Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 24

EPISODE1️⃣
FREE PAGE7️⃣

TYPING📲📲📲

Wuce kibani guri ko in tattaka ki gurin nan,jiki ba k'wari ta wuce d'akin su tana zagayen neman yadda zatabi bayan Halee kasuwa,tabar Baba Asabe na masifarta ita kad'ai,Chan kamar minti uku haka taji tsif dama tana tsaye ne bakin k'ofa,koda ta lek'a ta tabbatar da Baba Asabe tabar tsakar gidan aiko da sauri da sand'a ta fice gidan gudu gudu sauri sauri ta fice daga gidan har ta cimmata Dan dama tasan hanyar da Haleen ke bi har ta isketa.
💫Fa'eeh Bg💫
Itakuwa Baba Asabe data shiga toilet din tsakar gida Dan tayi fitsari,tana fitowa tafara kwala Kiran sunan Khady,Hadiza!Hadiza! Domin tagaya mata ta d'ora mata ruwan zafi,Tsif taji ba,a amsa mata ba k'ara Kiran sunan tayi sai dai shiru aiko da sassarfa ta lek'a d'akin nasu Dan tabbatar da zargin ta,aiko tana yaye labulan taga wayam babu Khady babu ba alamarta Jakarta kadai ta hango sargafe, Nan ta rike k'ugu bayan tasaki labulen d'akin tana cigaba mitar ta na rashin dawowar Halee da wuri da kuma fitar Khady gidan,ita kuwa Halee ta fiyarce tata gata ga kamar ta dama,dama bata da saurin tafiya ne,wannan kenan ....

💫Fa'eehBg💫
Mukoma cikin labari .......

Jirgin✈️ mu yayi landing lafiya😊

* INDIA,MUMBAI*

Babban Birnin India-mumbai garine Wanda yatara kowace irin al umma daga k'asashe daban daban,Wanda yakasance kowa da abunda yakawo shi garin inka cire yan asalin India din mazauna garin na Mumbai,wasu karatu wasu kasuwanci,wasu kuwa neman lafiya,wasu yawon shakatawa,wasu kuma aiki ne yakawo su.

Nasan wasu zasu ce Babban Birnin India ai new Delhi ne karku damu😊 wannan shine kawai abunda nayi ra,ayin sakawa🙏

-----------------------
Gujarat 105 unguwa ce Babba ta masu idon nera shiyasa zakaji ko ina tsif kamar ba bil adama acikin manyan ginukan na alfarma, inda na kutsa kaina acikin cikin wani katafaren gida Wanda yakasance upstair ne, kuma ya amsa sunansa house,Wanda yaji farin fenti da ash colour mai haske da daukar ido,gida ne Wanda yaji kawa ta ko ina tunda compond din gidan zaka shaidar da hakan,k'aton parking space ne achan gefen dama dauke da manya manyan motoci wad'anda ake Kira car wayenda akalla zasu Kai goma,daganin motocin dai bugun America ne new design yan 2022 sai 2023 wayenda bakowa ke taka su anigeria ba sai Wanda yaji gishiri da sugar,sai wani k'aton swimming fool dake Chan ta gefen hagu Wanda yakara kawata gidan,ruwan cikin sa har wani sky blue sukeyi gwanin burgewa, swimming pool din yadan shiga lungu da alama akwai kofar sa achan ta baya, bayan ta gaban gidan,ko ina tsaf ga iska tana kad'awa shuke shuken gidan sai kad'awa suke yi suna bada wani k'amshi mai dad'i ko ina sai walkiya yake yi part biyu ne acikin gidan iri daya gidan ya hadu iya had'uwa rabinsa duk gilas ne tundaga bakin kofar shiga ciki zaka gane hakan.
Muryar wani guy naji
Daga ciki yana kwala Kiran Ammar!cigaba da kiran sunan yayi kamar ransa abace,Ammar yakara furtawa! wai uban me kake jira haryanzu baka fitoba har na fita compound nadawo,shiru danaji ne yabani damar shiga cikin falon bayan wannan guy din yacire code din kofar,nikuma na antaya daga ciki🤗wani had'adden falo na fad'a Wanda yaji kayan more rayuwa ta ko ina gashi yasha had'addun cusions masu taushi farare kar dasu,ga katuwar Tv Nan manne abango,ga k'aton dinning table anan shima gwanin burgewa,Wanda yake kusa da wata kofa Wanda nafi tunanin kofar kitchen ne mai had'e da store, falo ne na kasa Wanda yake dauke da d'akuna uku agefe suna Dan nesa da juna agefen hagu,sai wani ahannun dama inda nake tunanin toilet, bayan nagama karema dakin kallo,kuma ina da tabbacin nan ne naji muryar wannan guy d'in,juyawar dazanyi kenan dan hawa kan upstair din da ya raba tsakanin hagu da dama,idanuna ne suka tsaya chak sanadiyyar kicibus da sukayi da wani had'adden guy a hoto yasaka kanana kaya ya daura labcoat akai irin dai shigar likitota wadda takara kawata shigar tasa,sai wani k'aton hoton Wanda yakara Jan hankali na yana sanye da kayan tiyata ajikinsa blue colour tare da abun awon Bp waton stethoscope ya rungume hannayensa akirji yana sakin wani had'adden murmushi chocolate colour skin dinsa sai sheki take yi,ga Zara zaran eyelashes dinsa cike wayenda suka Kara kawata manyan idanunsa wayenda ke kwance akarkashin cikakkiyar gashin gyarar sa,sumar kansa kuwa daganin ta kasan tana Shan gyara na musamman tare da sajen sa,pink colour din labbansa sai sheki sukeyi gwanin burgewa hancin Nan kuwa zungur kamar biro Masha Allah.
Sai wani hoton shima na wani farin guy shima dai kyakkyawane saye da irin shigar ta wancahna guy din na farko.
Maganar da naji daga saman ce ana furta Ammar Amma dai Kai Dan iska ne ace har yanzu baka shirya ba tun d'azu nabarka kashiga wanka fa Amma Dan wulakanci har yanzu baka gama shafe shafenka ba,shiyasa nayi maza nafada ciikn d'ai daga cikin dakunan wanda naji sautin maganar na fitowa,Muryar wannan guy dince tadawo Dani dai dai daganin zubin halittar Wanda ke zaune akan mirror da towel daure akugunsa daya kuma agefen kafadarsa, kwantaccen gashi ne abisa kansa Wanda dagani ya hada da jinin larabawa ko fulani daga bayan sa zaka fahimci yana da faffadan kirji tare da kwantaccen gashi Wanda yake luff gwanin burgewa jikinsa ko ina lui lui dashi daganin sa kaga Dan hutu kafafuwansa da tafin hannun sa wayenda yake ta faman murtsuka mai dasu gwanin burgewa Wanda dagani zasu yi kamar na sabon jariri,chocolate colour fatarsa sai sheki takeyi.inda wannan guy din yake furta ai narantse bazan jiraka ba tafiyata zanyi yana maganar ne kamar ransa abace kasan yau muna da meeting ga tarin patients na jiranmu Amma shine kak'i saurin shiryawa,wadannan maganganun dayake yi su suka dawo Dani daga sumar tsayen Dana yi, inda nakai duba na ga saurayin dake maganar,shima dai hadadden ne kamar Wanda naji ankira Ammar, ashe ma shine wannan fari tass din guy Wanda nagani afalo, yasha
Kyau cikin kananan kaya yadora labcoat akan kayan sa inda naga an rubuta Dr .Al Amin jabir Muhammad soja Wanda mafi yawan colleagues da abokansu suna kiransa da Dr AJ...
Dacin Raine bayyane akan fuskar Dr AJ bayan yagama mganar
Yana batun fita ne yaji anriko hannun sa,yana kucce kuccen ya kwace hannunsa kenan yaji an rungume shi dasauri ya turesa yana furta ji iskanci Kai fa Ammar Dan iska ne mtsww yaja dogon tsaki,jiyayi Ankara riko hannunsa wannan karon .....

Mu hadu next page🙏
Gobe in Allah yakaimu

Comment din ku kadai nake bukata...

💫Fa'eeh Bg💫

💫A MAFARKI NASANTA💫 FANS
INAYINKU OVER💯 MUSAMMAN MASU BIBIYATA FACE BOOK INA GANIN COMMENT DINKU INA GODIYA SOSAI🙏KUMA NA WHATSAPP INA GODYA MASU COMMENT DA WAYEN DA BASAYI

Pls like share and comment...

https://chat.whatsapp.com/HO4hVB1luhXGyRzaOdWy68

💫A MAFARKI
NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍
💫Fa'eeh Bg 💫

Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*

Dan Allah duk wanda yakaranta wannan page yayi mini Addu,A🙏
Allah yabiya mini da dukkanin bukatu na tare da dukkan kulluhin musulmi🙏

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.