Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️️6

TYPING📲📲📲

Gyaran murya sarki Ali yayi Wanda yasanya mahir d'ago manyan idanunsa yakallesa,muryar sarki Ali ke furta wai kai Baba yaushe zaka girma ne eh kullum Kullum haka kake komawa d'an jiya Yanzu idan ka karya mun kad'ar mata fa ya ida maganar Yana sakin murmushi,Dukkaninsu ma murmushin sukayi, cigaba da magana yayi wai ko kamanta akwai yuhanis A bayanka ne Yana rike hab'arsa irin mamaki...

Dariya mahir yasanya ganin yadda mahaifinsa yayi,A hankali ya furta Ayyah Abbanmu ni Dama nine Autan ba wacchan sakaryar ba,...

"Ai inson jiki ne da shagwab'a sai naga kamar ka fita ma inji" cewar sarki Ali
Murmushi kawai gimbiya hassana take ta saki jin rigimar tasu,bata cika sanya baki ba saboda Karrama sunan sunan mahaifinsu dake gareshi,shiyasa take d'an basarwa saboda Alkunyar jinin larabawa da Fulani dake yawo ajikinta..

A hankali ta furta Baba na meya dawo dakai gida irin wannan lokaci kai da kace kuna da lectures har har uku ko ma hudu ne,Agogon hannunsa ya duba karfe biyu 2:00 pm na rana ya mutsa fuskar sa yayi yana furta" unni kinga sai karfe hudu bayan la'asar zamu koma hall kuma kinga lecturen da zai muna lecturen karfe hud'un akayiwa mutuwa mahaifiyarsa ta rasu sanadiyyar gobara sanadiyyar wutar lantarki datakama gidan tsohuwar shine dukan mu duka yan hall din mu har lecturen da yake lecture awannan lokaci duk muka tafi gidan mutuwar muyi gaisuwa,shine daga chan nacewa su Abdallah na wuce saboda kaina dake ciwo",Addu,a suka yi ga mamaciyar cikin jimamin domin kowa yasan kunar wuta yadda take da azaba bare ma Ace duka jikinka ta cinye,ALLAH YAKARE MU DA SHIGA WUTAR JAHANNAMA🙏

Wanda Alokacin dukkansu sai da suka ji wani kololon aransu,ganin yanayin da mahaifannasa suka shiga yasanyasa jin ba dadi yanaji dama bai sanar dasu batun mutuwar ba domin yasan dama dole zasu badadi,tun da irin haka ta yataba faruwa ga uncle dinsu lokacin bashida wani wayo kuma Ammie tana yawan yin maganar agaban su cewa sun tab'a rasa family d'aya acikin zuri'ar su,ta sanadiyyar gobara,domin tana cewa dasu su rika sanya su a Addu'a,duk dashi yasan su harda yar tasu Sai dai bazai iya tuna yadda fuskokinsu suke ba duk da ance suna kama sosai ne da su,Ayanzu yana son yaji yadda labarin abun yafaru duk da yasan wani abu daga ciki...

Muryar mahaifinsa ce tadawo dashi daga tunanin zucinda yashiga"maheer kaci abinci sai kasha magani ko kaje ka d'an huta"?murshin yake yasaki jin maganar da mahaifinsa ya furta,gashi shikuma yana da tambaya agaresu,Amsawa yayi da touh! sai kuma ya bud'a bakinsa da murya mai rauni yace "Abba da Unni please ku k'ara sanar dani labarin su uncle dasuka k'one achan baya Domin Ammie tana yawan furta mu musu Addu'a inason insan silar wutar tasu...

Murmushin karfin hali irin na mahir sukayi sai kuma Ahankali sarki yafurta kanason kasan yadda labarin yake duk da nasan kasan su alokacin baya wanda bawani wayo ne dakai ba...

kai mahir yad'aga.

*LABARI*..........................
A wata safiyar laraba da bazamu tab'a mantawa da ita ba A cikin masarauta muka wayi gari cikin tashin hankali bayan samun labarin gidan D'an uwa na Sarki Umar Yakama da wuta.......

A lokacin da labarin ya riski sarki Ali dasauran mutane masarautar sun kid'eme sosai fiyeda tunanin mai karatu,koda aka kira fire service domin kawo taimakon gaggawa duka dukan gidan yacinye da wuta ba'asamu komai agidan ba face gawawwakinsu dasuka koma babu kyan gani,A lokacin Ammi da su hassana da husaina kamar su fad'a cikin wutar dakyar akasamu suka natsu bayan anrirrike su, musamman Ammar Inka ganshi yakoma kamar zararre duk da karancinsa,kowa kagani alokacin tashin hankalinsa Abayayne yake musamman na rashin ganin komai da yashafi yarsu kwaya d'aya tilo a duniya yar shekara biyu da ba'ayi ba sai tokar,mutun d'aya zuwa biyu wayen da suka nuna ko inkula akan kaddarar da ta farma su Sarki umar ,shine muhammad (Malan) Da mahaifiyarsa fulani duk da yadda suka nuna ko ajikinsa Amma babu wanda ya zarge su akan wani abu,duk da anyi bincike ba, angano sanadiyyar tashin wutar tahanyar jin kamshin fetur acikin sashen nasu wanda aka tabbatar zubasa akayi kuma shine sanadiyyar tashin wutar, kowa yayi mamakin kasancewar fetur din acikin gidan hankalinsu ne yakara tashi fahimtar kamar akwai wani abu akasa...

Anyi zaman makoki an watse lafiya wanda har lokacin Ammar bai koma dai dai ba tun bayan da yaji yaga yadda wuta ke cin gidan uncle dinsa,kuma yaji ance gabaki d'aya sun mutu har Auntynsa da norah, duk da yadda akayi kokarin boyemusu shida mahir da Al amin,yayi suma yayi biyar ana ukun ne yayi doguwar suma wadda bai farfado ba har saida akayi ukun su sannan,Tun alokacin yafara mugun mafarki naban tsoro agigice yake farkawa sai kuma yafara yadawo yafara yin na k'aramar yarinya na kuka tana neman taimakon sa wuta na cin jikinta sai yaje taimakon ta sai ta zille ta karasa fadawa cikin wutar bata bari yarik'o ta haka yake mafarkin kullum har mahaifiyarsa da mahaifinsa suka gane abunda yake faruwa agaresa bai dawo dai dai ba sai da akayi wata biyu,wanda Alokacin Al Alamin ne mai lallashin sa ko mahaifiyarsa inda zuwa lokacin mafarkin nasa yazamo yabar ganin karamar yarinyar acikin wuta..

A baya A kullum yakan yawaita furta uncle dinsa ba mutuba da auntynsa da norah d'insa sunyi tafiya ne,inda sai da ka tayarmasa tsaye aka dage da Addu'a yadawo normal ganin abun yafara tabasa yakusa zame masa hauka,Bayan samuwar kansa sai aka tura su k'aasar india ganin cewa idan yanisanta da gida zaifi dawo wa dai dai yasake kamar kowa,Achan suka cigaba da karatunsu tundaga primary three din da suke a nigeria,sai dai kamar yadda kayi tsammani bayan zuwansu kasar india nadan lokaci,suka ga yara ire irensu ga wuraren wasanni nan kuma karatun su suke ba wasa sai Ammar yafara mantawa yafara sakin jikinsa ga sauran makarantar tasu domin boarding ce,wanda kuwa afarkon zuwansu Al amin kadai yake mu,amala dashi,A lokacin ne mafarkin daya keyi achan baya yadawo masa,A wanchan lokacin yana ganinta cikin kuka ayanzu kuwa cikin tafiyarta irinta ta yara masu wayo yake ganin tana wasarta tana dariyar ta gwanin bugewa,bata ma kulasa duk da yana ganinta tana ganinsa.

Tun mutuwar nora dinsa yace bayason yin karatun likitanci bayan tabbatar da cewa dai tatafi domin dama danta zaiyi,shi burinsa dayatashi dashi shine karatun pilot waton matukin jirgi,wanda shikuma Al Amin nasa burin keman yayi karatun likitanci,wanda sai da mahaifinsa yabashi baki yace yayi yataimaki Al ummah saboda Alllah itama dasu uncle dinsa zasu samu lada wannan kenan.

Kaji dalilin zaman yayanku doctor akasar india, da kuma dalilin dayasa yayan ku yake zama india shida Al Amin har yazamana sun zamo manyan likitota akasar da batasu ba...
**********
*******
****
------------------------------------------------------------------
"Sarki Ali ne yaci gaba da maganarsa D'an uwana sarki umar a wanchan lokacin shine ya mulkar masarautar nan,yana "yaa norah wadda taci sunan kakarku hajiya sai kuma matarsa lailat ina fa'd'a make kawai duk da nasan kasani yadda zakaji komai yadda yake alabarin ne..yakai karshen maganar cikin wani yanayi yana jin komai yadawo masa sabo...

Hawayene Suka zubo a idanun mahir dasu yuhanis,da sumee da zuwansu kenan aka fara bada labarin sai da babu wanda ya lura dasu,sunyi sallama sai dai ba'a amsa musu ba shine dalilin dayasa suka shiga falon kaitsaye,Haka itama unni hawaye take zubarwa mai zafi maimartaba sarki Ali shine mai lallashin su,shine yafara lura dasu Nisa A tsayen dasuke ido jage jage da hawaye kyafato su yyi tahanyar yimusu Alama..

A hankali suka taka inda suka zauna akusa dashi suka sanya sa tsakiya,suna masu cigaba da zubar da hawayen su,domin su ana goyonsu ne lokacin basu san komai akan labarin ba sai yau duk Ammi na yawan furta musu sumusu Addu'a..

Share musu hawayen yayu yana furta musu kudaina kuka kunji "ya "yan Unni,kai suka d'aga masa da alamar toh,suna masu sake share hawayensu,"kara furtamusu yayi kumusu Addu'A kunji ita suke buk'ata agareku..

Yau ansamu long page😎

https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥

*MASU SON A TALLA TA MASU HAJARSU*
*SHOULD CONTACT ME VIA*
*+2348069059746*

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊

Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.