Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE6️⃣

dama na fada muku page dinku na friday sai yau to ga alkawarinku nan na cika✌️✌️

TYPING📲📲📲

Khady cikin murmushi ta furta tana daki na barota ta shiga wanka kai yad'a ga mata alamar gamsuwa,firarsa ya cigaba da yi da yarsa cikin lumana yana tambayar ta ya karatunsu na islamiyya da na boko tana bashi amsa da alhamdullillah, masha Allah sai akara dagewa kinji Ya furta cikin jin dadi,kai Khady ta d'aga masa tana furta in sha Allah Anan take sanar masa da Halee bata je ba yau,Assha!Assha! meya hanata zuwa injin dai ba ciwon kanne nata yatashi ba...Yakai karshen maganar cikin nuna tausayinta kara furta wa Khady yayi tun yaushe yatashi ?tun dazu da asuba,tashi ki kira mun ita in ta fito tau tace sannan ta tashi ta wuce dakin nasu domin kiran Halee.

💫Fa'eeh Bg💫

Kanshi ya juyo dashi gefen da Baba Asabe take Yana furta Laure shine baki gayamun ba tunda nashigo,Baba Asabe da tun da tun dazu take cike da jin haushin shi nakiran Halee da yayi da shalelensa duk da bayanzu ne tafara jin yana kiranta haka ba tun tana karama,Dan bata son yana nuna wa Halee soyayya fiye da Khady duk da yana kamantawa Acewar ta yar tsintuwa ba "ya bace,dakyar ta bud'a bakinta tabashi amsa saboda haushi ga tsoron ta nuna mishi taji zafin maganar da yayi mata dakuma Kiran Halee Shalelensa,Haba Baban Hadiza yanzu fa ka dawo,ruwa kadai kasha ni dama yanzu nake niyyar sanar maka takai karshen maganar cikin danne wani kololon bakin ciki da yataso mata,niyya ya maimata abayyane yana gyad'a kansa cikin alhini ya nagayamiki duk randa ciwon shalelena yatashi ki rika kirana awaya in ba nanan sai inturo nurse kamal ya duba ta Amma da yake ita ba Khadija bace sai kike yin biriss da lafiyarta,ace kullum sai na maimaita miki maganar cewa ita din amana ce ta Allah agare mu,Amma na fahimci bakya ganewa kuma na fahimci har yanzu na baki dauke ta amatsayin yarki ba dan ina da tabbacin da Khadija ce keda wannan lalura haka da kin kasance mai kulawa nasan da gudu zaki sanar mini in ya tashi amma dan rashin Amma ni kike shaida ma wai yanzu kike da niyyar sanar mini,nasan kuma da khadijan ce da tun da asuban nan kinkira kinsanar mini,nasan kin sani keda kanki kika karbi amanar yainyar nan ba wani ba dan haka kiji tsoron Allah ki kara riketa da Amana.
Duk wannan maganar dayake kanta nakasa dan tasan yau ta dan ballo wani yanki na fad'ansa,ita inbanda tasan duk randa Halee bataje makaranta ba ciwon ta yatashi da bazata san bata da lafiya ba,tunda kosu yaran sun sani ko sungayamata babu abunda take iya yi face ma tabi Haleen da zagi ko gwacine,batun yau ba Halee na rashin lafiya Amma Baba Asabe bata kiransa tasanar masa in baya gida da yake ba,a garin yake aiki ba in yatafi yana kwana biyar ko sati kafin yadawo shiyasa wasu lokuttan har ta gama jinyarta bai sani ba.
Maganar shi tadawo da ita daga maganar zucin da takeyi....Yana furta wallahi Laure ki guji b'acin raina izuwa wannan lokaci ransa yakara baci ya hasala jin saoboda shirun da tamasa,Cikin danyin kasa da kai Baba Asabe ta furta Baban Hadiza Allah yabaka Hakuri,bai tanka mata ba sai ma cigaba da maganar sa da yayi yana furta baki san girman Amana ba Laure ba shiyasa Amma zanyi maganinkin dan bana son kikawo mini shirme cikin gidana dan haka kikiyayi b'acin raina karki kai ni baango ...........
Sallamar su Halee ce ta dakarar shi daga sake yin magana,Assalamu alaikun dady nah
Halee ce ke ke maganar da murmushi kwance abisa kyakkyawar fuskarta kyau da annuri wanda ke nuna farin cikinta na dawowarsa gidan,cikin shigarta ta wata doguwar riga yadi pink mai taushi da d'an madaidaicin hijab dinta fari wanda yakara haska farar fatar ta wanda har kashe ido take yi kamar zinari acikin azurfa,inka kalle ta kyakkyawar fuskarnan sai sheki take yi kamar wankakken gold gwanin burgewa kai bazaka ce tana da daamuwa....

💫Fa'eeh Bg💫

Wslm Halimatu Sadiya mai tagwayen suna kuma shalelena inji cewar Baba Adee cikin farincikin ganin ta yake furucin murmushi kwance afuskar shi shima.
"sannu da dawowa ya hanya" ? inji Halee tana kara sakin kayataccen murmushinta jin yakira cikakken sunanta wanda kamar ga bakinsa aka rada sa,kuma tana jin dadi yakira ta da hakan,Alhmdllh lafiya qlau hanya yakarfin jikin ki ance baki ji dad'i ba, cewar Baba Adee,ehhh naji sauki alhmdllh ai har nasha magani na yanzu kafin in fito,d'anyin shiru tayi tuna yadda tasha maganin wanda sai da Khady tace zata hada ta da dady ne sannan tasha shi dakyar kamar tayi kuka dan ta tsani magani ko allura,Dan kallon khady tayi wadda itama ita take kallo jin yadda take bayani kamar ba sai da ta tilasta mata ba,kawar dakanta tayi daga kallon Khady tana maida hankalinta ga Baba Adee wanda ke furta masha Allah haka ake so ai har ina maganar akira likita ko muje asibiti
Murmushi tayi tana yin kasa da kanta wanda har kyawawan hakoranta farare tass suka bayyana gwanin burgewa tace Naji sauki dady kuma sosai,murmushi ya karayi yana furta to madalla Allah yakara Afuwa,Ameen Halee da Khady suka amsa, yakaratun su da makaranta ya tambayeta kaamar yadda yatambayi Khady,Alhmdllh ta furta,kara furta mata yayi ya gidan kuma dan shiru tayi sai kuma cikin yanayin sanyinta ta furta lafiya lau kai yajinjina kawai batare da yakara furta komai,Baba Asabe ce da tagama girkinta na jallof din taliya da taji alayyahu,Ahankali tasauke wanda ta zubowa Baba Adee agaban sa cikin wani filet na tangaram irin na da mai kyau tana furta Baba Hadiza ga abincinka nan tayi maganar fuskar ta sai sa sai sa ba fushi ba murmushi dan bataso tana wani abu yakara hawa,wadda tun lokacin da ta samu su Khady sukazo gurin ta bar wurin tare da kayansa ta kai masa daki sannan ta wuce kitchen.
Bayan ta aje abincin ne ta koma ta debo masa ruwa na randa masu sanyi acikin jug mai kyau na kofin silver sannann tazauna,bai cemata komai ba yajawo filet din da ta aje agabansa yadora gabansu Halee yana furta kuje ku wanko hannayenku kuyi bisimllah muci abinci koh cikin farin ciki suka amsa masa da tau,Baba Asabe ce tayi karaf tana da niyar da katar dasu tana furta gana su chan akitchen na zuba musu suje su dauka,hannu kawai yadaga mata yana kara mata maimaita musu da suje su wanke hannayensu,wanke hannayen su keda wuya suka fara cin abincin tare dashi bayan duk sunyi bisimillah abayyane yaji su suna ci da hannu shi da spoon,cikin natsuwa suke cin abincin su tare dashi gwanin burgewa wanda dagani sun saba ne,Baba Asabe bata kara furta komai ba harsuka gama cin abincin su suka sha ruwan randa masu sanyi wayenda takawo masa,bayan sun wanke hannayensu suka furta alhmdllh atare wanda dama dab'i ar da ya sabar musu da itace,zasu yi basmala atare hamdala atare komai suna yinsa atare ne sun tashi da soyayyar junansu tun suna kana na.
💫Fa'eeh Bg💫
Masha Allah ya furta to tunda duk kun koshi sai aje afara shirin zuwa makarantar islamiyya koh,ehh suka amsa suna mikewa suka wuce dakin su cikin natsuwa ..
Shima tashi yayi ya wucewarsa nasa dakin domin watsa ruwa,Baba Asabe bata iya cemasa komai ba har ya yi shigewar sa dan tasan ta ba'llo ruwa,tasan bazai jirata ta hada masa ruwan wankan ba duk da shi ba mutum ne mai riko ba.
Abunda yafaru kafin fitar Khady gidan shine bayan tadawo makaanta
Cikin sallama ta shiga madai daicin gidan dai dai rufin asiri gida ne mai dauke da daki uku biyu suna kallon juna sai daya achan gefe wanda yake shine nasu halee biyun kuma nasu Baba Adee da Baba Asabe,sai toilet daya natsakar gida, da kichen shima chan gefe farkon shigowa gidan ga tsakar gidan ma da wali gidan masha Allah ko ina ka duba kwal kwal yaji suminti,inda ta iske Baba Asabe tsakar gidan tana fifita da yake lokacin zafi ne,Sallamar ta Baba Asabe ta amsa mata da murmushi ta na furta tagaban goshina kindawo itama khady cikin mayar mata da murmushin ta furta ehh Babata nasame ki lafiya,lfyalau Hadizata
Babata yau Dady zai dawo koh!inji Khady,ashe kina lissafi yar nan yaufa ne zai dawo murmushi mai hade da murna khady tayi tana furta yo ba dole ba Babata, Munyi missing nasa ne tana maganar tana dosar dakinsu da gudu tana kwalawa Halee kira,Halee! Halee!

Tana yaye labulen taga wayam katifarsu bakowa adakin, katifarsu kadai ce da tasha lailaya sai kayan sip dinsu wanda Khadyn ta ya mutsa kafin taje makaranta,wanda Halee ce take aikin bayan tadan ji dama damar jikinta,tana cikin aikin ne Baba Asabe ta kirata ta Aiketa kasuwa kutsa kanta tayi cikin tare da kara lelleka ko ina dan tabbatar wa indagaske Haleen bata ciki ne har toilet dinsu ta leka bayan ta kwankwasa taji shiru tambayar kanta tayi toh ina Halee taje ita da bata lafiya kuma?ganin bata da mai bata amsa yasanyata fita daga dakin bayan ta sargafe jakkarta ama 'ajiyarsu,fitowar ta keda wuya ta yo tsinke gurin Baba Asabe tana mai furta Babata ina Halee taje ne,fuska adaure Baba Asabe ta furta na aiketa kasuwa,tun yaushe Khady ta kara furtawa cikin jin haushin Babar ta ta,shiru Baba Asabe tamata wanda dama tasan tunda taji tana kwala kiran sunan Halee tasan cewa sai tazo ta tsureta da tambayoyi kamar yar jarida ,kuma ta san tana iya bin bayanta yanzu dan haka kuwa bazata bartata fita ba komai kafuwarta
Khady ganin bata bata amsa ba yasa ta furta babata kinfa san bata da lafiya kika aike cikin wannan uwar ranar tana maganar kamar zatayi kuka shine kuma kika ta har kasuwa duk wayennan kantin basu isaba sai kasuwa.....
Baba Asabe ce ta furta an aiketa din wani ta fadawa bata lafiya ne eh dazaki zo ki tsare ni da surutun banza....

Nikam nace 💁Baba Asabe adaiji tsoron Allah.
ALLAH YASA MU DACE 🙏

muhadu daku anext page

Zuwa monday in sha Allah lahadi babu update.

jiya kunjini shiru nayi typing sai da nagama na danna wani gun by mistake duka ya goge ga dan ciwon kai danake fama dashi,kusakani a addu'o'in ku
🙏🙏🙏

💫A MAFARKI NASANTA💫 FANS
INAYINKU OVER MUSAMMAN MASU BIBIYATA FACE BOOK INA GANIN COMMENT DINKU INA GODIYA 🙏KUMA NA WHATSAPP INA GODIYA SOSAI MASU COMMENT DA WAYENDA BASA YI🙏
ku cigaba da bibiyar alkalamin
💫Fa'eeh Bg💫
in sha Allah daga gobe zamu bar kasar nan domin dauko muku rahoto sai kuma mundawo,in akwai masu zuwa su fito mutafi jirgi 🚄kyautane

Wayenda badasu za,a sai gyara zama tsaf dan jin rahotannin mu.....

* Allah yasa mudace*🙏🙏
Pls like share and comment

💫A MAFARKI
NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍
💫Fa'eeh Bg 💫

Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*

Ban amince a had'a mini document ba ko achanza mini wani sashe na littafi na inkuma kikayi nabarki da rabba👌

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.