A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 21 of 24
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣5️⃣
TYPING📲📲📲
Dasauri ta juya zuwa toilet din tana furta mama dije ruwan wanka na zasu huce tana dariya,tare da turo kofar toilet d'in,Dan tasan khady batason sunann nan na mama dijen da take kira mata ita kuma batason auntyn datake kira mata duk cikin su babu wanda yasan wanda yagirmewa wani acikinsu..
Khady da aka kira da mama dije har ta kumbura koda halee ta fito daga tolet daure da towel mai dan girma da hijab dinta d'an karami wanda tashiga dashi toilet din da zanen da tashiga dashi a hannunta,tunda ta fito take k'unshe dariyarta ganin yadda khady tayi kichin kichin da fuskaWadda har tabar kan madubin nasu..
d'an madaidaicin madubin nasu da yaji kayan gyara gwarwado na talaka,musamman turarukka sunfi yawa saboda Bba Adee akwai son kamshi,har sun saba da sanya sa ako da yaushe sai dai yana gargadin su kar su rika sanya mai tashi sosai inzasu fita ,sai dai su rika sanya wanda kamshinsa bai tashi kamar yadda annabi saw yasiffanta turaren mata,da na maza..Mai kala shine na mata amma kamshinsa bai tashi kamshi na jan hankali bare yazamacutarwa ga wani,wanda inkika shafa sai anmatso kusa dake za,aji kamshinsa,na maza kuwa marar kala ne sai dai mai karfi ne wanda duk inda suka giffta sai anji sa...
Bayan ta zauna akan kujerar madubin tafara yin "yan shafe shafen mu na mata akan lallausar fatar ta wadda kullum kamar ana mata wankan madara duk da bata da wata natsuwar zuciyah da kwanciyar hankali,turaruka ta fesa sunyi biyar nan da nan d'akin nasu yarikice da kamshi dan itama Halee nmba Banza ba wurin son k'amshi kajol tashafa da man baki lip glow take kyawonta yakara bayyana irin zubin larabawan qatar da fulanin eqypt..
A hankali tajanye hijab d'in dake kanta take yalwataccen gashinta mai laushi da santsi yabayyana wanda yake adunkule saboda kwana biyu baisamu gyara ba,warwareshi tayi masha Allah na iya furtawa, tajeshi tayi yasauka har kan gadon bayanta tasanya man gyaran gashi har wajen kala uku wanda take kannata yad'auki walkiya gwanin burgewa,Daure gashin take kokarin yi sai dai yana kuncewa sai danbe takeyi dashi gajiyar datayi ne yasanya ta fara alamar sakin kuka tana kallan khady ta madubi wadda ke zaune akan gabar katifar su,Khady dake ta k'unshe dariyar ta ce ta fito fili har tasauko daga fushin nata na wasa,'tana furta Allah yak'ara bake bace kinsan yadda gashin nan naki yake da santsi haka kika yi ta labta masa mai nikam ba abunda zan iya miki ta iyar da maganar ta na k'ara kwashewa da dariya har da rik'e ciki ganin yadda kyakkaywar fuskar Haleen ke nuna Alamar takai k'arshe kiriss take jira ta fasa kuka,kukan tafara kuwa dagaske harda buga kafafu ak'asa,fararen kafafunn ta kawai kake hangowa tana tsitsillasu akan tiles d'in d'akin kanta akan desk na madubi tana furta "nikam aske gashin zanyi na huta kawai, khady kuwa na kwasar dariya...
Rezor blade ta zago daga chan sakud'an madubi,harta d'aura akan jelar dogon gashin ta dake chan kan gadon bayanta tajawoshi gaba,zata yanke khady ta rik'e hannunta tana furta hurul aini meya yayi zafi haka yanzu dai bani rezor d'in mik'amata tayi tana cunno bakinta gaba,mik'ar da ita tayi tana daga kan madubin tana "furta mata Aunty yanzu idan kika aske gashinfa kuma kikayi Aure mijin ki naso yaza'ayi ....takai kqrshen maganar tana boye dariyarta ....
A hankali Halee ta furta sai insauka na kanti man irin na yan Nigerian film..
"Khady CE ta furta to inyace baya son sa fa ya zakiyi?,hararar khady tayi domin ta fara isarta da surutu Ga kanta yafara ciwo..
"A hankali ta furta Ke ni bazanyi Auren
Ba ma tana mai takawa izuwa sip dinsu sashen da kayanta suke ajiyeta bud'a dan kowa Dana sa gefe domin dinsu daban daban ne saboda Khady tad'ara Halee jiki,wata doguwar Riga roba ta fiddo da hijab karami,bayan ta sanya hijab har k'asa dama d'abi'ar tace sanya kaya acikin hijabi saboda kunyarta...
Ko khady dasuka tashi tare bazata iya kawo yadda take da kyan sura ba tunda suka fara girma ko bacci in zatayi sai ta sanya hijab,khady tayi tayi tabari Amma ina yazame mata jiki....
Tana cikin sanya rigar ne Tatsinkayi muryar khady na furta matar liman kiyi sauri kar Abincinmu ya huce gashi na zuba toh,tace mata tana furta,"Aa ah ba matar liman ba matar Malan cikin sakarma khady harara,dukan su dariya suka sanya na furucinta,tsaf ta shiya acikin doguwar Rigar ta wadda ta bayyanar da duka dirinta acikin hijab din kasancewar sa na roba ne kuma bakin kunkurunta ya tsaya ga tsayayyun breast din ta nan cikin rigar sun bayyanar da girman su saboda bata saka bra,acewar tana takura ta,turare ta fesa akan kayanta ta taka ahankali kan carpet din da Khady ta ke zaune wadda ta shimfid'a itama ta zauna,khady da ta fara cin abincinta CE ta furta zuba naki ga filet nan dan nikam naga alamar shirin naki bazai kare ba,filet ta dauka tazuba jalof din macaroni dan kad'an Khady CE tagaza yin hakurin maganar dake cinta ta furta " kin san wani abu?" Kai Halee ta girgiza mata, "wallahi Halee mijin ki zaiyi fama......
*GUSAU*
Abangaren su sarki Ali da unni bayan ya fito wanka ya kimtsa da taimakon ta...
manya manyan food flask ne farare kar tafara kwasowa daga falon nata zuwa uwar d'akin nata dakanta domin haka take bata yadda wasu suyi wata hidima ga mijin ta indai wurin cimakarsa ce dakanta takeyin komai,Kuma bata bari bayi su shiga har uwar dakin NATA inba Aminttacciyar masarauta ba wadda takasance tun ta kakanni ita take masa komai koda asashen sa ne.
Bayan tagama jera kulolin atsakiyar katuwar carpet din dake malale sai tayi masa I so yazauna kafafunsa ya tankwashe bayan zamansa,favourite food dinsa tazuba masa tuwon shinkafa da miyar kuka da taji busashen kifi zai tashin kamshi takeyi spoon tasanya masa aciki,d'ayan filet d'in tasanya masa farfeson kayan ciki dayaji gyara sai tashin kamshi yakeyi...
Abincinsa yake ci ahankali shayi ta had'a ma kanta itama tana kurb'a a hankali....
Muryar dan matashin saurayine dabazai wuce shekara ishirin da biyar ba ko da hud'u take yin sallama A cikin falon dukkaninsu Amsa sallamr sukayi suna masu kallon kofar shigowa,wani kyakkyawan saurayi ne Wanda daka gansa kaga gimbiyat hassana( unni)
Hatta farin fatar sa natane tsawonsa zai ne na mahaifinsa,kumbure fuska yayi ganin yadda duk suka tsira masa idanu kowa da kallon tuhumar da yakeyi masa....
Takowa yakeyi cikin tafiyar takama irinta tafiyar sa sak irinta Ammar zama yayi Ahankali kusa ga mahaifiyarsa yajingina da jikinta,sarki Ali dake kallonsa ne yagirgiza kai yana sakin murmushi yacigaba da cin abincinsa,kwantacciyar sumar kansa take shafawa da hannunta d'aya tana cigaba da kurbar shayinta....
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊
Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.