A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 19 of 24
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣3
TYPING📲📲📲
Juyo wa tayi a hankali tataka inda yake zaune ta kafesa da idanunta,jin idanunta akansa yasanya sa kawar da kansa Yana mai lakace tsinin hancinsa,irin yadda Ammar yakeyi inyana cikin yanayi mai kyau
Hannayensa ta rik'o tana furta Alhamdulillah aranta,A hankali ta bud'a bakinta tafurta nayi magana dashi shekaranjiya,yana lafiya shida d'an uwansa,tambayar ta yak'ara yi har yanzu yana kanbakansa duk da yana da labarinsa,Amsa tabashi cikin d'ar d'ar "eh amma ina nan ina kokarin janyo tunaninsa izuwa garemu da fushina...
" Dan duk lokacin da mukayi waya dashi ina nuna masa fushi na inbarsa cikin zullumi nasan cewa baison damuwar d'ai daga Cikin mu,ko sharekan da yayi nasan kai kafara nuna masa taurin kai irinka naka,Allah kad'ai yasan yanayin dayake ciki ayanzu,zuciyarsa akar ye take,ni nasan waye Ammar cikin sa da bayansa,kuma nasan waye mahaifinsa...takai karshen maganar cikin jin tausayin yaron nata wasu hawaye ne suka zubo a idonta..
Murmushi sarki Ali yasaki jin kalamin ta na k'arshe..
"A hankali ya furta na janye maganar bashi sarautar,ayanzu inaso su dawo kusadamu gaba d'aya
Ayanzu haka nakusa kammalla Gina masu babbar asibitinsa domin sudawo su rik'e ta shida d'an uwansa su kula da ita....
Farinciki ne mai yawa ya bayyana A fuskar gimbiya hassana,rungume sa tayi tana zubarda hawayen farin ciki da godiya ga Allah,daya nuna mata wannnan rana data dad'e tana mafarki
Shima rungume ta yayi cikin farin cikin dayasamu kansa a cikin cigaba da maganar sa yayi " nasan cewa Ammar yana da kud'in da zai Gina wannan Asibitin,Amma na zab'i inginata masa ita dakaina saboda inason yarike ta da mahimmanci idan yatuna wannann kyautar mahaifinsa ce a garesa,kuma A duk lokacin da akayi ceton rai acikin Asibitin nasan cewa ladar zata je garemu kobama Raye muda sauran iyayenmu...
In sha Allah wannnan Asibiti zata zamo Abin Alfahari acikin wannna kasar mu tana Nigeria dama sauran kasashen...
'Murmushi da dariya ne yake fita akan fuskar gimbiya hassana a lokaci d'aya k'ara rungume sa tayi acikin jikinta,
Murmushin ne shima yake yi na farincikin ganin yalwataccen farinciki a akan fuskar matar tasa,Wanda tada d'e batayi ba, Wanda tun bayan da yafara maganar murabus,juya mulki ga Ammar d'in,Wanda alokacin anti tak'addama sosai dan yakafe yace baiso mulkin shiyasa mai bai cika kawo musu ziyara tun da yaji anfara maganar,sai dai tawaya su gaisa shida mahaifiyarshi da "yan uwansa,Dan har wayar sarki yabar kira tun lokacin da akayi rigimar yakira mahaifin nasa yafi missed call ishirin bai d'aga ba,domin alokacin yana fushi dashi mai tsanani,saboda maganar da sukayi inda yake sanar masa kar yak'ara kiransa da mahaifinsa indai bazai karb'a ba,shiyasa daya kirasa bai d'aga ba domin yasan ba maganar da yakeson ji d'aga bakin sa bace zai furta masa...shiyasa shima sai yasharesa bai k'ara Neman saba tun lokacin duk da dukkansu suna azabtuwa,Amma zuciyar d'ayace,kowa kafiya da taurin rai..
Sarki Ali yatsinci kansa sosai cikin farinciki sanin da yayi Ammar d'nsa zaiyi farinciki fiye da nasa jin wannan labari....
Wayarta tadauko dasauri bayan mik'ewarta d'aga jikinsa,muryarsa ta tsinkaya yana furta karki sanar masa sai ankammala komai har janye maganar basa mulkin,b'ata fuska tayi,tana furta "saboda me adili"? "
Murmushi yayi ganin yadda tayi kamar wata k'aramar yarinyar,yana furta inaso ne kawai yazame masa Abun kamar A MAFARKI ne murmushi tasaki,tana furta hakan yayi, Amma dai bari insanar wa sister wannan abun farincikin sai muyi farincikin tareπ
"Murmushi yayi yana furta to ki kwatse ta koh kar ta kirasu ta sanar da Al Amin,Amsawa tayi cikin k'aramar dariya ai ko haka za,ayi......
Ruwan wanka ta had'a masa a cikin k'aton bahon wankan na silver mai kyau,dake a cikin had'ad'den k'aton toilet din dak'in nata Wanda yaji kayan k'yalk'yali ta ko ina......
Bayan yashiga yayi wanka tafito masa ta da kayan da zai sanya,sannan ta fita domin Bada umurnin akawowa abinci a turakarta,A falon da na biyu kamin kashiga uwar dakin nata,Abincin suka jera cikin tsari mai kyau akan wata had'addiyar carpet din dake malale afalon,Alokacin duka ma'aikata sun gama ayyukansu na rana...
Kuyi hakuri da wannan ba nida isashen chaji ne
Shinko kuna ganin Dr.Ammar zaiyi farinciki?
Kuma zai baro k'asar India?
Shin ko akwai sanadin da yakai sa k'asar India karatu,ko ko dai Ra,ayin kansa ne?.......
Jama'a ina labarin Halee nasan wasu harsun manta da ita ......
A gobe in sha Allah zamu lek'a rayuwar Halee baiwar Muji a wani hali take sannan wace irin rayuwa take fuskanta ne ayanzu shinko Baba Asabe ta shafa mata lafiya ganin idanun Baba Asabe ko kodai tacigaba da muzguna mata......
Wacece ita?
Mekuke tunani game da rayuwar Halee?
Mu had'u a comment section dan jin hasashen kowannenku.......✍️✍️
Shin tsintacciyar ce dagaske kamar yadda Baba Asabe ke yawan furtama taa?
Shin waya bada Amanar Halee da har Baba Adee yakirata da Amana?
Sannan waya bada Amanar ?
Waih........🤭
Nima fa kaina ya kulle 🤔
Kudai kawai kucigaba da bibiyar Alkalamina✍️✍️domin Warware muku wannan labari mai cike da darussa...
Kuyi sharing kuyi comment
💫 FA'EEH BG💫
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥
*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*
*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........
*+2348069059746*
*+2348084504630*
----------------------------------------------------------------
*💫A MAFARKI NASANTA*💫
*2023 novel is the story of an innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA KO MASU MUKAMIN *MENE DASU DA HAR ALKALAMINA YA KIRA SU MANYA KASA*....
*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA*
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER'S📚🖊
Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.