanyar kunna tvn dake bayan kujerar dake gabansa tare da makala bluthood a kunnen sa kamar yadda aj din yayi,cigaba da kallon yadda meeting d'in ke gudana sukayi,Bayan yayi joining duk wanda ke gurin yaga Dr ammar A hankali sukayi ta daga masa hannu alamar gaisuwa shima yana d'aga musu .....Bayan sungama gaisawa suka ci gaba da gudanar da meeting din su kamar yadda suka fara banbancin kawai dr.Ammar ayanzu yana musu yan gyare gyare ne,ko yayi solving wani issue tunda duk suna ganinsa ..
Dr.Aj ba abunda yake face murmushi da alhinin halayen dan uwan nasa baiyi zaton zaiyi joining meeting ba haka,ganin rigimar da suka sha tashi bazai je ba sai dai shi yaje ya wakilcesu,haka dai suka gama gudanar da meeting din atsanake har suka kai matsaya sukayi conclusion suka watse,sukuma suka kashe tvn....
Enucch ne yak'araso jiki asanyaye bayan ganin motar ta uban gidan nasa,Parkeyn yayi agefe,ya gaiggaisa da "yan uwansa,tsaye yayi gefen da ogan nasa yake,Bayan tsayuwar da minti biyar sai ga sauran bodyguard din sun iso gurin ta yin amfani da location,duk suka firfito daga cikin motocin su a hargitse......
A bangaren su Dr aj kuwa bayan gama meeting din su,shiru ne yabiyo baya,Dr aj yakatse shirun nasu ta hanyar furtawa Dr ammar wanda ke jingine da sit dinsa idanunsa alumshe,cikin murmushi "meya ka woka nan"shiru yayi masa duk da yana jin sa,"fitar mun amota"
wannan furuci na Dr aj ne yasanya sa a hankali ware manyan idanunsa masu cike da kwarjini da haske ga kwayar idonsa maroon mai shining,Kafe aj yayi dasu wanda har sai da Dr aj yakara ja baya yana furta lafiya?
Shiko uban gayyar murmushi ne ya wanzu akan kyakkyawr fuskar sa,yana ficewa daga cikin motar koda yafito enucch ya fara cin karo bawan Allah yana ta kame kame am yallab'ai sir kayi hakuri wallahi namanta wayana a gida kuma ina tsoron komawa gida bayan nayi nisa karkaga kamar namaka rainin wayau ko yanzu ma su joshu ne nakira da karamin wayana suka min kwatancen gurin (dai daga cikin yaran aj).......
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Duk wannnan maganar yanayinta da indiancine saboda shina bai jin turanci,kuma duk abunda yake fadi dr ammar najinsa sai dai bai ce masa komaiba har ya isa inda ya parka motarsa yaren sa dake gurin duk suka taso da hannu ya dakatar dasu yana shigewar sa motarsa ......
Reverse yayi yabata wuta sai kan titi tare da shara raara gudunsa,shima dr aj umurnin ya bawa yaransa wanda cikin minti daya suka bar wurin har yaran dr ammar din....
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Alkalamin Fa'eeh Bg mai kaifi ne kamar wuk'a,kucigaba da bibiyata dan jin karshen wannan labari mai cike da abun tausayi,soyayya,cin amana,ta,addanci duk acikin littafin amafarki nasanta....Nasan wasu zasuce ai haryanzu ba,a fara nuna mafarkin ba😂to karku damu kudai sanya hakuri duk zamu kai chan .......
Dan Allah kurka comment domin shine kwarin gwiwarmu akoda yaushe🙏
💫A MAFARKI NASANTA💫
in my dream i know her
By
Pha'eezah Almstapha
Daga Alkalamin ✍️✍️
💫Fa'eeh Bg💫
Dedicated to my lovely sis laila Almustapha Murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand 🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*
pen🖊️ is mightier than the sword🗡️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.