A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel
Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 24 of 24
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣8️⃣
TYPING📲📲📲
Duk da bata juyo ba tasan aikin waye,Nisa ce ke sakin karamar dariyarta tana tare da tafa hannayen ta a hankali bayan isowarta kusa da sumy ta furta acikin kunnenta "me kika gayawa yaya mahir naga yana sakin murmushi"
Aiko da jin maganar ta Nisa sumy ta kai mata d'an karamin dundu abayanta,da sauri ta Nisa ta juya dagudu bayan jin dundun da takai mata tana furta sai nagayawa Unni da Abba soyayya kukeyi,ai kafin takai ga bude kofar Second falon na Unni har mahir ya chafko hannunta ido ya raina fata Nisa A hannun mahir dan tasan bawai wani raga mata yakeyi ba take ta raina kanta hawayen karya tafara matsowa tana bashi hakuri tun kan ya kai ga hukunta ta ta.
Kansa kawai ya girgiza yana mai furta "mai kikace zaki fadawa su Unni ne "?
Shiru tayi sai dai faman girgiza kanta kawai takeyi tana cigaba da kakalo hawaye,warning ya buga mata akan kar ta yadda tasanarwa da kowa tagansa tsaye da sumy,Sannan yasake hannunta yana furta stubborn girl.
,,,,,,sai da ta bud'a kofar shiga falon sannna ta juyo ta murgud'a masa baki.
Itakam sumy dariyar ta kawai takeyi kasa kasa.
Bayan wucewar Nisa ya kalli sumy kallo irin na zamu had'u,ya juya ya yayi hanyar nashi dakin wanda yake chan jere shidasu dr Ammar A wani lungu da yashiga ta falon unnin.
Bayan wucewarsa itama sumy ta taka afalon na unni da tunani barkatai aranta.
A bangaren Abdallah kuwa yanayin yadda mahir ya amsa masa ne bai masa ba,Amma sai bai kawo komai aransa ba,face tunanin kila ciwon kannasa ne ya sanya sa zama haka
*BUG*
Abangaren su halee kuwa wallahi mijin ki zaiyi faman da khady ta furta ne,yasanya Halee data debo yar madaidiciyar loma a spoon tagaza kai ta kan d'an karamin bakinta wanda yake d'auke da pink lips,dasuke shekin maik'o dan maganar ta Khady ita dariya tabata,sai da takai lomar abakinta tana tauna a hankaali sannan cikin sanyin muryar da zame maata jiki ta furta"meya sa kikace haka"?
Cikin zakuwa khady tafara jero mata halayenta wayenda suka zame mata jiki ko ince wayenda aka halicceta da su ,"kinga na farko ni ban masan yadda zaiyi dake ba mutun kullum ciki hijab tafurta cikin dariya ni na namatsu in ganki gidan mijinki inga yadda zaki yi"
A bangaren Halee murmushi kadai ke wanzuwa akan kyakkyawar fuskarta tana cigaba da cin abincnta hankali kwance,khady ce ta cigaba da maganar ta"mutun inkayi magana bai baka amsa ina lafiya" wannan karon Halee sai da tadara harda rike ciki,wanda sai da fararen hakoranta suka bayyana, itama khady dariyar takeyi ganin yar uwarta na farin ciki.
A hankali ta furta bayan gama dariyarta "to me kike so ince ne yar karamar harara khady ta watsa mata chan takara furtawa "bari kiji mama dije cikin d'an murmushi wanda ya fito da side dimple dinta da ya lob'a gwanin burgewa ta ce ni bari kiji koda nayi Aure babu wanda ya isa ya hana ni sanya hijab dina,sai maganar dake cinki ta biyu dan naga kina kalllon filet dina,kinfi kowa sanin ban cika son cin abinci mai nauyi ba saboda bana son inyi kiba inkoma mama dije tulluka gaki nan kina ta zama lukutarki takai karshen maganar cikin sakin karamar dariya,itama khady dariyar tayi tana furta nice yar lukuta,zan rama ,ai gashi nan ke kuma kina ta zama iccen kara mutun kamar iska yakwashesa inbanda wannann abun da wannana abun da bakomai cikin ki tana nuna breast dinta da hips dariya dukkan su suka kwashe da ita musamman Halee da maganar ta bata dariya...
Bayan gama cin abincinsu ne, Khady tafara yiwa Halee kalabar dogon gashinta mai santsi da dubara,ana take shaida mata....
Ai Baba Asabe ta fita tun karfe takwas tayi wurin zaman makoki mamaar Babar Aminiyarta larai,sai maraice tace mata zata dawo.
*Niko nace kaga su Baba Asabe an zake dayawa sai kace masu wata hidima ta biki tun safe sai maraice,ko da yake yanzu haka nan akeyi musamman ingidan mutuwar akwai maiko Allah yasa mudace muyi kyakkyawan karshe.*
Hamdala Halee tayi A zuciyarta na farinciki jin wannnan labari na Khady ganin yau zata wala,Tambayar khady tayi cikin yanayin farin ciki "to amma meyasa baki tada ni ba nayi ayyukka na"
"yau ni tace in yi Ayyukkan bake ba" khady tace mata hakan ne kawai.
Halee dai tasan sarai karya khady ta fad'a mata dan tasan wacece baba Asabe,Tunano yadda sukayi da Bba Asabe tayi ajiya kan kawai ta dade ba kawo ko sawu daya na ruwa ba domin harda marinta tayi wanda ita kuma jira ta tarar a bohol din....
Hawaye ne shar suka silalo mata a ido tayi saurin gogewa gudun kar khady ta gani,sai dai khady ta riga taganta kai kawai ta iya girgizawa tare da share nata hawayen daya zubo mata na tausayin yar uwarta.
........Mganar Baba Asabe ce ta fad'o mata arai kafin fitar ta zuwa gidan gaisuwa Halimatu!Halimatu shine sunan da BAba Asabe take ta kwad'a kira,wanda sautin neya farkar da Khady jin Bba Asabe na doso d'akin nasu ta mike da sauri bayan bude idanun nata kazazam ta yi saurin lullub'awa Halee bed sheet dake tsakanin filonta da na Haee Sannan ta isa bakin kofar da sauri alokacin itama Baba asabe takawo bakin kofar....
Gaidata ta Amsa mata cikin sakin fuska
Sannnan ta furta" ina yar iskar yarinyar nan take bataji ina kiran sunan ta bane ko wani sabon iskan ci ne ta tsiro dashi ehh"?takai karshen maganar tana kokarin yaye labulen dakin sai dai Khady ta hanata ta hanyar kara kare bakin kofar tana ta faman susar kai na rashin gaskiya Baba asabe kuwa kafeta da idanu kawai tayi ganin wani sabon iskancin gun yarta furta wa Baba Asabe tayi innata tashiga toilet ne,Uhm meye na kare mun kofa eh sannan uban mi takeyi acikin toilet din tabarni inata turar labb'a ga yar iska,Ganin tana neman tada HAlee da hayaniyar ta yasanya ta marairaicewa tana furta innata kaina ke ciwo gashi kinata d'aga mun murya aka.
Sassauta murya Baba asabe tayi tana furta inta fito kigaya mata tadaura miki abun karin kumallo da ruwan zafi sannan ta gyara mini d'akina na Alhaji nasan basai nace ba ashare agoge ko ina ,harda toilet,sannan intagama acika kwannan gidann nan kuma akaimani ruwa makewayi na,saura kuma ki sanya mata hannu tunda nasaka ki tana gama maganar ta fuuu ta fice daga gidan har ta kusa ficewa khady ta furta inna ta inazaki tunda safen nan,gidan larai zani mahaifiyarta tsohuwa ta cika dazu anfada amasallaci,Ayyah khady ta furta" Allah yajikanta da rahama" Amin Ta furta tasa kai ta fice gidan.
KAI BABA ASABE AJI TSORON ALLAH WANNAN SONKAI YAYI YAWA.
Bayan fitar ta ne khady tayi dukanin ayyukan da Baba asabe yar sonkai ta lissafawa Halee domin tasamu koda hutu yaune kafun dawowar Baba
Adee.
Bayan Gama wannan tunanin sai ta fara jan Halee da fira duk da ba duka take amsawa ba domin har yanzu akwai sauran tunanin mafarkin nan aranta dakuma zaginta da Baba asabe ke yi.
*GUSAU*
A Bangaren sarki Ali kuwa bayan ficewar Nisa A dakin ne ya furtawa Unni "ya "yanki fa kamar akwai wani al amari atattare dasu ni gashi tuni har nafarawa ba indiyen yaronki kame,sai kuma naci karo da wannan sabon al amari yakai karshen maganr yana murmushi,murmushi Unni tasaki itama tana furta to dad'a yaran yanzu ba,a gane cikin su ta yuyu akwai wani abun atsakanin su amma suna boye wa ne duk da nasan Baaba na baida nuk'u nuk'u a irin wannan maganar kamar Ammar wanda har yanzu ko budurwa baida ita gasu girma nata zuwar musu gaskiya insuka dawo ka nema musu mata ko cikin ya yan kawayenka ne na matsu inga jikokinmu takai karshen maganar cikin dan murmushi najinin larabawa da fulanida ke yawo ajikinta,shikansa sarki Ali murmushi yayi yana furta gaskiya kam dole in nemo musu mata tunda har gimbiya sarautar mata tafara maganar jikoki agabana yakai karshen maganar yana leken fuskar Unni data sunnar kasa na kunya.
Wallahi soyayyar tsofaffin nan na burgeni...😄
Sai da taga yajanye daga kallon ta dayake yi sannan tacigaba da magana,maganar Ammaar mu kyaleta kawai Adili kabar ta bamusan Alkhairin da ke shirin shiga atsakaninsu ba wanda Allah ne kadai yabar wa kansa sani.
Hakane sarki Ali ya furta sannan yakara furtawa su mutanen india mubarsu sudawo muga inbasu fitar ba sai anema musu, shi yarima inbanda kaddara ai dayanzu da matar shi ahannu Allah ya jikanki norah keda mahaifanki,Ameeen suka amsa su duka cikin wani yanayi shikuma Al amin Auta ta zan bashi inyanaso..Yakai karshen maganar yana murmushi,itama Unni murmushin kadai tayi tana furta Allah yatabbatar da Alkhairi,Ameen sarki Ali ya Amsa.
yana mai Mikewa tsaye rawaninsa yanad'a wanda da taimakon Unni yadaurasa sannan ya sanya alkyabbarsa wata colour maroon mai stone da wata zaiba abun sai wanda yagani.
Shigowar Nisa da minti kusan Uku sai ga Sumy tashigo,A hankali sarki dake gyaran Alkyabbarsa yabfurta y"a yan ummi nizan koma fada,yaushe zaku wuce ne,cikin sauri Nisa ta Amsa da Abban Yanzu tana zunburarar baki dan duk gidan ya gundureta tunda mahir yayi mata rankwashi akai,
Murmushi kawai Unni tayi tana fadin har angaji damu kenan?kai ta girgizawa unni tana mai kara turo d'an karamin bakinta gaba.
Sarki Ali kuwa yar dariyah yayi yana furta waya tab'a mun Auta nah yana murmush,ai kamar jiran tambayar tasa takeyi sai ta fashe masa da kuka,jawota yayi yana lallashi yana kara tambayar ta meya faru?.
In sha Allah ayanzu har weekend zaku rika samun update domin namatsu mu gama book one.
DAGA ALKALAMIN✍️
💫FA'EEH BG💫
Pls like,share and
comment
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.