Complete Hausa Novels

A Mafarki Nasanta Complete Hausa Novel

Reading file: A_Mafarki_Nasanta_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 17 of 24

------------------------------------------------------------------
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE 2️⃣1️⃣

TYPING📲📲📲

...'Sallamar wani matashin mutun ne cikin shiga ta alfarma ta kayan sarauta alkyabba da rawani masu kyau tare da wani bafade guda amma shi yana bakin bakin kofa ne,Muryar shi ce ta katse da yazo dashi yakin furta meyasamu mamanah labari ya isar mun fada gata chan tana kuka,Murmushi matar da aka kita tana fad'n haba Babban sarki Norah ai ta dena kukan ma ka kwantar da hankalinka baka ji tayi shiru ba,cikin ya nayinsa da sanyin hali ya furta layla miko mun ita inganta,yana zama akan hadaddun rugs d'in dake falon na alfarma,tab'a jikinta yayi bayan tamika masa ita,ajiyar zuciya yasauke,jin jikin nata zau da zafi,lokacin baiwar Allah har ta fara baccin wahala,Murya asanyaye yace meyasameta ne.?..

A hankali gimbiya laila tafurta tafad'i ahannun mutumin tane,kaganshi chan gefe ma shima yana nashi kukan,duban sa yakai inda Ammar suke,Bayan yagama k'are musu kallo tsaf su duka,sai kuma Ahankali ya k'yafato su ,alamar su zo,a hankli suka taso hannyensu rik'e dna juna,Ammar ne ya duk'a k'asa yayi kneeldown tare da kama kunnuwansa yana tsiyayar da hawaye yana kallon norah dake baccin wahala beauty face dinta tak'ara fitowa fess, cikin wani yanayi ya furta kace norah tayi hakri itace fa tasa na sake ta ba da ganganba,dodon kunne na naji zai fashe yakai karshen maganar kamar ya yayi ihu yake ji na jin zafin halin da norah din take ciki.....

Murmushi wanda aka kira da uncle yayi yana share ma Ammar hawayen sa dasuka kasa tsayawa,jawoshi yayi yazaunar agefensa inda D'an uwansa yazauna,A hankali yafurta mai sunan Autan maza yana jin wani abu na taso masa bayan kiran sunan Autan mazan,kayi shiru kadaina kukan nan kaji Halimatu sadiya tayi bacci ma kaga tadaina kukan yakai karshen maganae yana shafa beauty face dinta,

Ajiyar zuciya ammar yasauke mai nauyi kamar wanda waci bakar wahala yasamu hutu,Jin cewa ta hakura, wanda har uncle din saida yaji fitar ta,har Aunty da yanzu tazauna bayan gama bawa ma'aikatan dake cikin kitchen umurnin abunda zasu aiwatar yau domin bazata samu damar shiga kitchen dinba norah ba lafiya...

murmushi mai taushi gimbiya laylat ta sauke tana mai shafa lallausar sumar dake shimfid'e abisa kansa,domin kuwa tana mugun son Ammar musamman yadda yake nuna kulawar ga norah dinta,wadda tun ranar da fad'o duniya yake kokarin daukar dawainiyarta duk da karancin shekarunsa,wannna soyayya dayake ma nora har maamaki take bata ba ita kadai gaba daya a halin ma sun san yadda norah take agurin Ammar ,shiyasa take jin wani kud'uri yana shigarta ahankali ..........

Bayan kwana biyu tun faduwar da norah tayi kullum cikin kuka take ga rashin bacci har saida aka kira family doctor nasu ya duba ta sannaan yatabbatar musu da ciwon kaine ke damunta mai tsanani,tun lokacin tasamu sauki bayan an rubuta mata magungunna,daga baya sai abun yadawo wanda duk bayan kamar watanni sai tayi ciwon kai da zazzabi mai zafi,Ammmar shine mai jinyarta lokacin duk da yarintarsa dan Alokacin yana da shekara shidda itakuma shekara daya da rabi Aduniya, kuma tun alokacin yadau alkawarin zama likita saboda norah ganin yadda take wahala,Domin yakula da ita ita kadai...Wannnan kenan............

*MUKOMA CIKIN LABARI*

Bayine ta ko ina suna gabatar da dukkanin ayyukan dasuka zame musu Al adah wato kai kawo domin gudanar da aikin su,kowa da kalan uniform na sashen da yakewa hidima da masu kula da kofa fada, masu kula duk wani motsi na fadar,masu kula da dawakai,abun gwanin burgewa sai wanda yagani...

Tangamemiyar masarauta ce mai tsaunukkan gine gine masu kyau irin dai yadda kuka san ginin gidajen sarauta suke,tako wanne gefe haskene tar kamar rana na ban mamaki ko lif lif da shuke shuke,ga gurin aje dawakai da motoci na alfarma.

Wata faffadiyar koface wadda zata sadaka da fadar sarki nan na kutsa kaina domin dauko muku rahoto duk da manyan dakarun dake tsaronnata ..

Had'addiyar fada ce mai abun burgewa tako ina fadawa ne atsaitasye ga wata kujera ta alfarma wadda tasha adon gold sai shining take yi ga fadawan dake gefen kujear baibaye da ita sai fifita sukeyi ma wanda ke kan kujerar ta alfarma Ahankali duk da AC din dake huro iska mai dadi wanda yahadu dawani kamshi...

A hankali fadawan suke furta gyara dai sarki Mai dubbanin alkhairai,Allah yakara lafiya,jin tarin dayake yi wanda ke nuna alamar mura ke damun mai yin tarin,Hannunsa yad'aga cikin nuna mulki da Izzah,Alamar ya isa A hankali naji kyakkyawan dattijon da bai haura shekara sittin ba yayi magana da muryarsa mai nuna dattako da manyan taka,yana mai furata "har yanzu yarima baice komai ba ne galadima"?
Mutumin da naji ankira da galadima ne naga yaduk'ar dakansa yana furta Allah yataimaki sarki,ehh haryanzu bai nuna yaga sak'on mubah,yau wata takwas kenan,ni anawa ganin Allah yataimaka sarki kawai akyale sa sannan Ku gyara tsakaninku....

Wani murmushi mutumin yasaki Wanda yatsaya iyakar labbansa,zaka gane hakan inka kura mai ido duk da yana cikin rawani ,shiru baiba galadima amsa ba,saima mikewa da yayi,Dan danan fadawa suka fara karesa suna furta gyara dai sarki mai dubbanin alkhairi,gyara dai sarki mai masarautar gado mai garin na sambo,,,

Mai garin na sambo zai fito,wata murya CE ke d'aga wannnaa sauti a waje,kirari suka cigaba da yimasa tare da kara gyara masa alkyabbar sa ta alfarma sai walkiya take na duwatsun gold,A hankali yake takawa harsuka fito daga babbar fadar tasa sai dai yau baibi ta kofar dazata sadashi da sashen UNNI ba
Yafito ne ta kofar dazaka iya ganin komai dake gudana atsakiyar masarautar,tafiya yake yi Ahankali inda duk inda sukabi ma'aikata bayi sai sun masa irin gaisuwar nan da yan Korea suke yi a series dinsu na sarauta ga shuwagabannisu gamasu kallon su zaku gane yadda nake nufi Niko vow suke cemishi....
( Adan sunkuyar dakai kadan sai alankwasa hannu biyu ahade su guri daya kamar mai daidaton sallah,sai a saita shi akan tsakiyar goshi)Allah yasa kunhgane😜

Kansa kawai yake d'agawa alamar karba gaisuwar tasu acikin lemar da suka ware masa ta alfarma, har ya isa inda manyan motocin suke aparkey na alfarma,Isar sa wurin d'ai daga cikin fadawan da ke lullube dashi ya bude masa wata arniyyar parado new design bak'a wulik mai tinted glass irin yan 57billion dake parkey agefe cikin wata had'addiyar rumfa inda dagani nan ne mazaunin aje wasu motocin na musamman😱 kai FA'EEH wannan karya...koda yake abunda nagani ne ai😇

Ahankali yashiga cikin motar dai dai Wanda ke rike da dai Wanda ke rik'e da had'addiyar umbrellan da suka kara masa tun lokacinda aka shimfida masa bugaggiyar carpet ta alfarma an rubuta MURAI'S PALACE akanta cikin tsari mai kyau....

Bayan shigarsa motar tafiya kad'an sukayi da direban da yatuk'osa da sauran fadawan sa dasuka k'asa da algaitu da busa suna masa kirari,motar drivern yafaka A wani tangamemen gida dake d'ai daga cikin gidajen masarautar na alfarma,take fadawa suka zagaye motar suna masu kakkaresa bayan yafito a lokacin har an kara shimfida masa carpet tare da bud'e masa umbrella ta alfarma abun gwanin burgewa sai Wanda yagani wollah in maku hausar mu ta sakkwato😀.

Tafiya kad'an yayi ya Iso kofar shiga mai rike da had'addiyar kofar ce wadda zata sadaka da falo, ya wangale masa bayan ya rusuna masa alamar gaisuwa

Shigarsa had'adden falon na alfarma yabani damar debe keyar ido nah masha Allah nake furtawa tsayawa kwatantamuku tsaruwarsa bata lokacin ne,falon yaji komai na more rayuwa....

A hankli dukkanin bayin dake kai kawo suna hidima asashen suke rusunawa suna gaidashi hannu kadai yake iya d'aga musu har ya isa wata kofar inda naga wata dattijiwa mai uniform wasu colour masu kyau tafito,Ashe Babbar Amintacciyar masarauta ce tun lokacinsu Ammi take hidima dasu,
Inda yanzu ma ita keyiwa sarauniya hassaana da sarki duk da bawata hidimar bace kawai dan duba sauran ma,aikata ne sai yin iso ga sarauniya,
Iso tayi ma sarki ga sarauniya bayan tagama yimasa kirari nuna gasuwarta bayan ya karba tawucewar Alokacin duka ma,aikatan kowa yacigaba da aaikinsa....

Sallamar ce acikin uwar dakin tasanya kyakkyawar matar dabazata wuce shekara Arba'in wadda daka ganta kaga zubin larabawa, in kallo daya zaka mata kagane wacece ita idan har kasan gwarzon d'anta,Amsa sallamr tayi atsanake cikin murya mai nuna farinciki,furtamasa tayi "marhaba biki shugaba adili ya zaujaty ,Abul mahir Abul yuhanis,Abul Abdul rashid " takai karshen maganar ciki. Kara kawata fuskarta da murmushi,Murmushi yake ta saki Wanda yake kara kawata fuskarsa dan yana mugun son wannan kirarin Nata murmushinsa ne yafara gushewa jin furucinta nakarshe Wanda dama tasan hakan zata faru shiyasa bakasafai take yimasa shiba,Wanda aduk lokacin da tamasa kirarin ta ambaci sunan Abdul rashid,Abu uku ne ayanzu ke zomasa arai damuwar d'an yarima,dakuma k'anensa daya b'ata shekara talatin da suka wuce dakuma dakuma babban rashi dasuka yi na dan uwansa da iyalansa a shekarun baya,b'at murmushin dake kan fuskarsa yakyau zuwa hawaye bayan jin komaai yadawo masa sabo arai.......

Chakwakiya to ko meyasamu dan uwan nasa da iyalansa?wane kalar rashine ne wannan

Shin wanene kuna d'ayan d'an uwansa daya b'ata kuma ashekarun baya?

Ko suwaye wayen yan uwan NASA?
Gaskiya yabani TAUSAYI dattijon nan 😢nima kamar inzubda masa da hawaye
Shin ko kungane wane yarima ake
magana ?

Duka zaku samu cikon amsoshinku anan gaba kadan
Kucigaba da bibiyata duk zan warwaremuku in sha Allah In Allah yamauna aron rai

💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥

*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*
*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........
*+2348069059746*
*+2348084504630*
----------------------------------------------------------------
*💫A MAFARKI NASANTA💫*
*2023 novel is the story of an innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA*KO MASU MUKAMIN *MENE DASU DA HAR ALKALAMINA YA KIRA SU MANYA KASA*....
*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA*
--------------------------------------------------------------------
https://chat.whatsapp.com/GNSky8tcQT72iE1IVm7Vpt

💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥

*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*
*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........
+2348069059746
+2348084504630
---------------------------------------------------------------
*💫A MAFARKI NASANTA💫*
*💫In my dream i know her💫*

*2023 novel is the story of aninnocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA KO MASU MUKAMIN MENE DASU DA HAR ALKALAMINA YA KIRA SU MANYA KASA*....
*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA*
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝

ESSENTIAL WRITER'S📚🖊

Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.